Skip to content
Part 35 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Da akace komai na da lokacin shi, a cikin lissafin mutuwa, aure, haihuwa da arziki sune sama. Komai sai yabi bayansu har suna danne wasu abubuwan, a shafuka na kwakwalwar Julde yanda lokaci ya kasance a bangarenshi saiya sha shi tunanin ba zai taba nuna masa karfin ikon da Allah ya bashi ba. Ba zai cika akan shi ba, cikar da ta fara da bankado sirrikan da yake boyewa a wajen Saratu a wayewar safiyar da ta gaji da tashin shi don yin sallar asuba har gari ya waye. Ya fito tsakar gida ya sameta da tsohon cikin da yake jikinta, ta daga ido tana kallon shi, yanajin yanda take yawatawa da idanuwan a jikin shi kafin ta tsayar dashi akan wuyan shi

“Jambakin waye a wuyanka Julde?”

Ta jefe shi da tambayar da ta sakashi saurin kai hannu ya taba wuyan, rashin gaskiyar shi na nunawa har kan fuskar shi. Ranar na bude musu wani babi na tashin hankalin da bai taba hangowa ba. Saratu na sakashi raina zafin zuciyar da yake tunanin yana da ita. Tana nuna mishi daga jikin Datti ya fito, amman a halayen shi bai dauki komai ba. A tsakiyar tashin hankalin ne takai mishi wata damka da yaga ta neman taimako ce a cikin idanuwanta

“Bayana, bayana ya karye Julde.”

Ta fadi tana durkusawa, su duka abin sai ya zame musu bako, sai da yaga numfashinta na barazanar barinta tukunna ya samu ya kwace daga rikon da tayi masa yana rugawa gidansu ya kira Dije da ko mayafi bata nema ba tabi bayanshi. Haka aka wuni, dare ya batar da hasken rana, duhu na mamaye ko’ina, amman nakuda Saratu takeyi babu alamar zata tsagaita mata. Yanayin da ya daga hankalin kowa musamman Julde da yake ganin kamar laifin shine. Haka kawai sai Hammadi yake ta fado masa a rai, da yajuyo wani nishi da Saratu tayi a tsakiyar dare kamar ana zare mata rai sai da zuciyarshi ta tsinke.

“Daman watan haihuwarta ne?”

Wata mata da aka kira ta tambaya, yanajin Dije ta amsa da.

“Akwai sauran satika uku kafin watan ma ya tsaya.”

Yana tsaye a tsakar gidan da yake mamaye da duhu, baka ganin komai sai taurari da sukayiwa sama ado suna dishe hasken watan daya fara nuna alamar bankwana don ya ba wani hanya, ya tsinkayi muryar Yelwa da baiji shigowarta ba.

“Hamma har yanzun shiru?”

Ta tambayeshi, juyawa yayi, hasken fitilar dake hannunta na shigar masa ido, sai yaji kanshi ya sara, bayan gajiya, zullumi da yunwa akwai rashin bacci daya hade masa tare da komai. Da Saratu ta fada masa tana tunanin akwai ciki a jikinta.

“Allah ya saukeki lafiya.”

Ya furta batare da yasan me yaji ba, haka da cikin ya fara nunawa a jikinta. Randa ya motsa  suna zaune ta kama hannunshi da sauri tana dorawa akan cikinta, wannan karin motsin na faruwa kamar a cikin jikinshi. Yaji zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa tare da motsin abinda yake cikinta. Yanayine da babu kalaman da zasu misalta shi, idan akwai ta ina zai fara? Ta ina zai fara cewa Saratu bata taba saka zuciyarshi ta motsa ba, amman daga ranar dayaji motsin abinda yake cikinta idan ya kalleta sai ya tsinci idanuwanshi da saukowa dai-dai cikinta, waje daya da ya saka zuciyarshi motsawa a tare da ita.

