Skip to content
Part 29 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

“Ina saurarenki.”

Ya faɗa mata da fusata a muryarsa, fuskarshi a ɗaure tamau. Ganin ta ƙi magana, ta duƙar da kanta ƙasa tana ta rusa kuka.

Daƙyar ta iya sassauta kukan da take yi, idanunta na kallon ƙasa kamar wacce ke gaban surukinta. A hankali ta fara magana

“Tabbas na biya kuɗi don ayi aikin da za’a salamta Fareeda. Amma wallahi ni ban ce ayi aikin da za ka kasa kusantar Fareeda ba. Don girman Allah…”

“Idan kika sake haɗa ni da girman Allah sai na zubar miki da haƙora. Za ki tafi kai tsaye kiyi min bayani dalla-dalla na abinda ya faru ko sai na miki wani mugun shaƙa da zai sa ki fara jiyo ƙamshin mutuwa?”

Ya katse ta da faɗin haka cikin tsawa.

Ta sani Mukhtar ya daɗe da wuce saninta. Duk abinda ya ce zai aikata tabbas sai ya aikata shi. Jikinta na rawa ta buɗe baki za ta cigaba da magana ya sake katse ta a karo na biyu

“Sauka ƙasa ki zauna.”

Ya faɗa cikin gadara da iko.

Ita da gadon kwanciyarta haka ta sauka ƙasa ta zauna kan dandaryar tiles tana fuskantarsa. Kamar baiwa a gaban ubangidanta.

Nishi yake ja a fusace yana kallonta. Zuciyarsa cike da wani irin takaici da baƙin cikin da ko kusa baki bazai iya baiyanawa ba.

“Wani tsinannen mai magani ne yayi miki wannan aikin?”

Da rawar jiki ta buɗe bakinta ta fara faɗa mishi tun farkon yadda al’amarin ya kasance.

Maman Murad wata tsohuwar mai aikatau ce da Fatima tayi tun tana da cikin Ummee. Daga bisani zamansu baiyi tsawo ba bayan haihuwar Ummee, saboda su biyun da mun gamu ne da mun dace. Maman Murad ɗan banzan ƙwaɗayi da roƙo, ita kuma Fatima balaƴaƴƴen rowa da wayau. Ko da tafiyar ta ɓaɓe lokaci bayan lokaci Maman Murad tana kai ma Fatima ziyara. Haifaffiyar garin Gusau ce a jihar zamfara, amma tana zaune a hayin rigasa da ƴaƴanta da mijinta.

Wata rana ta kawo ma Fatima ziyara sai ta cimma Ramlah a gidan, ta kawo ma Fatima wasu magunguna, a gabanta kuma suke ta maganar maganin ba tare da tunanin ita da take zaune gefe ɗaya kan kafet ba. Ko da Ramlah ta tafi, sai Maman Murad ta gyara zama ta ce ma Fatima.

“Hajiya Fatima, ni kuwa na ce da irin waɗannan magungunan da ake kawo miki na ƙila wa ƙala me zai hana in haɗa ki da Kawuna ki biya shi kuɗi ƙalilan yayi miki aikin salamta kishiya?”

“Ban gane ba. Miye kuma salamta kishiya?”

Fatima ta tambayeta da mamaki sosai a fuskarta.

Ko da Maman Murad tayi ma Fatima bayanin abinda kalmar take nufi, ta kuma kira ƙanin mamanta wanda yake aikin a waya ya ƙara yi ma Fatima cikakken bayanin yadda aikin yake, da irin nasarar da mace take samu a gidan miji idan aka yi ma abokiyar zamanta irin wannan aikin. Jikinta na rawa ta ɗauko dubu ashirin ta damƙa ma Maman Murad. Dubu goma aka ce mata kuɗin aikin, amma saboda son ayi mata zazzafan aiki yasa ta bada dubu ashirin.

Duk da zuciyarta na ƙila wa ƙalan idan aikin zai tabbata kamar yadda Maman Murad da kawunta suka faɗa, amma tana fatan ko ɗan yaya ne aikin ya ci. Babban burinta a duniya shi ne tasha gaban Fareeda ta ko wane ɓangare a zaman gidan Mukhtar.

