Skip to content
Part 55 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

To a warrior, that’s my grandma, who has been battling with cancer for 45 years now.

*****

“Hey Mug…”

Ya kira a hankali, cikin muryar da ta ratsa shirun studio din tana kuma isa kunnuwan Madina duk da hankalinta yayi nisan kiwo, juyowa tayi tana kallon shi, idanuwanta tsaye akanshi, sai dai rashin gilashinta yasa bata ganin shi sosai, ta kara kankance idanuwanta kamar hakan zai wanke mata hoton shi. Yanayi ne da babu wasu kalamai da zasu misalta yanda Salim yaji, ya kamata ace ya dago hannun shi ya dafe zuciyarshi da take barazanar fitowa daga kirjinshi saboda tsallen da takeyi, amman bayason komai ya katse mishi yanayin, komai na nufin har numfashin shi da yake kokarin daukewa, tayi kyau, badon batayi mishi kyau kullum ba, bakuma dan bai taba hasaso ta da kayan mata ba, asalima tun kafin yasan zuciyar shi na doka mata, duk idan zaiga mace tasha kwalliya sai yayi kokarin dora fuskar Madina a cikin tata.

“Hamma…Hamma Am.”

Ta kira shi, tana saka shi sake kallonta, a kasan duka kwalliyar fuskarta yana hangowa kuncin da baisan ta inda zai fara rage mata radadin shi ba. Kwalliyar kuma na baje mishi har yana hangota kwanaki biyu da suka wuce tsaye a wajen jira na asibitin koyarwa na Aminu Kano, kanta babu ko dankwali, gashinta da bai taba sanin haka yake ba ya hargitse, santsin shi yasa wani daga cikin sashen ya barbazu ta gefe da gefen fuskarta, ribbon din data saka ta kama gashin dashi yayi baya sosai ta yanda zaka iya ganin yalwar gashin da Allah yayi mata duk kuwa da tsayin jelar a nannade yake. Wando ne a jikinta mai roba daga karshen, sai rigar da ta sauka har wajen cinyoyinta, kafafuwanta babu ko takalmi sai safa.

A yanda ya kula, shine karshen zuwa wajen, saboda har Adee tana nan, ta kuma yanayin kumburin idanuwanta zaka gane kukan da taci, saboda daya dauke idanuwanshi na yan dakika daga kan Madina, kauda kanta tayi kamar tana kokarin boye masa hawayenta. Daada na zaune kamar kowa, Julde na kusa da ita ya kama hannunta ya dumtsa cikin nashi, daga nesa wani zai iya cewa lallashinta yakeyi, amman shi daya kara matsawa yaga Julden ne yake neman lallashi a wajenta. Daga Madina sai Kabir ne a tsaye, dan shi yana bakin kofar dakin da alamu suka nuna Yelwa na ciki, kamar kiris yake jira ya bankada kofar ya shiga. Madina ta jingina bayanta da bangon wajen, kafafuwan shi a saitinta suka tsaya.

Kamar wadda taji karasowar shi sai ta dago tana kallon shi ta cikin gilashinta, numfashi ta fara ja da baiga sanda ta fitar ba, kamar shi take jira, kamar shi kadaine zaifi kowa fahimtar hargitsin da take ciki haka ta kalle shi.

“Lafiya kalau muka kwanta Hamma, a karo na farko munyi hira, sosai mukayi hira, me yasa zamu tashi haka? Me yasa zan tasheta taki tashi? Na kiraka baka dauka ba”

Ta karasa maganar da alamar tuhuma, yabar wayarshi cikin mota ne da yazo asibiti, sai da yayi tunanin ya kirata ne ya kula da hakan, da yaje ya dauka ba kiranta kadai ya gani ba, harda na, Khalid, Adee, Nawfal da ma Saratu. Yawan kiran yana tabbatar mishi da cewar ba lafiya ba

“Kirjina zafi yakeyi…”

Madina ta fadi tana kai hannu ta murza kirjinta inda zuciyarta ke mata wani irin ciwo, ta dauka tun akan Daada ta gama sanin meye tashin hankali sai asubar yau da ta tashi Yelwa taki tashi, ta kunna fitilar dakin ta dagota taga farar fuskarta tayi wani irin haske kamar babu jini a jiki. Sai kuma da ta ga Julde ya dagata ya saba a kafadarshi kamar babu rai a tare da ita sannan wani abu ya rabe a cikin kirjinta da take jin zafin shi har yanzun. Hannunta ya kama batayi musu ba ta bishi, ya jata yana karasawa da ita inda Khalid da Nawfal suke zaune ya zaunar da ita a gefen Nawfal daya kalle su. Tunda suka shigo asibitin, babu yanda basuyi da ita ba shi da Khalid, musamman shi, maganar duniya yayi mata bata ko daga kanta ba, haka ya gaji ya hakura ya samu waje ya zauna.

