Skip to content
Part 18 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Daƙyar ya iya yin wanka saboda wani irin zafi da zuciyarsa ke masa. Yana fitowa ya zura kayansa, a gaggauce ya fice daga ɗakin.

Bai tsaya a falon ba, buɗe ƙofa yayi ya fice daga apartment ɗin ba tare da damuwar tsalawar da dare yayi ba. Lokacin ƙarfe uku da minti biyu na dare.

Duk da yana da tabbacin Fareeda ta daɗe da yin barci ɓangarenta ya nufa, ya murɗa hannun ƙofar ya ji ta a kulle. Ƙwanƙwasawa yayi a hankali sau biyu, a zuciyarsa yake jin rashin kyautawa, bai kamata ya tasar da ita a wannan lokacin ba.

To amma ya zaiyi ne? a wannan lokacin da ita kaɗai yake so yayi tozali ko zai ji sauƙin damuwarsa. Zai so ya rungumeta a ƙirjinsa, a hankali sai ya ja ta su zauna kan kujera ya cusa kanshi a ƙirjinta, ya dinga sauke ajiyar zuciya akai-akai. Idan yayi hakan yana da tabbacin zai samu sauƙi da rangwamen halin da yake ciki.

Tun yana ƙwanƙwasawa a hankali har ya fara bugawa da ƙarfi, amma ko kaɗan bai ji alamun za’a buɗe daga ciki ba.

Ga sanyi-sanyi a wajen na alamun ketowar alfijir, ga wasu bala’ƴaƴƴun sauro da suka taso shi gaba da cizo haɗe da kuka wiiiii kamar an kunna jiniyar ƴan sanda.

Haka nan yaja sanyayan gwuiyawunsa irinna rashin samun abinda zuciya taso ya wuce ɗakin baƙi.

Duk abinda yake yi har ya fice daga Fatima tana jin sa, tana kwance inda ya barta, kuka take yi ƙasa-ƙasa na zallar baƙin ciki da takaici. Amma saboda rashin tausayi haka yasa ƙafa ya fice ya barta ba tare da ya bi ta kanta ba.

‘Wannan wane irin mummunan baƙin dare ne yau take gani a idanuwanta? Idan ta tuno daki-daki yadda abin ya faru kawai sai ta ji hawaye sun sake ɓalle mata.

Bata taɓa tsammani ba, abu ne da bata taɓa tunanin zai faru ba. Tun shigowarta gidan duk abinda ta tsammaci faruwarsa na matsanancin farin ciki akasinsa ne ya faru.

Me yake faruwa ne haka? A ina ta kuskure a matakan da tabi tun fara neman aurenta har zuwa yau da ya kasance mummunan daren farko a gurinta?

Laifi ne don ta fi mayar da hankali kan gyaran ƙasarta a bisa gyara suɗaɗɗun mamanta? Laifi ne don ta kashe maƙudan kuɗaɗe domin amfani da magunguna da turarukan da za su taimaka mata wajen mallake Mukhtar da zuciyarsa?

Ganin tsanar ramarta ko tsanar yadda nonuwanta suka kwanta abu ne da bai taɓa faruwa tsakaninta da tsohon mijinta ba. A ko da yaushe lallaɓata yake yana gwada mata soyayya, suɗaɗɗun nan haka yake tattarosu ya damuƙa da hannayensa cikin rawar jiki da shauƙi, kuma daga yadda jikinsa ke ƙara ɗaukar harama a lokacin da yake taɓa ta za ta iya rantsewa da girman Allah duniyar shauƙi da jin daɗi ya faɗa ba akasinsa ba.

To me yasa bata ga irin wannan daga Mukhtar ba?

‘Ke ma dai Fatima da wani zance, maza ai kala-kala ne. Wani namijin duk ramar mace ba ya damunsa, wani kuwa ko a ƙafa aka bashi ramammiya zai tsinke ya gudu.’

