Skip to content
Part 28 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Ƙara matse mata waje yayi, a hankali ya riƙo tsintsiyar hannunta yana ɗan matsawa

“Ina son ki Fareeda.”

Ya faɗi kalaman cikin salo a rarrabe.

A yanzu ma dai kallonshi ta sake yi, sai kuma ta taɓe baki ta mayar da fuskarta ga t.v.

“Haushi na kike ji?”

Ya tambayeta, da muryarsa a sanyaye.

“A’a”

Ta amsa daƙyar bayan ta ɗauki tsawon daƙiƙu tana jan fasali.

Ya buɗe baki zai sake magana ta katse shi da cewar

“Haba Mukhtar, saboda Allah abincin ma baza ka barni in ci cikin kwanciyar hankali ba? Sai da safe ce ya kawo ka ko? to na amsa, Allah ya tashe mu lafiya. Don Allah ka kwashi kulolinnan ka koma gurin matarka, bazan ɓoye maka ba Allah ya sani na fi jin daɗin zama ni kaɗai ba tare da wani a kusa da ni ba.”

Ta faɗi maganganun da dukkan gaskiyarta.

Ya daɗe yana kallonta, zuciyarsa a jagule. Ya kasa ce mata komai, wai yau shi Fareeda ke ce ma ta fi jin daɗin zama ita kaɗai ba tare da shi a gefenta ba. Ya murgina kai gefe ɗaya abin tausayi, ya sani, Ibrahim ya faɗa masa. Shi da kanshi ya ƙona sunkurun kashinsa, don haka fushin fari ba nashi bane. Dole zai cigaba da bin ta yana lallaɓata har zuwa sa’adda za ta sakko don kanta ba tare da ya tilasta mata ba.

“Fareeda, ni dai ina neman afuwa. Allah ya huci zuciyarki. Bari in tafi, Allah ya tashe mu lafiya.”

“Ameen”

Ta amsa da sauri.

A kasalance ya miƙe ya nufi ƙofar fita.

“Ka kwashe waɗannan kulolin, ka mayar mata da kayanta.”

Ta faɗa ganin zai bar mata abincin Fatima a gabanta.

A hankali ya juyo, gabanta ya tsuguna ya ɗauki kular abinci ya bar mata na kayan ciki. Ya kalli cikin idanunta, a marairaice ya ce.

“Zan mayar da abincin, waɗannan biyun kayan ciki ne, farfesu da soyayye. Don darajar fiyayyen halitta SAW kar ki ce baza ki ci ba ko kuma ki ce in mayar. Don Allah.”

“Shi kenan! Allah ya ƙara buɗi.”

Ta faɗa saboda darajar waɗanda ya haɗa ta da su. Ya ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, sun fi ƙarfin a roƙe ta yin abu don su ta ce a’a.

“Bari in juyo ka mayar da kulolin.”

Har za ta miƙe sai ya dafa kafaɗunta ya komar da ita ta zauna.

“Yi zamanki Baby. Bari in ɗauko wasu kulolin in juye a ciki.”

Ko da ya shiga kicin ɗauko kulolin sai da ya haɗo mata da faranti da cokali, ko da za ta ɗiba ta ci ba sai tayi wahalar tashi ba. Duk da ya ga ruwa a gabanta sai da ya ɗauko wani ya ƙara ajiye mata.

“In ɗiba miki ko kaɗan?”

Ya tambayeta sa’adda yake juyewa a kulolinta.

Abinku da mai ƙaramin ciki, tun sa’adda ya buɗe kular ƙamshin farfesun ya daki hancinta miyaun bakinta ya tsinke. Amma saboda ta tankwaɓe shisshigin da yake mata sai ta ce

“A’a! Ba yanzu zan ci ba. Pls rufe kular, ƙamshin ya fara hawa min kai.”

Da sauri ya rufe jikinsa na rawa. Bawan Allah sai sannu yake jera mata ganin yadda take yamutsa fuska. Bai tashi a gabanta ba sai da yaga ta daina ɓata rai, haka ya fice gwuiyawunsa a saɓule, kamar wanda yayi amai da gudawa.

