Skip to content
Part 4 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Kasancewar tana da lafiyayyiyar soyayyar miyar da tayi jiya da daddare, sai kawai ta ɗora sanwar farar shinkafa.A gurguje ta faɗa bayi tayi wanka ta ɗauro alwala, tana fitowa ta wanke shinkafarta ta zuba sannan ta tayar da sallar la’asar da basu samu damar gabatarwa ba suna gurin ƴan sanda.A mafiyawancin lokuta in dai yana gari idan yayi sallar magriba ba ya fita daga masallaci sai ya sallaci isha’i, akwai karatun littattafan addini da Limamin masallacin yake musu tsakanin magrib da isha’i, in dai yana nan ba ya son rasa karatun.Ko kafin ya koma gida ta kammala girkinta tsaf, tana da ƙanƙarar pure water a frig, sai tayi amfani da wannan damar ta dafa zoɓo da kayan ƙamshi ta jejjefa ƙanƙara a ciki. Ya shiga falon ne a daidai lokacin da ta gama shirya komai kan ɗan madaidaicin teburin cin abincinsu da yake can gefe ɗaya a cikin falon.”Sannu da dawowa Masoyi.”
Tayi maganar a tausashe, fuskarta ɗauke da lallausan murmushi, tana kallonshi cikin ido.

“Yauwa”

Ya amsa a taƙaice, da fuska kadaran kadahan.
A taƙaice ya kalleta ya ƙara kalla, ta yi kwalliya cikin wasu riga da wando na shan iska, kayan ko a ido basuyi alamar nauyi ba, kuma roba ne duba da yadda suka bi fatar jikinta suka lafe, sun fitar da ainihin shape ɗin jikinta.

‘Fareeda ba dai ƙirar jiki mai kyau ba, tubarkallah ma sha Allah, baƙa ce a kalar fatar jikinta, amma ba irin baƙinnan ƙirin ba, baƙinta mai kyau ne da ɗaukar idanun mai kallonta.

Doguwa ce a yanayin halittarta, sai dai irin tsawonnan da bai yi ma mace yawa ba, ga kuma ƴar ƙiba da cikar baya da ƙirji da take da shi, waɗannan abubuwa uku su suka taka muhimmiyar rawa gurin daidaita tsawonta.

A fuska baza a kirata kyakkyawa ta gaban kwatance ba, amma kuma baza a jefata layin munana ba, tana da kyau daidai gwargwado.

Kuma kasancewarta wacce ta laƙanci sirrin gayu da iya ɗaukar wanka idan ta fito baza’a taɓa cewa bata yi ba, za’a kalleta a ƙara kallah, ba kuma wai ɓata lokaci take a gurin shafa wannan goga wancan a fuskarta ba, a’a!

Ƴar powder kawai take shafawa sama-sama, sai ta goga man baki a laɓɓanta da suka kasance masu ɗan tudu, sanin sirrin gayun ƴa mace kuma yasa take ɗan ƙara tsuke bakin, lokaci bayan lokaci kuma tana ɗan tura leɓen ƙasa gaba sak na shagwaɓaɓɓun mata.

Idan ta ɗan zizara kwalli a idanuwanta, kasancewarta mace mai yalwar gashin gira tana ɗaukan wasu daƙiƙu gurin tacewa da daidaita kwanciyarsa.

Har yanzu da take cikin shekarunta na ashirin da tara fuskar ƴanmata ƴan sha takwas take da, idan ba sani aka yi ba baza’a taɓa cewa ita ce tayi haihuwa uku ƴaƴa huɗu ba saboda kyawun jikinta.

Haihuwarta na farko da na biyu duk basu zo da rai ba, sai na uku ne ya tsaya, da lokacin haihuwar yayi ta haifi ƴan biyu duk maza.