Amman hankalin shi duka yana kanta, Salim na shigowa ta kalle shi kamar shi take jira, bai ko yi mata magana ba ta fara fada masa matsalarta kamar tana tsammanin maganinta a tare dashi. Haka kawai sai yaji zuciyarshi tayi masa wani iri, musamman yanda ta riko Salim din bayan yayi kokarin zare hannunshi daga cikin nata

“Ruwa zan kawo miki Madina.”

Ya fadi yana zare hannun shi daga cikin nata. Bai kuma dade ba ya dawo da robar ruwan da batayi musu ba ta karba. Ya ajiye mata silipas din da yake amfani dasu a asibitin, sai da yaga tashi ruwan tukunna ya mika mata rigar shi, itama karba tayi, daga zaunen ta saka tana zage zip din, shiya kamo hular da take hade da rigar ya dora mata saman kanta.

“Ki zauna nan, kina jina? Ki zauna, zanje in duba inga me yake faruwa…”

Saida yaga ta daga masa kai a hankali sannan ya tafi. Ya shiga dakin, sun fito tare da likitan suna karasawa Office din shi, Julde na rufa musu baya. Sai dai shi kadai ya iya fitowa saboda Madina tana jiran shi, Julde ya kasa fitowa, ya barshine ya kifa kanshi da teburin ofishin likitan, sai dai daya fita ba idanuwan Madina bane kadai akanshi, na dukan sune, ahalin shi, suna jiran yayi musu bayanin da baisan ta inda zai fara ba. Kasancewar bangaren ba nashi ba baya nufin baida sani kadan akai, kuma tunda likitan ya kira.

“Stomach cancer, last stage…”

Sauran bayanin ko baiyi masa ba ya rigada ya fahimta, ciwon yayi rassa a cikinta, yayi girman da babu wani taimako da za’a iyayi mata a likitance daya wuce dirka mata magungunan da zasu rage mata radadin da take ciki kafin kwanakin da suka rage mata su cika, abinda kowa yake jira da ciwo ko babu ya tabbata akanta. Sai dai bai ganowa Madina ita dan ta rasata ta wannan hanyar ba, daya ganota bai hango bata da isashen lokaci haka ba.

“Hamma mutuwa zatayi ko?”

Madina da baisan ta karaso inda yake ba ra furta cikin wata irin karamar murya

“Stomach cancer”

Ya tsinci kanshi da furtawa, tashi muryar na fitowa kamar rada, sai da ta hadiye wani abu kafin ta iya ce masa

“Wanne mataki?”

Numfashi yaja yana fitarwa a hankali

“Na karshe…”

Rawar da kafafuwanta sukayi da bai rikota ba faduwa zatayi, sai da ta dai-daita kanta, ya kuma tabbatar idan ya saketa ba zata fadi ba sannan ya saketa din, batare data kalle shi ba tace

“Wata nawa sukace?”

Rayuwa a hannun Allah take, hasashen likitoci arashine kawai da akan samu, amman wani ya isa ya hasaso adadin daya rage maka a duniya? Shine abinda ya tsara fadawa Madina sai wani abin daban ya kubce masa

“Kwanaki, sati daya idan an dade ko kasa da haka.”

Kafin yayi saurin dorawa da

“Sai dai mu da muke da lafiyar ma bamu da tabbas idan muna da wannan lokacin Madina…”

Kalaman na koma masa da wani irin firgici, koda ayyukan alkhairi ya shafe shekarun shi yanayi bayajin zai iya shiryawa mutuwa a dan kankanin lokaci haka, idan kuma ayyukan basu karbu bafa? Kamar tuban shi da bai dade da farawa ba, da wanne guziri zaiyi rayuwar barzahun da ake kira? Rayuwar da tafi kowacce firgici idan baka samu dacewa da Rahmar Allah ba, shekaru ne da babu wanda yasan adadinsu, dari biyar, dubu dari biyar, miliyan dari biyar kafin a tashi duniyar azo filin alkiyama, firgicin da yake ji yana da yakinin yafi wanda yake gani shimfide a fuskar Madina. Ita mahaifiyarta take ji, shi kanshi yake hangowa, zunuban shi da baisan ko yana da lokacin da zai wanke daudar su ba yake tunani.

