Skip to content
Part 10 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

“Gashi nan Daada, ya fadi me yake ce mun a gabanki kiji, watakila ke kina da kalaman da zaki fada mishi ya fahimci wannan bashi bane lokacin da ya dace…”

Julde ya karasa maganar yana kallon Nawfal da yake zaune cikin kujerar da take kallon tashi da yanayin babu abinda zai canza ra’ayina kwance cikin idanuwan shi. Taurin kai ba bakon abu bane ba, asalima in za’a koma wasu shekaru baya, tabbas da yawan mutane zasu iya cewa ko kafar shi Nawfal bai kama a taurin kai ba, in harya saka ma ranshi yin abu to babu wanda ya isa ya sauya mishi ra’ayi.

“Idan kuskure ne kubarni, kuskure na ne, ni zanyi dana sani akan duk abinda zai biyo baya. Kunyi na ku bangaren, kun fada mun gaskiya nine dai ban dauka ba.”

Yakan fada duk idan an nemi hana shi abinda yayi niyya, shima din idan yana dan ganin kanka da gashi. Sai dai yau a karo na farko baya son ace taurin kai a ahalin sune, kar ace wannan ra’ayin rikau din jini yake bi. Saboda Nawfal ya dauko mishi abinda bai taba hangowa ba ko a tunani balle kuma yasan yanda zai shiryama daukar shi.

“Aure nake sonyi Daddy, ina so a daura kafin in koma.”

Kalaman Nawfal din suka da ke shi kamar wanda babbar mota tayi sama da shi tana sauke shi da wani irin yanayi da bayajin akwai kalaman da zasu kwatanta shi. Kallon Nawfal ya yi yana so yaga ko zolayar shi yake, sai yaga wani yanayi shimfide cikin idanuwan Nawfal din kafin ya dora zancen shi da.

“Tun a waya zan fada maka, sai na bari tunda zan zo bikin Adee, da na zo din ma ina neman ta inda zan fara fada maka ne…”

Yar dariya ce da Julde ba zaice ga ta inda ta fito ba ta kubce mishi, sosai yake kallon Nawfal.

“Shaye-shaye ka fara Bajjo?”

Idanuwan shi Nawfal ya saka cikin na Julde yana fadin,”Daddy…”

Wani numfashi Julde yaja yana saukewa, kwata-kwata ya rasa inda zai ajiye kalaman Nawfal balle ya yi tunani akan su harya sami kalaman furtawa

“Daddy karka ce inje inyi tunani, kar kace in sake dubawa, ko kace shekaru na sunyi karanci…”

Cewar Nawfal din shima yana fitar da numfashi kafin ya dora da,

“Watakila duk haka ne, amman ina son ta, ko yanzun, ko nan da wasu shekaru babu abinda zai canza, me yasa zamu jira wasu shekaru in muna da wannan tabbacin?”

Kallon shi kawai Julde yake, cikin tashin hankali yace,

“Baka da hankali ko Bajjo? Aure? Kasan meye aure? Yaushe ka fara karatun? Duka nawa kake da zaka rungumo maganar aure? Da me zaka rike ta? A ina zaka ajiye ta? Ko soyayyar ce ta hana kai da ita yin wannan tunanin?”

Kai Nawfal ya ke girgiza mi shi, ya bude baki zaiyi bayani Julde ya katse shi,

“Waye zai dauki yarinya ya baka? Kana fadamun kafin ka koma kake son a daura aure? Sati biyu kace zakayi, yau kwanan ka shidda, a cikin sauran kwanakin za’ayi maganar aure har a daura… Kaga Bajjo baka taba batamun rai ba kar yau ya zama na farko.”

Julde ya karasa maganar yana ma Nawfal din wani irin kallo mai cike da tarin ma’anoni. Saboda tun tasowar Nawfal yana da manyance, yaune rana ta farko daya fara ganin haukan yaron, rashin hankali na sa’annin shi da kuruciya duk Nawfal baiyi ba, duk da a baya yana danganta hakan da rashin iyayen shi a kusa, duk da yana iya kokarin ganin ya bashi duk wata kulawa da zai bukata gwargwadon yanda lokaci ya ara musu.

