Tana zaune a ɗakinta kan gado tana sauraren karatun Ƙur'ani cikin ƙira'ar Sheikh Minshawi tana bi a hankali ya turo ƙofar da murmushi a fuskarshi.
Murmushin ta mayar mishi, sai da ayar ta kai ƙarshe tukunna ta kashe.
"Yaya Mamdud... Ka shigo mana."
Shi ga ya yi yana jingina bayanshi da ƙofar.
"Karatun da kike ne ya min daɗi shi ya sa na shigo."
Murmushin da ke fuskarta ya sake faɗaɗa.
"Ina son karatun shi ne."
Numfashi ya ja yana sauke shi da wani nisantaccen yanayi da ya sa ta faɗin. . .