A cikin kunnen shi aka bude kofar dakin duk da baccin da yake mai nauyi ne, kuma da alamu a hankali aka so budewa. Tunda satin bikin Adee ya kama baya samun wadataccen bacci, baisan me akeyi a harabar gidan ba, amman yana jin kai kawon mutanen da ba zaice duk daga ina Nannar su ta samo su ba. In har suna da wasu dangi da suka hada jini dasu a garin Kano daga Daada sai Madina ya sani. Ko da wasa bai taba jin daga Daddy har Nanna sunyi zancen wani dangin su bayan Daada ba. Bai san ko. . .