“Zasu bani, sunce zasu bani, kawai zaka ga Kawunta da yake Abuja ne, saboda suna son sanin ina da dangi a Nigeria, ba wani abu za’a kai ba banda sadaki…”

Kallon da Julde yayi mishi wannan karin na kashedi ne,

“Bajjo…”

Haka ma yanda ya kira sunan shi da bai hana shi ci gaba da magana ba

“Ina aiki, kudin bamai yawa bane ba, saboda yanayin karatu ba wasu awanni nake yi ba, itama kuma tanayi, duka karatu muke, zamu gina kalar rayuwar da muke so a tare… Daddy kar kace banda hankali, karka ja layi akan abinda addini bai haramta mun ba.”

Mikewa Julde yayi.

“Daddy…”

Nawfal ya kira muryar shi na karyewa.

“Ka taso muje.”

Yanda ya yi maganar ne yasa Nawfal din bai mishi musu ba ya bi bayan shi, babu wanda ya ke magana a motar har suka karasa gidan Daada, ko da ma suka shiga banda sallama babu abinda Nawfal ya kara cewa ya nemi kujera mai zaman mutum daya ya zauna. Yana kallon yanda Julde ya amsa tambayar .

“Julde, lafiya dai ko?”

Da Daada tayi mishi, da kuma yanda ta kalle shi bayan Julde ya gama magana.

“Idan kaga ban aure ka ba, matsalar daga bangaren ka ne. Za su tambayeni idan ina son ka, idan aure ne abinda nake sonyi a yanzun, zasu bani shawara bayan jin amsata, daga karshe zabi na zasu yi amfani da shi. Haka rayuwar a halina take, shekaru na sha takwas, sun yarda ina da ‘yan cin da hankalin sanin me ya dace da ni.”

Maganganun Murjanatu suka dawo mishi, da gaske matsalar daga bangaren shi ne, shakkun da yake cikin idanuwan Julde kawai ya isa ya tabbatar mishi da haka, bai kuma son kalmomin da zai yi amfani da su wajen gamsar da shi ba. Bayan tsayawa da kafafuwan shi, aure ne abu na biyu a cikin jerin abubuwan da yake son yi, saboda yana son samun nashi ahalin, wanda duk ruwa duk rana yasan zasu kasance da shi. Ta ina zai fara fadawa Juldea da Daada cewa babban tsoron shi a duniya shine kadaici. Shine ranar da duk zai neme su a duniyar shi ya rasa?

Yanda duk yake son ace ya kira su da na shi shi kadai kaunar su rabata yake da sauran mutane, yana son abinda zai kira na shi, yana bukatar a kaunace shi, kaunar da ba zaiji tsoron rabata da kowa ba balle har azo a ture shi daga dan inda yake a tsugunne.

“Idan na tambayeka me ka dawo yi zaka ce mun bikin Adee, kana da naci Nawfal, bana kaunar ganin ka kusa da ahalina, in zan iya rabasu da kai ba karamin dadi zanji ba, amman ba zan taba daina kokarin hakan ba…”

Maganganun Saratu ne suka kara mishi karfin gwiwar tunkarar Julde da tun bayan bikin Adee ya ke juyayin yanda zai same shi. Yanda duk yake kaunar su yana da tabbacin soyayyar da take tsakanin su da Saratu ta girmi wannan, kauna ce da ba zai kwatanta dorata a sikeli da tashi ba sam.

“Aure zanyi Daada…”

Ya yi maganar muryar shi na fitowa da wani irin sanyi yana sa Daada jin kamar ya juye mata bokitin ruwan kankara kafin wani irin zafi ya maye gurbin sanyin da ya ratsa ta, jikinta gabaki daya ya dauki dumi, zuciyarta na soma wani irin tsalle-tsalle kamar tana neman sabon wajen zama a sauran jikinta, yanayin bugawar da take har cikin idanuwanta da take kallon Nawfal da su take jin karfin shi.

