Skip to content
Part 6 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

“Karatu ne ya rike ni Daada…”

Shine uzurin farko daya fara kawo mata a cikin shekaru biyu, a kuma karo na farko da taji muryar shi ba sakon gaisuwar shi a bakin Julde ba. Yanda take kwana tana tashi a cikin shekarun Allah ne kawai shaida, sai kuma ita da ta san kalar damuwar da take ciki, tunani babu kalar wanda batayi. Duk idan Julde yace mata,

“Munyi waya da Bajjo, yace a gaishe da ke sosai.”

Sai ta dauki dakika tana kallon kwayar idanuwan shi ko zata ga karyar da take tunanin yayi mata. Amman saiya fada murmushin shi da cewa;

“Kinsan akwai banbanci awa kusan biyar tsakanin mu da su, sanda zai kira zakiga sai wajen karfe goma da rabi na dare, da na kira kinji muryar shi.”

Tun tana yarda harta fara saka kokwanto a cikin ranta, ta san damuwar da Julde yake karanta a fuskarta yasa shi hada mata wayar tafi da gidan ka ta telephone tunda salular ta hannu da ake yayi tace bata so. Sanyin daya ratsa zuciyar ta bayan jin muryar Nawfal sai da ya saukar mata da wata kasala ta ban mamaki.

“Bajjo”

Ta kira kamar ta kasa yarda muryar shi ce take ji cikin kunnenta kamar yana gabanta. Sai ma da yayi dariyar nan tashi sai taji idanuwanta sun cika taf da hawaye, tsoron da take kwana tana tashi da shi ta nema ta rasa.

“Ka dinga kirana kullum ina jin lafiyar ka kaji ko? Shirun nan shine yake daga mun hankali fiye da rashin dawowar ka.”

Ya kuma ji maganarta, kullum karfe tara na dare agogon Najeriya yake kiranta, wasu ranakun sukan dauki fiye da mintina talatin suna hira, wasu ranakun kuma gaisawa kawai sukeyi zaice mata yana da ayyuka da yawa da zaiyi.

“Wata rana ki rike mun Madina da hira mana Daada, kar tayi bacci mu gaisa.”

Nawfal ya roke ta, sai dai ta amsa shi da to, dan bata san ta inda zata fara mishi bayanin canjin da Madina takeyi da duk rana ba, a yan shekarun yarinyar komai nata da ka’ida takeyi, in ta dawo daga makaranta karfe shidda zata sake share gidan ko da kuwa Daada ta share, tayi sallar Magriba, taci abinci, a tsakanin ne kafin isha’i zatayi nazarin litattafan ta, ko tayi aikin gida idan tana da shi, tana idar da sallar isha’i take kwanciya. Wani kallo duk yanda take son shi baya shiga tsakaninta da baccin da tasan tana bukata. Yan kunshi yanzun har sun gane, in dai ba alhamis da juma’a ba da yamma, in kazo ma ba zaka samu ba.

Sai dai ko lokacin hutu, kallo kuwa ran asabar da lahadi zata zauna tayi da rana haka, karatu dai dakin Madina cike yake da takardu da litattafai, shisa lokacin da ta fara wani irin ciwon idon da bayan kaita asibiti saida suka yi mata gilashin da gashi nan tana ta fama da shi Daada tace,

“Kallon takarda, ace mutum idon shi ba zai huta ba, kullum cikin karatu ba dole ido ya lalace ba.”

Yanda duk Madina da Julde suka so fahimtar da ita cewa ba karatu bane ba ya ci tura, sai gajiya sukayi suka kyale ta. Har yanzun bata daina mita lokaci zuwa lokaci idan ta ga Madina manne da littafi, takarda ko ta kosai ce suka siyo suka cinye sai Madina ta dauka ta karanta taga meye a ciki. Littafi duk wanda ta rubuta sai Julde ya siyo mata.

“Hamman ki na gaishe ki, yace in rike ki da hira har lokacin kiran shi yayi dan ku gaisa.”

