Skip to content
Part 37 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Tana zaune a ɗakinta kan gado tana sauraren karatun Ƙur’ani cikin ƙira’ar Sheikh Minshawi tana bi a hankali ya turo ƙofar da murmushi a fuskarshi. 

Murmushin ta mayar mishi, sai da ayar ta kai ƙarshe tukunna ta kashe.

“Yaya Mamdud… Ka shigo mana.”

Shi ga ya yi yana jingina bayanshi da ƙofar. 

“Karatun da kike ne ya min daɗi shi ya sa na shigo.”

Murmushin da ke fuskarta ya sake faɗaɗa. 

“Ina son karatun shi ne.”

Numfashi ya ja yana sauke shi da wani nisantaccen yanayi da ya sa ta faɗin, 

“Lafiya dai? Menene?”

Girgiza mata kai ya yi. 

“Come on Yaya Mamdud… Za ka iya yarda da ni. Ka zo ka zauna mu yi magana…”

Zainab ta ƙarasa tana gyara zamanta kan gadon don ya samu waje. Bai musa ba ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon. Shiru ta yi tana kallon yadda yake kokawa da abinda ke damun shi. 

Yadda koma menene yake da nauyin fitowa daga bakin shi. 

“A rayuwata ina son in zama uban da yarana za su yi alfahari da shi. Ina son basu komai na rayuwa in zan iya.”

“Me zai hana? In sha Allah za ka basu.”

Girgiza kai ya yi. 

“Ba da kuɗi ba kawai, ina son kasancewa a komai na rayuwar su, makarantar su, komai.”

Daƙuna fuska Zainab ta yi don ba ta ga matsalar ba har lokacin. Ɗago kai Mamdud ya yi yana kallonta cikin fuska

“What if yarana suka zo in koya musu karatu?”

Dariya zainab ta yi. 

“Kaifa kake koya min abu idan bangane ba. Wannan ba zai zama matsala ba. Kuma ba gani ba, ga su Yaya Anees in ba ka da lokaci.”

Cike da damuwa ya ce, 

“Ba karatun boko ba… Na addini Zainab. Da girmana na samu na ɗan shiga Islamiyya don ina sallah ne kawai yadda na ga kowa na yi. 

A nan na samu na san menene sallah, ya zan yita dai-dai da gyaran kuskurenta. In za ki yankani bazan iya karanta miki Ƙur’ani ba. 

Sai surori guda shida da na haddace a kaina saboda gabatar da sallah. Ina son sanin addinina…”

Kallon shi Zainab take cike da tausayawa. Ko da su Mummy suka watsar da su. Koda basu samu kulawar su ba, sai Allah ya basu Labeeb m, ya kula da makarantar su ta duka ɓangare biyu. 

“Zan koya maka, Ƙur’ani, Fiqhu, wasu Hadisai da litattafai da yawa.”

Kallon ta ya yi fuskar shi ɗauke da wani yanayi mai nauyi ya ce, 

“Na gode.”

“Banda godiya, tsakanin mu ne wannan mu kaɗai.”

Kai ya ɗaga mata yana murmushi. 

“Ka cika son yara da yawa. Allah ya baka ko guda goma.”

Ta Faɗi cike da tsokana, dariya ya yi ya miƙe yana faɗin, 

“Ki ce kamar talatin dai… Goma ai sun min kaɗan. Da yawa nake so…”

Ya ƙarasa maganar yana nufar ƙofa, mamakin shi ya hana ta amsa har ya fice. Son yaran shi har mamaki yake bata. 

****** 

Sai lokacin hawaye masu ɗumi suka zubo mata. Bata ga ta haihu ba, amma hakan baya nufin ta cire rai daga samun rabo. Haihuwa kyauta ce da Allah yake baiwa wanda yaso. 

Amma a yanayi haka irin na Mamdud, babu wani buri, komai ya ƙare ta wannan fannin. Ƙaddara ce mai girma a rayuwar shi da zuciyarta ta soma addu’a Allah ya bashi ikon jurewa. 

Bata taɓa jin yana maganar wani abu cikin abinda yake son samu a duniya da ya wuce yara ba. In kowa zai ce yana son samun abu kaza, shi dai zai ce su yi mishi addu’a yara yake so da yawa don haka ma ba zai yi mata guda ɗaya ba. 

Asad ta ga ya dafa kafaɗar Anees. Ya rasa kalar tashin hankalin da suka shiga yau ɗin nan. Arif ne awanin kaɗan da suka shige. Da har yanzun ya kasa gane ta yadda akai ya zo Nigeria har ma yadda ajali ya same shi. 

Yanzun kuma Mamdud, baya jin zuciyarshi za ta iya ɗaukar rashin ‘yan uwanshi biyu a rana ɗaya. Komai tsaya mishi yayi sai yanzun da suka zo asibitin. 

Maganganun likitan kuma sun jefa shi cikin wani ruɗani na daban. Ya rasa abinda ya kamata ace ya soma fahimta a cikin abubuwan nan guda biyu. 

