A cikin kunnen shi aka bude kofar dakin duk da baccin da yake mai nauyi ne, kuma da alamu a hankali aka so budewa. Tunda satin bikin Adee ya kama baya samun wadataccen bacci, baisan me akeyi a harabar gidan ba, amman yana jin kai kawon mutanen da ba zaice duk daga ina Nannar su ta samo su ba. In har suna da wasu dangi da suka hada jini dasu a garin Kano daga Daada sai Madina ya sani. Ko da wasa bai taba jin daga Daddy har Nanna sunyi zancen wani dangin su bayan Daada ba. Bai san ko su Khalid ba, amman shi bai taba tambaya ba, ya yarda cewar idan akwai dangin daya kamata su sani za’a nuna musu su.
A ranshi dai yaga kamar wata uku da aka saka bikin Adee yayi kusa, amman Julde na da halin da zaiyi mata komai, watakila shisa basu jashi da nisa ba. Watannin ma sauri sukayi mishi matuka. Yau dai ya daya rage saura kwanaki biyu daurin aure, ya hada yar jakar shi, zai kama hotel ne har sai an gama hidimar bikin gabaki daya kafin hayaniya ta haukata shi. Karar haduwar takalmi da tayals din dakin kamar sukuwar doki ta sa shi jan wani dogon tsaki.
“Ubanka kakeyi da baka wuce ba har yanzun Khalid?”
Salim ya fadi yana jin kanshi kamar ba zai bude ba, kamar ma jan kafa Khalid din ya sakeyi saboda ya mayar dashi sa’an shi, bude idanuwan shi yayi yana sauke su cikin na Nawfal daya kwashe da dariya.
“Bajjo”
Salim ya fadi cike da kashedin da bai boye murnar shi ba. Ya dauka Khalid ne, ko da wasa baiyi tsammanin zuwan Nawfal din ba.
“Normal mutane ko basu rugo sun tarbeni ba zasu tashi zaune daga kwanciyar su suyi mun sannu da zuwa.”
Cewar Nawfal yana murmushi.
“Da dariya a muryar su.”
Juyawa Salim yayi, yafi son kwanciya akan kujera fiye da yanda yake son kwanciya akan gado. Bai kuma san dalili ba, amman in har yana gida da rana kuma ko da daddare ma zaka gan shi kwance a falo kan kujera .
“Hamma…”
Nawfal ya kira da karfi yana saka Salim jin kamar ya saka lasifika ne.
“Kayi na bakunta Bajjo…karka kara.”
Dariya Nawfal din yayi, tunda ya hau jirgi yake jin shi sama-sama, daya sauka airport ya samu taxi zuwa gida zuciyar shi dokawa takeyi ba kadan ba. Kan shi tsaye bangaren su ya wuce, ranar da aka sa ranar Adee ta kira shi, su tsakar dare ne ma.
“Bacci kake ko? Ban tsaya kirga awanni ba yau, sai da naji muryarka na tuna tsakar dare ne.”
Tashi zaune yayi, banda Adee a gabaki daya rayuwar shi babu wanda yake kiran shi a lokacin da baya daga waya ya dauka, ko da Daddy ne, kusan zaice saboda Adee ne baya saka wayar shi a silent in ba yana cikin aji ba. Shima daya fito yaga kiranta yake bin bayan shi.
“Kace zaka zo bikina Bajjo, idan ba zan takura ka da yawa ba.”
Shine rokon da tayi mishi.
“Zan zo Adee, In shaa Allah zan zo.”
Duk da ba saboda bikinta kawai yazo ba, bikin natane ya karfafa dayan dalilin na shi. Filon kujera da yaji an jefe shi da shi yasa shi rike bayan kan shi.
“Kofato ne a kafarka wai?”
Dariya Nawfal yayi, da gaske ya dawo gida. Sai ma daya tura kofar dakin su yana jin kamshin turarukan Khalid sun daki hancin shi, kafin ya hade tunanin shi waje daya yaji Salim ya watsa mishi zagi. Da gangan da yazo tura kofar ya buga ta, mukulli yabi da shi kar Salim din ya same shi cikin dakin, jakar shi ya fara saukewa yana jan karamin akwatin shi ya ajiye gefe daya. Sai da ya shiga wanka ya fito sannan ya bude dakin, akwatin shi ya janyo ya dauki wata farar riga da wani wando fari iya gwiwa ya saka. Shima baccin ne a idon shi saboda jikin shi ya saba da bambanci lokaci. Kwanciya yayi abin shi.