Za ta so ganin yadda Fareeda za ta wulaƙanta a gurin Mukhtar. Shi yasa ba ta jin ƙyashin kashe ko nawa ne wajen siyan maganin da aka tabbatar mata da asiri aka haɗa shi.

Bayan kwana uku Maman Murad ta sake komawa gidan, ta tabbatar mata aikin salamta kishiya angama. Bayan aure ta zuba ido tasha kallon abinda zai faru. Saboda tsananin farin ciki kyautar dubu biyar ta ba Maman Murad.

Bayan bikinta ganin babu wani canji na rashin daɗi tsakanin Mukhtar da Fareeda sai tayi tsammanin duk magungunan da tayi asarar kuɗinta tayi. Bata san aikin ya ci ba sai da Allah ya matsi bakin Mukhtar ya faɗa mata shi fa baya iya kusantar Fareeda.

A lokacin tayi mamaki ƙwarai, domin ba irin aikin da aka ce za’a yi mata ba kenan. Amma da yake ita ɗin mai bala’in wayau ce da iya samar ma kanta mafita cikin sauri nan take ta shirya ma Fareeda gadar zare, shi kuma ya hau ya zauna daram. Tonuwar asirin maganar cikin ƙanƙanin lokaci haka abu ne da bata taɓa tsammani ba.

Ƙara sunkuyar da kai ƙasa tayi bayan ta gama faɗa mishi duk abinda ya faru.

Mukhtar kallonta yake babu ko ƙyafta idanu. Zuciyarsa cike da tsoro da mamakin halayen ƴaƴan Adam. Kiyi tarayya da ƙawa zuciyarki ɗaya ashe ita ko kaɗan ba ta ƙaunarki ba ta ƙaunar ci gabanki. Ya kasa haƙuri sai da ya ce

“Fatima, ko dai akwai wani abu ne da Fareeda ta taɓa miki na mugunta tun kuna yara wanda har yanzu kike riƙe da shi a zuciyarki?”

“Babu komai. Wallahi Allah bata taɓa min komai na mugunta ba. Alkhairi ne tsakanina da ita…”

“Dalla rufe min baki algunguma. Ita kaɗai ke nufinki da alkhairi. Me yasa ke ba kya ƙaunarta?”

Ɗif tayi, ta kasa cewa komai. Sai mutsu-mutsu take yi tana ƙara sunkuyar da kanta ƙasa kamar wacce tayi ƙarya a gaban sarki.

“Ki zauna anan ƙasa har a kira sallar asubah. Ko yunƙurin miƙewa kika yi sai na miki wani hamɓari da zai sa ki faɗi ki karye, ki zubar da haƙora, ki fasa baki, da bala’in ƙarfi zan tokareki ta yadda zan tabbatar kin ƙarasa gaban tsohon madubinki kin fasa kai. Muguwa kawai.”

Ya faɗa mata maganganun da wani fitinannen haushinta a fuska da muryarsa. Ƙaƙƙarfan ƙwafa yayi, yaja tsaki haɗe da galla mata harara.

Kwanciya yayi kan gadon ya juya mata baya, zuciyarsa sai tuƙuƙi yake yi, ko kallonta ba ya son yi.

Haka ta zauna a watangare tana kallonsa yana kwance, ga gajiyar kusan kwana ana harraƙawa, ga wannan fitinannen tashin hankali da Mukhtar ya zo mata da shi bagatatan. Ga wani bala’in fitsari da ya riƙe mararta kam! Amma saboda tsananin tsoron kar ta motsa ya ce ya sake ta ko numfashi a hankali take saukewa. Kwatsam, Allah ya taimaketa ladanin unguwarsu ya kwaɗa kiran sallar asubahi.

Addu’a take tayi a zuciyarta kan Allah yasa Mukhtar baiyi barci ba, ganin ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ya yi. Ana gama kiran sallar sai taga ya yunƙura ya tashi zaune, ya miƙe tsaye zai wuce banɗaki. Da sauri ta janye yatsun hannunta na hagu da yake ƙasa ganin yana ƙoƙarin take ta.

Bayan ya gama laƙaiƙaita a banɗaki ya ɗauro alwala ya fito. A gurguje ya shirya saboda yana so ya sallaci raka’atanil fijr kafin a tayar da sallar asubahi. Ya kama hanya zai fice daga ɗakin ta bishi da kallo, idanunta ciccike da hawaye, tana so ta roƙe shi zuwa bayi tai fitsari tana tsoron kalmar da zai fito daga bakinsa.

