Daƙyar ya iya yin wanka saboda wani irin zafi da zuciyarsa ke masa. Yana fitowa ya zura kayansa, a gaggauce ya fice daga ɗakin.
Bai tsaya a falon ba, buɗe ƙofa yayi ya fice daga apartment ɗin ba tare da damuwar tsalawar da dare yayi ba. Lokacin ƙarfe uku da minti biyu na dare.
Duk da yana da tabbacin Fareeda ta daɗe da yin barci ɓangarenta ya nufa, ya murɗa hannun ƙofar ya ji ta a kulle. Ƙwanƙwasawa yayi a hankali sau biyu, a zuciyarsa yake jin rashin kyautawa, bai kamata ya tasar da ita. . .
Hhhhhh cin amana baiyi ba Fatima
Amma na ji dadin chapter din nan😂😂😂Astaghfirullah