Ashe akwai ranar da zata zo da zai kalli Madina zuciyar shi cike fal da kishinta, kishin ma akan abinda ba a karkashin ikonta yake ba. Sai yau, da yake zaune a falon Daada, sai yau da suke gaisa da Yelwa, yaga Madina zaune a kusa da ita, kishi bai kara cika masa zuciya ba sai da akazo cin abinci, Madina ta saka lomar farko a bakinta, ta kai hannu da sauri tana fifita abincin a cikin bakin nata da alamun batayi zaton yana da zafi haka ba. Yelwa taja filet din gabanta tana bude mata abincin yanda zai sha iska sosai, kamar wata karamar yarinya. Ta ma bar nata abincin tana kallon Madina idanuwanta dauke da wani yanayi mai wahalar fassarawa. Duk wani fata nata ya cika, ba mahaifiyarta kawai tagani ba harda mahaifinta, harda wanketa daga zargin kowa akan asalinta.
Shine babu wani buri akan bayyanar nashi iyayen. Sunje Marake shi da Khalid, da tambaya suka gano gidan Baabuga, ko da Khalid ya tsayar da mota a kofar gidan, baisan hannun shi na rawa ba sai da Khalid ya kira sunan shi a hankali
“You are shaking Bajjo, ka tabbata ka shirya fuskantar wannan babin?”
Numfashi yaja ya fitar, ya sake ja yana fitarwa, yayi hakan na kusan minti biyu sannan ya jinjinawa Khalid din kai, robar ruwan dake cikin motar Khalid ya dauka ya bude yana mika masa, ya karba, baisan yaji kishi haka ba, kadaj ya rage a robar, ruwan na samar mishi da nutsuwar bude murfin motar ya fito. Da suke aika cikin gidan ayi musu sallama da Baabuga, kafin ya fito kafafuwan shi Nawfal yaji suna rawa, dole ya tsugunna yana wani irin maida numfashi. Wata muryace take ta masa ihu cikin kai tana karasawa zuciyar shi da wani irin amo
“Kakan ka zaka hadu dashi yau, Baban Bukar”
Da wani yaro ya fito daga cikin gidan sai Nawfal ya bishi da kallo yana tunanin ko dan gidan ne, idan dan gidan ne, jinin da yake jikin shi shine a jikinshi kenan? Ya zasu karbe shi? Bayan basu san dashi ba, in suka tsane shifa? In suka tambaye shi ina Bukar fa? Ina mahaifiyar shi? Me zaice musu? Wacce amsa yake da ita? Wacce hujja ma yake da ita daga farko da zata tabbatarwa da Baabuga cewar shi din jinin Bukar ne? Duka wannan shakkun da yake dashi sai yabi ruwa lokacin da Baabuga ya fito da sandar da alamu suka nuna tana taimaka masane wajen tafiya, ya kuma zabi ya fara sauke idanuwan shi akan Nawfal din, yana kallon shi, kallo na tsanaki, kafin mamaki, tantama, wani sabon mamakin ya mamaye fuskar shi.
“Ko ba’a tona ba yaro kai jinin Dije ne…”
Baabuga ya fadi yana maida idanuwan shi kan Khalid, sai lokacin kuma Nawfal din ya samu ya iya mikewa tsaye, wannan karin da Baabuga ya kalle shi sake matsowa yayi yana kama hannun shi, muryarshi na rawa yace
“Jinin Bukar ne kai?”
Kaine kawai abinda Nawfal ya iya dagawa, makoshin shi ya bushe kamar bai sha ruwa ba,murnar dake fuskar Baabuga na saka shi sauke numfashin da ya tafi da kaso mai girma na karfin shi, da Baabuga ya kamashi yana kokarin janshi cikin gidan saiya kalli Khalid, kallo da yake fassara
“Ya zanyi Hamma? Anya na shirya? Ka taimakamun.”