Cikin kanshi kalaman basu da wata ma’ana ko a wajenshi, ya zai fara furtasu har wani yaji? Waye zai fahimta? A wajen iyayen shi ya fara ganin aure, yaga menene aure, Hammadi saiya nuna masa aure a wajen kowa da yanda kowa ya dauke shi ya bambanta. Asalin ma’ana ta aure ta wuce hasashe, ta kuma wuce a kwatanta maka. Gashi a cikin aure, nashi kuma ya bambanta da duka wanda ya gani. A tsakanin fadan Datti, akwai fahimta ta Dije da kuma hakurinta da yake rike da igiyoyin aurensu, idan ka ajiye duka wannan a gefe suna hira da juna, bai taba ganinsu a tare sun rasa abin cewa juna ba. Ko da fadane kuwa zasuyi, shirun da yake cikin zamantakewar su bashi da yawa.

Amman yaune fada na farko da sukayi da Saratu tunda sukayi aure. Shiru yafi komai yawa a zamansu, duk da inya koma yaci abinci ya sake ficewa sai tayi bacci yake komawa wasu ranakun, wasu ranakun kuma baya dawowar ne da wuri saita fara bacci, inda Allah ya soshi ma bata da nauyin bacci, inda duk zai kwankwasa gidan sau daya zuwa biyu zaiji takun tafiyarta tazo ta bude masa. Bata taba masa magana akan dadewar da yayi ba kamar yanda bata taba tambayar shi inda zashi ba idan ya gama cin abincin dare. Wani abu da yake masa dadi a tare da ita.

Tana kokari, da yawan lokutta Saratu na kokarin jan shi da hira, ko ta bashi labari, amman idan ya gama amsa mata, saiya duba cikin kanshi yaga babu wani labari daya da yake dashi wanda zata so taji. Mutanen da zai kira da abokai yanzun hirarrakinsu duka akan matan da suke bine ko wanda idanuwansu yake kai. Labaraine da yasan ba zata so taji ba, haka shiru zai sake samun wajen zama a tare dasu.

“Zuciyata sai bugawa takeyi Hamma.”

Yelwa ta katse masa tunanin da yake, sosai ya kalleta, tayi wata irin rama kamar abincin duk da zai shiga cikinta baya samun nutsuwar da zai yawata har ya samu wajen zama. Gabaki daya kamar ba kanwarshi ba, idanuwanta kamar anyi mata musanyarsu, akwai wani kyalli da yake cikinsu ada da yanzun babu shi. Julde baisan ko shi kadai yake ganin haka ba, idan tayi dariya sai sautin ya dirar masa daban, tun jinyar da tayi bayan rabata da Kabiru bata dawo dai-dai ba, jinyar da kowa ya fitar da rai da tashinta, dan lokacin ta tabbatar masa da idan kaji ana cewa maza dauriya suke da ita to lallai abinda zai fito da hawayensu ne bai faru ba.

“Baba dan Allah kabarta ta auri Kabirun, idan akan shi take jinyar nan kabarta ta aure shi.”

Ya roki Datti a lokacin, sai dai ya kalle shi, wani kallo daya ja layi a tsakanin su, kafin kalaman shi su saka layin yin kasa yana bayyanar da wani fili mai zurfin gaske da Julde baya tunanin zai tsallaku a wajen shi harya samu Dattin su sake zama bangare daya.

“Gara in binneta da in dauketa in ba yaron nan.”

Baice komai ba, ya mike, ya tafi yana barin Dattin inda ya same shi. Sai dai sanda duk zai ganshi sai kalaman sun dawo masa da wani yanayi da baisan ya zai fassara shi ba. Yelwa ta tashi, amman ya kasa daina jin kalaman sun dawo masa duk idan ya kalli Datti, da duk rana kuma da yanda yake jin suna kara yiwa juna nisa duk da kusancin da suke dashi na mahaifi da kuma da. A yanda kalaman da zasu cewa junansu bayan gaisuwa da maganar kasuwanci suke musu karanci yake kara jin da gaske nisa suke yiwa juna, nisan da baisan ya zai tsayar dashi ba.

“Me yasa kika boyemun Kabiru?”