Cikin bacci yaji kamar ana jijjiga shi, inda yake jin hannun ya kama ya ture yana juya kwanciya.
“Bajjo… Bajjo… Dalla ka tashi.”
Khalid ya fadi muryar shi cike da farin ciki yana sake jijjiga Nawfal din daya daga idanuwan shi dakyar.
“Ka barni inyi bacci Hamma…”
Ya furta yana shirin gyara kwanciya Khalid din yana kai hannu ya janye filon da kan Nawfal yake kai.
“Tashi zakayi muyi labari.”
Wani irin numfashi Nawfal ya sauke.
“Kayi missing dina na sani, amman ina nan, ba yau zan tafi ba ko wani abu, ka kyaleni inyi bacci na.”
Baki Khalid ya bude zai magana Nawfal ya tashi zaune da sauri yana katse shi da
“Kana da kati a wayar ka? Ara mun…”
Fuskar Khalid dauke da alamun mamaki ya zaro wayar shi kirar Nokia yana mika ma Nawfal din da ya karba yana mika hannu ya dauko tashi wayar, kallon shi Khalid yakeyi yana danne-danne da alamar sako yake turawa. Yana gamawa ya mika ma Khalid wayar.
“Nagode”
Yayi maganar hamma na kwace mishi saboda baccin da yake idon shi.
“Ka kwanta, zan fita ne nima, Nanna ta aikeni.”
Da wani yanayi a fuskar Nawfal yace,
“Shine ka tashe ni?”
Dariya kawai Khalid yayi ya mike yana ficewa daga dakin. Kasa komawa baccin yayi, kamar cikin shi jira kawai yakeyi ya farka ya cigaba da tunasar da shi yunwar da yake dawainiya da ita da ta saka shi mikewa zaune babu shiri yana saukowa daga kan gadon gabaki daya. Rigar jikin shi ya kalla, duk ta yamutse saboda baccin da yayi da ita a jikin shi, cire ta yake kokarin yi yaji ana kwankwasa dakin.
“Come in.”
Ya furta yana karasa cire rigar dai-dai lokacin da Salim ya turo kofar yana runtse idon shi.
“Ewwwww, Bajjo”
Dariya Nawfal yayi dan yanda Salim din yayi wani zaiyi zaton babu kayane a jikin shi gabaki daya.
“Ka sa kaya, idanuwa na”.
Cewar Salim da har lokacin idanuwan nashi suke a runtse, rigar daya cire ya mayar a jikin shi yana dariya, a hankali Salim ya dan bude idon shi daya kafin ya bude su gabaki daya yana mika ma Nawfal ledar da sai lokacin ya kula da tana hannun shi, karba yayi cike da mamaki.
“Kifi da dankali na siyo… Bakomai kake ci ba, akwai kayan tea a kitchen.”
Kai kawai Nawfal ya iya jinjinawa saboda wani abu da yaji ya mishi tsaye a zuciya
“Idan baka ci….”
Da sauri Nawfal yake girgiza mishi kai.
“Zanci, ina ci… Miyetti.”
Kallon shi kawai Salim yayi, kafin kaji fulatanci a bakin shi zaka dade, Julde yana musu, Nanna ma lokutta da dama shisa duk suke ji, amman kana iya ma Nawfal magana ya mayar maka da hausa.
“Kar inji motsin ka.”
Hannu Nawfal ya daga yana ma Salim din alamar salute hadi da jinjina kan shi. Sai da ya fice daga dakin sannan ya samu waje nan kasa kan kafet ya zauna ya bude ledar. Harda ice cream har roba biyu, wani irin numfashi ya sauke.
“Allah ya biya maka bukatunka Hamma.”
Ya furta a hankali saboda har ranshi yaji dadin ice cream din fiye ma da kifi da dankalin. Shi ya fara sha tukunna ya ci sauran, yana cikin shan dayar robar Khalid ya shigo da sallamar da kafin ya amsa ya mika mishi wayar shi.
“An maka text.”
