Skip to content
Part 8 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Saɓanin yadda ya saba dawowa daga gurin aikinsa duk ranar juma’a, a wannan karon sai da ya shafe sati biyu cif bai waiwayi iyalinsa ba.

Kuma ko a waya ba ya nemanta, sai ita ce ma take kiransa amma sam ba ya ɗagawa. Kwanaki biyu da fara samun sauƙinta ta fara jera mishi kira akai-akai. Duk a tunaninta bai san abinda yake faruwa da ita ba, amma da taga ta kira sau ba adadi bai ɗauka ba sai ta haƙura, abu ɗaya da bata daina ba shi ne tura mishi saƙo mai ɗauke da kalaman soyayya, fatan alkhairi da neman yafiyar laifin da bata fito fili ta bayyana ba.

Kwanakinta huɗu a gadon asibiti aka sallameta, duk iya waɗannan kwanakin Masrura ce take jinyarta, ƴan’uwanta kuma suke shafe ko wace yini wajen zuwa gurinta da dafo mata abinci mai rai da lafiya. Ko kafin a sallameta jikin yayi sauki sosai da sosai, sai ƴan abubuwan da baza’a rasa ba.

Rashin ganin Mukhtar ko wani nasa wajen duba Fareeda shi ya dasa Yaya Mustapha ayar tambaya, ba tare da sanin Fareeda ba ya kira Mukhtar a waya, amma abin mamaki da ɗaure kai don hakan bai taɓa faruwa a tsakaninsu ba shi ne kiran Mukhtar sau bakwai bai ɗaga waya ba. Ya katse kiran da tunanin zai biyo bayan kiranshi daga baya amma har aka shafe kwanaki biyu bai kira shi ba.

Ranar da aka sallami Fareeda shi ya kwashe su a motarsa zuwa gidan Fareeda, Aunty Murja, Masrura, Fareeda, sai shi, Aunty Binto ce kawai ba ta saboda ɗanyen jegon da take fama da shi.

Daman wannan lokacin yake jira na sallamarta daga asibiti, titsiyeta yayi nan cikin falonta ya tambayeta abinda yake faruwa tsakaninta da mijinta. Duk ƴan’uwan sun san irin soyayya da shaƙuwar da yake tsakaninsu, in dai halin lafiya suke da mijinta ba’a shafe yini guda cur ba tare da ya kira ta a waya ko kuma ita ta kira shi ba. Sai ga shi wannan karon duk ƴan’uwan sun fahimci mijin ba ya kiranta a kwanakin da ta kwanta asibiti, mahaifiyarsa bata je duba ta ba, cikin ƴan’uwansa ma babu wanda ya je duba ta duk da kyakkyawar dangantakar da ke a tsakaninta da dangin mijinta.

“Me yake faruwa tsakaninki da mijinki?”
Yayi mata tambayar idanunsa na kanta.

Waɗannan maganganun na Yayanta kamar fami ne a inda yake mata ƙaiƙayi. Nan take idanunta ya cicciko da hawaye, ta sunkuyar da kanta ƙasa, cikin damuwa da tashin hankali ta kora musu gaskiyar bayanin duk abinda ya faru da ita.

Nan take Ya Mustapha ya rufe idanu ya fara zazzaga mata bala’i ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ɗari bisa ɗari na laifin ya ɗora shi a kanta ne, ya kuma rantse da girman Allah ko shi ne zai ɗauki matakin share ta fiye ma da yadda shi Mukhtar ɗin yayi. Kamar zai tsinke ta da Mari saboda masifa, bata taɓa ɓata mishi rai irin na wannan lokacin ba.

Ita dai kanta na duƙe a ƙasa, sai kuka take yi gwanin ban tausayi. Damuwar da ke zuciyarta ya ƙara ninkuwa.

A ƙarshe Ya Mustapha ficewa yayi daga cikin falon ba tare da ya ƙara saurarenta ba. Allah sarki ƴan’uwa mata rabin jiki, Murja da Masrura kam sun fahimceta, rungumeta sukai suna rarrashinta da faɗa mata tausasan kalamai har sai da ta samu nutsuwa, ta daina kuka, sai sauke ajiyar zuciya akai-akai. Duk yadda Mustapha yake ta danna musu horn su fito ya sauke su gidan Aunty Binto ƙin fita suka yi, sai da suka tabbatar ta samu nutsuwa sannan suka tafi.

Ko da suka fice a gidan ta daɗe zaune inda suka barta, tunani take yi.
‘Tun da take satar fita ba tare da izinin mijinta ba me ta taɓa tsinta na alkhairi? Babu! idan ba ta manta ba sau uku ne kawai ta taɓa satar fita taci lafiya ba tare da asirinta ya tonu ba. Me yasa baza ta yiwa kanta faɗa ta zauna a cikakkiyar matar gida kamar yadda mijinta yake buƙata ba? Da farko dai da take amarya ba kasafai kullen ya cika damunta ba. Amma tunda Allah yasa mijin Fatima ya rasu, ta samu ƴancin zuwa duk inda take so kai tsaye, to wani sha’anin ita take faɗa mata, kuma ta biyo mata su tafi, ko ta faɗa mata mijinta bai bata izini ba haka za tai ta tunzurata tana kwaɗaita mata ababen burgewar da ke cikin inda take so su je.

Fatima, sai yanzu da ta nutsu ta gane tabbas Fatima tana ɗaya daga cikin wacce take taka muhimmiyar rawa gurin ƙara tunzura taurin kanta wajen bijire ma umarnin mijinta.

Ita daman Fatima tun tale-tale haka take, ba dai ki je gurinta da neman shawara kan daidai ko rashin daidai ta ba ki shawarar bin daidai ba, da farko kwance-kwance za tayi ta fahimci ina ne ra’ayinki ya fi karkata? in dai ta ga hankalinki ya fi son bin rashin dai dai ɗinnan to tabbas nan za ta ƙarfafeki da bi, a gurin Fatima babu wani babban laifi da istigfari ba ya kore shi, tana fa sane kuskure za a aikata, amma za ta zuga ki ki aikata sai ta ƙara miki da cewa bayan kinyi kiyi Istigfari. Allah mai gafara ne mai jin ƙai.

Duk cikin ƙawayensu su takwas da suka yi ƴanmatanci a lokaci ɗaya Fatima ta dame su ta shanye a wayau, saboda ta fi su shekaru nesa ba kusa ba. Amma da yake ita irin mai ƙaramin jikinnan ne sai suka taso kamar sa’anni. A cikinsu ma da yawansu sun fita girman jiki, ko ita ta fi Fatima tsawo da murjewa a jiki.

Da yake a ƙawance shekaru lamba ne kawai haka suke ta cakuɗeɗeniya tare da ita a matsayin ƙawa ta ƙud da ƙud, sadda suke tashen ƴanmatanci kasancewarsu ƴan unguwa ɗaya duk inda za suje tare suke zuwa, har wani kirari ake musu su biyun, idan aka ga Wata to tabbas Zara na tafe. Mutum mai nisan hankali da wayau ne kawai zai kalli su biyun kai tsaye a ce Fatima ta girme mata nesa ba kusa ba.’
Nannauyar ajiyar zuciya ta ja ta sauke, agogo ta kallah, ƙarfe biyar da rabi na yamma.

‘Yau asabar, tun jiya ya kamata Mukhtar ya dawo bai dawo ba, hmmm! Ya Allah ka kawo min komai da sauƙi don girman zatinka.’
Ta ƙarasa tunanin da addu’a, lumshe manyan idanunta tayi tai shiru, babu abinda take hasasowa sai irin bala’in da zai sauke mata idan ya dawo gidan, to ko zai dawo a wannan satin?
“Allah masani.”
Ta faɗa a fili.

Wayarta da yake ajiye a gefe ta ɗauka, lambar Fatima ta lalubo ta danna mata kira, lallai ya zama wajib ta bata labarin duk iftila’in da ya afka mata a dalilin fitar da ta tunzurata tayi ba tare da izinin mijinta ba. Sannan za tayi mata gargadi daga yau ko da wani abu ya faru a cikin ƙawayensu ko abokan arzukinsu kar ta kuskura ta sake faɗa mata, ita yanzu ta shiryu, ta tsallake manyan masifu biyu da ƙyar, baza ta afka cikin na uku tana ji tana gani ba.