Sun shekara ɗaya da wata takwas cif kafin mahaifiyarsa wacce suke kira Hajiyarmu ta ɗauki ƴaƴan yaye, a yanzu haka suna can gidanta a unguwar dosa. Ta ko wane ɓangare Fareeda ta kai irin macen da ko wane namiji mai hankali zai so aura a matsayin matarsa, babban matsalarta rashin jin magana da taurin kai. Shi ya ƙi sakar mata mara ta dinga fita yadda take so, ita kuma a matsayinta na wacce take ƙasansa ta ƙi haƙura ta watsar da tsarin rayuwarta ta bi abinda yake so. Sai yaushe ne za ta gyaru…?’ “Masoyi lafiya dai ko? ga abincinka na gama haɗa duk abinda za ka buƙata”Saukar muryarta shi yayi nasarar dawo da shi daga duniyar zurfin tunanin da ya afka. Bai ce mata komai ba, kuma a maimakon ya nufi ɓangaren da ta jera mishi abinci sai ya kama hanyar zuwa ɗakinsa.

Da sassarfa ta bi bayanshi, yana shiga ɗakin ta ɗora ƙafa a inda ya cire tasa.

“Ya aka yi?”

Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.

Narai narai tayi da idanu suka cicciko da ƙwallah, ta riƙo hannayensa guda biyu a cikin nata.“Na san na ɓata maka Mijin Fareeda, don Allah kayi haƙurii…”

“Na zaci mun gama wannan maganar?”Ya katse ta idanunsa a cikin nata.

Ƙwayoyin idanunta ta saukar da su ƙasa a hankali, sai a lokacin ta ba hawayen damar sauka zuwa kumatunta, sai ta sake ɗaga idanu ta kalle shi“Walwalarka nake buƙatar gani Masoyi, idan baka huce ba don Allah kayi min faɗa, kayi ta faɗa idan ta kama ma ka haɗa min da duka har zuwa sadda za ka ji sauƙin zuciyarka. Wannan yanayin damuwar da nake gani shimfiɗe a kyakkyawar fuskar mijina sam ba na jin daɗinsa.”

Sai kuma ta fara ɗan jan hanci tana shessheƙa, hawaye wasu na korar wasu.

Ya buɗe baki zaiyi magana ta yi saurin katse shi da cewar“Don Allah ka yafe min mijina…”

A sannu ta silale zuwa ƙasa za ta durƙusa kan gwuiwoyinta yayi saurin riƙe kafaɗunta, ya ɗagota tsaye ya rungumeta a jikinsa.

Kamar daman hakan take jira, da saurin gaske ta sa hannayenta biyu suka zagaye bayansa ta ruƙunƙumeshi, tana cigaba da jan shessheƙar kukanta a hankali, da wani irin salo na karyar da zuciyar wadda aka yi ma laifi. Ta sani Mukhtar ɗin yana da faɗa, amma duk masifarsa ba shi da riƙo ko kaɗan, faɗarsa kamar mai hawa da saukar aljanu da yayi suka jirge shi kenan zai koma kamar ba shi ne ya gama zazzage tsiya ba.

Ko yanzu ta tabbatar yana wannan ciccijewar ne don bai samu ya sauke tsiyar da ke cunkushe a cikinsa ba, haƙuri da uzuri akan laifin da aka yi masa ba halinsa bane sam, ko ɗan yaya ne sai ya zazzageta. Da wannan rashin walwalar da ya tsira ita kam gara ya balbaleta da bala’i a wuce gurin.

Ƙananun kitson kanta da suka bayyana saboda hularta da ya faɗi ya shafa da hannunsa na dama, yayi ƙasa ƙasa sosai da muryarsa, faɗan dai da take jira yayi yau ba ya ra’ayi.“Faree, ina tsananin sonki kin sani. Me yasa baza ki taushi zuciyarki ki bi abinda nake so mu zauna cikin farinciki ba?”“Wallahi zan bi, na ma bi in Allah ya yarda. Don Allah kayi haƙuri, kayi min faɗa.”