Amsa daga can cikin zuciyarta.

Ta ja shessheƙar kuka sau uku, a fili ta ce,

“Allah ya isa tsakanina da ke Ramlah! Babu yadda banyi da ke in sayi zumar ƙiba da naga ana talle a group na whatsapp kika hana ni.

Babu yadda ban nemi shawararki kan in sayi garin Sabaya da ake talle ba kika hana ni. Na nemi shawararki kan in fara dama kunun alkama da kunun gyaɗa ina sha tunda an ce suna taimakawa jiki ya murmure kika ce a’a!

Kika ce hakan da nake na fi kyawun kallo a matsayin abar sha’awa da burgewa, kuma ɗan zama na lokaci kaɗan za muyi Fareeda ta ragwaɓe ni kuwa ina nan ƙyam abar sha’awa. To ai ga irin ɗanyen madarar wulaƙancin da kika janyo min nan. Allah ya isa, wallahi Allah ya isa, muguwa kawai.”

Sai ta sake fashewa da matsanancin kuka kamar wata ƙaramar yarinya.

Bata gane Mukhtar yagalgalata yayi ba sai da ta nemi miƙewa zuwa banɗaki. Saboda tsananin zafi da azaba bata san sa’adda ta buɗe baki da ƙarfi ta ƙwalla ihu ba.

Wani irin mugun azaba da raɗaɗi take ji, irin azabar da ko a daren farkonta bata ji shi ba. Ga yadda take jin gurin da yake a tsuke tunda aka yi mata ɗinkin ƴar sha biyar yanzu ya buɗe hayam shi ne abinda yake ƙara ba ta tsoro.

Fitsarin da ya matseta har tana jin kamar za ta sake shi kan gadon yasa dole ta ƙara motsawa da ƙarfi.

“Wasssshhhhh! Wayyo Allah na zafiiiii..”

Ta ja kalmar zafin ta sauke shi da wani irin huci mai ƙarfi da gurgani kamar matar da naƙuda fara kankama mata.

Izuwa yanzu kukan ma ya ƙi zuwa, sai zare ido take yi kamar ƙwai a ledar biredi, lokaci ɗaya kuma tana haɗawa da cije laɓɓa saboda tsananin raɗaɗin da take ji, duk da fankar sama na ɗakin a kunne yake ta haɗa zufa tai kashirɓin.

Babu yadda ta iya, tana ƙarasawa gefen gadon da ta kasa sauka da ƙafafunta sai kawai tayi shahadar ƙuda ta faɗa ƙasa, daɓas haka tayi zaman ƴan bori.

Kasusuwan mazaunanta suka daki dandaryar tiles, wani marayan ihu ta ƙara sakewa a karo na ba adadi.

Ta ɗauki sakanni tana sauke numfashi sannan ta lallaɓa a hankali da rarrafe ɗaya biyu har Allah ya taimaketa ta ƙarasa banɗaki. Sai a lokacin magana mai harshen damon da nurse ɗin da tayi mata ɗinki ya dawo mata daram a zuciyarta, kamar a lokacin take faɗa mata.

“Kika ce inyi miki ɗinki ki koma kamar yarinya ƴar sha biyar?”

Sai da ta kaɗa idanu tayi fari da yalwataccen murmushi a fuskarta ta amsa da eh!

“Shi kenan! Tunda kin biya ni wadataccen kuɗi zanyi miki aiki har ma fiye da yadda kike tsammani. Amma fa ki sani, shi tsukewar gaban mace ya koma kamar ta budurwa idan tantanin budurci ya tafi a karo na farko ya tafi kenan har abada.

Ban ce baza ki tsuke ba, za ki tsuke tsam, don fatar ciki da ta waje duk zan haɗa in ɗinke miki tsaf! Amma kar ki ce ban faɗa miki ba, duk sadda Oga ya kawo kai zai shige gurin ba ƙaramin azaba za ki ɗanɗana ba.