Wayar tana fara ringing sai aka katse daga can ɓangaren, ita kuma aka rubuta mata User busy. Da sauri ta sake danna ma lambar kira ba tare da tunanin komai ba, a wannan karon sai ta ji Fatima tana waya daga can ɓangaren, jin haka sai ta katse kiran, ta san duk halin da ake ciki Fatima za ta biyo bayan kiranta idan ta gama wayar, yau kwanaki huɗu kenan cif basuyi waya ba.

Da yake ta yi sallar la’asar, sai kawai ta miƙe ta shige cikin ɗaki, kayan jikinta ta canza zuwa na zaman gida ta fara ƙalƙale gidan da ya ɗanyi ƙura a wasu guraren saboda rashinta a gidan.

Duk a ƙoƙarinta na son zama kamar yadda mijinta yake so har ranar sunan babyn da Auntynsu ta haifa ya zagayo bata leƙa ko ƙofar gida ba. Amma fa tsakani da Allah daurewa kawai tayi, ƙafafunta har wani ƙaiƙayi suka dinga yi mata. Wannan sunan sun ci mishi buri ita da ƴan’uwanta ba tun yanzu ba. Yanzu shi kenan duk ƴan’uwanta suna can suna shiga da fita a cikin ankon da ita da hannunta ta zaɓa a kasuwa ita tana nan gida? saboda zafin da zuciyarta tai tayi da yadda shaiɗan yake ta zuga ta ta fice, ta fita babu abinda zai faru, kawai sai ta shige ɗaki ta zauna a gefen gado ta fashe da kuka.

Tana wannan kukan Ya Mustapha ya kirata ga shi a ƙofar gida, cikin sauri ta share hawayenta ta wanke fuskarta, har kwalli ta zizara a idanunta don kawai kar ya gane tayi kuka.

Babban hijabinta na sallah ta zumbula da sauri ta fita tsakar gida ta buɗe mishi ƙofa ya shigo, ko da ta nemi ya shigo da motarsa ce mata yayi ba zama ya zo yi ba, ta ce ya shiga falonta ya ce nan tsakar gida ya isa.

Kanta ta saukar ƙasa, lokaci ɗaya wasu sabbin hawaye suka sake cicciko idanun amma sai tayi ƙoƙarin haɗiyesu, bata bari sun zubo ba, Har lokacin fushi yake da ita, ko da tai ta kiranshi don ta bashi haƙuri da alƙawarin baza ta sake ba ƙin ɗaga wayarta yayi.

“Kuka kike yi?”
Ya tambaye ta.

“A’a!”
Ta amsa da rawar murya.

Taɓe baki yayi ya koma gurin motarsa ya fito da wasu manyan ledoji biyu farare, shaƙe da kayayyaki a ciki. Yana shigowa kai tsaye ya miƙa mata, da cusasshiyar murya mare walwala ya ce
“Ga shi, Aunty Murja ta tilastani wai dole sai na kawo miki, girke-girke da soye-soyen da suka yi a gidan suna ne. Wai har naman ƙauri da aka rarraba kwanaki uku baya naki yana ciki.”

“Tam! Na gode. Allah ya raya mana Abdurrahman”
Tayi maganar a sanyaye.

Har ya kusa fita daga gidan sai ya juya da sauri, hannunta ɗaya ya kamo ya riƙe a cikin nashi. Da wani irin kasalar jiki ta ɗaga idanunta ta kalleshi, lokacin hawayen idanunta gaf suke da zubowa.
“Kiyi haƙuri ƙanwata.”
Ya faɗa a tausashe, sai ya cigaba da yi mata nasiha da salama a muryarsa.
“Ki kiyaye abinda mijinki ba ya so, sai Ubangiji ya zame miki ja gaba a cikin lamuranki. Kin manta fiyayyen Halitta SAW ya ce da ace za’a umarci ayiwa wani abin halitta sujada tabbas mace ce za’a umarta tayi ma mijinta? Ko kin manta kissar matar nan da aka aike mata mahaifinta ba shi da lafiya, saboda mijinta ba ya nan ta aika neman izini a gurin Manzon Allah SAW ya ce ta zauna tabi umarnin mijinta, bata je ba har uban ya mutu, a sanadiyyar haka ita da mahaifin suka samu aljannah. Kin manta?”