“Za ku iya zuwa ku ganshi.”

Maganar likitan ta katse musu tunanin da suke yi. Dawud ya fara fita don yanayinsu na fama mishi tabon da ke tashi zuciyar.

Tsayawa ya yi a bakin ƙofar, zai barsu da moment ɗin nan tukunna. Har sai sun ɗan nutsu, yana kallo Labeeb ya sa hannun shi a handle ɗin ƙofar amma ya kasa turawa. 

Sai da Zainab ta ɗora hannunta kan nashi sannan suka tura ƙofar a tare. Dukkansu yanayin Mamdud ɗin ya jefa su wani sabon tashin hankali. 

Ƙafarshi da ta karye a naɗe take da wani bandeji an rataye ta. Haka hannun shi guda ɗaya. Ɗayan kuma jini ne ake saka mishi. 

In ba kasan shi ba, raunukan da ke fuskarshi ba za su bari ka iya gane kamannin shi ba. Da gudu Zainab ta ƙarasa wajen gadon tana saka hannuwanta jikin ƙarfen gadon. 

Numfashi take ja tana fitarwa da sauri-sauri. Su Asad ma ƙarasawa suka yi gefenta, Asad ya juyo ya kalli Anees, wasu siraran hawaye na zubo mishi. 

“Ta yaya za a ce ba zai haihu ba? Duka burin rayuwar shi akan yara ya tsaya… Na kasa gane ko me ya sa ba zai haihu ba…”

Ganin Anees ya kauda kanshi ya sa hannuwa yana share ƙwalla ya sa Asad ƙarasawa wajen Labeeb, matsawa ya yi daf da shi. Cikin fuska yake kallon shi

“Yaya za ka gyara komai ko? Kamar yadda ka saba… Ba za ka bari wani abu ya samu Yaya Mamdud ba… Za ka fita da shi daga ƙasar… Za ka kai shi in…”

“Enough! Ya isa! Ya isheni Asad..”

Labeeb ya faɗi a tsawace, yana sauke muryar shi tare da ɗorawa da faɗin, 

“Ka kalle shi…”

Yana nuna Mamdud da ke kwance. 

“Ikon komai baya hannuna Asad, da bamu zuba wa Arif ƙasa ba… Da ban baro shi inda mu duka yake jiranmu ba. 

Akwai abubuwan da ba zamu iya kaucewa ba. Ciki har da ƙaddara… In ta Mamdud ta zo da haka waye ni?”

Kallon shi Asad yake yi, sabbin hawaye na zubar mishi. 

“Haka za ka barshi kenan? Haka za mu kalle shi? Me zamu faɗa mishi in ya buɗe idanuwan shi?”

Girgiza kai Labeeb yayi yana ware hannuwanshi duka biyun. Ya rasa me zai ce wa Asad. Shi kanshi so yake ya gama fahimtar abinda ke faruwa. 

Gaba ɗaya komai ya jagule. Komai na rayuwar ya kwance mishi. Dama can wauta ce ɗan Adam yake yi. Gani kake kana da iko akan abubuwa. 

Bayan ba ka da shi, ba ka da iko akan komai sai abinda Allah ya tsara maka. Amma tsaf abinda yake faruwa da Mamdud ɗin yai mishi tsaye a gefen mutuwar Arif. 

Ya ɗauka ya tsani Mamdud, duk da yana jin abinda Mamdud ya yi ba zai taɓa gyaruwa ba. Amma ganin shi a nan kwance ya canza wani abu a zuciyar Labeeb. 

Yanzun yana iya fita in Allah Ya so abinda ya fi wannan da ke faruwa da Mamdud ya faru da shi. Ya gama tsorata da firgita da yanayin rayuwa gaba ɗayanta. 

Tunani yake, da Allah ya so fa sai dai su zo su ɗauki gawar Mamdud. Wani numfashi ya ja, yana ɗago hannun shi ya dafe goshin shi da shi. 

“Gida nake son zuwa… Gida zan tafi.”

Labeeb ya faɗi yana kallonsu dukkansu. Suma kallon shin suke yi, wani yake so ya lallashe shi. Wani yake so ya riƙe shi ya faɗa mishi komai zai yi dai dai. 

In yaso sai ya dawo ya lallashi su Zainab. Yanzun ba zai iya basu komai ba, zai barsu su ɗan ji da abinda yake faruwa kafin ya samu nutsuwar da zai riƙe hannayensu. 

Kafin ya samu ƙarfin da zai iya taya su ɗaukar abinda suke ji. Yanzun kam ƙiris yake jira ya fashe. Ba kuma ya son ya yi hakan a gaban su. 

Da baya baya yake tafiya kafin ya juya ya fice daga ɗakin. Dawud da ke tsaye ya kalla. 

“Ka bar wajen nan da ni… Please…”

Ya ƙarasa muryarshi can ƙasa. Kai Dawud kawai ya ɗaga mishi yana kama hanya suka fice daga asibitin zuwa wajen motar da suka zo da ita. 