Amma idan Allah ya taimake ki kika sami mai haƙuri zai ta lallaɓawa yana bi a hankali har ya samu nasarar shiga, duk da haka dai za ki sha wahala, amma ba sosai ba.

Idan kuwa kika samu jarumin maza mara haƙuri… Hmmm! Wallahi sai ya miki fata-fata, duk wani ɗinki da muka yi miki zai kekketa shi…”

“Aunty Nurse, kar ki wani damu. Ke dai kiyi aikinki yadda na ce. Daman a cikin yaƙin ƙwato ma kai daraja ta musamman dole sai an sha wahala. A mai haƙuri ko mare haƙuri na tarar da Aban twince zan jure ƙwarai don in ƙara samun tambarin jarumar mata a zuciyarsa.

Idan komai ya kammala nasan ba ƙaramin tarairaya da gata zan gani a wannan dare ba, saboda ya tarar da ni a yadda bai taɓa tsammani ba.”

Wasu zafafan hawaye ne suka sake silalo mata da zuwa ƙarshen tunaninta.

Kamar wacce ta haihu, haka tai ta tara ruwa mai zafin gaske tana shiga ciki, duk azaba haka ta jure.

Fiye da sau takwas tana canza ruwan kafin Allah yasa ta fara jin dama-dama. Ta gwada miƙewA tsaye taga ta miƙe, ta gwada tafiya taga tana yi a hankali, duk da ƙafafunta a tattale suke kamar ta ɗan shayi ai babu laifi, matar da a ɗazu ta kasa tafiya, yanzu da take yi ko a bobbotsere ne ai ta gode Allah.

Balle ma tana saka ran yinin da za tayi yau tana shiga ruwan zafi zuwa dare komai na jikinta zai koma yadda yake. Idan yaso ma a sake zagaye na biyu.

Yo miye a ciki? Wannan ai shi ne auren. Gara ta lallaɓa ta koyi juriya, so take su gogu ita da Aban Twince, su murzu sosai a cikin kwanaki ukunta na amarci. Tunda wancan ƴar buƙulun ta ƙi ƙara musu kwanaki.

*****

Lamo yayi akan katifa kamar mai zazzaɓi, saboda tsabar damuwa da tunanin da yayi masa yawa ya kasa janyo filo a gefensa ya ɗora kai. Hannayensa biyu yayi matashin kai da su, ƙwayoyin idanunsa na kallon sama, a kallon farko sai ayi tsammanin ƙirga layin PPC da aka sa a saman ɗakin yake yi, amma ba haka bane, tsananin nisa a cikin tunani ne.

Surar jikin Fatima kamar hoton da aka maƙala a duk inda ya juya idanunsa, sam ta ƙi ɓace masa a cikinsu.

Mamaki yake yi, mamaki mai tsanani ƙwarai. Wai don Allah me ya shiga cikin nutsuwa, hankali, da idanunsa har ya kasa gano ramar Fatima? Yadda yake gogagge kuma wayayyen matashi ai ya kamata ko a ido ya iya banbance kayan kanti da na shago.

Bazai manta wani abokinshi Sunusi da yayi aure shekaru uku baya ba. Ya auro wata yarinya a ƙauye ramammiya sosai, saboda ramewarta shi yayi tsammanin sikila ce.

Tunda Sunusin ya tabbatar mishi ba sikila bace haka yanayin jikinta yake ya tasa shi gaba da tsokana da dariyar mugunta.

Minti ɗaya biyu sai ya kalli Sunusin yana ƙyalƙyala dariya ya ce

“Kai kuwa Sunusi don Allah me ka gani a jikin wannan lamba One ɗin? Kana ganin mace ko a cikin kaya ba tsoka ba alamar tsoka ina ga ta tsaya zir a gabanka? Ƙarmanjola kenan.”

