Saɓanin yadda ya saba dawowa daga gurin aikinsa duk ranar juma'a, a wannan karon sai da ya shafe sati biyu cif bai waiwayi iyalinsa ba.
Kuma ko a waya ba ya nemanta, sai ita ce ma take kiransa amma sam ba ya ɗagawa. Kwanaki biyu da fara samun sauƙinta ta fara jera mishi kira akai-akai. Duk a tunaninta bai san abinda yake faruwa da ita ba, amma da taga ta kira sau ba adadi bai ɗauka ba sai ta haƙura, abu ɗaya da bata daina ba shi ne tura mishi saƙo mai ɗauke da. . .
Normal