Sai Khalid din yayi masa murmushi yana dan daga masa kai kawai. Haka ya bi Baabuga har cikin gidan yanajin shi kamar mai yawo akan iska, yanda duk akayi dashi haka yake binsu, murmushin dake fuskar shi yakeji kamar plaster aka manna masa, ya rasa asalin abinda yake ji, bawai dan sune yan uwan shi daya hada jini dasu daya fara gani ba, gasu Khalid, amman yanajin kamar nan din tushen Bukar ne, mahaifin shi, yan uwan shi da suka hada uba dasu. Sai tambayoyin da yake hanawa kanshi a tsayin shekarun nan suka taso suna lullube shi. Ina Bukar? Me yasa zai kawo shi ya ajiye shi bai sake waiwayen shi ba? Ina mahaifiyar shi? Me yasa ko idanuwanshi ya rufe, yanda duk zaiyi yawo a cikin tunanin shi baya iya lalubo ko da muryarta ne, anya akwai abinda ya kai rashin sanin iyaye ciwo?
Akwai kadaicin da yafi na ka taso ba a kusa dasu ba zafi? Ranar duk wani taro na iyaye da za’ayi a makaranta, idan yaga Julde sai yaita kallon shi, idan ya juya yaga wasu iyayensu duka biyun suka halarta sai wani abu ya motsa a cikin zuciyar shi, idan suka dawo da sakamakon su, yaga su Khalid sun nufi bangaren Saratu shi ya nufi nasu da sakamakon da bashi da mahaifiyar da zai nunawa ta gani ta tayashi murna sai wani irin kadaici yayi masa rumfa. Da suka fara hankali sai Khalid ya wuce bangarensu tare dashi. Duk wani abu da zai kara masa radadin rashin nashi iyayen a kusa Khalid na kauce masa. Bashi kadai bama har su Adee, saboda duk yanda ake bikin ranakun iyaye na duniya ko Julde bai taba ganin sun saka ba, ko da suna sakawar suna tabbatar da baigani ba balle ranshi ya sosu.
Daga baya zai samu Salim a tsaye a bakin kofa, zai mika masa hannu alamar ya bashi sakamon yana dorawa da
“Kayi abin kirki ko ka kunyatani?”
Haka daya tafi kasar waje, schedule dinshi gabaki daya Salim ya saka ya tura masa ta email, yana ganin duk wani motsin shi, ranakun da yake da presentation, test, da kuma jarabawa. Sai daya zamana duk wata nasara da zai samu a harkar makaranta, yana da wanda zai raba hakan dashi. Sunyi duk wani kokari, suna kanyi wajen rage masa kadaicin da suke tunanin sunsan yanaji. Amman a cikinsu babu wanda zai taba fahimta, babu wanda zai gane, Madina ce kadai zaice tasan abinda yake ji, ta fahimta, ita kadaice yake kallo yanajin bashi kadai bane ba, akwai wanda ya fahimta.
Shisa yau yakejin wani irin kishinta da bai taba tunani ba, a wani sashi na zuciyarshi sai yakejin kamar taci amanarshi ne da tabarshi ya tsaya shi kadai yanzun a wannan kadaicin na rashin majingini. Ya zataga nata iyayen ita kadai? Shi kuma fa? Ta ina zai fara yanzun? Wa zai kalla ya fahimce shi batare da yace komai ba. Ya dauka ganin su Baabuga, ganin yawan dangin da yake dasu ya rage masa wani kaso a cikin wannan kadaicin, ashe karya yayiwa kan shi. Ya daiji dadi, ko yanzun akayi masa maganar tsatson shi yana da inda zai nuna, yana da dangin da zai nuna yace tushen shine, asalin shi. Ko Baabuga bayan sun natsa ya kalle shi yace masa
“Bukar fa?”
Yanajin idanuwan Khalid da yake zaune a gefe suna bin shi, ya hadiye wani katon abu dayaji ya tokare masa makoshi kafin ya iya fadin
“Bansani ba, bansan inda yake ba.”
Da dukkan gaskiyar shi, kai Baabuga ya jinjina masa kamar ya fahimta. Sunyi sallama cike da mutunci da alkawarin Nawfal din na cigaba da kawo musu ziyara lokaci zuwa lokaci, ya kuma yi musu alkhairi. Da suka fito daga gidan suka shiga mota saiya kalli Khalid ya ce,
“Hamma anya mun kyauta idan muka juya bamu nemi ahalin Daada ba?”
Kafadu Khalid ya daga masa, shi ba mai hayaniya bane ba, asalima zai iya kirga abubuwan da suke bata masa rai da lokuttan da hakan ya faru da yatsun hannuwan shi. Sai dai a gabaki daya labarin Daada da yaji daga bakin Nawfal, ranshi yayi bacin da bai tabayi ba, zuciyarshi ta sosu da yanda dangin Daada suka juya mata baya a lokacin da tafi bukatarsu.