Daada ta gwada fadawa Madina da ta saka hannu tana gyara gilashin daya cinye kusan rabin fuskarta kan karan hancin ta tana yin murmushin da baka raba fuskarta da shi sannan tace,

“Hamma baya kira da wuri Daada, kice in yana so mu gaisa ya kira kafin lokacin bacci na yayi.”

Shima da ta gaya mishi abinda Madina ta ce dariyar yayi yana amsawa da

“Daada komai na a tsare yake, bana son shigar da wani abu cikin lokacin yin wani abin.”

Kai kawai ta girgiza, Nawfal yayi mata nisan da bata ganin canjin da yau da gobe take yi wa rayuwar shi, amman iya hakan ta fahimci sun hadu waje daya tare da Madina, sun dauki wata akida ta kayyadaje yanda ranakun su zasu kasance, har suna ganin ba zasu iya canza hakan dan wani ba. A kauye ta tashi, kauyen da karatun addini ma sai da ta shigo binni ta neme shi da kanta, shisa bata shiga cikin irin wannan rayuwar ta su Madina da tafi karfin fahimtar ta, Madina ma da take gabanta da yawan abubuwa sai dai ta bita da addu’ar neman shiriya ko samun sauki, balle Nawfal da yake wata duniyar.

Sallamar da akayi ta katse ma Daada dogon tunanin da take zaune tana yi, sai da ta sauke numfashi sannan ta amsa tana mikewa jin kamar karar sauke wani abu mai nauyi, tana fitowa kuwa Salim ne ya ajiye buhun shinkafa a tsakar gida.

“Karka ajiye anan, ka shigo da shi daga ciki.”

A hankali ya daga idanuwan shi yana kallon ta, idan wani yana wajen zaice kamar a takure yake, wani ma idan yaga kallon zai dauka shine karo na farko da ya taba ganin Daada, yana kallon ta ne da mamakin dalilin da zaisa tayi mishi magana, kamar ba zai amsa ba yace;

“Akwai wasu kayan…”

Cikin muryar shi da take a bude amman yanayin kalaman sun fito ne cikin sanyi da abinda mutane izzar da tasa mutane da yawa suke daukar ya fito tsatson sarauta, ko da Daada tayi niyyar fadin wani abu Salim bai tsaya ba balle yaji, juyawa yayi abin shi, tana bin shi da kallo, shigar kananun kayane, dogayen kafafuwan shi basu sa yaji akwai bukatar ya dinga suturta su ba, wandon da yake jikin shi ruwan madara da kadan ya wuce gwiwa, sai riga da tayi ma Daada kama da ta sanyi kalar ja, mai dogon hannun da yadan tattare yana ja sama, sai hular sanyi daya tura baya rabin gashin shi a waje, ita kuma kala daya da wandon shi.

Gashin in da yake a bude, yanzun daya dawo dauke da kwalaye biyu da alamu suka nuna na taliya ne, Daada ta kula da a cukurkude gashin yake, yayi wani irin aski da in ka ganshi cikin masallaci mamaki zai kamaka na kasancewar shi musulmi, ko hausa kaji yayi saika juyo ka kalle shi. Daga yanayin kirar jikin shi, tsayin shi har shigar shi bata nuni da cewar ba bahaushe bane shi, bafullatani ne gaba da baya, kuma mabiyi addinin musulunci. A cikin yaran Julde duka daga Adee sai Khalid ne suke zuwa wajen ta akai-akai.

Da dalili ko babu sukan zo harma su kwana, Salim in ba aiko shi akayi ba, ko kuma motar Julde ta samu matsala yasa ya kawo shi, da kan shi bai taba wanko kafa yace yazo ya gaishe da ita ba. Idan zuwan yayi ma gaisuwa ce take hadata da shi, yanda yake magana kamar an shaqe shi an saka shi dole na daya daga cikin dalilin da yasa ko tambayar shi ya sauran yan uwan shi batayi. Tas ya gama shigo da kayan abincin da suka hada harda doya da mai fari da na ja, tukunna ya kalli Daada yana furta;

“Ina kwana”

Murmushi tayi

“Lafiya kalau babban dan aike, sannu da kokari, Allah yayi albarka.”

Salim ya amsa da

“Kitchen zan shiga da su?”

Maimakon amsa addu’ar da tayi mishi, ya jita, ya kuma amsa a zuciyar shi, maganar duk da zai motsa labban shi yayi ta in yana da halin takaitata zaiyi. Kai Daada ta jinjina mishi tana komawa cikin dakin dan ta bashi hanyar wucewa, haka ya dinga daukar kayan yana kaiwa Kitchen, ya kuma yi mata magana dan ta nuna mishi inda zai saka mata komai, yana karasawa yace

“Gas fa? Daddy yace in dauka a sake filling.”

Kofar da zata hadaka da bayan kitchen din inda cylinder din gas din take Daada ta nuna mishi ya wuce ya kwanto, daman ya kare, ko da safen a risho Madina ta soya musu dankali, basa rabuwa da kalanzir a rishon su tunda gas idan ya tashi karewa babu ruwan shi da ka cika tukunya da shinkafar da ta dauko dahuwa.

“Da ka taimaka in kira Madina sai ka kaimun ita kasuwa tayo mana cefane…siyayyar da dan dama kar in saka yawo a kasuwa.”

Numfashin Salim ya fitar yana dan daga mata kai a hankali, in ba ita ba, babu mai saka shi wannan aikin. Shi Madinar ma rabon daya saka ta a idon shi harya manta, idan zai fadi gaskiya ya ma manta da ita ne gabaki daya sai yanzun da Daada ta ambace ta, ba zai manta surutun yarinyar da yake hau mishi kai tun tana yar mitsitsiyarta ba. Balle kuma yanzun da yasan ta fara jin tashen yan matanci, yasan waye shi, tun kafin mata su kara nuna mishi shidin wani ne yasan ko da bashi da kudi yana da kyan da suke bi kamar zasu lashe shi. Yanzun ko matan da yake bi yana da mugun zabe, kuma kashe din shi na farko shine.

“Bana son surutu, komai zai mun dai-dai idan zamuyi abinda zamuyi mu gama banji muryar ki ba…”

Manyan mata ma, riqaqqu suna rikicewa a kan shi balle yan yaran nan da yake gani yan aji daya a makaranta suna bin shi kullum da.

“Yayaa Salim dan Allah zaka duba mun assignment dina.”

Har rasa yanda akayi ya zama Yayaa a wajen su yake yi, yakan karba a wajen ya nemi bango ya dora idan na abin rubutawa ne ya rubuta musu, su kadai kuma yake tsayawa har ya danyi wa bayani wasu lokuttan, saboda ‘yan yara ne, saboda yana da kanwa shima, zai so in ta nemi wani ya taimaka mata da abinda ya shige mata ta harkar karatu ya taimaka mata din. Balle kuma Madina da ba zai iya kiyasta shekarunta a yanzun ba, ko yace zai iya hasaso matakin karatun ta.

In da yake tsaye anan Daada ta dawo ta same shi.

“Ka zo ka zauna kafin ta fito.”

Kai ya girgiza saboda baya son cire takalmin da yake kafar shi, in dai zai karasa cikin falon ya zauna dole saiya cire, ba zai taka mata kafet din da yake shimfide kusan cikin dakin da takalma ba, ko da zai shiga kitchen ta gefe-gefe wajen tayal ya dinga bi. Agogon da yake daure a tsintsiyar hannun shi ya dan daga hannun yana kalla. A cikin kan shi yake hango wasu mintina sha biyar zuwa ashirin kafin Madina ta fito, ya tabbata zata tsaya iyayin kwalliyar nan da yake saka shi kwankwasa dakin Adee ya watsa mata zagi in dai tare zasu fita, baya son jira.