Dawud ya buɗe mishi motar ya shiga ya zauna yana haɗa kanshi da gaban motar. Sai shi ya sake rufe murfin ya zagaya ya shiga. 

**** 

Bai ɗago kanshi ba sai da Dawud ya ce mishi, 

“Mun iso…”

Ɗagowa ya yi. Ta cikin motar ya ga a Dialogue suke. Kallon Dawud ya yi. 

“Na gode… Na gode sosai.”

“Kana nan lokacin da na rasa Abba… Kana nan lokacin da na rasa Ummi… Sajda… Zuciyata na jin haushin ka. Sai yanzun na gane a kowanne hali, ‘yan uwa basa guje wa junan su. 

Bansan sa’adda za mu wuce wannan wajen ba… Na dai san ba zamu wuce shi in ba ma tare da juna ba. Ka tafi wajen matarka.”

Sauke numfashi Labeeb ya yi, maganganun Dawud na ɗan rage mishi zafi ta wani fannin. 

“Su Zee Zee…”

Labeeb ya faɗi. 

“Ka tafi kawai… Zan koma wajen su. Zan kira ka in suna buƙatar ka.”

Fita Labeeb ya yi daga motar. Yana jin yadda har ya mutu ba zai manta wannan karamcin da Dawud yai mishi ba. Yana cikin abubuwan da za su zauna da shi har ƙarshen rayuwar shi. 

Da sauri-sauri ƙafafuwan shi suke ɗaukarshi zuwa ɓangaren da Ateefa take. Yana hango ɗakin da take yana ƙara sauri. Da ƙarfi ya tura ɗakin. 

Ta ɗago, lumshe idanuwanta ta yi tana sauke wata ajiyar zuciya, fuskarta kaɗai ya kalla yasan ta ci kuka ba kaɗan ba. 

“Tee…”

Ya faɗi. Saukowa ta yi daga kan gadon ta ƙaraso inda yake. Rungume shi ta yi ta zagaya hannayenta ta baya ta riƙe shi sosai. 

Jikinshi ta rungume amma a zuciyarshi yake jin abin. A Zuciyarshi yake jin nutsuwar da hakan ya samar mishi. Kuka take sosai yana jin yadda jikinta ke kyarma. 

Shima nashi hannayen ya zagaya a bayanta yana sake riƙota jikin shi tare da ɗora haɓarshi a saman kanta yana rufe idanuwanshi. Cikin kuka take faɗin, 

“Text ɗinka na gani… Arif… Arif ya rasu… Na kiraka baka ɗauka ba… Duka su Zainab na kira su basu ɗauka ba… Bansa me zan yi ba… Hankalina ya tashi sosai.”

Bai ce komai ba, sun kusan mintina biyar a haka riƙe da juna. Ya samu nutsuwa, amma ya kasa buɗe damuwarshi. Ya kasa buɗe abinda ya kamata ya buɗe. 

Zuciyarshi a kumbure take gab da ta fashe, amma tare da Ateefa hakan ya ƙi samuwa. A hankali ya saketa yana zamewa daga jikin ta. Ya kamata ya kaita kan gadon ya zaunar da su. 

Idanuwanshi ya sauke daga fuskarta zuwa cikinta. Nan ya tsaida gaba ɗaya hankalin shi da nutsuwar shi, kafin a hankali ya kai hannun shi yana dafa cikin nata. 

Hannunta ta ɗora akan nashi, ba tare da ya ɗago kanshi ba, muryarshi na rawa ya ce 

“Mamdud ya yi accident…”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Ya ji ciwo? Yana ina?”

Ateefa ke faɗi cikin tashin hankali. 

“Abin nan dake cikinki Tee… Yaron mu ko yarinyar mu… Wanda kika so salwantarwa… Mamdud ba zai taɓa samu ba. Ba zai taɓa haihuwa ba, bani bane ba. Bansan me yasa nake jin haka ba.”

Ɗayan hannunta Ateefa ta kai tana tallabar fuskar Labeeb ɗin, tana son ko yaya ne ta rage mishi damuwar da yake ciki. 

“Kinsan yara nawa na watsar? Bansan ko nawa Allah ya rubuta min ba… Na ɗauki zubda waɗancan ba komai ba… Gashi wani ba zai sake samu ba… Kuma fa ba shi kaɗai bane ko?”

Ya ƙarasa maganar yana ɗago kanshi ya zuba mata idanuwanshi da ke ɗauke da damuwar da bata taba gani a idanuwan kowa ba. Hawaye ne suka zubo mata, hannunsu da ke kan cikinta ta ƙara dumtsewa. 

Tana jin gaskiyar maganganun shi. Allah ya bata kyauta mafi girma, ta rasa rashin hankalin da ya sa ta tunanin zubdawa ma tun farko. 

“Duka burin shi akan yara ya tsaya… Na san yayi abinda ya cancan ci hukunci… Amma…”

Hannu tasa ta rufe mishi baki tana girgiza mishi kai. 

“Ba a ɗora alamar tambaya akan ƙaddara… Hukuncin Mamdud ba a hannunka yake ba. Rubutun ