Kasancewar tana da lafiyayyiyar soyayyar miyar da tayi jiya da daddare, sai kawai ta ɗora sanwar farar shinkafa.A gurguje ta faɗa bayi tayi wanka ta ɗauro alwala, tana fitowa ta wanke shinkafarta ta zuba sannan ta tayar da sallar la'asar da basu samu damar gabatarwa ba suna gurin ƴan sanda.A mafiyawancin lokuta in dai yana gari idan yayi sallar magriba ba ya fita daga masallaci sai ya sallaci isha'i, akwai karatun littattafan addini da Limamin masallacin yake musu tsakanin magrib da isha'i, in dai yana nan ba ya son rasa karatun.Ko kafin ya. . .