Skip to content
Part 1 of 4 in the Series Ranar Birthday by Abba Abubakar Yakubu

Fadakarwa

Wannan labari an ƙirƙire shi ne domin faɗakarwa, ilimantarwa da nishaɗantarwa. Ba a yi shi don cin zarafi, ɓatanci, ko aibata wani ko wata ba. Ko da kuwa an ga wani sashi na labarin ya yi kama da wani abu da ya faru na zahiri to, dace ne kawai aka samu.

Doka

Ba a yarda wani ko wasu su ɗauki wannan labari ko wani sashi da cikinsa don sa wa a cikin wani littafin na daban, ko a cikin fim, ko wani aiki na bincike ta fuskar ilimi ba, har sai an nemi izini daga marubucin labarin.

Sadaukarwa

Na sadaukar da wannan littafi baki ɗayansa ga kakata, wacce ta yi raino na kuma ta tarbiyyar da ni tun ina ƙarami, marigayiya Hajiya Lauratu Garba Fari. Allah Ya ƙara haskaka makwancinki, Ya yi miki sakayya da gidan Aljannatul Firdaus. Amin.

Jinjina Ta Musamman

Ya zama wajibi a gare ni in jinjinawa jarumina, kuma abokina Jibrin Adamu Jibrin Rano (Barista) wanda da tallafinsa da goyon bayansa, wannan littafi ya zo hannunku har ku ke karantawa. Babu shakka ban san irin godiya da jinjinar da zan yi masa ba. Ina roƙon Allah Ubangiji Ya saka masa da mafificin alheri, Ya ƙara ɗaukaka darajarsa da mutuncinsa. Ya kuma ƙara albarka a rayuwarsa da ta iyalinsa. Sannan ba zan taɓa mantawa da gwarazan Gasar Hikayata ta BBC Hausa na 2022, Amira Souleymane, Hassana Labaran Ɗan Larabawa, da Maryam Muhammad Sani, bisa tallafin da suka bayar na buga wasu littattafai da suka cancanci a wallafa su, ga marubutan da ba su taɓa buga littafinsu ba, wanda nima nawa ya samu shiga. Allah Ya ƙara haɗa kanku, kuma Ya ƙara muku basira da ɗaukaka. Na gode ƙwarai da gaske.

Tukwici

Wannan littafi tukwici ne ga dukkan ýan’uwana marubuta, maza da mata, daga ƙungiyoyin marubuta daban daban, musamman marubuta na jihohin Filato, Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, Gombe, Sakkwato, Zamfara, Kebbi da Neja. Ina yabawa da zumuncinku da goyon bayanku da addu’o’inku gare ni. Ba zan manta da mambobin ƙungiyata ta Jos Writers Club irin su Sumaiyya Babayo Abdullahi, Badawiyya Ahmad Mu’azu, Aisha Sani Abdullahi (xayyeesherthul-humaerath), Tameem Garga, Asma’u Abubakar Musa (Jasmine), Ummu Salma (Queeyn Salmerh), Ummu Abiha Tasiu, sai Mubarak Abubakar Idris, Kano. Har wa yau, ina yabawa ƙwarai da girmamawa da karamcin dukkan mambobin ƙungiyar Jarumai Writers Association, musamman shugaban ƙungiyar Nana Basira Abubakar Musa, Khadija Salis Ibrahim, Iƙilima Adam, Fadila Sani Bakori, Zee Sardauna, da sauran mambobin ƙungiya baki ɗaya.

Godiya

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya nufe ni da kammala rubuta wannan ƙaramin littafi mai suna RANAR BIRTHDAY, wanda na rubuta shi da zimmar faɗakar da ýan’uwana Musulmi game da wasu abubuwa da muke aikatawa na nishaɗi a rayuwa, waɗanda duk da ba su haramta kai tsaye ba, amma muna shigar da wasu bidi’o’i da za su iya haramta aikin, saboda munin su. Ina fatan Ubangiji zai karɓi wannan aiki da na yi da kyakkyawar niyya, Ya kuma yafe min kurakuran da na aikata.

Sannan zan miƙa godiya ta musamman ga mutanen da suka kasance makusantana kuma masoyana, sakamakon gudunmawar da suka bayar a rayuwata. Iyayena, da suka riga mu gidan gaskiya, Marigayi Yakubu Sarki Garba Fari, da Marigayiya Salamatu Yakubu, ina addu’ar ubangiji Ya ƙara haskaka makwancinku baki ɗaya, Ya kuma yafe dukkan kurakuranku. Babu shakka ba ni da madadinku a rayuwa.

‘Ýan’uwana na jini da bani da kamar ku, Hajiya Kande Isma’il, Kabir Yakubu Sarki, Amina Abubakar Sadeeq, Safiyanu Yakubu, Abubakar Maharazu, da sauran ýan’uwa baki ɗaya, ina yi muku godiya ƙwarai da gaske. Allah ya bar zumunci.