“Su suka cireta daga cikinsu, su suka kyamaceta, me yasa zamuje wajen su?”
Khalid ya fadi da zafin da yakeji a zuciyarshi.
“Babu abinda lokaci ya koya maka ne Hamma? Baka kallon Daada? Baka ganin kewar tsatsonta a tare da ita? Bakaji bane ba, bakaji muryarta sanda take bani labarinsu ba, bakaga zubar hawayenta ba da kaine mutum na farko da zai fara nemo mata su yayi kokarin gyara alakar da take tsakanin su.”
Kauda kai Khalid ya yi, ranshi a bace yake shisa kalaman Nawfal din basu tabashi ba, ko da suka nemo gidansu Daada, dakyar Nawfal ya shawo kanshi ya fito daga mota, sai dai ba’aje ko ina ba, hawayen da yake zuba daga idanuwan yan uwanta mata guda biyu da suka samu a gidan ya fara karya masa zuciya. Da akaje aka kikkira sauran sukazo suka zagaye su sai komai yayi masa wani iri, sai rikesu sukeyi suna fadin
“Jikokin Dije ne, Dije tana raye”
Gabaki daya gidan ya hargitse da koke-koke, dakyar suka bari suka taho su kadai bayan sunyi musu alkawarin dauko Daada su kawota, dan mutum biyu cikin yayyenta maza sunso binsu, sai dai basu shirya ba, sunyi musu maganar su kwanane su kuma sukaqi, suka dai taho da alkawarin zasu koma. Da suka hau hanya sai da Khalid ya sauka gefen titi yana hade kanshi da sitiyarin motar na dan wani lokaci. Nawfal baice masa komai ba, ya barshi ya dauki lokacin da yake bukata wajen tattara nutsuwar shi kafin ya iya jan motar suka cigaba da tafiya.
Yaji dadin yanda Murjanatu bata tambayeshi komai ba, ta dai kama hannuwan shi taja shi jikinta tanayi masa rungumar da yake bukata. Ranar ne kuma ya samu hotel inda ya kama musu na sati biyu, kamar yasan Yelwa zata dawo. Yau da yace mata ta shirya su taho gidan Daada tare, kallon shi tayi batare da tace komai ba.
“Kema sai ku gaisa”
Kallon shin dai ta sakeyi
“Jaan”
Ya kira
“Zanje mu gaisa, amman ba yau ba, yau kaje cikin ahalinka”
Matsawa yayi yana rikota
“Kema ahalina ce”
Ta sauke numfashi
“Nasani, amman yau ne zaku fara haduwa, kuma ku duka zakuje, baka tunanin zaiyi wani iri idan nayi muku zaune? Kowanne yanayi zaku shiga sai dai inyi kamar na fahimta, amman kasan bansan me kukeji ba, zanje idan duka kun samu natsuwar da zamana a cikinku ba zaiyi wani iri ba.”
Amman da tazo da yanzun tana zaune kusa dashi, da zai juya ya kalleta, zai rage wannan kadaicin da yakeji na ganin Madina ta samu duk wani abu da take mafarkin samu. Duk da yanzun daya nutsar da hankalin shi akanta yaga kamar akwai wani abu a tattare da ita, tayi wani irin sanyi da bai taba gani ba. Bai san sanyin jikinta na da alaka da Salim bane ba, ta dawo gida a jiyan. Ta samu Daada a daki, saita karasa jikinta ta kwanta tana sauke numfashi
“Daada…”
Ta kira da sanyin murya tana dorawa da
“Yayi kusa idan nayi aure yanzun?”
Kallonta Daada tayi
“Shi aure baya kusa kuma baya nesa ai Madina, musamman a rayuwar mace. Aure kike so?”
Numfashi taja ta sauke tana rufe idanuwanta, yanayinta take ji babu dadi haka kawai, bugun zuciyarta ma kamar yayi kasa
“Hamma Salim”
Ta furta kamar sunan kawai ya isa ya amsa tambayar da Daada tayi dama wadda zatayi a gaba. Wannan karin da wani yanayi a fuskar Daada take kallon Madinar kamar tana neman tabbacin maganar da taji.
“Salim? Salim kike so ki aura?”