“Banga biro bane ba fa, da zan rubuta abubuwan kar in manta, amman na samu fensiri.”

Muryar Madina ta fara dukan kunnuwan shi kafin ya sauke idanuwan shi akan ta, wani dan karamin sauti ya kwace daga makoshin shi da yafi alaka da tsantsar mamaki. Yanda ya ganta yanzun ya goge duk wani hoton yarintarta da yake da shi cikin kan shi balle ya nemo ya gwada ya tabbatar da wannan yar mitsitsiyar halittar ta gaban shi itace Madinar da ya sani. Zai dawo da batun kankantar ta da ya gani, shigar jikin ta, shigar ta ita ce abinda yasa sautin kwace mishi. Wando ne jeans da ta lankwashe daga kasan kusan ninki biyu kamar yayi mata yawa, sai takalmi kafa ciki, rigar da take jikinta yana da tabbacin ko shi ya saka zai iya yawo a ciki saboda girmanta, hijabin da ta saka da alamu yar karama ce fara, sai ta dora rigar a sama ta yanda kanta da wuyanta kawai hijabin ta rufe.

Bai san me zai kira rigar jikin Madina da ita ba, kaurinta yayi yawan da bai kamata ace ta sakata a yanayin zafin da akeyi ba, ga dogon hannaye rigar take da shi da ta dan ja baya kamar yanda yayi. Rabon da yaga kalar yellow harya manta, sai yau da ya ganta a riga da takalman da suke kafar Madina. Ji yayi kalar har shigar mishi idanuwa takeyi, gilashin da yake idonta ya kai kuncinta saboda girman shi. Daga inda yake yana hango maikon da fuskar Madina takeyi ga kurajen da suke fuskarta da ake kira da pimples, ita din gabaki dayanta kamar an cirota daga wani shirin fim din kasar ketare aka direta a inda take yanzun.

Murmushine ya bayyana akan fuskar shi da yake jin girman shi na kara fadada da duk dakika, rabon da wani abu ya saka shi nishadi irin yanda ganin Madina ya samar mishi harya manta, ko matan da yake bi da ya ture su daga jikin shi yake jin wani duhu ya rufe shi ruf, nishadin daya samu ya dishe kamar anyi ruwa an dauke. Dariya ce mai sauti ta kubce mishi da Madina ta kalle shi tana yin murmushin ta daya bayyana duka hakoranta, sannan ta dan daga hannunta cikin alamar gaisuwa tana son tuna in da ta san shi, kafin cikin mamaki ta ja gilashinta kamar zata cire shi tana sake gyara mishi zama.

“Hamma Salim… Hamma Salim ne ko?”

Ta karasa maganar da alamar tambaya tana kallon Daada da ta jinjina mata kai, itama murmushin takeyi. In dai akan zabin suttura ne na Madina ta hakura. Ba don ita ta wanketa tun jariranta ka ba, haduwa sukayi a hanya zatayi zaton ko mata-maza ce, sai jinsin namijin yayi rinjaye a kanta, ba kwalliya takeyi ba, mai ma kafafuwan ta kawai take shafawa da Daada zata rantse ko tambayar Madina akayi abinda tafi so a jikinta to kafafuwan zata zaba, fuska kuwa in ba muku-mukun sanyi ya shigo ba da sauran jikinta bata damu da shafa musu mai ba,takance fuskarta da kanta take maiko ko bata shafa mai ba.

Yanda bata kaunar hada hanya da duk wani abu daya danganci kyale-kyalen mata yana ba Daada tsoro. Kafafuwan dai sune matsalarta, kullum cikin safa suke, takan ce;

“Daada bakya jin iska na shigar miki kafa?”

Ko

“Daada haka zaki fita baki saka safa ba? Kar wani ya taka miki kafa.”