Ko da ya koma can ɓangaren Fatima duk tsawon lokacin da ya ɗauka gurin Fareeda tana zaune gaban abincinsu tana jiranshi. Duk da ranta ya sosu da daɗewar da yayi, ko kaɗan bata nuna mishi ba.

“Sannu da zuwa Haskenah”

Ta faɗa da fara’a sosai a fuskarta.

“Ya Auntyn tawa take? Ina fatan ka tarar da ita lafiya kalau?”

Ta sake faɗa kafin ya amsa sannu da zuwan da take mishi.

Da murmushi a fuskarsa ya amsa mata. Sosai ya ji daɗin yadda ta tambayi lafiyar Fareeda, ya tuno yadda ita Fareeda ta gama kushe lamarin Fatima yanzunnan kafin ya baro wajenta. Hakan ya saka shi jin babu daɗi kaɗan a zuciyarsa, bai bari tunanin yayi nisa ba ya watsar da komai ya zauna cin abinci.

Bayan sun gama tana  tattare kwanonin zuwa kicin shi kuma yana zaune kan kujera, wayarsa ce a hannunsa yake dannawa. Jefi-jefi yana ɗaga idanu ya kalli Fatima da take zirga-zirga a gabansa.

Ta zo za ta gitta ta gabanshi ya riƙo hannunta ɗaya haɗe da cewa

“Zo nan in gani Amaryata”

Ya janyo ta a hankali ya zaunar kan cinyarsa.

Yana kallon idanunta ya ɗaga hannunsa a hankali  ya zura ta saman rigarta. Idanu ya ɗan bubbuɗe jin tudun da ya shafo, tun dazu da take wucewa yana ta kallonta gaba da baya ya zaci cikon da ya hana ta yi ne tayi. Shi yasa ya yanke shawarar dubawa don kar ma ya tambayeta ta faɗa mishi ba daidai ba.

“Iyyeeeee… Amaryar tawa ce haka? Yaushe aka samu wannan gwaggwaɓar cigaban ba ni da labari?”

Ya tambayeta yana ɗan mammatsa mazaunanta yana jin yadda tsoka ya fara rufa ma ƙasusuwan gurin asiri, da murmushi a fuskarsa.

Hajiya Fatima dai ta kasa magana, a yangace ta ɗan saki siririyar haɗe da kwantar da kanta a ƙirjinsa.

“Au! Abin ƴar haka ne? Baza ki faɗa min ba Fatina?”

Ya raɗa mata a kunne yana taya ta dariya.

“Haskenah ka ga ka bari, ba na so.”

Ta faɗa a shagwaɓe tana ɗan dukan ƙirjinshi.

Aikin da bata ƙarasa a wannan dare ba kenan. Tun a nan falon wasan ya sauya salo, daga ƙarshe dai cak ya ɗauketa kamar wata baby zuwa cikin ɗakin barcinsu.

A wannan dare, Mukhtar ya shayar da Fatima zallar madarar farin cikin da ta daɗe tana burin kwankwaɗa a auren matashi sabon jini. Irin wannan salon soyayyar ta indiyawa ne yasa a mafiyawancin lokuta zamanin marigayi take cizon yatsar auren tsoho. Ta zaci a wancan ranar ne da ya tabbatar ta samu lafiya ne suka ci amarci, ayau ta tabbatar wancan ranar ba’a yi komai ba illah shafar mai. Yau ita ce ranar da suka ci uwar sabada ita da Haskenta. A daren ta ƙara tabbatar da Haskenta wani Haske ne mai muhimmanci a cikin rayuwanta, tun yanzu ya fara tsundumata cikin wasu daɗaɗan duniyoyi da ko kusa basu taɓa ziyarta ita da Babansu Ummee ba ina ga can gaba sun ƙara dunƙulewa ta hanyar zama abu ɗaya?

