Ashe akwai ranar da zata zo da zai kalli Madina zuciyar shi cike fal da kishinta, kishin ma akan abinda ba a karkashin ikonta yake ba. Sai yau, da yake zaune a falon Daada, sai yau da suke gaisa da Yelwa, yaga Madina zaune a kusa da ita, kishi bai kara cika masa zuciya ba sai da akazo cin abinci, Madina ta saka lomar farko a bakinta, ta kai hannu da sauri tana fifita abincin a cikin bakin nata da alamun batayi zaton yana da zafi haka ba. Yelwa taja filet din gabanta tana bude mata abincin yanda zai sha. . .
Aslm mallama munagodiyya maitarin yawa