“Kema kina tunanin banda hankalin ko Daada? Wannan ba shi bane lokacin daya kamata in zo da maganar aure ba…”

Nawfal ya fadi yana dora da,

“Dan Allah idan kina da dalili ya sha bamban dana Daddy…”

Kallon shi dai takeyi zuciyarta na cigaba da dokawa kamar zata fito waje, dalilinta ko daya bashi da alaka da duka tunanin su, dalilinta bata san ta inda zata fara furta shi ba.

“Kina jin shi ko Daada, kice wani abu.”

Julde ya fadi yana kallonta, da idanuwan shi ya ke rokonta da ta taimaka mishi don yanayin Nawfal din kawai ya tabbatar mishi da cewa bawai ya fada mishi bane saboda yana neman izini, goyon baya yake so kawai, amman ko bai amince ba da wahala idan maganar auren nan ba zata zama abu na farko da zai haddasa wata tsaga a alakar su ba.

“Yarinyar yar ina ce?”

Daada ta tambaya tana saka Nawfal sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba.

“Murjanatu… Sunan ta Murjanatu, duka iyayenta suna zaune ne acan kasar da nake karatu, amman asalin su yan garin Adamawa ne, dangin su da yawa suna can, wasu suna zaune a Abuja, suma aiki ne ya kai babanta can, yayyen ta guda biyu duk suna nan Abuja suma…ni ba zama zanyi acan ba Daada, zan dawo, zamu dawo tare idan muka gama karatun mu.”

Ya karasa maganar yana kallon Julde da har lokacin akwai shakku cikin idanuwan shi.

“Daada kiyi magana da yaron nan, da gaske fa yakeyi…”

Baki Daada ta bude sallamar Madina ta katse mata maganar ta, Nawfal ne ya amsa.

“Hamma… Daddy.”

Cewar Madina cikin sigar gaisuwa.

“Zafi nake ji wallahi.”

Ta furta tana wucewa nufar hanyar dakinta, sai lokacin suka ga Salim da ya yi sallama cikin budaddiyar muryar shi, daga makaranta ya wuce yaje ya dauko Madina saboda tunaninta ya hana shi sukuni har a aji, motar shi ta fara tsaitsayawa, da kyar ya iya samun waje gefen titi ya yi parking dinta ya kira mai mishi gyara. Sai da yazo ya bashi mukullin tukunna suka tako shi da Madina tunda sun kusa gida, tun a hanya take ce mishi zafi take ji tana shiga gida zata fara watsa ruwa kafin tayi shirin islamiyya. Motar Daddy daya gani ne a wannan lokacin a gidan Daada yasa shi yanken hukuncin shiga dan yaga ko lafiya, in yaso sai su wuce da Daddy ko bai mayar da shi makaranta ba ya rage mishi hanya.

Kallon su yayi yana zare takalman shi hadi da shiga cikin dakin, yanayin su bai nuna kome suke tattaunawa mai dadi bane ba.

“Ina wuni.”

Ya furta kamar wanda akayiwa dole yana kallon Daada.

“Daddy…”

Ya kira, duk yanayin da Nawfal ya ke ciki bai hana shi kallon Salim ba, daga shi har Madina suna son kiran sunan mutum a maimakon gaisuwa. Sai dai kafin Daddy ya yi magana Salim din ya juya, baya son hayaniya. Yana da tabbacin kome suke tattaunawa bai shafe shi ba, baya son sani balle kuma suyi tunanin saka shi ciki.

“Ina zaka je?”

Julde ya tambaya, dan juyawa Salim ya yi yana amsawa da.

“Naga kuna magana ne…”

Kamar hakan kawai hujja ce da zai bar musu gidan.

“Ka dawo ka zauna ayi maganar da kai.”

Dan runtsa idanuwan shi yayi yana bude su, dole dai sai sun tsoma shi cikin zancen nan da ya san bai shafe shi ba ko kadan. A nutse ya taka yana samun hannun kujera ya zauna a kai

“Aure Nawfal yake son yi, so yake a daura kafin ya koma.”

