Ƙara matse mata waje yayi, a hankali ya riƙo tsintsiyar hannunta yana ɗan matsawa
"Ina son ki Fareeda."
Ya faɗi kalaman cikin salo a rarrabe.
A yanzu ma dai kallonshi ta sake yi, sai kuma ta taɓe baki ta mayar da fuskarta ga t.v.
"Haushi na kike ji?"
Ya tambayeta, da muryarsa a sanyaye.
"A'a"
Ta amsa daƙyar bayan ta ɗauki tsawon daƙiƙu tana jan fasali.
Ya buɗe baki zai sake magana ta katse shi da cewar
"Haba Mukhtar, saboda Allah abincin ma baza ka barni in ci cikin kwanciyar hankali. . .
Za ma ki yi bayani ne Fati amma kin ji kunya wallahi. Mukhtar dai ya jawo duk wannan masifar wallahi.