"Ina saurarenki."
Ya faɗa mata da fusata a muryarsa, fuskarshi a ɗaure tamau. Ganin ta ƙi magana, ta duƙar da kanta ƙasa tana ta rusa kuka.
Daƙyar ta iya sassauta kukan da take yi, idanunta na kallon ƙasa kamar wacce ke gaban surukinta. A hankali ta fara magana
"Tabbas na biya kuɗi don ayi aikin da za'a salamta Fareeda. Amma wallahi ni ban ce ayi aikin da za ka kasa kusantar Fareeda ba. Don girman Allah..."
"Idan kika sake haɗa ni da girman Allah sai na zubar miki da haƙora. Za ki tafi. . .
Ana wata ga wata, lallai wannan al’amarin babba ne