Da sauri ta girgiza kai tana matsan ƙwallah.

“To idan baki manta duk waɗannan da hadithan da suka kawo bayani kan girman miji ba me zai sa kiyi ta biye ma son zuciyarki kina saɓa ma umarnin mijinki? Duk jikanmu ƴan’uwanki mijinki ya fi girman haƙƙi a kanki fiye da mu, ke yau ko da iyayenmu na raye mijinki ya fi su girman haƙƙi a kanki. Don Allah Fareeda, don Annabi, daga wannan matsalar da kika samu a dalilin satar fita kar in ƙara ji, don Allah kar ki kuskura ki sake maimaita irin wannan kuskuren. Idan fita ya kama dole kuma ya hana ki, ban ɗaukewa kowa riga ba a cikin family, ko sha’anin waye ki kira ki bada uzurin baza ki sami zuwa ba. Kin gane?”

“Eh! Kayi hakuri. Bazan sake ba in Allah ya yarda. Don Allah kayi haƙuri Yayana”

Cikin ƙanƙanin lokaci suka shirya da ɗan’uwanta, sai ga su suna ƙyalƙyala dariya. Shi da ya ce bazai shiga ba ya daɗe a cikin falonta suna hira da dariya, cikin hikima irin tasu na maza yake ƙara nunar da ita hanyoyin da za ta bi su daidaita da mijinta. Ya faɗa mata kalaman kwantar da hankali masu yawa. Ta ji daɗin zuwansa ba kaɗan ba, sun rabu cikin farin ciki da ƙaunar juna. Sakayau take jin zuciyarta, duk wani damuwarta ta aje shi gefe ɗaya, ta fuskanci al’amuran rayuwarta, har a sallah take addu’ar Allah ya bata ikon daina abinda mijinta ba ya so, shaiɗanin da ke shiga cikin zuciyarta ya dinga uzzurata da son zuwa sha’ani Allah ya kawar mata da shi.

***

Sati biyun da Mukhtar ya shafe cif bai dawo ba ta wani fannin bai dameta ba, ciwukan jikinta sun warke sumul, kamar ma bata ji ba, kyakkyawan halittarta ya dawo tsaf, duk wannan kumburin baki, goshi, da shatin yatsun da suka kwanta ɓaro-ɓaro a kumatunta tas sun ɓace.

Kwatsam wata ranar alhamis da misalin ƙarfe biyar na yamma ba zato ba tsammani sai jiniyar motar Mukhtar ta ji daga can tsakar gida.

Allah sarki Fareeda, ita da kanta bata san ta yi kewarshi da yawa haka ba, a guje ta miƙe jikinta na rawa ta fice da sassarfa zuwa tsakar gidan, yana fitowa daga mota bayan ya gama daidaita fakin ta ƙarasa gurinsa da sassarfa ta rungumeshi.
“Oyoyo Mijin Fareeda.”
Ta faɗa da wani irin sanyi da ɗokin ganinsa a muryarta.

A yadda ya tsara ma zuciyarsa ko da ya iso gidan bazai shiga harkarta ba sam-sam, duk wani ƙwainane da iyayin da za tayi domin jan hankalinsa bazai kulata ba. Amma yanzu ya rasa dalilin da yasa ya kasa gwasaleta, bai san sa’adda ya mayar mata da martanin rungumar ba, ita da shi shiru sukai riƙe da juna suna sauke ajiyar zuciya akai-akai.

Ba ita kaɗai tayi kewarshi ba, shi kanshi yayi kewarta ba ɗan kaɗan ba. Ƙarfin hali da zaƙin sabuwar soyayyar da ya fara ne suka riƙe shi a can har tsawon wannan lokacin ba tare da ya waiwayota ba.