Haka ya sake ɗaukarta cak suka shige banɗaki, bayan wankan tsarki a tare suka yi na soso da sabulu. Yana cuɗa mata baya tana cuɗa mishi, kamar wasu ƙananun yara har da su wasan watsa ruwa da shafe-shafen kumfa bayan an ɗauraye jiki. Wannan wanka a lalace suka ƙarasa shi sannan suka fice daga banɗakin.

Da sauran awa ɗaya kafin a kira sallar asubah, don haka suka bi lafiyar gado. Tana kwance luf a ƙirjinshi tana sauke ajiyar zuciya sannu sannu.

“Barci za kiyi Fatina?”

Ya jefa mata tambayar bayan ya ji numfashinta ya fara canzawa.

“A’a! Kawai dai na ɗan gaji ne.”

Ta amsa a kasale.

“Na san kin gaji. Sannu da ƙoƙari, ki daure muyi sallar asubah sai mu kwanta. Yanzu dai tashi muyi magana.”

A hankali ta zare jikinta daga cikin nashi ta zauna a tsakiyar gadon. Shi ma zaman yayi, amma sai ya juya yana fuskantarta. Hannayenta biyu ya kama ya riƙe a cikin nashi, babu alamun ɓacin rai ko kaɗan a fuskarsa, sai ma wani ƙayataccen murmushi da yake sakar mata akai-akai.

“Fatina, tambayarki zanyi. Amma ina so ki ɗaukar min alƙawarin duk abinda na tambaye ki za ki faɗa min gaskiya tsakaninki da Allah da ya haliccemu.”

Ƙure shi da kallo tayi, zuciyarta cike da tunanin me zai tambayeta.

“Tambayar mecece?”

“Ai baki ɗaukar min alƙawarin ba…”

“Na ɗauki alƙawari. In dai na sani zan faɗa maka gaskiya tsakani da Allah.”

Ta katse shi da ƙagauta a muryarta.

Shiru yayi yana tunanin ta inda zai fara magana. Can sai ya daure ya ce

“Fatina, a gurin binciken abinda ke damuna har yake hana ni kusantar Fareeda an tabbatar min matsalar ba daga ita bane, daga ni ne…”

“Daga kai kuma? to taya ni baka fuskantar irin matsalar a gurina?”

Tayi mishi tambayar tana yatsuna fuska.

“Mai maganin da ya faɗa min haka ya ce, da yawan mata idan za suyi aure musamman zawarawa sukanyi amfani da magunguna daban daban domin su gyara jikinsu. Idan kuwa gidan da za su shiga akwai wata matar suna ninninka yin magunguna saboda su sha gaban uwaren gidansu. Shi ne mai maganin ya ce in tambayeki, wata ƙila a irin haka kika gamo ni da wannan matsalar ba tare da kin sani ba…”

“Wani tsinannen mai magani ne zai ƙulla min wannan sharrin?”

Ta katse shi a fusace. A zabure ta ƙwace hannunta daga cikin nashi ta dira ƙasa daga kan gadon tana zazzare idanu.

“Banyi komai ba. Ni kam babu abinda nayi na wani shirmen magani can. Mu gidanmu da muke ahlussunnah ta ina za’a bar mutum yayi wani magani? Babu abinda nayi, ba ruwana. Kar shegen da ya kuskura ya ƙulla min jakar tsaba balle kaji su bi ni da tsattsaga. Alum da bagaruwa kawai na san nayi ta tsarki da su shi yasa ka ji ni a matse, bushewar da ka ji nayi a farko kuma saboda ban haɗa da lalle wajen tsarki bane. Yanzu da na fara amfani da lalle shi yasa ka ji ni zam-zam yadda ake son ko wace mace mai ni’ima…”

Haka ta saki baki tana ta zuba shaaaaa, ta kamo wannan maganar ta saki wancan. Duk a ƙoƙarinta na wanke kanta daga maganganun da Mukhtar ya tunkaro ta da shi.