Kallon Nawfal din Salim yayi, sai dai a nashi idanuwan babu komai sai mamaki, saboda aure baya cikin tsarin abubuwan da yake hango rayuwar shi da shi, hayaniyar nan ba zai iya ba. Amman hakan baya nufin dan wani yana so yayi sai ace kar yayi. Adee ma gashi nan tayi, kuma har ran shi ya yi farin ciki da auren nata

“Kana ganin auren ne abinda kake son yi a wannan matakin na rayuwar ka?”

Salim ya tambaya, kai Nawfal ya jinjina mishi.

“Karka amsa ni idan kana da shakku, ka tabbata?”

Kai Nawfal ya sake dagawa, girar da Salim ya daga mishi yasa shi cewa,

“Ban fada ma Daddy ba sai da na tabbata, shekara daya ina neman tabbaci a kowacce rana…”

Mikewa Salim yayi ya kalli Daddy.

“Nenne tace sanda kukayi aure da kadan ka girmi Bajjo, karkayi amfani da shekarun shi a matsayin hujja Daddy, in baka da dalili mai karfi karku hana shi…”

Numfasawa ya yi saboda kan shi harya fara sarawa da maganar da ya ke yi.

“Ku barshi yayi auren shi…”

Wanda duk yazo da maganar aure a cikin kannan na shi zasu samu dukkan goyon bayan shi, zai yi duk wani abu da zai iya wajen ganin basu fada irin rayuwar da ya ke ciki ba.

“Aure zai hanaka biye-biye, zai nutsar da kai waje daya.”

Haka ya ji wani a ajin su ya fada. Yana da yakinin Nawfal na da dalili mai karfi da yasa yake sonyin aure a wannan matakin na rayuwar shi, kasar yabari don karatu, Allah kadai yasan kalar mutanen da suke zagaye da rayuwar shi.

“Ka tabbata ba kayi dana sanin zabin nan ba Bajjo.”

Ya fadi yana saka Nawfal din yin murmushi,

“Hamma…”

Hannu ya daga mishi, shi duk irin wannan abubuwan baya son su.

“I love you.”

Nawfal ya fadi yana fadada murmushin shi ganin yanda Salim din ya bata fuska yana taku biyu da nufin karasawa kan kujerar da Nawfal ya ke yana saka shi mikewa babu shiri, kallon shi Salim ya yi cike da kashedi yana ficewa juyawa ya fice daga dakin.

Kamar bai fadu maganganun da zasu canza komai ba.

Maganganun da zasu zama silar faruwar komai.

Kwallar da Daada taji ta fara tarar mata cikin idanuwa tayi saurin saka hannuwa ta dauke su kafin ma wani ya kula. Shikenan abinda ta gina a cikin zuciyarta ya rushe, hangenta ya datse lokaci daya. Wata ta maye wajen da take fatan Madina ce zata zauna a wajen. Yanda kaddara take wasan kura da rayuwarsu a kowanne juye na karya mata zuciya. Ba dan kar tayi sabo ba da ta tambayi dalilin da yasa ko sau daya rayuwa ba zata tafi kan tsarinta ba.

“Hamma ma yace karku ce a’a, kaji Daddy, dan Allah karka ce a’a…”

Nawfal ya katse ma Daada tunanin da take yana sata kallon Julde da fuskar shi take dauke da yanayin rasa tudun dafawa.

“Daada…”

Ya soma ta girgiza mishi kai.

“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, kaje kaga dangin yarinyar kafin ka yanke wani hukunci…”

Murmushin da Nawfal yayi bayan ya dawo inda yake ya zauna na saka zuciyar Daada kara tsinkewa saboda kamannin shi da Bukar da suka kara fitowa fili. Kafin wani ya sake cewa wani abu Madina da ta fito cikin shigar islamiyya ta riga su da fadin.

“Hamma kana nan har in dawo amman ko?”

Kai Nawfal ya girgiza mata.

“Zamu dan fita da Hamma anjima, kilan in dawo dai, me zaki ajiye mun?”

Dariya ta yi.

“Zan dafa maka kifi.”

Kai Nawfal ya jinjina.

“Zan dawo.”

Dunkule hannunta tayi tana daga mishi babban dan yatsan ta alamar hakan yayi mata.

“Daddy na tafi…Daada sai na dawo.”