Ya tambayi Yelwa, yana ganin murmushin da tayi da yasa kirjinshi zafi.

“Duka ya wuce ai Hamma, ya zama tarihi.”

Numfashi yaja yana fitarwa.

“Na so in sani.”

Cikin ido ta kalle shi

“Zaka iya canza ra’ayin Baba?”

Sai da ya juya maganar yanajin tasirinta har cikin jikinshi tukunna ya girgiza mata kai, ya bude baki ta rigashi ta hanyar canza akalar hirar. Bai sake daga mata zancen Kabiru ba har yau, yana dai nuna mata cewar idan tana son maganar kofar hakan a bude take a wajenshi. Ya bata tazarar da take bukata tayi jinyar zuciyarta harta warke kafin ya tambayeta ya soyayya take saboda yana son sani. Daga bakin Yelwa da tayi soyayyar da take da tasirin canzata har haka.

“Nima tawa zuciyar…”

Ya bata amsa yanzun.

“Ba abinda zamu iyayi sai dai muyita jira ko?”

Kai ya daga mata a hankali, da bangon wajen suka jingina suna jiran, kowa da tunanin da yakeyi. Bata haihu ba sai bayan asuba inda aka fito masa da jaririn da aka saka a hannun shi, ya kalle shi yana jin wata irin kauna da bai taba sanin akwai irinta ba a cikin duniya ta cika kirjin shi. Dan shi, dan shi na farko ya rike a hannun shi, dan da bai hango samun shi a kusa haka ba.

“Salim”

Sunan ya gifta cikin kanshi, sunane da yaji an kira wani yaro a cikin Kano. Sai sunan yayi masa dadi, kamar yanda bai hango samun yaro nan kusa ba, haka bai hango sunan zai zame masa mai muhimmanci har haka ba. Ranar ya kamata ace ya saka rayuwar shi gabaki daya manhangar tunani ya fara canzata.

Amman ya zaiyi da kaddarar da take bibiyarshi?

Kaddarar da kowanne mai rai da kalar tashi.

Tun Saratu na zaman jego ya san cewa rigimar da nakuda ta yanke musu bata kare ba a tsakaninsu. Salim yake sakashi kusantar inda take saboda hararar da take binshi da ita duk idan idanuwan kowa baya kansu. Baisan me ya bashi yakini da kuma kwarin gwiwar cewa sirrin shi a adane yake a wajen Saratu kamar yanda yake adana abinshi. Ba zata taba daga maganar ta wuce tsakaninsu ba. Shisa yake baccin shi hankali a kwance, sai kuma ta tabbatar masa da hakan. A cikin gidansu tayi zaman jegonta duk kuwa yanda yan uwan mahaifiyarta suka so ta koma wajensu.

Abu bata duba halinta ba, bata duba yanda darajarta a idanuwan Saratun bata da wani yawa ba, ita ta zauna mata, kwanakin nan tayi tsaye akanta yanda uwa zata tsaya akan yarta. Saboda a wajen Abu zatayi fiye da haka akan duk wani da yake da kusanci da Hammadi balle kuma yarshi. Julde da kanshi ya roketa da ta zauna tare dasu, zama har iya lokacin da rayuwa ta ara musu.

“Kwanakin nan na jure sune a tare daku saboda ina hango karewarsu duk safiya Julde. Kayi hakuri, nisana ba zai taba dishe kaunarku a raina ba balle ya yanke zumuncin mu.”

Wannan yanayin, yanayin nan mai cike da kwarjini da yake tare da Abu shiya hana masa yi mata musu. Datti daman bai gwada ba, zai iya kirga haduwarsu, ko da yasan zata tafi ma, sallamarshi daga bakin Dije ta fito, daya ganta sai ta tuna masa da yanda Hammadi ya barsu, bari na har abada, saiya kasa tsaida hawayenshi. Kewar dan uwanshi tana nukurkusar shi fiye da yanda zai fada. Musamman a watannin nan da yake jin kamar bashi da kowa a filin duniya banda Dije da Saratu. Ga yaranshi yana kallon su amman ji yake sun masa wani irin nisa. Basa hira dashi kamar da, daga Julden har Yelwa babu mai doguwar hira dashi, yanda suke mikewa bayan sun gaisa na saka kalaman da yai niyyar fadi koma masa.