“Kiyi sallah kafin in dawo. Ki tabbatar kin shirya zuwa gidan tsinanniyar matar nan.”

Ya faɗa mata haka yana gaf da ficewa.

Da gudun gaske ta faɗa banɗaki, ko da ta sauke nauyin mararta maimakon ta ɗauro alwala kamar yadda ya umarceta sai ta fito, wayarta da ke ajiye gaban madubi ta ɗauka jikinta na rawa ta lalubo lambar Maman Murad ta danna mata kira. Idanu ta bubbuɗe ta ɗora hannun hagu akai ta fara hawaye jin kamfani na sanar da ita wayar a kashe take.

Cikin daƙiƙu ƙalilan ta kira fiye da adadin da ita kanta baza ta ƙididdige ba, amma duk amsa ɗaya take samu, lambar da take kira a kashe take, bata ankara ba sai jin sallame sallar asubah tayi a masallaci. Da sauri ta aje wayar, a guje ta sake faɗawa banɗaki ta ɗauro alwala.

Tana raka’ar ƙarshe Mukhtar ya shiga cikin ɗakin. Wani irin faɗi da gabanta yayi sai da ta runtse idanunta, ta cije baki. Nan take karatun sallar ya ɓace mata, haka ta ƙarasa ibadar a daburce har ta sallame. Ta daɗe hannayenta a sama tans roƙon Allah ya rufa mata asiri, Allah ya taushi zuciyar Mukhtar a wannan yini duk abinda zai je ya zo kar Allah ya bashi ikon sakinta.

“Ina kwana Haskenah?”

Ta faɗa bayan ta shafa addu’ar tana kallonshi da raunanan idanunta da ƙarara suke bayyana irin tashin hankalin da zuciyarta take ciki.

Kamar mai gadi, haka yake tsaye ƙiƙam a bakin ƙofa yana jiran ta idar. Ko da ta gaishe shi maimakon ya amsa kawar da kansa yayi, hannayensa biyu naɗe a bayansa ya fara takawa zuwa cikin ɗakin har inda take zaune kan sallaya.

“Fatima?”

Ya kira sunanta da wata garjejiyar murya.

“Na’am Haske…”

“Daga yau idan kika sake ce min Haskenki sai na miki ɓarin makauniyar da zai yi sanadiyar zamowarki mai wawulo. Kina ji na?”

“Na ji Aban Twince, Allah ya huci zuciyarka.”

Ta faɗa a sanyaye.

“Tashi mu tafi.”

Yana faɗin haka ya fice daga ɗakin.

Haka nan ba don zuciyarta na so ba ta bi bayanshi, gwuiyawunta a sanyaye kamar wacce ta kwana tana zawo. Da duku-dukun asubahi haka suka shiga mota, ya fige ta a guje suka bar gidan.

Wani irin tuƙi Mukhtar ke yi na gagari, da yake kuma da duku-duku ne babu cinkoson motoci haka yake ta ƙure malejin mota ba tare da ya fuskanci matsalar go-slow ba. Babu mai cewa uffan a tsakaninsu, Fatima kwantar da kai tayi a jikin ƙofa tana ta jan duk addu’ar da tazo cikin zuciyarta.

“A wace unguwa take?”

Ya tambayeta sa’adda suka shiga hayin rigasa.

“Maƙera”

Ta amsa a taƙaice.

Ko da suka shiga cikin layin maƙera daƙyar ta gane gidan. Sau uku tana nuna mishi layuka mabanbanta, sai sun shiga ta gama waige da dube-dube sannan ta ce mishi ba nan bane. A ƙarshe dai Allah yasa ta nuna mishi wani gida ta bashi tabbacin nan ne gidan Maman Murad.

“Kin tabbatar?”

Ya tambayeta yana ƙure ta da kallo.

“Eh! Na tabbata, nan ne. Bari in je inyi sallama da ita.”

Har ta kama hannun ƙofar motar za ta buɗe ta fita ya dawo da ita ta hanyar janye hannunta. A tsorace ta waiga tana kallonshi da alamar tambaya a fuskarta.

Wani baƙin gilas da yake ajiye a gaban motar ya ɗauka ya ƙwama a idanunsa.