Haihuwa ta fara bambanta Madina da sauran mata, yanzun kuma kaf dabi’unta. Bata son kazanta, kamshine abu daya da tafi so a rayuwarta, ko dakinta ka shiga wani kamshi mai sanyi ne zai fara dukan hancin ka. Sai dai tana cikin mutanen da basu damu da su mayar da duk wani abu da zasu dauko a mazaunin shi ba, kayane akan gadon ta a cike, Daada tayi fadan harta gaji. Banda litattafan ta, babu wani abu da yake a kammale cikin dakin, ga wajen ajiye takalmanta, Madina wani kwali ta samu tana zuba su a ciki, kayan wanki ma kwalin ne ta samu, har kwando Daada ta siyo mata, a store ta tsinto ko sati daya ba’ayi ba Tsakani.

“Kwandon ne kika watsar Madina? Asarar kudi nayi kenan?”

Ta tambaya

“Wallahi duk ya cika mun dakine fa Daada, ba watsarwa nayi ba, ajiyewa nayi idan na sake shirya dakin sai in masa waje.”

Kyaleta kawai Daada tayi, tasan babu wajen da zatayi mishi, duk shirgin da yake dakin ta, kwandon ne bata so a ciki, tafi gane ta zuba su cikin kwali, irin Madina kam, Daada bata jin ko an tona a fadin Kano zasu kai su biyu. Da wahala ma idan ba ita kadai bace ba, kullum cikin neman wani abu nata da bata san in da ta ajiye ba take. Safa kuwa ko makaranta zataje da wahala kaga iri daya a kafarta, hankalinta a kwance zata hada bakar safa da ja taci gaba da hidimarta, idan anyi magana zata ce

“Banga yan uwan bafa, kuma a cikin wata jaka na saka.”

Tunda dai taji kafarta a rufe shikenan, shisa duka fata da addu’ar ta akan Madina take zagaye da Nawfal. Burin ta mai girma ne, zata kirga lokuttan da ta taba ganin fara’a a fuskar Salim, amman yau ba murmushi bane kawai, har dariya yayi. Ko ba shiga da yanayin Madina ba, ita din takan saka nishadi a tare da duk wanda zata ci karo da shi. Ko bata sanka ba kuka hada ido zatayi maka murmushinta da zai wahala ka kasa mayar mata da shi.

“Muje kafin rana ta bude da yawa.”

Madina ta ce tana wucewa da kara fadin

“Daada sai mun dawo.”

Bin bayanta Salim yayi yana mamakin yanda take iya sauri da gajerun kafafuwanta, ko

“Allah ya tsare ya dawo da ku lafiya.”

Da Daada ta furta bataji ba balle ta amsa, a bakin mota ya sameta a tsaye. Da kadan kanta ya wuce kugun shi, yar dariya ya sake tsintar kan shi dayi yana zagayawa ya sa mukulli ya bude murfin motar ya shiga. Hannu ya mika ya bude mata itama tana shiga ta zauna hadi da jan murfin motar.

“Wacce kasuwar zamu je?”

Salim ya tambaya yana yin baya da motar, dan jim Madina tayi sannan ta amsa shi

“Kasuwar cefane…in da ake saida su nama da kifi.”

Kai Salim ya jinjina, ya kan kai Saratu lokaci zuwa lokaci.

“Hamma Khalid yace likita zaka zama ko?”

Kan dai ya sake daga mata, haka kawai saiya tsinci kan shi da son tambayarta.

“Ajin ki nawa? Me kike son zama ke?”

Kallon shi tayi yana ganin girman gilashinta ta gefen idon shi.

“Aji hudu uku zan shiga hudu yanzun…”

Kamar tasan gilashin yake tunani a ranshi ta kai hannu tana gyara zaman shi, ya kula takan yi hakan ne saboda ta saba, ya zamar mata kamar habit, bata mintina bata kai hannu fuskarta ta gyara zaman gilashin kamar wanda zai fado ba.

“Ina son zama yar jarida.”