Ko yanzu babban maƙasudin dawowarshi ba don ita bane, don ya fuskanci al’amarin ƙarin aurenshi ne gadan-gadan. Da gaske ya shirya samarwa kanshi maslaha, a shekarunsa talatin da takwas bazai tsaya wata ƴa mace ƙwallin ƙwal tayi ta wahal da zuciyarsa ba. Ga irinta da waɗanda suka fi ta nan da yawa, kamar jamfa a jos! Da ƴan kuɗaɗensa a aljihu don haka gara ya karkata akalarsa zuwa wani guri ko zai samu nutsuwar zuciya, itama wacce zai ɗauko idan bai samu dalilan da suka jagorance shi zuwa gare ta ba zai koma wani ɓangaren ne. Kamar hula suke fa, zaiyi ta gwadawa ne yana cirewa har sai ya samu wacce ta shiga daidai da yanayin jikinsa da halayensa.

Kumatunsa ta shafa a hankali har zuwa kan laɓɓan bakinsa. Ɗan murmushi ta saki, ganin ya dawo daga duniyar tunanin da ya faɗa, a hankali ta sake shi, ta ɗan ja baya kaɗan.

Jakar hannunsa da sauran ledojin ta miƙa hannu za ta karɓa tana cewa
“Habeebi, barka da zuwa. Mu shiga daga ciki ka huta, ka sha hanya, ina roƙon Allah ya ƙara maka lafiya mijina da nisan kwana mijina, Allah ya ƙara tsare min kai.”

“Ameen”
Ya amsa haɗe da ɗan taɓe baki, ko kaɗan kalaman ba wai sun wani burgeshi bane, Fareeda mai ladabin kunama kenan, za ta bi ka luf luf sai ka fara sakankancewa da ita sai ta sakar maka ƙari. Tsaki ya ja ƙasa-ƙasa.

“Lafiya?”
Ta tambayeshi da mamaki jin yana tsaki, abinda bai cika yi ba, ko ita tayi sai yayi mata magana.

Bai ce komai ba ya nufi hanyar shiga ciki ya barta nan tsaye jikin motarsa. Har ya kama ƙofar falonsu zai shige sai ya waiga, ɗayan apartment ɗin da aka fara gini ba’a kammala ba yake ƙarewa kallo, an kai tsawon linta, anyi rafta, an buga kwano, har ƙofofi an saka. Abinda ya rage plasta ne da P.O.P sai tiles da jan wuta. Murmushi ya saki, yana ayyana da ya huta a darennan zai nemi masu aiki su lissafa mishi adadin kuɗaɗen da suke ganin ƙarasa ginin zai iya ci. Daga haka ya shige ciki ba tare da ya ƙara kallon inda take tsaye riƙe da kayayyaki a hannu ba.

Ko kafin tabi bayanshi zuwa ciki har ya faɗa banɗaki ya fara yin wanka, bai damu da jiran ta shigo ta haɗa mishi ruwan wanka ba.

Tsananin mamaki kawai sai ta riƙe baki, jikinta a sanyaye ta ajiye mishi jakarshi nan gefen gado, ledojin da taga kayan cefane sai ta wuce da su kicin.

A tsarin da tayi ba don ya dawo yau ba sam baza tayi girki da daddare ba, shayi da biredi tayi niyyar za ta sha ta kwanta barci.

Amma sanin da tayi mishi duk ranar da zai dawo bai cika sake jiki ya take ciki da abinci ba, da ya dawo yayi sallah da wanka zai nemi abinci ne.

Don haka ta yanke shawarar a gurguje ta dafa mishi indomie da busasshen kifi, tana cikin yanka albasa sai ya shiga kicin ɗin.

“Me kike ƙoƙarin yi Baby?”
Ya tambayeta yana kallon yadda take komai cikin hanzari.

“Abinci zan samar maka, ban rage komai na abincin rana ba. Kuma baka sanar min yau za ka dawo ba shi yasa ban shirya maka komai ba…”

“Kar ki damu, dawowar ba taki bace shi yasa baki sani ba. Zo, magana za muyi, sauri nake zan fita.”