Karba Nawfal yayi da sauri yana duba wayar yaga Khalid bai bude text din ba, sai da ya dan sake kallon shi yaga waje ya samu ya zauna yana jan ledar da take gaban Nawfal din da kifin da ko rabi bai ci ba, sake mayar da hankalin shi yayi kan wayar yana karanta text din, replying yayi yana ajiye wayar da kamar haka take jira ta fara ruri, kamar ba zai daga ba, Khalid yake kallo da yake cin kifin shi hankali a wance, daukar wayar yayi yana daga kiran hadi da karawa a kunnen shi, numfashin da bai san yana rike da shi ba ya sauke.
“Jaan…”
Ya kira cikin wani irin sauke murya da yasa Khalid daga kai ya kalle shi fuskar shi dauke da alamar tambaya.
“Wanne zan fara amsawa yanzun? Bakomai fa, na danyi bacci ne.”
Ya amsa kafin yayi jim yana sake fadin.
“Um um, ina zaune, naci abinci, muna tare da Hamma Khalid.”
Murmushi yayi yana mika ma Khalid din waya.
“Ana son magana da kai.”
Yanayin fuskar Khalid din na saka shi yin yar dariya, karbar wayar Khalid yayi ya kara a kunnen shi hadi da yin sallama.
“Kullum sai naji labarin ka.”
Aka furta daga dayan bangaren bayan amsa sallamar shi, cikin wata murya mai sanyin gaske, idanuwan Khalid na kan Nawfal yace,
“Abin mamaki ganin yanda ni banji naki labarin ba.”
Zunguri Nawfal ya kai mishi.
“Hamma”
Ya kira a hankali, kafadu Khalid ya dan daga, yarinyar da har lokacin bai san sunanta ba tayi dariya mai sanyin sauti kamar muryar ta.
“Sunana Murjanatu. Yar asalin Nigeria, garin Adamawa, an haifeni a New York, I’m your brother’s girlfriend.”
Ta karasa maganar cikin harshen turanci, yanayin yanda ta ajiye kowacce kalma na sake tabbatar wa da Khalid din da gasken tashin turai ce, sai dai kalamanta na karshe sun saka shi rasa abinda zai fada ko abinda ya kamata ya fada, har Nawfal ya miko hannu ya zare wayar daga kunnen shi bai ce komai ba.
“Hello…”
Nawfal yace yana dorawa da.
“Ina da tambayoyi da tarin bayanai da zanyi, muyi magana anjima?”
Kai ya jinjina yana sauke wayar daga kunnen shi yana kallon Khalid.
“Ban tabbatar ba shisa ban fada maka ba, da na tabbatar kuma bansan ta inda zan fara ba… Kawai ya faru ne.”
Numfashi Khalid yaja yana fitarwa a hankali, soyayya abune da yake hange da nisan gaske a rayuwar shi, duka shekarar shi ta uku yake a jami’a, yana son tsayawa da kafafuwan shi, tsayuwar da idan wata ta jingina da shi ba zasu fadi ba su dukan su.
“Kace wani abu dan Allah.”
Nawfal ya fadi yana kallon Khalid din, Murjanatu ce abu na farko da yaji baya bukatar amincewar kowa a kai, amman yana son goyon bayan Khalid, ko yaya ne yana son Khalid ya kara mishi karfin gwiwa.
“Ban san me zance ba ne ba.”
Khalid ya furta cikin sanyin murya yana dorawa da.
“Da gaske na rasa abinda zance, na san abune da zai faru wata rana, amman yanzun baiyi sauri ba?”
Kafadu Nawfal ya dan daga mishi cikin rashin tabbas, mutane na tsoron abubuwa mabanbanta, kananu da manya, duka biyun ne suka hade mishi waje daya, babban tsoron shi bai wuce kasancewa shi kadai a filin duniyar shi duk kuwa da rashin girman ta, yana da su ya sani, amman ba zai kira su nashi shi kadai ba, Nanna ta sha jaddada mishi ita da duka ahalinta ba nashi bane ba, rabasun da takeyi da shi ba zabinta bane ba, dole akayi mata. Yana son ya samu wani abu da zai kira nashi.
“Nawfal…”
Khalid ya kira yana saka shi sauke numfashi.