Sai ya sake kwashewa da mahaukaciyar dariya ya cigaba da nuna Sunusin da yatsa, a lokuta da dama har ƙwalla yake yi saboda dariyar mugunta.

Ashe shi ma yana da rabon auren irin wannan matar a rayuwarsa? Ku gane Shi fa ba ramammiyar mace ne ba ya so ba, amma a gaskiya ba ya son macen da ramarta ya cika yawa sosai ɗinnan.

“Fatima kin ha’ince ni.”

Ya sake faɗa a karo na biyu zuciyarsa na ƙara ƙuntata.

Wani abu ne ya faru a yanzu da ko a cikin tarihinsa na baya bazai ce da wayonsa ga sadda abin ya faru ba, wannan abu ba komai bane face fitowar wasu ƴan ƙananun ƙwallah a idanunsa.

Ya runtse idanunsa da ƙarfi, ƙwallar suka gangara gefe da gefe har cikin kunnuwansa, zuciyarsa cike da addu’ar Allah yasa barci ya ɗauke shi ko zai samu sauƙin tunanin da yake yi, barcin bai zo ba ya ji ladanin unguwarsu ya kwaɗa kiran sallar farko.

*****

Ko da ake cewa ba’a iya barci a daren da aka tabbatar miji yana can zai haɗa shimfiɗa da wata macen ita kam yau an samu akasin lissafi a kanta.

Tunda suka fice da zantukan rainin wayonsu suka barta cikin ƙunci, tai takwa-takwa da fuska za ta fara hawaye da sauri ta haɗiye kukan.

‘Kukan me za kiyi kuma Fareeda? Bayan aikin gama ya riga ya gama?’

Ƙoƙarin tattare tunaninsu tayi ta ajiye a gefe ɗaya. Taje ta rufe ƙofar falonta, ta dawo ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala, tana ji ya dawo yana ƙwanƙwasa ƙofa taba banza ajiyarshi. Ta shimfiɗa dadduma tayi shafa’i da wutiri.

Ya ke ƴar’uwa mai karatun wannan labari, ina baki shawarar ki saki kowa ki kama Allah. Kar ki kuskura ki manta da Allah a lokacin farin ciki ko ƙunci. Shi fa Ubangiji ako da yaushe ƙofofin rahamarsa a buɗe yake, jira yake kawai bawa ya roƙa da ikhlasi ya amsa masa. A duk sa’adda kika dogara da Allah mafificin dogaro na haƙiƙa kuma da zuciya ɗaya tsarkakakkiya tabbas addu’arki za ta dinga amsuwa kamar yankar wuƙa. Idan kuma ba abin alkairi bane kike roƙa Allah zai sanyaya miki zuciya, ya cire miki damuwa da son ganin biyan buƙatar da gaugawa, a sannu a hankali sai ya canza miki da mafi alkhairi. Ko da duk duniya maƙiyanki ne aduk lokacin da suka nufo ki da yaƙi Ubangiji shi zai tare miki. Ko ba’a so ana ji ana gani za kiyi ta cigaba, a rasa ta yadda aka yi duk wani mugun abu baya samunki. Dogaro ga Allah yayi ƴan’uwa, ku gwada za kuga alkhairi.

A wannan dare bayan ta idar da shafa’i da wuturi, ta ɗauki lokaci tana istigfari, hailala, tasbihi da godiya ga Allah kan ni’imomin da yayi mata.

Abu uku ta daɗe tana roƙa, abu na farko ta samu nannauyan barci a wannan dare, na biyu Allah ya cire mata damuwar Mukhtar na can kwance da tare da Fatima. Na uku ta roƙi Allah yasa duk ni’imar da Mukhtar zai ɗanɗana a jikin Fatima kar ya ɗanɗani ko kwatan wanda yake ɗanɗana a jikinta.