“Kin ga na miki kama da ɗan’iska wanda bai san abinda yake yi bane?”

“A’a!”

“To Idan ba haka bane ta ya kike tunanin zan barki ki shiga bayan tun ɗazu ina kallon yadda kike ta danna ma lambar matar kira? Ni da kaina zan je inyi sallama da ita. Fita muje.”

Jiki babu ƙwari ta buɗe ƙofar ta fita, yabi bayanta bayan ya kulle motar. Ko da suka isa ƙofar gidan a gefe ta tsaya, shi kuma ya matsa ya ɗauki wani ƙaton dutse ya fara ƙwanƙwasa ƙyauren gidan da yake a kulle.

Bai ɗauki minti ɗaya ba ya ji ana ƙoƙarin zare sakata ta ciki. Don haka yaja gefe ya tsaya, hannayensa naɗe a ƙirji, fuskarnan a ɗaure tamau, kamar bai taɓa sanin wata aba wai ita dariya ba.

“Malam lafiya da sassafennan kake mana irin wannan bugun? wa kake nema?”

Wanda ya buɗe gidan ya tambayi Mukhtar.

“Maman Murad muke nema. Tana ciki? Allah yasa bata nan ta tafi garinsu.”

Fatima tayi maganar a daburce cikin rawan baki.

Jin abinda Fatima ta ce yasa Mukhtar dafe bangon gidan yana kallonta da mamaki, sai kuma ya ɗanyi murmushi, zuciyarsa cike da tunanin irin tsiyar da zai shuka ma Fatima idan ba’a samu wannan matar a gida ba.

Shi kuwa wannan mutumi da ya buɗe gidan kallon ƙurilla yake ma Fatima, irin kallon nan na anya wannan lafiyarta ƙalau? Ta faɗi ga wacce suka zo gurinta, amma kuma take fatan ace matar ba ta nan?

“Maman Murad tana nan, jiya da daddare ta dawo daga garinsu. Amma ba ni da hurumin da zanyi muku sallama da ita kai tsaye, bari in kira muku mijinta sai ku nemi izinin ganinta daga gare shi.”

Ya amsa musu bayan yayi tunanin lafiyar Fatima ko akasinta ba abinda ya shafe shi bane.

Cikin gidan ya koma. Minti biyar tsakani wani dattijo ya fito ƙofar gidan. Fuskarsa cike da kamala, hannu ya miƙa ma Mukhtar suka yi musabaha. Ko da Mukhtar ya faɗa mishi sun zo ganin mai ɗakinshi ne ɗan jim yayi, sai kuma ya ce

“Malam Muntari Allah yasa dai lafiya?”

“Lafiya ƙalau Baba. Wata harƙalla ce ta shiga tsakaninta da wannan matar a kwanakin baya. To an samu matsala, shi ne muka zo takanas ta kano don a warwara wannan matsala cikin maslaha ba tare da tashin-tashina ba. Amma fa idan ita mai ɗakinka ta bayar da haɗin kai.”

Uzuri dattijon ya nema a gurin Mukhtar, ya shiga cikin gidan, can sai ga shi ya sake fitowa, a bayansa Maman Murad ce. Fuskarta dagaje-dagaje da yawun barci, da alamun ko sallar asubah bata samu gabatarwa ba saboda yadda take ta sakin hamma tana mutsuttsuke idanu, alamu ne na wacce aka taso ta daga nannauyan barci.

A ƙyamace Mukhtar yake kallonta, sai kuma ya mayar da hankalinsa kan Fatima da ta raɓe jikin bango ƙirjinta na bugun tara-tara ya ce

“Ita ce wannan?”

Yai mata tambayar yana nuna Maman Murad da yatsarsa manuniya.

A kasale ta ɗaga kai alamar eh, ita ce.

Sai a lokacin idanun Maman Murad ya faɗa cikin na Fatima, faɗaɗa fuskarta da fara’a tayi ta ce

“Maman Ummee, ke ce yau a gidan namu? Bismillah shigo mana? Baban Murad baka gane ta ba? Maman Ummee ce fa wacce na yi ma aiki shekarun baya a unguwar rimi, baƙin alkhairi ne ba na tsiya b…”

“Idan kin so, shi ne za mu zame miki baƙin alkhairi. Idan baki so ba kuwa akasin haka ne zai kasance.”