“Ban sani ba Hamma, watakila yayi sauri, kawai ya faru ne…”
Baki Khalid ya bude zaiyi magana aka kwankwasa dakin.
“Waye? Shigo?”
Cewar Khalid bayan an sake kwankwasa dakin a karo na biyu.
“Nanna tace ka fita da motar ta a duba za’ayi abu da ita yau.”
Kai Khalid ya jinjina.
“Ka karbo mun mukullin…”
Sanin halin Lukman ya sa shi mikewa ya bude kofar yana kiran Lukman da har ya kusa kofar da zata fitar dashi daga bangaren nasu.
“Yanzun fa, ka dawo yanzun ka kawo mun.”
Juyawa kawai Lukman yayi cikin sanyin yanayin shi da baisa tafiyar shi ta kasance ta malalata ba. Yana da kazarniya sosai, kawai hayaniya ce bayayi, dan ta Lukman duniyar bata tashi ba, babu wanda zaice ya taba ganin ran yaron a bace, ko a ranakun da babu makaranta ba kullum kake ganin shi ba. Komawa cikin dakin yayi, kallon ledar kifin da yake ci yayi cikin wani yanayi da yasa Nawfal fadin.
“Ka sa a fridge mana, in ka dawo sai kaci a nutse…”
Dan jim Khalid yayi.
“Bafa harshen kowa bane irin naka…zaiyi sanyi, bari dai in kai Kitchen kawai. Muyi magana idan na dawo?”
Ya karasa yana tsugunna ya tattara ledar kifin.
“Ni ma zanje wajen Daada, na so inga Adee, naga kaman akwai mutane da yawa a bangaren.”
Kai Khalid yake girgiza mishi tunda ya kira sunan Adee din.
“Bata gidan ma, ni na kaisu wajen gyaran gashi ne ko meye ita da kawayenta tun dazun, tace in sun gama zata kira ni…ka shirya, bari in bi Lukman in karbo mukullin sai in sauke ka.”
Khalid ya fadi yana fita daga dakin da ledar kifin shi a hannu. Shima tashi yayi yana hada duk wani abu da yake son tafiya da shi gidan Daada din a jakar shi ta goyo, dan sai da Khalid ya dan jira shi da ya dawo, ko rigar da yaso ya sake bai samu ya saken ba suka fita.
*****
Daga bakin titi Khalid ya sauke shi saboda motar nata rirrikewa, da kafafuwan shi ya taka ya karasa shiga, yana hango gidan yana jin zuciyar shi na tsalle har cikin tafukan kafafuwan shi, dan duk wani taku da zaiyi sai ya kara gudun zuciyar shi. Bai san yayi kewar Daada har haka ba sai da ya taka soron gidan yaji tsalle-tsalle da zuciyar shi takeyi, rabon da ya ji shi kamar yaro dan shekara uku da yake dokin ganin wani nashi haka harya manta. Kamar ya karasa da gudu ya shiga cikin gidan haka yake jin shi.
“Daada…Daada Am…”
Shine abinda ya iya furtawa a madadin sallama, sunan na fitowa daga wani lungu na zuciyar shi inda yake jin kewar Daada kamar yasa ihu.
“Daada…”
Ya kara kira yana jin kafafuwan shi sun gaji, kamar dakin nata ya kara nisa. Daada da take daki a zaune, hankalinta yana kan labaran da take kallo a talabijin dinta ta jiyo muryar shi a kiran farko da yayi mata, kira na biyu ne yanayin yanda ya furta “Daada Am” din ya saka taji kamar ruhinta ne yake shirin kubcewa daga gangar jikinta saboda yanda muryar ta dake ta.
“Bukar…”
Ta furta da wani irin yanayi mai wahalar fassarawa tana dafa kujera ta mike dakyar, kira na ukku ne ya mayar da ita ya zaunar tana wani irin maida numfashi, zuciya kenan, babu abinda ya kaita wahala a kaf halitta ta tsarin jikin dan adam, da bata yaudare su haka ba. Kafin tunanin ta ya tsawaita Nawfal ya karasa bakin kofar inda yayi tsaye kamar yana son daukar sababbin hotunanta ne cikin kan shi ya adana a kusa da tsofaffin da yake da su.