Ba zan manta soyayyarku da ƙaunarku gareni ba, matana abin alfaharina Fatima Abubakar Yakubu, da Fatima Saleh Abubakar. Sai ýaýana masu albarka, Aliyu Abubakar Yakubu (Imam), Yakubu Abubakar Yakubu (Sayyid), Hameed Abubakar Yakubu (Aslam), Abubakar Abubakar Yakubu (Ashraf). Allah Ya ƙara ƙauna da zaman lafiya a tsakanin mu baki ɗaya, Ya kuma bar mu tare cikin aminci da fahimtar juna.

Ina ƙara godiya da yabawa gareku abokaina da malamaina, Malam Hassan Ahmad Yaro, Malam Auwal Abubakar Mustapha, Mubarak Idris Abubakar, Malam Kabiru Yusuf Fagge, Malam Ibrahim Muhammad Indabawa. Malam Muhammad Bashir Yahuza Malumfashi, Malam Muhammad Kabir Muhammad, Malam Al-Ameen Ciroma, Malam Ibrahim Hamisu, da sauran ýan’uwa da abokan arziƙi.

Allah Ya sakawa kowa da alheri. Na gode ƙwarai da gaske.

Babi Na Daya

A shekarun baya can ba kasafai za ka ji ana maganar wani ko wata na shirya bukin zagayowar ranar haihuwa ba, musamman a nan ƙasar Hausa, saboda al’adu da yanayin fahimtar da aka yi wa koyarwar addini a lokacin. Ba wai babu masu shirya bukin zagayowar ranar haihuwa ba ne,

amma ko da akwai ba su da yawa, kuma ana yi musu kallon ‘yan boko ne masu iƙirarin wayewa, ko kuma ma dai ba Musulmai ba ne.

Amma a hankali a hankali wannan al’ada ta shirya bukin zagayowar ranar haihuwa da aka fi sani da Birthday Party tana ƙara samun karɓuwa a tsakanin Hausawa Musulmi, maza da mata, musamman ‘yan mata da jaruman shirya finafinai, mawaƙa da wasu fitattun mutane ko masu ganin gabansu da kyau, wato masu hannu da shuni!

Rukayya Mohammed da ake yi wa laƙabi da Rukky na ɗaya daga cikin rukunin waɗannan mutane, kasancewar ta marubuciya kuma ‘yar makaranta, wacce ke da ilimi da wayewa daidai gwargwado a ɓangaren addini da boko. Ƙawayen ta na unguwa da wasu ‘yan makarantar su Musulmi suna kiranta da Ustaziyya, saboda yadda take da kamun kai, natsuwa da son addini. Duk da kasancewarta budurwa matashiya, hakan bai hana ta suturce jikinta da kaya na mutunci, wanda ke ɓoye surar jikinta da ƙara mata kwarjini a idon mutane ba.

Idan ba wanda ya santa ba, duk wanda ya ganta a waje tana tafiya zai yi mata zaton ko matar aure ce, saboda yadda take rufe fuskarta da wani bakin kyalle da aka fi sani da Niqab, wato ƙyallen da ake ɗaura shi a kan hijabin da aka sa domin ya ƙara suturce fuskar mace, sai dai ƙwayar idanunta kawai za a gani.

Idan tana tafiya, takun ta gwanin ban sha’awa, cikin natsuwa da wani yanayi na rausaya ba tare da ya ja hankalin maza da ke waje ba. Amma duk da haka idan har mutum bai kai zuciyarsa nesa ba, da ƙyar ya kiyaye da kallo ɗayan da Sunnah ta amince ya yi wa macen da ba muharramar sa ba. Kai, ko da mace ce ‘yar uwarta sai ta waiga ta sake kallonta.

Sau da yawa za ka ji mata na gulmar yadda take tafiya, kamar mai tausayin kasa ko kuma a rika ce mata Rukayya Yanga, duk kuwa da cewar ita har ga Allah a zuciyarta ba da niyyar yanga take yi ba. Haka dai tafiyar ta take, tun ma tana ƙarama. Abin da wasu da suka yi mata farin sani ke ganin yana da nasaba da gado, saboda an ce kakarta ta wajen uba, Hajiya Zuwaira wata kyakkyawar bafulatana ta yi tashen kyau kuma ta yi wasa da zuciyar maza. Sakamakon yadda aka ce take tafiya da rangwaɗa da nuna isa da ƙasaita na cikar ‘ya mace.

Ko da yake ita Ruƙayya ba ta biyo ta a cikar kyawun da ake kururutawa ba, amma fa ita ma ba baya ba ce. Tana da kyan diri da sura mai ɗaukar hankalin duk wani ɗa namiji da tsautsayi ya sa

ya ƙyallara ido ya ganta lokacin da ba ta sanye da burmemen hijabin da ta saba sanyawa, wato idan tana cikin gida kenan. Don hatta ‘yan uwanta mata suna yaba kyan halittar ta, duk da yake ba jin daɗin hakan take yi ba. Don haka ne ma mafi akasarin lokuta idan dai ba a cikin ɗakin ta take ba to, ba za ka rasa ta da hijabi ba, ko doguwar riga sakakkiya da ba ta bayyana surar jikinta.