Binta da kallo Daada tayi, Julde ne ma ya iya cewa.

“A dawo lafiya.”

Wani abune Daada taji yayi mata tsaye a kirjinta, lokaci daya duk wani tunani da takeyi akan goben Madina ya sauya. Ta ina zata fara yanzun?

“Daada yanzun duka Nawfal nawa yake?”

Julde yace cikin nauyin murya, ko shi da Salim yake magana akan auren wuri da yayi, bawai zabi aka bashi ba a lokacin, kawai hadasu akayi da Saratu.

“Zamanin mu da nasu ba daya bane ba.”

Murmushi Daada tayi kirjinta ya yi mata nauyi, hakan yasa Nawfal mikewa yana nufar dakin daya kan kwana ciki duk idan yazo gidan dan ya basu damar yin magana.

“Shisa zaka barshi yayi auren shi, zamanin ba daya bane ba…kar kaja maganar nan da shi Julde…ka kyale shi tunda ba wani abu marar kyau bane ya dauko.”

Wani irin numfashi Julde ya sauke, ranshi a jagule yake jin shi, a saman bukatar ta da fatanta kasancewar Bajjo a cikin su yafi muhimmanci, hana shi aure don bukatar ranta ta cika ba zai zama sanadin da zata rasa shi gabaki daya ba. Idan har jinin Datti ne yake yawo a jikin Nawfal to tasan wannan maganar auren ba izinin su yake nema ba, goyon bayan su kawai ya ke bukata, ko sun yarda ko basu yarda ba ba zai canza komai ba.

“Karka ja maganar nan da shi…”

Ta kara jaddadawa, yanayin muryarta nasa wani abu tsirgama Julde saboda yasan inda tunaninta yake son kaita.

“Ai shikenan…”

Ya furta yana sauke ajiyar zuciya

“Amman ba zai zauna kasar nan ba, yana gama makarantar nan dawowa zaiyi.”

Dan murmushin karfin hali Daada tayi.

“Daman yace ba zama zaiyi ba.”

Sai dai ita kanta ta maimaita kalaman ne ba dan ta aminta da su gaba ki daya ba.

“Zan dawo Daada.”

Taji wannan kalaman har sun isheta a tsayin rayuwar ta, sai dai a duk mutanen da suka furta mata su Nawfal ne na farko daya fara cikawa, shakkun da take da shi kan kalaman ya dade da kafa rassa a cikin zuciyarta, dan ya dawo yanzun baya nufin in ya koma zai sake dawowa, wannan ma tagan shi akan Yelwa. Da zatayi fata ne, fatan kar ya zamana Nawfal bai cika alkawarin shi na zai dawo ba. Sai dai numfashi kawai ta sauke

Kowanne rai da nashi kaddarar, yau ma ta sake ganin wannan kaddarar da take tunanin ta shiga tsakanin Nawfal da Madina kamar yanda tayi fata, shisa ba zata sake wani fatan ba a yanzun, idan kaddarar Nawfal ta hada da dawowa zai dawo, idan bata hada ba sai dai ta sake rungumar kaddara a duk yanda tazo mata a karo na ba adadi kenan. Fatanta bashi da tasirin canza komai.

*****

Wayar shi Nawfal ya mika mishi, karba Khalid din yayi.

“Na fara gajiya fa…ni bana ma amfani da wayata yanda nake so saboda kun isheni kai da ita…ka siyi layi Malam.”

Dariya Nawfal ya yi.

“Kai Hamma, yaushe muke isarka din? In ba irin wannan lokacin ba ai bama waya… Layin zai zama asara tunda ba dadewa zanyi ba. Haka zakayi ta hakuri da mu.”

Kai kawai Khalid ya ke girgiza, ya kalli inda ya ajiye kayan wankin da aka kawo mishi da yamma.

“Na kwashe na shirya maka duka wardrobe dinne ma.”