Gudun shi sukeyi, da babu Saratu, da baya ganinta, da bata shiga duk daren duniya tana masa hira da yaji kamar bashi da yara a cikin watannin nan. Saboda zabin da yake ganin don gobensu yayi shi, saboda yana kokarin saita musu hanyar da zasubi a zamansu na duniya batare da sunci karo da komai ba. Sun kasa ganin yanda su biyun ne fiye da rabin duniyarshi. Lokutta da dama yana so yayiwa Dije maganar amman saiya rasa ta inda zai fara tunda ita bata tabayi masa ba. Bai kula da nisan da Yelwa tayi masa saita hada harda ita a ciki ba. Yanda bayajin hirarta haka itama, har Julde ma, yana gaisheta, yana zuwa ya zauna kusa da ita, amman Yelwa na fitowa zasu tashi tare, suna rayuwa kamar basu da kowa sai junansu.

Sai suka kara mata kewar su akan ta Bukar da take fama da ita. Tayi kokarin magana da dukkan su taji matsalarsu, kamar sun hada baki kowanne a cikinsu ya amsa mata da.

“Bakomai Daada, me kika gani?”

Yanda duk tayi amsar su idan batazo daya ba to tana shige da juna. Sun saka wata kofa a tsakaninta da damuwarsu sunja sun rufe. Saita koma gefe ta saka musu ido, Abu da take gani tanajin dadi tayi mata nisa itama, wasu abubuwan kuma ba tasan ta inda zata fara maganarsu da Datti ba, waje kawai ta share a zuciyarta ta zubasu tana jin yanda suke kara taruwa. Komai dai shiru, irin shirun da zai saka maka shakku akan abinda zai biyo bayanshi.

Hakan ta faru dasu kuwa, hayaniyar da ta biyo bayan shirun ta bankado sirrikan Julde da aka samu Datti har wajen dabbobi aka fada masa, daga bakin mutumin da shine na karshe da Datti yayi tsammanin zai samu kwarin gwiwar tsayawa dashi ido cikin ido ya fada masa magana. Saboda daga mata har maza a gidan Balarabe babu na kirki, daya a cikin matan ma ta balle ta shiga duniya, labarin karshe da Dattin yaji akanta ana fada shine kudu ta gudu, gari mabanbanta a bakin mutane, wasu suce tana Lafia, wasu suce tana Makodi. Har zancenta ya shude saboda sababbin labarai da suka danne nata. Kusan kowa a garin ya sallama indai akan yan gidan Balarabe ne.

Shima kamar ya daina damuwa da zantukan mutane, yanda duk ake cewa ya murzawa idanuwan shi toka, Datti bai hango yakai har haka ba, ya kai matakin da zai kalle shi yace masa.

“Ciki danka yayiwa ‘yata.”

Batare da ko yi masa sallama ba balle kuma su gaisa. Zantukan nayi masa daban, kamar da wani yare yayi masa magana ba da fulatanci ba, a karo na farko da ya kalli Balarabe yana jira ya fassara masa abinda yake nufi.

“Yanzun haka tana can rai a hannun Allah saboda kokarin zubar da cikin da tayi.”

Ya sake dukan shi da wasu kalaman da yakejin su baki a cikin yarenshi. Kallon Balarabe kawai yakeyi, sauran maganganun shi na wucewa tare da iskar da take kadawa a ciki. Can ya tsinkayi tashi muryar cikin wani yanayi yana tambayar Balarabe.

“Wanne yaron nawa?”

Saboda kalmar yaro yasan tana nufin abubuwa da yawa, ciki harda wanda suke aiki a karkashin shi bawai iya Julde kadai ba.

“Kana da wani yaron daya wuce Julde ne?”