Ɗago kanta yayi daga ƙirjinsa yana kallon fuskarta, hawaye ne kaca-kaca, ƴar kwalliyar da akayi mishi duk ta gama ɓaci da hawaye. Ƙayataccen murmushi ya sakar mata, yasa babbar yatsarsa ya fara ɗauke mata hawayen, har lokacin murmushin da yake yi bai bar kan fuskarsa ba.“Wannan faɗan da kike ta maimaitawa inyi miki yau dai ba na jin yin ta. Ko dole ne?”

Ƙara shagwaɓe fuskarta tayi ta girgiza mishi kai alamar a’a!

“Ki gane wani abu Baby, ba abin arziki bane kusan ko wane lokaci a gidannan inyi ta ɓaɓatu ina maimaita faɗa kan abu ɗaya. Maganar fita unguwa ba tare da izinina ba daga jiya na ɗaukar ma kaina alƙawarin in Allah ya yarda bazan sake miki hargagi na tashin hankali ba. Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kin sha fita ba tare da izinina ba, na kuma faɗa miki ba na so, in dai faɗa da tashin hankalin miji na sa mata ta daina laifi da tuni kin daina.

Ya kike so inyi miki? wane mataki kike so in ɗauka a kanki? ko so kike in fara bi cikin ƴan’uwanki ina kai ƙararki?”Ya girgiza kai sannan ya cigaba.

“Baza’ai haka da ni ba in sha Allah! Ni bani da ra’ayin in kai ƙarar matata gurin iyaye ko ƴan’uwanta. Soyayya ta sa na auro ki, wannan soyayyar ita za ta sa in cigaba da haƙurin zama da ke iya yadda zan iya. Amma fa ki sani, ni dai a matsayina na mijinki bazan daina hana ki zuwa unguwa marasa muhimmanci ba, tsarina ne wannan, ra’ayina ne. Ke kuma ra’ayinki ne kibi dokar da na shimfiɗa miki, idan ba ki so ba kuma ki bi son zuciyarki. Ni kuma duk sadda haƙurina ya gaza zan ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ne da baki taɓa tsammanin zan iya ɗaukar irinsa ba.

Magana ta wuce, don Allah kar mu sake tayar da wannan zancen. Na haƙura, na yafe miki fitar da kika yi jiya, ina roƙon Allah ya yafe miki tsinuwar da mala’iku sukai ta miki jiya tun daga ficewarki a gidannan har zuwa dawowarki.”

Jikinta ne yayi sanyi, sanyi kuma sosai. A iya zamantakewarsu basu taɓa zama yayi mata irin waɗannan maganganun masu bala’in kashe jiki da jefata cikin tunani ba.

A hankali ta mayar da kanta a ƙirjinsa ta kwantar, zuciyarta cike da addu’ar Allah ya bata ikon daina fita ba da izininsa ba, Allah ya bata ikon daina aikata duk wasu abubuwa da ta san ba ya so a halayyarta.

“Na gode Mijinah”Ta faɗa mishi haka da muryarta mai bayyana sanyin da jikinta yayi.

Bata mishi alƙawarin za ta daina satar fita ba, domin ba wannan ne karo na farko da tayi mishi alƙawarin ta daina ba. Amma ta sha alwashin zai gani a ƙasa, za ta daina in sha Allahu, daga jiya in Allah ya yarda baza ta sake ba.

“Wayyoooo… Faree cika ni mana? Yunwa fa nake ji kin sani, na shigo ɗaki kuma kin biyo ni kin ƙwaƙumeni. Ko kema yunwar abinnan kike ji in fara ƙosar da ke kafin in ƙosar da cikina?”

Da saurin gaske ta sake shi tana ɗan dariya haɗe da sunkwui da kanta ƙasa alamun ya bata kunya, ta kasa cewa komai.