Kai ta tsinci kanta da dagawa Daada a hankali tana sake shigewa jikinta. Kallonta Daada takeyi har lokacin, ta rasa mamaki ne take ji ko taraddadi, ba zatace mamaki ba, sai dai tace tayi kokarin nisanta kanta da wannan tunanin duk kuwa da alamun da Salim yake nunawa a yanayin ziyarar shi da siye-siyen da yakeyiwa Madina, dama kacokan yanda a tare da ita halayenshi suke canzawa. Tasha hangowa Madina aure, amman har ranta ba da Salim ba, da Nawfal take hango mata wannan rayuwar. Burinta ya dishene lokacin da Nawfal yayi aure, amman bawai ya bace bane gabaki daya. Kuma yanzun ta ina Madina zatace ta auri Salim bayan abinda Julde yayi kokarin yi? Idan ta sani zata yarda ta aure shi? Idan ta aure shi ta sani daga baya fa? Zata iya yafewa Julde harta cigaba da zama da Salim din a matsayin miji?
Kaddarar su mai nauyi ce tasani, ta dauka zata tsayane kawai akan yaranta, amman alamu suna nuna har kan jikokin nata zata tsallako. Wani abu da zuciyarta take tabbatar mata ba zata iya dauka ba
“Ke kina son Salim din?”
Ta tambaya da wani yanayi a muryarta da yasa Madina bude idanuwanta tana nazarin fuskarta
“Ba kya son shi Daada?”
Kai ta girgiza mata a hankali, saita dago daga jikinta tana kallon cikin idanuwanta
“Ba kya sona da Hamma Salim”
Madina tayi maganar wannan karin da tabbaci tana dorawa da
“Me yasa?”
Kai Daada take girgiza mata, wani abu takeji yayi mata tsaye a kirjinta
“Ina son shi”
Ta furta a hankali tanajin kalaman sun zauna mata, kafin ta mike a hankali tana barin dakin. Haka kawai tun jiyan yanayin Daada yaki barinta, ta kuma rasa dalilinta nakin Salim tunda a iya hange da tunanin Madina bata ga wani abu da zaisa a guje mata aurenshi ba, idan za’ayi zancen gaskiya ma shi ya kamata a gujewa aurenta, bayyanar iyayenta yanzun, ko dama ace suna cikin rayuwarta tun daga farko, in ba kaddara ba Salim ba irin namijin da zai kalleta sau biyu bane dan hanya ta hadasu. Har yanzun data yarda zata aure shi tana jinjina abinda yagani a tare da ita yaji yana son aurenta. Duk da ta sha karanta yanda ake cewa so baisan kama ba, baya kuma bukatar dalili.
Rabin abinci ta iyaci tana mikewa ta kai plate din kitchen, data fito ta bayan kujerun tabi ta wuce zuwa dakinta. Yanda duk Nawfal ya dinga kallon kofar dakin baisa ta sake fitowa ba har suka tafi. Haka kawai sanyinta sai yayi masa tsaye a rai. Sanyin da ba ita kadai tayi shi ba har Yelwa, dan bayan tayi sallar isha’i ta shiga dakin Daada ta sameta zaune tana jan carbinta. Yanda suka saba yi mata daga ita har Julde tayi wannan karin, tana daukar shekarunta ta ajiyesu a gefe, ta kwantar da kanta a kan cinyar Daada tana sauke numfashi
“Daada bakice kin yafe mun ba.”
Kallonta Daada ta yi
“Na yafe miki tun kafin ki tambaya Yelwa, na yafe miki tun ranar da muka nemeki muka rasa, na yafe miki tun bansan inda kika shiga ba.”