Batace komai ba, rabashi tayi tana wucewa ta tura dakin da Yelwa take ciki ta shiga. Baiyi kokarin binta ba, bai kuma cewa kowa komai ba tunda yasan sunji su, barin wajen yayi zuwa Office din shi. Wayar shi dai na tare dashi, duk mai bukatar shi zai nemeshi, da azahar tayi dai ya fita yayo musu takeaway sannan ya koma. Daya ba Madina nata kallon shi ta yi.

“Kina bukatar abinci ko bakyajin yunwa.”

Ya fadi, kai ta dan daga masa a hankali

“Kaci dani to.”

Ganin kamar yana son yi mata musu yasata dorawa da

“Hamma…dan Allah”

So yake yace mata ya ci nashi, bashida wajen saka wani, amman saiya kasa, zama yayi, cokalin dayar robar abincin yayi amfani dashi yana hadiye batare daya tauna ba saboda da gaske ya koshi. Kuma saboda ita ya zauna yaci abincin, tun na safe ne da bai samu yaci ba. Yanzun ma gashi yana kara wani saboda ita. Ya kuma zauna tare da ita har akayi la’asar, magariba, isha’i, bai bar gefenta ba sai karfe goma na dare da jaddada mata in tana bukatar shi waya kawai zata daga ta kirashi

“Kaje aikinka Hamma”

Yanda ya kalleta kamar bayason barinta ne yasa ta yi masa murmushin karfin hali, kamar tana son fada masa Yelwa ta tsallaketa tun bata kwana a duniyar ba, babu abinda ya sameta kuma, ta rayu, bambancin da yake tsakanin wancen lokacin da wannan bashi da wani yawa. A wancen Yelwa bata da zabi, wannan dinma bata da zabi, bambancin kawai idan ta tafi yanzun babu taraddadi, babu duban hanya, sunsan ta tafi kenan. Saida ya kara kallon Madina yana son tabbatarwa kanshi da in ya tafin tana da sauran karfin zuciyar rike masa kanta. Kwana biyu tsakani ta kirashi tace yaje tana son ganin shi, zuciyar shi a cikin bakin shi ya karasa wajenta saboda basu fi awa daya da rabuwa ba, kafin ya furta wani abu ta rigashi

“Ka aureni Hamma…”

Ta furta tana maida numfashi kamar tayi gudu, yana kuma hangen hawayen da yake cike tafi da idanuwanta

“Bata ga abubuwa da yawa a tare dani ba, ba kuma zata ga wasu da yawa ba, bana so auren mu ya zama cikin jerin abubuwan da ba zata gani ba Hamma, ka aureni”

Abinda yake sonji ne, amman ba haka ba, yana son aurenta, aurenta ne abu na karshe da yakejin zai zama cikon rayuwar shi, sai dai baiyi wani shiri ba, kudaden da yake dasu a account dinshi bayajin zasu isheshi hidimar aure, yana da gida da Julde ya sai masa kamar kowa a gidan, amman yan haya ne a ciki, kuma baima san yaushe kudin da suka biya zai kare ba ballantana kuma watannin da za’a kara musu su nemi wani wajen daban. Akwai hidima da yawa a aure, kananu da manyan abubuwan da suke bukatar shiri, shiri kuma yana son lokaci, a yanda Madina take masa magana bayajin yana da lokacin da zaiyi duk wannan shirin.

“Kaji…”

Ta sake fadi tana kallon shi

“Akwai shirye-shirye da yawa fa, banda inda zamu zauna, ga su lefe”

Da sauri tace

“Duka wannan sai ayi daga baya, a daura auren dai ta gani…bata da lokacin jiran duk wannan, watakila mu muna dashi…”

Ta karasa cike da wani yanayi na nuna rashin tabbacin rayuwa, saiya tsinci kanshi da daga mata kai, yana kuma samun Julde a daren a karo na biyu tunda na farkon daya same shi saiya rasa abinda zaice masa, daya kalle shima wani zafi yaji kirjinshi na dauka, saboda tunda abin ya faru basu hadu haka su biyu kawai ba, duk haduwar da sukayi a cikinsu babu mai natsuwar dawo da ranar balle har su fuskanci junansu, sai da Salim ya hadiye wani abu da yaji tokare da wuyanshi sannan muryar shi can kasa yace

“Ina son Madina…Daddy ina sonta. Zan aure ta, tunda ga Babanta yanzun, ka nemar mun aurenta a wajen shi.”