“Daada…”
Ya sake kira cike da tsantsar kaunar ta, ya manta yanda ita kadai take saka shi yaji abinda yake ji haka, yanda matsayinta ba zai taba haduwa da na kowa ba a wajen shi.
“Bajjo”
Ita ma ta kira shi, sai dai nata idanuwan ba kaunar jikan nata bane da kewar shi kawai, harda hawaye taf a cikin su da wani yanayi a shimfide da ita kadai zata iya fassara shi. Ko takalma bai cire ba ya karasa cikin dakin, itama mikewa tayi yana samunta a tsaye, batare da tunanin komai ba ya zagaya hannuwan shi yana riketa a jikin shi.
“Ina kaunar ki Daada, ban taba fada miki ba ko? Yau dai na fada, nayi kewar ki da yawa… Ba kadan ba fa, da yawa sosai har bansan ya zanyi in fada ba.”
Dariya tayi, hawayenta na samun damar zubowa, yayi girma saboda ba zaka kirata gajera kai tsaye ba, amman kanta da kadan ya karasa kirjin Nawfal din, sake riketa yayi kamar zai cike gurbin kewarta da yayi na shekaru biyu.
“Kashin tsufa Bajjo, karka karyani.”
Dariya sukayi a tare yana sakinta dakyar, dan har lokacin wata irin kewarta yakeyi kamar bata tsaye a gaban shi.
“Ina Madina?”
Ya tambaya yana kallon cikin dakin da bai canza mishi ba sam.
“Tana dakin ta da littafi, in dai da littafi a hannun ta bata ji bata gani.”
Dariya ya sake yi yana zame jakar shi daga kafada ya ajiye akan kujera, sai lokacin kuma ya kula da takalman da suke kafar shi, dan murza goshin shi yayi, yana rankwafawa ya zare takalman ya dauke su ya mayar bakin kofa, da hannu ya nuna inda yake tunanin dakin Madina ne cikin alamar neman tabbaci, kai Daada ta daga mishi, kai tsaye ya nufi bakin kofar yana kwankwasawa, jin shiru ya saka shi sake Kwankwasawa da karfin wannan karin, yanda ya kasa kunnen shi yasa shi jin takun tafiyar ta, shekaru biyu kamar wasa.
Zuciyar shi bata doka ba sai da yaga ta murza kofar alamun budewa zatayi, idan yace yanayin da yake ciki yana da fassara zaiyi karya. Numfashin shi ne ya dan tsaya na dakika kafin yaja iskar da itama baiji inda ta tafi ba bayan Madina ta bude kofar, wandone a jikinta ta nannade shi har kusan gwiwarta, sai rigar sanyi marar nauyi, mai hade da hula da ake kira da hoodie a turance, dogon hannu ne shima ta ja shi kadan, hular nada zaren da ta kama ta kulle shi dan hular ta zauna mata a kai sosai, sai gilashin ta da ya rufe rabin fuskarta.
Ko ya hasaso yanda Madina ta koma a shekaru biyu rak yanzun daya ganta tsaye a gaban shi komai ya goge, su duka kallon juna suke, ita tana mamakin yanda akayi ta gan shi a kofar dakinta, karatu take na wani littafin kimiyya da Salim ya siyo mata, da highlighter a hannunta tana shaida a duk wajajen da take da tarin tambayoyin da idan yazo zata tsare shi ya amsa mata taji an kwankwasa dakin, zaton ta Daada ce zata tambayeta wani abin da ta ajiye ta rasa inda ta kai shi. A nisantaccen mafarki bata hango kasancewar Nawfal cikin gidan ba, shisa ganin shi ya zama kamar an kwada mata guduma a tsakiyar fuska.
“Madina”
Ya kira, muryar shi na dira cikin kunnuwan ta, tana nan yanda take, muryar shi, sam bata canza ba duk da ta dade bata jita ba, shi dinma banda tsayi bata jin ya canza.
“Madina…”
Ya sake kira ganin kamar ta kasa yarda shi dinne a tsaye, dariya yayi mai sauti yana kai hannun shi ya taba goshin ta da tayi kokarin karewa tana murmushi.
“Kin canza.”
Ya furta saboda ya kasa rikewa a cikin shi, ta canza ba kadan ba, wani irin canji da bai taba tunani ba.