Baiga tashin hannun shi ba sam, sai karar marin daya wanke fuskar Balarabe dashi da yaji cikin kunnuwan shi. Balarabe yayi kokarin ramawa sai Datti ya rike hannun shi yana sake wanka masa wani marin. Ba za’a kira abinda ya wakana tsakanin su da dambe ba, tunda ko sau daya Balarabe bai samu damar rama marukan da Datti ya dinga jera masa kafin a rabasu ba.

“Idona zaka kalla kace dana yawa yarka ciki? Iskancin ka a kaina zai juyo yau? Ni sa’anka ne?”

Dakyar aka sha kan Datti bayan yaci alwashin duka Marake babu wanda ya isa ya hanashi nunawa Balarabe iyakarshi. Inda yasan zai sami Julde ya nufa kanshi tsaye.

“Yace bayajin dadi ya tafi gida.”

Aka fada masa, sai yayi gidan. Inda ya sami Julde zaune kusa da Daada, tunda ya tashi da safe yake jinshi wani iri. Har Saratu saida ta tambaye shi ko wani abu yana damunshi tunda taga bai dauki Salim ba. Ko cikin dare ya tashi yana kukan rashin dalili, kuma taga ba yunwa yakeji ba, Julde zai karbeshi, tun tana dariya idan yace ta goya masa shi har ta saba, haka zaita jagalniya dashi yace ta koma baccinta.

“Kawai jikina ne yayi mun nauyi.”

Ya amsa mata a takaice yana fita. Wajen la’asar ya dawo, abinci ma kadan yaci ya sake fita. Sai dai ba nisa yayi ba, gidan Daada ya shiga saboda koya yakejin zuciyarshi babu dadi zama a kusa da ita na rage masa wannan nauyin ko da ba hira sukeyi ba. Balle yau hirar ma sukeyi da suka kwana biyu basuyi ba, tana bashi labarin irin al’adun na Marake da yanzun zamani ya fara shudewa dasu, abubuwan da suka canza. Yanata mamaki, yanajin kamar anya da rayuwa akeyi ta jin dadi kuwa? Kamar sun tsaurara a cikin lamarin su da yawa.

Yanda Datti ya shigo gidan, kallo daya Julde yayi masa yaji zuciyar shi ta buga a cikin kirjinshi, kafin ta koma mazauninta.

“Balarabe yace kawa ‘yar shi ciki… Me yasa Balarabe zaice kawa ‘yar shi ciki? Me yasa zai hada sunanka a waje daya da wannan kwamacalar?”

Datti ya fadi cikin wata irin murya da take nuna yanda ranshi yayi kololuwa wajen baci. Yanayin da yasa zuciyar Julde sulalowa ta fado kan tandaryar kasa. Wani tashin hankali da bai taba sanin akwai shi ba yana maye masa gurbinta. Karasa takowa Datti yayi yana zama gefen Julde da ya sadda kanshi kasa, kwakwalwar shi tayi nisan kiwo saboda babu komai a cikin kanshi, wayam yake ji.

“Akan me zai kira sunanka? Akan me zai kira mun sunan yaro?”

Ya karasa maganar yana kallon Dije da takejin bugun zuciyarta har cikin kunnuwanta. Julde ta kalla, sai taji jijiyoyin dake rike da zuciyarta na tsinkewa, saboda abubuwa da yawa a yanayin shi ya nuna rashin gaskiyarshi, lumshe idanuwanta tayi abubuwa da yawa na mata yawo cikin kai, a cikinsu harda wani sabon shafin tashin hankali da kaddara ta bude musu.

“Zai iya yiwuwa ba karya yayi ba.”

Julde yai maganar, muryarshi na korar duk wata hayaniya da take cikin gidan, har iskar dake kadawa sai da kararta ta dauke musu kamar taji yanda kalaman Julde suka fito suke kuma canza komai.

“Me kace?”

Datti ya tambaya, dago kai Julde yayi suna hada ido da Datti.