Kamar Julde ba zai magana ba, ya nisa yace

“Ita tana son ka?”

Kai Salim ya daga masa

“Shikenan, zanyi masa maganar…”

Numfashi Salim ya sauke a hankali yana mikewa daga zaman da yayi a gefen gadon Julden, har yakai kofa Julde ya kirashi

“Salim…”

Tsaye yayi, hannun shi rike da handle din kofar kafin a hankali ya juya

“Kayi hakuri, kayi hakuri duk da yin hakurin ba zai taba goge hoton dana dasa a zuciyarka ba, kayi hakuri, dan Allah kayi hakuri…”

Baice komai ba ya bude kofar ya fice, saboda baisan meya kamata yace din ba, ya hakura? Bayan zuciyarshi zafi takeyi kamar zata kone, bayan baisan ya zai kalle shi baiga hoton shi tsaye yana kokarin haramta masa Madina ba. Lokaci na tafiya da komai, haka mutane suke cewa, yana dai da yakinin ko lokaci ba zai tafar masa da wannan mummunan hoton ba. Sunyi maganar ne shida Julde batare da hango zasu tashi da ciwon Yelwa ba. Da kuma ya same shi a karo na biyu sai ya natsu yana nazarin fuskar shi, yana ganin ramar da take idanuwanshi kamar tare suke jinyar da Yelwa. Yanda ya amsa gaisuwar shi da wani irin sanyi na saka zuciyar shi matsewa a cikin kirjinshi.

“Daddy ko jikin ne? Kana shan magungunanka kuwa?”

Murmushin karfin hali yayi yana fadin

“Wannan magungunan ba zasu yiwa ciwon da yake damuna ba Salim, ya akayi?”

Numfasawa Salim yayi kamar ba zai fada masa ba saboda yanayin shi yayi masa wani iri.

“Madina tayi mun magana, tana so a fara daura auren, komai sai yazo daga baya, tana so Mamanta ta gani kafin…”

Ya kasa karasawa saboda yanda yaga wani abu ya gilma a cikin idanuwan Julden kafin ya lumshe su a hankali yana sake budewa.

“Zanyiwa Kabirun magana anjima idan na shiga asibiti.”

Cewar Julde, duk da ya kula Kabirun yana zillewa haduwa dashi, kuma a wannan gabar baiga laifin Kabirun ba, randa ya fito daga dakin likitan nan bayan ya tabbatar da ciwon Yelwa ba mai warkewa bane ba, kanshi tsaye inda Kabiru yake tsaye ya nufa yana shako shi da dukkan karfin shi kafin ya soma jijjigashi.

“Ka dawomun da kanwata yanda ka gudu da ita Kabiru, ka dawomun da ita yanda ka bar Marake da ita.”

Su Nawfal kasa kwatar Kabiru sukayi, saida Daada tazo ta kamashi saiya kasa yi mata musu, ya saki Kabiru ya barta taja hannunshi ta zaunar dashi, daya fashe da wani irin kuka ma batayi kokarin yanashi ba, zama tayi kawai a kusa dashi. Sai dai a yan kwanakin nan ya kasa hana idanuwanshi bin Kabiru da harara duk haduwar da zasuyi. Amman yanzun Daada ya fara samu da zancen Salim da Madina kafin ya fara yiwa Kabiru maganar.

“Nasani, Madina ta fadamun, ba kuma kinta da Salim nakeyi ba, abinda zaije ya dawo ne nake gujewa, ina tsoron wata kaddarar Julde.”

Kanshi a kasa, idanuwanshi cike da hawayen da suka zame masa abokai a satikan ya ce,

“Wacce irin kaddara ce bamu gani ba Daada? Akwai wata fuska ta kaddara kuma da bamu gani ba?”

Numfashi ta sauke

“Allah yayi mana jagora yasa alkhairin juna ne.”