Dariyar shi ma yayi, yana son matarsa, ganinta cikin farin ciki ba ƙaramin jefa shi a farin ciki yake yi ba. Ƴar soyayya ce ita, ta san salo-salo na kwantar da hankalin ɗa namiji, a mu’amalarsu ta auratayya tana ba shi ƙololuwar farin ciki, shi yasa ko wane lokaci kishi da soyayyarta yake ƙara ninninkuwa a zuciyarsa. Shi fa bai ƙi ace a duniyarta bata san kowa ba sai shi kaɗai, shi kaɗai yake so ta fuskanta kuma ta sa a gabanta, idan ya ce mata baƙi fari ne ta kalle shi a fari tas tas! Idan kuma ya ce a’a ya zauna a a’a har abada.

“In kawo maka abincin nan ne?”Ta tambaye shi bayan ta riƙe hannunsa na hagu a cikin na damanta.

“A’a! zan fita falo. Wai da so nake in ɗan watsa ruwa a gurguje ko zan fi jin daɗin cin abincin.”

Da sauri ta shige banɗakinsa ta tara masa ruwan ɗumi daidai yanayin zafin da yake so.Ko da ta koma cikin ɗakin har ya gama shirin shiga wanka.

“Allah yayi miki albarka.”

“Ameen mijin Fareeda. Ko inzo in cuɗa maka baya?”Ta ƙarasa tambayar haɗe da kashe masa ido ɗaya.

“Ina maraba da hakan ƴan matana”

Musayar murmushi suka yi a tsakaninsu, ya damƙi ƙugunta ya riƙe suka fara taku a hankali kamar wasu indiyawa zuwa cikin banɗaki, sai musayar kallon cikin idanun juna suke yi da lallausan murmushi kan fuskokinsu, masana sun ce kallon cikin idanu tsakanin miji da mata yana ƙara danƙon soyayya.A ƙarshe dai sunyi wanka sun fito, bayan sun ɗauki lokaci mai tsayi suna murje juna da salon soyayya.

A gurguje suka gama shiryawa suka nufi falo, kai tsaye teburin cin abinci suka wuce, cike da girmamawa taja mishi kujera ɗaya daga cikin huɗu da suke gurin ya zauna.

Ita ta ciyar da shi cikin yanayin soyayya yana ci tana kora mishi da sassanyar zoɓo har ya bata tabbacin ya ƙoshi. Ko da ya nemi ya ciyar da ita ɗan kaɗan taci, tashin hankalin da ta shiga a yinin yau ya taka muhimmiyar rawa gurin cunkushe mata cikinta, ba ta jin yunwa sam, kuma ba ta jin cin komai.

Falonsu ya koma ya zauna kan kujera mazaunin mutum uku yana kallon labaran duniya ƙarfe tara. Ita kuma ta tattare kayan abincin ta kai kicin, a daren tayi wanke-wanken kwanonin da suka ɓata, sauran abincin kuma ta adana shi yadda bazai lalace ba.

Har ta kama hanyar fita daga kicin ɗin sai ta koma. Kofi ta ɗauka ta tsiyayi ruwan zafi ta jefa lipton a ciki.

Ta fasa ƙwai guda ɗaya a wani kofin daban ta karkaɗa shi sosai ya tsinke, sannan ta sake ruwan lipton ɗin a ciki ta jujjuya ya haɗe jikinsa. Runtse idanu tayi ta shanye.

Da sauri ta buɗe ɗaya daga cikin durowar kicin ɗin ta ɗauki cingam ƙwara ɗaya ta ɓare ta jefa a bakinta saboda tashin zuciya.

Ita ɗin ba gwanar shan magungunan mata bane, amma duk wani abu da za ta ji an ce natural ne tana ƙoƙarin gwadawa don ta ga ingancinsa. Ƙwai da lipton tun da ta gwada sau ɗaya ta ga yayi mata aiki sosai, da gaugawa yake saukar da ni’ima a jikinta, shi yasa tun da ta riƙe sirrin ba ta wasa da shi.