Bayan ta gama addu’o’in ta bi lafiyar gado, ta kwanta ta tasa ƴaƴanta a gaba ta rungume su. Tana hammar barci ta janyo wayarta ta kunna ƙira’ar Sudais cikin suratul Baƙara, ta daidaita ƙarar wayar baiyi yawa ba baiyi kaɗan ba ta aje wayar, ta lumshe idanunta tana sauke numfashi cikin nutsuwa.

Wani nannauyan barci ne yayi awon gaba da ita irin wanda ta daɗe rabon da tayi irinsa. Fitsari bai tashe ta ba, ƴaƴanta biyu da Hajiya ta ce ta dinga saka su fitsari cikin dare basu tashe ta ba, kuma basuyi fitsarin kwancen ba. Duk ƙara irinna alarm ɗin wayarta da yake bugawa ƙarfe huɗu na dare sam bata farka ba. Ta farka ne a daidai lokacin da Ladan ya tada iƙamar sallar asubah.

Cikin nutsuwa ta farka da salati a bakinta, da farko kamar a mafarki take ji an tayar da sallah, sai da ta ƙara saurarawa sosai sai taji da gaske fa sallah ake yi.

Sai ta miƙe a firgice tana taɓa wandunan yaran, ko da taji basu tsula ba ajiyar zuciya ta sauke. Ta ɗauke su ɗaya bayan ɗaya takai su bayi suka yi fitsari, bayan ta sake kwantar da su ta koma bayi ta ɗauro alwala.

Zuciyarta sakayau, babu nauyi balle damuwa ko kaɗan, ta ma manta da Mukhtar balle wata Fatima karan kaɗa miya.

Cikin nutsuwa ta gabatar da sallar raka’a tanilfijr sannan ta gabatar da sallar asubah! Bayan gama tasbihi tayi azkhar, ta ɗauki lokaci mai tsawo tana karatun Alƙur’ani mai girma, har gari yayi haske sosai bata kammala ba, kwatsam taji ana ƙwanƙwasa mata ƙofar falo.

Sai da ta kai aya sannan ta miƙe a nutse da hijabin jikinta taje ta buɗe ƙofar.

Yana shigowa da wani irin zafin nama ya kai mata wawuyar runguma.

Kasancewar tana ankare da shi, matuƙar ƙoƙari tayi gurin gocewa ya rungumi iska. Cikin wayancewa da ƙwarewa a iya basarwa ta ja da baya a tsorace, ta zazzaro idanu waje, hannayenta biyu dafe da ƙirji ta ce

“Oga Lafiya?”

“Lafiya ƙalau”

Ya amsa da wata shaƙaƙƙiyar murya. Kafin ta ce komai ya sake cewa

“Miye haka? ina ƙoƙarin riƙe ki kin wani zille”

“Da alwata ta.”

Ta faɗa kai tsaye.

“Me ya haɗa riƙe kin da zanyi da alwalarki…?”

“Oga mana, ka san kai ɗin fa ba dama ne. Alwalata zai iya karyewa daga riƙon da kake mishi kallon ba wani abu bane.

Ta ƙarasa haɗe da kashe mishi ido ɗaya.

“Ina kwana Angon Fatima? Ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya kai da amaryarka?”

Da murmushi sosai a fuskarta ta gaishe shi, har tana ɗan duƙawa a ƙasa.

Ya buɗe baki zaiyi magana buff aka buɗo ƙofar falon, a tare su biyun suka kai idanunsu kan ƙofa, wa za su gani?

Fatima ce tsaye ta riƙe ƙugunta da hannu biyu. Ta sha kwalliya sosai, ta fito a amaryar turawa sak! Domin kuwa ta tsuke ne cikin wani matsattsan wando wanda da kaɗan ya ɗara gwuiwarta da ƴar fingilar riga.

Ta yi amfani da kayayyakin cikonta gaban da bayan sun taso ɗam-ɗam gwanin ban sha’awa.

Lokaci ɗaya Mukhtar ya fara harhaɗe girar sama da ƙasa zai ɓalle tsiya, daman kwana yayi da masifaffen haushinta a ransa.