Shi dai yana ta kallonta, yana ƙara karantarta. Bai ga komai ba illah naɗe tabarman kunya da hauka da take ƙoƙarin yi. Ganin ta yi shiru tana zare idanu yasa shi ƙara kamo hannunta a karo na biyu, kusa da shi ya zaunar da ita.

“Fatima. Kinga ni magana ce nazo miki da ita na nutsuwa da fahimtar juna. Don Allah ki saurara min, ki kwantar da hankalinki, ki zurfafa tunani ki faɗa min, a cikin matan da kika sayi magani a hannunsu babu wacce ta ambata miki magana makamanciyar wannan matsalar tawa kan wani magani?”

A maimakon ta amsa, ko kuma ta nutsu ta zurfafa tunani yadda ya ce, kawai sai ta fashe da kuka. Ta ƙwace hannayenta ta fara yarfe su kamar wacce ta tsoma a ruwan zafi

“Na shiga uku! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Haskenah zargina kake yi? Daman na sani ba ka so na, ba ka ƙaunata, ka aure ni ne don kawai Fareeda ba ta jin maganarka, na sani. Amma ina so ka tuna abu ɗaya, soyayya da ƙauna ce tasa na aure ka. Ni ina son ka Mukhtar, na daɗe ina son ka, ko don soyayyar da nake maka ban cancanci irin wannan wulaƙancin da tozartawa ba.”

Izuwa yanzu, zuciyarshi ta fara kaiwa ƙololuwa gurin ɓaci. Sanyayan halayen da ya aro ya yafa kan halayenshi na zafin rai tuni sun fara yin nasu wajen. Ya fara dawowa asalin Mukhtar ɗinshi mijin Fareeda.

Kamar ba shi ne yanzu ya gama ɗaga ta sama yana rirriƙewa cikin soyayya kamar jaririya ba. Wani gigitaccen tsawa da ya daka mata a take ta haɗiye kukan da take yi kamar ɗaukewar ruwan sama. Ya kalleta da jajayen idanunsa, alamun rashin gaskiya ne ƙarara a tattare da ita.

“Baza ki faɗa min gaskiya ba ko Fatima?”

“Gaskiya nake faɗa maka. Wallahi gaskiya ne nake faɗa, na rantse da Allah. ka yarda dani don girman Allah…”

Tsam ya miƙe tsaye ya fice daga ɗakin kafin ta kai ƙarshen maganganun da bai ɗauke su a komai ba illah tsagwaron ƙarya.

Ta zaci ya bar maganar kenan. Ta gyara zama haɗe da takurewa tana sauke ajiyar zuciya kawai sai ga shi ya dawo cikin ɗakin, a hannunsa takarda da biro ne.

“Hasssssskkkkkeeeh! Mmmmmmmme kakkkkkkkeeeee ƙoƙƙƙƙƙƙƙarinnnnnn yiiiiiii?”

Ta tambayeshi bakinta na rawa da wani balaƴaƴƴen in-ina a muryarta.

Gefen gadon ya zauna, ya buɗe takardar ya yago falle ɗaya, ya ɗora biron akai alamun zai fara rubutu. Ya kalleta a ɗage

“Fatima tunda kin ƙi faɗa min gaskiya na rantse da girman Allah babu abinda zai hana ni datse igiyoyin auren da ke tsakaninmu. Banga amfanin don kawai na auro ki wata ƙozai ƙozai da ke ki shiga ki fita ki hana ni kusantar matata abar ƙaunata ba. Gara ni da ke duk muyi biyu babu.”

Ya sauke idanunshi ƙasa, cikin sauri ya fara rubuta

“Ni Mukhtar…”

“Na sani, wallahi tallahi na sani, zan faɗa maka gaskiyar, don ya rasulullahi kar ka sake ni Mukhtar.”

Ta faɗi maganganun cikin ihun kuka na tashin hankali haɗe da fincike biron hannunsa…

<< Rabon A Yi 27Rabon A Yi 29 >>

1 thought on “Rabon A Yi 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×