Can falo ta koma, a gefenshi ta zauna, ta zame ta ɗan kwantar da kanta a kafaɗunsa suka cigaba da kallo.

Basu tashi daga kallon ba sai sha ɗaya da kwata na dare, bayan labaran duniya arewa24 ya maida suka kalli shirin da ake haskawa a daidai wannan lokacin.

Da ganin take-takensa ta san a ɗakinsa za su kwana, don haka ta ba shi uzurin za taje tayi shirin barci a ɗakinta. Kwalbar zumanta mai kyau da yake ajiye a gaban madubi ta ɗauka ta tsiyayi cokali uku ta shi, ta dangwali kaɗan tayi matsi da shi. Yana saurin saukar da ni’ima, ko a bushe kike ƙayau mayau in dai ya karɓeki minti biyu yayi yawa za kiji saukar lema a ƙasa.

Wani irin biyayya da soyayya take sabunta masa a wannan dare, ta faranta masa fiye da yadda yake tsammani, ita ta riƙe linzamin dokin ta barshi yayi sukuwa yadda yake so, ko kaɗan bata nuna gajiyawa ba, sai shi ne ma ya dinga tausaya mata yana shi mata albarka.

*****

A iya tsawon kwanaki huɗu da ya ɗauka na hutunsa zama na zallar farin ciki da soyayya ne a tsakaninsu. Har wani suna ya raɗawa kwanakin.

“Ranakun sabunta amarci.”

Tun ranar litinin ya kamata ya koma gurin aikinsa can kudancin kaduna, amma saboda armashi da daɗin da yake tattare da waɗannan kwanaki ya kira Ogansa yayi ƙaryar ba ya jin daɗi.

Kwanaki biyu aka ƙara masa, bahaushe ya ce daɗinsa da gobe saurin zuwa. Sai ga shi kuwa har ranar tafiyarsa ta zo. Soyayya ruwan zuma, kamar wasu sabbin aure haka Fareeda ta tasa shi gaba da ƴan koke-koke duk inda ya ɗaga kafa nan take mayarwa.Sai da ya dakatar da duk wasu shirye-shirye da yake yi yayi rarrashi mai dalili, ya kwantar mata da hankali tare da alƙawarin ranar juma’a da wuri zai dawo in Allah ya yarda. Haka dai suka rabu ba tare da zukatansu sun so rabuwa a daidai wannan lokacin ba.

Da gaske ne fa soyayya ba ta tsufa sai dai masoyan su tsufa, ko ɗan kaɗan ne mu dinga ƙoƙarin sabunta soyayyarmu a zukatan mazajenmu.

*******Tsawon sati uku da suka biyo baya zaman lafiya da ƙaunar juna ne a tsakaninsu. Yau litinin yayi sammakon komawa gurin aiki, tun da ya tafi ta kwanta tana sharɓar barci, wayarta na ajiye a daidai kanta, amma da yake ta rage ƙarar wayar shi yasa aka kira ta har sau biyu bata ji ba, sai a kira na uku ta jiyo ƙarar kamar a mafarki.

A kasalance ta buɗe idanu, miƙa tayi haɗe da salati, ta ɗauki wayar yana daf da tsinkewa. Ƙanwarta Masrura ce take kira“Hello, Ummu Sultan barka da rana.”

“Aunty Fareeda, kina gida ne?”Ta tambayeta da murya mai baiyana damuwa da rashin walwala.

Ƙirjinta ne ya buga dam! da sauri ta miƙe zaune daga kwance, hankali tashe ta amsa da cewar tana gida, me yake faruwa?

“Tun ɗazu ga mu a asibitin Garkuwa da Aunty Binto, kiyi sauri ki zo, haihuwa ce ta zo mata da gardama, ni da Mustapha tun ɗazu ga mu a asibitin…”Ƙit wayar ta katse…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 3Rabon A Yi 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.