“Hamma… Da gaske kaine?”
Tace tana kasa daina murmushi, kai Nawfal ya daga mata shima ya kasa daina murmushi, ganin yana kara takowa cikin kokarin hade space din da yake tsakanin su yasa ta daga hannun ta tana matsawa, kai take girgiza mishi, duka alamu sun nuna rungumarta yake sonyi, shi din dan uwanta ne, duk da na rana daya Daada bata taba mata bayanin dangantar da take tsakanin su ba. Ta san shi din baya cikin jerin mazan da suka halarta su rungumeta, tana zuwa islamiyya, tana kuma iya kokarin ta na ganin bata tsallake wasu layuka da zasu iya wasa da lahirarta ba.
Babban abinda take tsoro bai wuce kwanciyar kabari ba, lahira na ba Madina tsoro fiye da zaton mai zato, ko mutuwa taji anyi duk yinin ranar bata da sukuni, musamman idan a cikin unguwar sune, sai ta kasa cire tunanin yanda mala’ikan mutuwa ya kasance unguwa daya da ita, amman ba wajenta yazo ba, tuni dai yayi mata na zuwan shi babu sanarwa.
“Madina…”
Nawfal ya kira wannan karin yana jan sunan nata, dariya tayi, mamaki yake ba kadan ba, har tayi girma haka, girman da take kokarin jan layi a tsakanin su. Hango ranar daya bar kasar yakeyi, yanda dakyar ya bambare Madina daga jikin shi, dakyar ma ta bar shi ya tafi, amman yanzun har tayi girman da take ganin ta wuce ya rungumeta, shekaru biyu suna da nisa ne har haka? Yayi tambayar cikin kan shi yana neman amsa duk a waje daya.
“Fito to… Nayi kewar ki.”
Dariya tayi sosai.
“Ni ma haka, baka kira sai nayi bacci.”
Kallon ta yayi.
“Ke kuma ba zaki jira ni ba.”
Dariyar dai ta sake yi, har lokacin ta kasa yarda shine a gabanta, wani irin yanayi take ji har jikinta na daukar dumi saboda murna. Tare suka jera zuwa falon, sam ya kasa daina kallon ta, sosai ta canza mishi kamar ba Madinar da ya sani ba, dariyar ta ce kawai bata canza ba, har yanzun idan tayi dariya duka idanuwanta sai sun rufe, sai su kansu idanuwan, basu kara girma ba. Kallon ta kawai na saka shi jin lallai yazo gida. Wani numfashi da baisan yana rike da shi ba ya sauke bayan ya zauna.
“Daada baki ce mun zai zo ba.”
Kallon shi Daada tayi.
“Nima ban san zai zo ba Madina, yanda kika gan shi haka nagan shi.”
Kai Madina ta jinjina tana murmushi.
“In kawo maka ruwa?”
Ta tambaya saboda ta ma rasa abinda ya kamata tayi, kai Nawfal ya daga mata badon yana jin kishin ruwa ba, shima zuciyar shi ta cika taf da farin ciki. Yana son ganin Adee da Daddy, amman anya kuwa zai iya barin gidan Daada a yau? So yake ya kwana suna labari, in sun gaji suyi shiru su zauna tare da juna kawai, wannan yanayin na yau yana son ya adana shi a wajaje fiye da zuciyar shi yanda in ya tafi zai dinga ziyartar wajajen suna saka shi nishadi. Ruwan kuwa ta kawo mishi a kofi ya karba.
“Abinci fa?”
Kai ya girgiza mata yana saka dayan hannun shi ya bubbuga gefen shi kan kujera
“Ki zauna muyi labari… Nayi kewar ku da yawa…”
Zaman kuwa tayi, Daada na bin su da kallo zuciyar ta cike da farin cikin, tsoron da take kwana da shi tana tashi yana barinta da ganin Nawfal din. Idanuwanta ne kawai akan su, tunaninta yayi nisa, ba zatace ga abinda suke fada ba, amman dariya sukeyi, sosai dariya suke kamar basu da wata damuwa a fadin duniya.
Haka take son ganin su tare da juna cikin farin ciki. Haka take fatan rayuwar su ta kasance. Sai dai kaddara ta riga fata