Kallon shi Khalid ya yi, yana sake kallon yanda dakin ya samu kulawa ta daban tun zuwan Nawfal din, bawai shara bace bayayi, yana share dakin kusan kullum, kawai dai bashida lokacin mayar da wasu abubuwan wajen daya dauke su. Nawfal kuma ya kasance cikin jerin mutanen da suke son ganin komai a tsare, har litattafan shi idan ka duba jakar shi ta makaranta a wani irin tsare suke, bi da bi. Inda yake ajiye fensiran shi da biro ma daban ne. Ko yaya ka taba mishi kaya yana dawowa wajen zai nufa ya gyara abin shi yanda yake son ganin shi.

Wajen wardrobe din Khalid ya karasa ya bude yana ganin yanda Nawfal ya shirya komai, harta kananun wandunan shi layi daban ya saka su. Sai yaji kamar ace karya taba kayan, ya hargitsa shirin nan.

“Aure zanyi Hamma.”

Nawfal ya fada cikin sanyin murya, wardrobe din Khalid ya rufe.

“Na sani, kowa ma ai aure zaiyi idan lokaci yayi, ko dan ka yi budurwa sai ba zamu huta ba?”

Kallon shi Nawfal ya yi.

“Aure zanyi Hamma…”

Ya sake maimaitawa yana sa Khalid kallon shi.

“Ina nufin kafin in koma za’a daura, aure zanyi kafin in koma.”

Sosai Khalid ya ke kallon shi wannan Karin.

“Nasan ya kamata in fada maka tunda na dawo, amman na bari ne in fadama Daddy tukunna, shi ya kamata ya fara sani kafin kowa.”

Kai Khalid ya jinjina.

“Allah ya sa alkhairi.”

Ya furta yana rasa abinda ya yi niyyar yi kafin Nawfal din ya sauke mishi wannan zancen saman kai

“Hamma…”

Nawfal ya kira, amman hankalin Khalid din ya ki komawa kan shi.

“Hamma mana…”

Waje Khalid ya samu gefen gadon ya zauna yana daukar wasu dakika kafin ya daga kai ya kalli Nawfal.

“Me yasa? Ka fahimtar dani yanda zangane.”

Saboda har a ranshi yana son gane dalilin da zaisa Nawfal yanke wannan babban hukuncin da yake ganin baiyi hankalin da zaiyi shi ba, duk da tsiran da yake tsakanin su bawani mai yawa bane ba. Ya yi girman da yasan duk inda za’ayi magana ta aure ba karamin abu bane ba.

“Ni kadai ne Hamma, tun banda hankalin mutanen daya kamata su tsaya tare dani suka fara watsar dani, ina da ku na sani, ina jin kamar bai kamata ba da nace maka ni kadai ne…”

Kallon shin dai Khalid yake yi.

“Ina kaunar ku, ina kaunar ku fiye da yanda zan fada, nasan kuna kaunata, da yawa, ba zan kira ku nawa ni kadai ba, ba zan kiraka nawa ni kadai ba, ina rabaka da mutane da yawa a yanzun, lokaci zaizo da zan sake rabaka da wata… Ina son abinda zan kira nawa.”

Wani sauti ne ya kwace ma Khalid din da yake tsakanin dariya da wani yanayi da bashi da suna.

“Ita din ba zaka rabata da wani ba?”

Ya tambaya yana jin wani abu ya tokare mishi makoshi.

“Ba kaman ku ba…”

Kokarin hadiye abin da yake a makoshin shi Khalid yake yi, maganganun Nawfal sun mishi zafin da ya kasa fahimtar su.

“Tana da iyaye da yan uwan da ta taso da kaunar su kafin taka, ka fadamun bambancin da yake tsakanin ta da mu… Kana so ka fadamun mu ba zamu taba zama naka kai kadai ba, amman ita zata iya zama? Mu muna da wani lokaci na barin rayuwar ka… Ko dan kaine kasa lokacin barin mu saboda ka samu wadda zaka kira taka?”

Tunda ya fara magana Nawfal yake girgiza mishi kai.

“Idan baka fahimce ni ba babu wanda zai fahimce ni Hamma, dan Allah karka fassara kalamai na idan baka fahimta ba, karkayi mun haka.”

Nawfal ya karasa muryar shi na karyewa.