“Zai iya yiwuwa ba karya yayi ba Baba…”

Marin shi Datti yayi, abinda bai taba yi ba tun haihuwar shi, yanajin wani abu na tarwatse a cikin kirjinshi da karar marin, sai dai a wajen Julde marin ba zai sa ya canza kalamanshi ba.  Gaskiya ya fada, idan cikine a jikin Jummai yar Balarabe to tabbas akwai yiwuwar nashine. Kome zai fada a wannan bigiren, a wajen Datti da Dije dai asirin shi ya gama tonuwa, a duka Marake ma harda kewayenta, labarin shi zai iya tsallakawa. Saboda yayi ban ruwa a gidan da fitowar shukar yake dai-dai da ganin idanuwan kowa.

“Kayi mun maganar da zan gane.”

Da wani yanayi Julde ya sake kallon shi.

“Me zan sake cewa Baba? Me kake so in sake fada?”

Tari Datti yayi, kwarewa yayi, amman a cikin kirjinshi yake jin wasu abubuwa sun sarke, sosai yake tari ga wani irin juyawa da yaga gidan yanayi masa. Sama-sama yake jin muryar Dije tana masa maganar da bata karasawa cikin kanshi balle ya fahimta. Harta rike masa kafada ba zaice ga abinda yake faruwa ba. So yake ta jijjigashi ta tashe shi daga wannan mugun mafarkin da yakeyi. Ta tashe shi ya fara sake rayuwa kafin Yelwa ta jajubo Kabiru daya fara canza musu komai har zuwa yau, kanshi ya dan karkata yana kallon Julde da yake zaune kamar an dasa shi. Sai yaga kamar baya numfashi, kamar gawarshi ce a gabanshi binne shi kawai yake jira yayi.

Saboda danshi mai rai, wanda ya fito daga jikinshi ba zai masa abinda Julde yayi masa ba, ba zai mayar dashi abin magana da kwatance a cikin garin Marake yanda yaga ya’yan wasu sun mayar dasu. Shi da yake zama ayi labari dashi? A kwatanta lalacewar yaran wani gidan da wani, a la’ance su tare da shi. Yaushe abin ya tsallako kanshi? Numfashi yaja ya fitar yanajin wani irin ciwo marar misaltuwa, tarin ya tsagaita masa, amman gara tarin da abinda yakeji.

“Allah ya isa tsakanina da kai Julde… Allah ya tsine maka albarka.”

Kalaman suka kwace masa suna binne masa Julde da yake gabanshi. Yelwa da ta shigo itama kalaman taji.

“Baba…”

Ta kira muryarta dauke da tashin hankali.

“Kema rayuwar da ya zaba zaki zaba in hadaku tare in sallamawa duniya?”

Datti ya tambaya yana kallonta, dauke idanuwanta da suka cika da hawaye tayi tana kallon Dije da idanuwanta suke a lumshe da dukan da kalaman Datti sukayi mata, saita kalli Julde, Julde da wani abu ya canza mata a tare dashi lokaci daya. Takawa tayi har inda yake ta kama hannunshi tana kokarin dago shi, tashin yayi, yanajin shi babu nauyi, kamar iskar da take kadawa zata iya dibar shi, bai saka takalmi ba, bin Yelwa da take janshi yakeyi.

“Ki sake shi ya fitar mun daga gida Yelwa.”

Muryar Datti ta tsaida takunta, sai dai bata juyo ba.

“Idan kuka tafi tare Allah ya isa.”

Kafarta daya da tayi mata wani irin nauyi ta daga tana sauketa gaba tare da hawayen da suka sulalo mata. Ta sake jan Julde suna cigaba da tafiya. Kallon su Datti yakeyi su duka suna barin gidan, komai yaji yana kwance masa, yanajin Dije ta zauna a kusa dashi, yana kuma jin muryarta dake furta.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Sai dai idanuwanshi akan su Yelwa da suka fice daga gidan suke, suna fita tare da kaso mafi girma daga zuciyarshi.

Sai dai wata kaddarar bata ma soma ba!

<< Rai Da Kaddara 34Rai Da Kaddara 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×