Sai dai duk wannan abin da Ruƙayya take yi, ba tana yi ne don rashin wayewa ko duhun kai ba, tana hakan ne saboda biyayya ga umarnin ubangiji na tsare kai daga shaiɗan da idanun mazan da ba muharramanta ba. Sannan ta bambanta kanta daga ‘yan matan da suke bayyanar da kyan halittar su, don jan hankalin maza, da nuna rashin damuwa da sharrin da hakan ke haifar wa ga al’umma, musamman ma dai yadda batun yi wa ‘yan mata da ƙananan yara mata fyaɗe ya yi yawa a cikin al’umma.

Ta yi ajiyar zuciya yayin da take kammala shiryawa bayan ta sanya doguwar riga, mai launin ruwan ganye da aikin ruwan zinare a ƙirjinta da wani ƙaramin hijabi fari da ya sauka kan kafaɗarta, kamar dai irin shigar nan ta matan ƙasar Malaysia, bil hasali ma dai kayan ma tsaraba wata matar yayanta Al-Ameen ta kawo mata daga can Malaysia, bayan sun dawo daga karatun shekara biyun da yayanta ya je yi, inda ya yi karatun digirinsa na biyu kan fasahar ilimin sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Ta koma ta zauna kan ƙaramar kujerar da ta tashi daga kai, tana fuskantar madubin kwalliya da ke cikin dakin.

Yau ce take murnar zagayowar ranar haihuwarta, wato huɗu ga watan Afrilu. Tun da take ba ta taɓa shirya wani buki ko wata hidima don wannan rana ba, akasari ma har sai ranar ta zo ta wuce ba ta ma tuna da ita ba. Saboda a ganinta babu wani abin buki ga mutumin da yake ƙara kusantar kabarinsa, kwanakinsa a duniya na ƙarewa.

Amma a bana ta sha alwashin in dai har Allah ubangiji ya ja kwanan ta, za ta shirya wani ƙwarya ƙwaryar taron mata, musamman kawayenta da sa’o’inta ‘yan mata da suka ɗauki bukin zagayowar ranar haihuwa ko Birthday Party wani abin gasa da tilastawa kai, dole sai an yi, don kada a riƙa musu kallon rashin wayewa. Wani lokaci ma har su kai ga aikata haramun, don dai su cimma burinsu.

Burinta shi ne ta faɗakar da su yadda ya dace a Musuluntar da irin waɗannan bukukuwa, don su dace da koyarwar Musulunci. Ko da yake dai kai tsaye Musulunci bai zo da batun shirya bukin zagayowar ranar haihuwa ba, amma hadisai sun kawo yadda Manzon Allah (wanda tsira da aminci suka tabbata a gare shi) yake azumtar kewayowar ranar haihuwarsa. Kamar yadda ita ma a yau take cikin azumi.

Sannan kuma ta nunar musu cewa, za a iya shirya taro a yi murna ba tare da an saɓawa Allah ko an ɗauki zunubi ba, yadda kuma za a ƙaru da juna har kuma a samu tsarabar da za a yi ta tunawa da ita har wata shekarar ta zagayo.

Ta dai aika da gayyata ga daliban makarantar su ta Islamiyya da makarantar su ta haddar Alƙur’ani da suke zuwa kullum da asuba, ban da Alhamis da Jumma’a, da kuma ƙawayenta na cikin anguwa da wasu ‘yan uwanta na jini. Musamman yanzu da kusan kowa ke gida saboda rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya ta sa aka yi, saboda yaƙi da yaɗuwar cutar COVID-19 da ake kira da Corona Virus, cutar da aka ce tana saurin yaɗuwa a tsakanin jama’a.

Shi ya sa ma ta takaita iya yawan mutanen da ta gayyata, kada su wuce 30 zuwa 40. Kuma ta sa aka shirya wurin zaman ta yadda za a samar da tazara na mita biyu tsakanin baƙin nata, don biyayya ga ƙa’idojin da masana harkar lafiya suka bayar na zaman jama’a, don a rage cunkoso da matsuwa a wajen zaman jama’a. Ta kuma aika da bokiti mai kan fanfo da ta sa aka sayo mata a kasuwa jiya, aka zuba ruwa da garin sabulu mai dauke da sinadarin kashe kwayoyin cuta, don a ajiye a kofar shiga dakin taron da za a gudanar da taron, domin a riƙa wanke hannaye kafin a shiga.

Ta dauki waɗannan matakai ne domin yin biyayya ga shawarwarin da mahaifin ta Dakta Abdallah babban jami’in lafiya ne, a Babban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, ya ba ta, yayin da take bayyana masa burinta na shirya wannan buki mai tarihi a wajen ta.

Sannan kuma don ta ƙara nuna muhimmancin da ɗaukar waɗannan matakai na rigakafi ke shi, sakamakon yadda ta lura mata sun saki jiki babu ruwansu da ɗaukar matakan kariya, sai dai surutun kawai a baki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Ranar Birthday 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×