“Ka fahimtar dani Bajjo…”

Numfashi Nawfal ya sauke zuciyar shi na rawa.

“Idan baka so zan hakura, zan bar maganar nan… “

Dan tunda ya yanke hukunci bai dauka akwai wani dalili da wani zai bashi ya sauya mishi ra’ayi ba. Yasan Khalid na da muhimmanci a wajen shi, bai taba tsayawa ya auna girman muhimmancin ba sai yanzun, da a karo na farko tun haduwar shi da Murjanatu ya ji zai iya barinta idan har zata zama silar samun matsala tsakanin shi da Khalid din.

“Babu wani abu a yar duniyar nan tawa da yake da muhimmancin alakar da take tsakanin mu.”

Cewar Nawfal yana saka Khalid jin kafafuwan shi sunyi sanyin da in ba’a zaune yake ba zasu kasa daukar shi, yaja iska ta bakin shi yana fitarwa yafi a kirga kafin ya samu natsuwar fadin.

“Ka kalleni Bajjo, lokaci daya nake da shi na barin rayuwar ka, lokacin da ba rayuwar ka bace kawai abinda zan bari, duniyar ce gabaki daya…ba kai kadai bane ba, duk tunanin da yake fada maka haka ka karya ta shi, idan kana jin baka da kowa kana da ni, kana jina ko?”

Kai kawai Nawfal ya iya daga mishi.

“Idan aure ne zabin da kayi ni banda matsala da hakan, kawai ina so kasan ba abu bane da zaka zaba yanzun ka canza anjima, rayuwar yarinyar mutane ce akan layi Nawfal.”

Khalid ya karasa da kiran asalin sunan shi dan ya san maganar da yake na da muhimmanci.

“Bana jin zan iya ba mai shekarun ka ‘ya ta Bajjo, ba kuma zan daina ganin wautar mutumin nan ba…kadaici kowa yakan ji shi lokaci zuwa lokaci, karya zama dalilin da kawai zaka aure ta, ka hanga shekaru masu zuwa, a cikin shekarun ka duba hali na rashin tabbas, hali na rashin lafiya, ka duba yiwuwar jin dadi da rashin shi, kana ganin kanka a tare da ita a duka yanayoyin?”

Numfashi Nawfal ya sauke, kalaman Khalid din na ratsa zuciyar shi.

“Idan ka shiga cikin auren ba zaka iya fita da saurin da ka shige shi ba… Ba zaka iya ba…Bajjo wasan nan ba da rayuwarka kawai zakayi shi ba harda ta Murjanatu da duka ahalinta… Karka fara abinda ba zaka iya karasawa ba…”

Cikin idanuwa Nawfal ya kalli Khalid din.

“Ina son ta.”

Ya amsa.

“Soyayya kawai ta yi kadan.”

Idan Nawfal bai sani ba, shiya sani, wasu zasu karyata ana ganin soyayya kwance a idanuwan mutane, idan baiga soyayyar Julde a idanuwan Saratu ba shima zai iya karyatawa, amman bata hana su samun matsalar da suke tunanin baya kula ba, suna fada ko da baisan me yake hada su ba, sosai suke yawan yin fada yana kula da hakan. Da soyayya ta isa da wadda Nannar shi take ma Daddy ta hana musu samun matsala.

“Bansan sauran abubuwan ba Hamma, amman zamu neme su a tare, shine kawai alkawarin da zan iya a yanzun…”

Kai Khalid ya jinjina.

“Aure zakayi Bajjo, aure zakayi.”

Khalid ya ke fadi wata dariyar mamaki da tsoron wannan babban matakin da rayuwa ta kawo dan uwan shi na kwace mishi, shima dariya Nawfal ya yi, tsoron da yake gani a fuskar Khalid din na taba shi, a karo na farko shima matakin na bashi tsoro, sai dai tare da tsoron babu shakku ko kadan.

Rai da kaddara

Murjanatu na daya daga cikin kaddarorin shi.

Tana daya daga cikin hasken da zai yaye wani bangare na duhun da yake bibiyar rayuwar shi yana jiran cikar lokaci.

<< Rai Da Kaddara 9Rai Da Kaddara 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×