Mukhtar ya katse ta da sauri jin yadda take ta zuba tana cika mishi kunne da zantukan da bai ɗauke su a komai ba sai shirme. Kafin ta ce komai ya cigaba da cewa

“Tunda duk kun gane juna to Alhamdulillah! Ke baiwar Allah, kin tuna aikin da ƙanin mamanki yayi ma wannan matar da kike kira Maman Ummee ko? Ba komai ne ya kawo mu a daidai wannan lokacin ba sai don sanin ta inda aka hau ta nan ake sauka.”

“Ban gane ba.”

Maman Murad ta faɗa tana yamutsa fuska, bayan ta haɗe girar sama da ƙasa.

Gilashin idanunsa ya cire ya riƙe a hannu, ya sake haɗe fuska sosai, babu alamun rahama ko ƙanƙani a tattare da shi.

“Za ki gane yanzunnan. Ta faɗa min, a wancan lokacin ta waya kawai kika kira kawunki suka gama maganar mugun aikin zaluncin da take so ayi mata kan Uwargidana. To a yanzu dai wannan aikin ba ta buƙatarshi, ni ne mijinta. Don haka ina umartarki ki kira Kawunki yanzunnan ki faɗa mishi ya warware wannan ƙullin da yayi…”

“Taɓɗijan! Wasa ma kenan! Ai wannan aikin aka yi shi anyi kenan. Makarinsa kawai ka saki ita waccan matar ne ka zauna da Maman Ummee ita kaɗai, ina tabbatar maka ko wata matar ka auro haka za ka ji ta Salam, mahaɗar jin daɗi da gamsuwar buƙatarka na auratayya an haɗa shi da Maman Ummee ne…”

Maganarta ya ɗauke ɗif ne, sanadiyyar wani ɓarin makauniyar mari da Mukhtar ya sauke mata ba zato ba tsammani. Ɗif ta ɗauke wuta, babu abinda take ji a kunnuwanta sai wani irin wiiiiiiiiii kamar jiniyar ƴan sanda. A idanuwanta kuwa babu abinda take gani sai wasu taurari masu bala’in haske da ƙyalƙyali suna shige da fice a jikin junansu.

“Baba kayi haƙuri na ɗora hannu kan iyalinka  Na rantse da girman Allah idan matarka da ɗan’uwanta basu warware wannan mummunan asirin da suka yi tsakanina da matata ba hukuma ce za ta shiga tsakaninmu. Daga nan state CID za mu wuce kai tsaye, tun ɗazu na kira babban abokina da yake can na faɗa mishi abinda yake faruwa. Yanzu haka kiran wayata kawai yake jira, zai turo mota yanzunnan a tafi da ita. Idan mun je can aka je har can garinsu aka ɗauko ɗan’uwan nata luguden mintuna goma ya isa su samo hanyar warware wannan ƙullin da suka yi.”

“Kayi hakuri Malam Muntari, abin duk bai kai haka ba…”

Ihun da Maman Murad ta ƙwalla cikin azaba shi ya ankarar da su ta dawo cikin hankalinta. Ta buɗe baki za ta sake ƙwallah ihu a gigice da sauri Baban Murad ya janyo ta ya rufe mata baki.

Cikin gidan ya ja ta, bayan yayi ma su Mukhtar umarnin su bi bayanshi zuwa cikin gidan. Duk da gidan haya ne jin irin gaggarumin maganar da ke tafe da su Mukhtar shiga da su cikin gidan shi yafi alkhairi da tsayuwarsu a waje. Ga unguwar irin ghetto ɗinnan ne, duk da safiya ce mutane masu wucewa har sun fara tsayuwa ganin kafcecen marin da aka saukewa Maman Murad.

A tsakar gidanma mata da maza ne tsaitsaye suna hum-hum-humm!

“Baban Murad lafiya kuwa?”

Biyu daga cikin mutanen gidan suka haɗa baki wurin tambayarsa.

“Lafiya ƙalau.”

Ya amsa a gundure. Ya bankaɗa labulen ɗakinsu ya shige ciki, su Mukhtar suka bi bayansa. Maman Murad kwance a jikinsa ranga-ranga kamar sumammiya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 28Rabon A Yi 30 >>

1 thought on “Rabon A Yi 29”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×