Wani numfashin Yelwa taja tana fitarwa
“Bansan me zan cewa Madina ba, har yanzun. Shima yace mun baisan me zaice mata ba…Daada me zance mata? Tayi hakuri banso barinta ba? Haukan da nayi na shekara biyar ne, wanne uzuri zan bata na sauran shekarun? Bansan inda kuke ba? Inajin kamar banyi kokari da yawa wajen nemanku ba Daada, saina kwanta a gida na bar Kabiru da wannan aikin…kamar inda nayi kokari ta bangare na dana gano ku da wuri, da na samu wasu shekaru tare da ita…”
Ta karasa maganar da hawaye cike da idanuwanta. Ita, Madinar da alamu duka suka jima da nuna ita kadaice rabonsu a duniya. Saboda bayan ita ko batan wata bata sakeyi ba balle su saka ran wasu yaran. A tsayin shekarun nan kuma ko da wasa Kabiru bai taba yi mata zancen Madina ba, kamar yana tsoron fama mata ciwon daya san tafi shi ji. Kuka tayi sosai a jikin Daada kafin ta iya mikewa ta nufi dakin Madina bayan ta wanke fuskarta, a kwance ta sameta da littafi a hannunta, saita sauke littafin bayan taji ta zauna a gefen gadon, kafafuwanta taja ta mike su akai, sannan ta kamo hannun Madinar tana dumtsewa cikin nata.
“Duk idan naga littafi a hannun wani lokacin muna Marake, ko a kasuwa sai inta kallo inajin daman na iya karatu danace Baba ya siyomun”
Kallonta Madina tayi
“Ban iya karatu ba a lokacin, na iya na hausa yanzun, na koya daga baya…naga litattafai da yawa a dakin nan”
Kai Madina ta jinjina
“Ina son karatu, ina so in zama babbar yar jarida…”
Kallonta Yelwa takeyi tanajin kamar ta maida hannun agogo baya
“Amman ina karanta komai fa, ba sai abinda ya shafi harkar aikin Jarida ba, labarai, kimiyya, tarihi, abubuwa da yawa dai haka. Hamma Salim inya tashi siyomun litattafai akan abubuwa mabambanta yake siyowa…”
Hira sukeyi har wajen sha biyu, Madina na bata labaran yanzun, ita kuma tana bata labarin Marake, al’adunsu da duk wani abu da take so a garin, harda kuruciyarsu ita da Saratu, fadan da Saratu tayi da rikicin Julde, kadan daga abubuwan da zata iya tunawa game da Bukar, labaran da Yelwa ta adana a kirjinta zata bawa yaranta wata rana, labaran da ta dauka damar bayar dasu ta wuceta ce ta samu yau, a cikin hirar ne Madina ta kalleta, kallo na sosai tace
“Me yasa kika barni? Da zaki tafi me yasa baki daukeni ba? Sai kika barni, me yasa kika barni”
Ta karasa muryarta na karyewa, idanuwan Yelwa suka ciko da hawayen da take kokarin ganin basu zuba ba
“Tunda na dawo nake hada kalmomin da zasu zame mun uzuri, kalmomin da idan nayi amfani dasu zasu sa ki yafemun, zasu wankeni a idanuwanki, amman bandasu Madina, banda wasu kalmomi, zan sake son kaina, kiyi hakuri dana barki, ki yafemun da nayi miki nisa a lokacin da kike bukatata…kiyi hakuri banzo da wuri ba, nasan na makara, amman kiyi hakuri”
Gilashinta Madina ta cire tana saka bayan hannunta ta share hawayen da kamar ta ba wasu kofar fitowa ne, rikota Yelwa tayi, wani irin kuka takeyi kamar ba zata daina ba shisa Yelwar bata sake cewa komai ba, a tsakanin kukan da ajiyar zuciyar da Madina takeyi ne tace mata
“Karki sake bari na, kinji, dan Allah karki sake barina…kinga zanyi aurema, dan Allah ki zauna”
Sai lokacin ta bari nata hawayen suka zubo, ta daga mata kai
“Aure? Wa zaki aura?”
Hanci Madina taja, muryarta harta dishe tayi kasa saboda kukan da takeyi
“Hamma Salim, amman Daada bataso bansan me yasa ba”
Hannun Madina da yake cikin nata ta murza wani abu na tsirga mata. Wasu hawayen na neman kubce mata
“Dare yayi, kiyi bacci da safe sai muyi magana”
Kai Madina ta jinjina tana gyara kwanciyarta ta sake shigewa jikin Yelwar, ta kuma dumtse hannunta a cikin nata kamar hakan zai hana wani abin ya sake kwace mata ita. Addu’ar bacci ta karanta batare da ta bude idanuwanta ba ta tofa a hankali tana fatan ganin wayewar gari
Safiyar da zata zo mata da sabon al’amari
Safiyar da zata sake girgiza duniyar su a karo na ba adadi
Saboda kowanne rai da tasa kaddarar…
Aslm mallama munagodiyya maitarin yawa