Lura da hakan da tayi cikin kissa da iya ƙwarewa a ladabi ba don Allah ba sai don tura ma wata haushi da saurin gaske ta zube a gabansa gwuiyawunta a ƙasa.

Kamar an buɗe famfo sai ga hawaye shar! shar!! Bakinta na rawa ta ce,

“Allah ya baka haƙuri Haskenah. Don Allah don Annabi kayi haƙuri, Allah ya huci zuciyarka. Yunwa, yunwa ce ta fito da ni har linzamin tunanina ya ƙwace na faɗo muku kai tsaye ba tare da sallama ba. Haskenah, ɗan abinda na ci jiya da daddare duk ya gama tsiyayewa…”

“Ke dallah saurara min kina ta wani zuba shaaaa kamar kanyar da ba zaƙi. Kije ɓangarenki ki dafa ruwan zafi, zan taho miki da kayan tea da biredi.”

Yayi maganar a gundure, fuskarnan a ɗaure tamau.

Cikin nutsuwa Fareeda ta juya zuwa cikin ɗakinta, kwatsam ta tsinkayi muryar Fatima a raunane tana cewa.

“Ko za ka yi ma Aunty Fareeda magana ta sammin ruwan zafi…”

“Saboda me? ita ɗin baiwarki ce?”

Ya jefa mata tambayoyin cikin tsawa.

Sai da ta sunkuyar da kanta ƙasa, a yanayi na muzanci da jin kunya ta ce,

“Dama… dama… dama… ba ni da gas ne. Ban samu sararin sayen gas ba, abin girki da gawayi na zo da shi kuma babu gawayi.”

Mukhtar da ya tsani tsaki a yanzu ƙarfi da yaji yawan tsakin na nema ya aure shi. Wani dogon tsaki yaja ya galla mata harara, ko kaɗan kwalliyarta bata burge shi ba, domin ya ga gaskiyar abinda ake rufewa wannan kwalliya duk bula ce.

Fareeda na gaf da shigewa cikin ɗakinta ya kira sunanta a tausashe.

A hankali ta juyo ta zuba manyan idanunta cikin nasa.

Ƙoƙarin tausasa maganar da zaiyi yayi, ba don komai ba sai don kar Fareeda ta ji babu daɗi.

“Ko kina da ruwan zafi a flask ki sammata? kin ji ba ta da gas sai abin girkin gawayi…”

“Idan ka fita ƙofar gida, nan ɓangarenmu gida na huɗu a hannunka na hagu suna sayar da gawayi. Suna ƙulla na hamsin da ɗari, kwatan buhu, rabin buhu, buhu guda zuwa buhu ashirin duk suna sayarwa.

Ka siyo mata gawayin kawai. Ni wallahi shigowarka ce ta fito da ni falo, karatun Alƙur’ani nake yi. Don Allah kar ka tilastani ba ta ruwan zafi alhalin ba hakkina bane.”

Cikin ɗakinta ta shige ta barsu a gurin.

Mukhtar da Fatima suka rakata da idanu har ta ɓace ma ganinsu.

Fareeda ce tayi maganar, amma Allah ya sani haushin Fatima ya ƙara ji a zuciyarsa. Tana tsugunen nan yayi mata wata muguwar damƙa a kafaɗarta ɗaya ya miƙar da ita tsaye, kafin ta gama daidaita tsayuwa ya finciketa da ƙarfi suka fice daga falon, tana wash-wash saboda ciwon da yaji mata amma bai saurara mata ba sai da suke je falonta, ya watangarar da ita ta tafi taga-taga za ta ci da baki da saurin gaske ta dafe hannun kujera, idanunta a warwaje saboda bala’in tsoron da ta ji.

<< Rabon A Yi 17Rabon A Yi 19 >>

2 thoughts on “Rabon A Yi 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.