Kai Salim ya jinjina

“Glasses dinki…”

Ya soma kafin ya karasa ta amsa da

“Blurred vision…bana ganin abubuwa da kyau sai da shi.”

Dan kallonta Salim yayi yana maida hankalin shi kan tukin da yakeyi. Baisan me yasa yake son tambayar ta abubuwa haka ba, rayuwar mutane ba abinda ya shafe shi bace ba. Tauna bakin shi yayi ta ciki don ya gujema wata tambayar kafin ta sake kubce mishi. Shirun ne yayi ma Madina yawa, saboda ita mutum ce da Allah ya halitta da tambaya da kuma son hira, ko bakunta bata iya ba, ko mun girmanka tasan kalar hirar da zatayi da kai da ba zaisa zaman ku ya gundure ka ba.

“Baka jin kida kai a motar ka? Hamma Khalid da kida a motar shi, duk idan yazo zamu je waje yana kunna mana.”

Cikin sanyin murya Salim ya amsa da

“Bana son hayaniya.”

Bayajin ya taba kunna ko da radio din cikin motar ne tunda Daddy ya bashi ita. Ko TV zai kalla da yawan lokutta sautin gabaki daya a kashe yake, sai dai yayita kallon hotunan.

“Ko kai ma kana da matsalar kunne ne kamar yanda nake da ta idanu?”

Murmushi Salim yayi

“Nace bana son hayaniya kina ta mun surutu.”

Dariya Madina tayi

“Ni bana so idan ba karatu nakeyi ba inji nayi shiru…baya mun dadi.”

Bata kuwa yi shirun ba har suka karasa kasuwa, sai dai a karo na farko a rayuwar shi da surutu bai hau mishi kai ba, asalima ko bai amsa ta ba nishadi take saka shi. Bai fita daga mota ba, anan ya jirata, da yake ta iya wahalar da kanta duk abinda ta siyo sai ta dawo ta kawo sannan ta sake komawa. Da ta siyo kifi harda lemon roba na coke ta hado mishi .

“Kana ta zama ko? Yanzun zan gama, saura abu guda biyu.”

Ta fadi tana mika mishi lemon.

“Ka sha wannan, ko kana jin yunwa in samo maka wani abin?”

Yanda take mishi maganar sai ka rantse yaron goye ne ta bari a mota, dariya ta bashi ba kadan ba

“Wannan ma ya isa, nagode.”

Ya fadi bayan ya karba. Ya kuma ji dadin lemon, da ta gama zasu koma hira ta dinga mishi tana bashi labarin yanda sukayi da inda tayi siyayyar ta.

“Me yasa baka zuwa? Ka dinga zuwa dan Allah…kaga ni ban sanka ba sosai.”

Madina tayi maganar cike da roko tana kallon shi ta cikin gilashin ta, sai ya tsinci kan shi da daga mata kai, murmushin da tayi na saka shi jin wani bakon yanayi .

“Dan Allah da gaske? Ko zaka dawo anjima? Miyar kifi zanyi, da dadi wallahi, Daada tace na iya abinci, ko Hamma Khalid ma yana so inyi idan ya zo”

Kai ya girgiza mata

“Makaranta zanje Madina… Zan dawo ba yau ba dai.”

Cike da fahimta tace

“To shikenan, Allah ya baka sa’a, Allah ya tsare ka ya taimake ka.”

Addu’ar ta fito mata a saukake.

“Amin”

Ya furta yana tsintar kan shi da dorawa da

“Nagode”

Kai ta jinjina tana mishi murmushi, tsaye tayi a kofar gidan kamar tana jiran ta ga tafiyar shi tukunna, shisa yaja motar, ta mudubin shi yake hango tana daga mishi hannuwan ta duka biyun, murmushi yayi, a hankali ya furta,

“Madina…”

Batare da ya san girman rawar da madaukakiyar sunan zata taka a rayuwar shi ba.

<< Rai Da Kaddara 5Rai Da Kaddara 7 >>

5 thoughts on “Rai Da Kaddara 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×