Jikinta a sanyaye ta bi bayanshi zuwa falo, a maimakon ta zauna kusa da shi kamar yadda ta saba, sai kawai ta zauna gefe ɗaya a ƙasa kan kafet ta zauna, suna fuskantar juna.

“Kin tuna na daɗe ina neman transfer daga Kafancan zuwa nan cikin garin kaduna ko?”

“Eh na tuna”
Ta amsa da sanyin murya, idanunta a cikin nashi.

“Yauwa, to a wannan karon Allah ya nufa na sami transfer…”

“Alhamdulillahi ! Habeebee na taya mu murna, Allah mun gode maka. Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi.”
Ta faɗa da wani irin karaɗi na tsananin murna da farin ciki, saboda tsananin farin cikin samun abinda suka daɗe da fitar da rai har goshinta takai ƙasa tayi sujadar godiya ga Allah.

Duk wannan murnar da take yi hankalinsa ba shi a kanta, yana karanta saƙon da aka tura masa a waya ne yana sakin wani lallausan murmushi, har ta gama karaɗinta ta nutsu, ta dawo da hankalinta gare shi.
“Yauwa sai magana ta biyu, zan ƙara aure.”

Wuta ne ya ɗauke mata na wucin gadi, wani hazo-hazo ya taho da saurin gaske zai gitta ta idanunta da sauri ta rufe ido.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Ta ja salatin cikin wani irin murya mai rauni da miƙa wuya ga Allah maɗaukakin sarki. A hankali ta saukar da kanta ƙasa, zuciyarta sai wani irin bugu da tsallen baɗaken tashin hankali take yi, daƙyar da jiɓin goshi tayi ƙumajin cewa
“Allah ya sanya alkhairi.”

“Ameen thumma Ameen.”
Ya amsa cikin rashin damuwa da halin da ya ga ta shiga lokaci ɗaya.

Tsam ya miƙe da wayarsa a hannu zai fice, daman ya ɗau wankarsa cikin wata ɗanyar shadda getzner fara kar, sai ɗaukar idanu take yi. Har ya riƙe ƙofar falon sai ya waiga yana kallonta ya ce
“Baki tambaye ni yarinyar da zan aura ba?”

A hankali ta ɗaga idanu ta kalleshi, daƙyar ta iya fito da harshenta ta ɗan lashi laɓɓanta da ta ji sunyi mata wani irin bushewa kamar ta yini bata shafa musu mai ba.
“Ya shafe ni ne dole in san yarinyar…?”

“Ƙwarai kuwa! Ai tabbas ya kamata ki san wacce zan kawo miki gidannan a matsayin abokiyar zama. Ko da yake miye ma na wani kwana-kwana? abinda ba haramci za muyi ba sunnar ma’aiki za mu ɗabbaƙa, ba wata ba ce zan aura face ƙawarki Fatima, ko in ce aminiyarki…”

“Fatima? Fatima dai Mukhtar? Ita ta amince za ta aure ka…?”

“Da gudu ma, ke a banzan tunaninki akwai wata haɗaɗɗiyar mace da za ta ga sankacecen miji kamar Mukhtar ɗin Fareeda ta ce ba ta so?”

“Babu fa! Allah yasa alkhairi.”
Ta faɗa cikin wani irin matsanancin ƙarfin hali da juriya, daga zaunen da take tana ganin wani jiri da yake neman rufe mata idanu, tana gani Mukhtar ya sauke mata wani ƙatoton murmushi wanda a take ta fassara shi da murmushin ƙeta, ya fice daga falon sannan ya buga mata ƙofa, bugun da ya sauka har a cikin zuciyarta.

Lumshe idanu tayi a fili cikin wani irin mawuyacin hali take ta jan addu’ar
“Laa’ilaha illallul azeemul haleem. Laa’ilaha illallahu rabbul arshil azeem, laa’ilaha illallahu rabbus samawati, wa rabbul ardhi, wa rabbul arshil kareem.”
Daga zaunen da take ta dungura ƙasa kamar wacce ta tafi sujuda, amma ba sujada ta tafi yi ba, sumewa tayi.

<< Rabon A Yi 7Rabon A Yi 9 >>

1 thought on “Rabon A Yi 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.