Ta furta da wata irin sanyin murya, daya samu Kabiru ma suka zauna yayi masa maganar nisawa yayi yana amsawa da

“Yaran duka nakane Julde, duka yaushe na shigo rayuwar Madinar da nake da bakin cewa a cikinta?”

Kai Julde ya girgiza masa

“Bana sonka kasani, banajin akwai wani dalili da zaisa zuciyata ta soka, amman dan kazo rayuwarta a makare ba zai canza matsayinka ba, shisa nake tambayarka, nake nemar wa dana auren ‘yarka Madina.”

Muryar Kabiru a karye ya ce,

“Na bashi, in dai bakina ake so aji na bashi Madina”

A ranar juma’ar, bayan sallar isha’i, a masallacin, Julde, Kabiru, Salim, Nawfal, Khalid, limamin daya jagoranci sallar da mutanen da suke cikin masallacin suka zama shaida, aka daura auren Salim da Madina akan Sadaki dubu dari, Sadakin da Julde ne ya bayar daga aljihun shi, za kuma kaga mamakin da yake shimfide a fuskokin su Khalid, musamman Nawfal da yaji kamar an sakko masa wani dutse a saman kai, tunda basu san da zancen ba, daurin aure kawai sukaji kamar a shirin fim, banda raba idanuwa babu abinda sukeyi har Julde ya tasa su gaba suka fito daga masallacin, daman kiran da yayi musu kenan? Dan su kara zama shaida a auren Salim da Madina? Sun kara tabbatar da iya kiran kenan ganin bai musu bayanin komai ba ya nufi hanyar gida, Kabiru kuma daya fito suka kara gaisawa a waje shima sallamar yayi musu yana wucewa ya koma asibitin da zai je.

“Ni kadai ne bansan da maganar nan ba?”

Nawfal ya fadi yana kallon Khalid.

“Fuskata tayi maka kama da nasan da auren nan Bajjo?”

Kai Nawfal ya girgiza masa yanajin shi wani iri, tare suka karasa cikin gidan, suka shiga motar Khalid ya mayar dashi hotel din da suke zaune shi da Murjanatu, Khalid kuma ya kamo hanya ya dawo gida ya nufi bangarensu, inda ya samu Salim zaune a falo da kofin shayi a hannun shi, ya kai bakin shi yana hura iska a ciki a hankali

“Ka fadi abinda yake zuciyarka Khalid, tun a masallaci nake jin idanuwanka suna bina da kallo.”

Kallon nashi Khalid yakeyi, kafin ya girgiza kanshi a hankali yana rabawa ta gefen kujerar da nufin karasawa dakin shi.

“Khalid…”

Salim ya kira cike da kashedi, juyowa Khalid din yayi

“Me zan fada maka da baka sani ba Hamma? Ta yanda baka dace da Madina ba? Yanda in har baka shirya gyara halayenka ba kayi sahihin tuba ba zaka taba dacewa da ita ba? Ko tsorona zan fada maka na gudun karka sake karya mana zuciyoyin da suke a karye?”

Runtsa idanuwa Salim yayi yana budesu a hankali, baisan ta inda zai fara fadawa Khalid ko bai auri Madina ba yayi hannun riga da bin wasu matan, yaga kunyar duniya a tare da Julde, kuma iya idanuwansu kunyar ta tsaya, har yanzun idan ya fita waje mutane suna gaishe dashi, suna kallon shi da rigar mutuncin nan, bashi da kwarin gwiwar tsayawa gaban Allah da tarin daudar nan, kamar yanda bashi da kalaman amfani dasu wajen yiwa Khalid bayani

“Maganganuna basu da yawa Khalid, kasani, banda abin fada maka, zan dai ce maka na daina, ina kokarin rage zunubaina, ba kuma saboda Madina ba, da soyayyarta a raina nake laifuka na, ba don ita na bari ba, na bari don kaina da lahirata…”

Wani irin numfashi Khalid ya sauke

“Allah ya yafe mana ya cigaba da yi mana jagora. Allah yasa alkhairi da albarka a aurenku…”

Kai Salim ya jinjina yana amsawa a cikin zuciyar shi, Khalid yace auren su

Shi da Madina
Kaddara ta rantse akan su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 54Rai Da Kaddara 56 >>

3 thoughts on “Rai Da Kaddara 55”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×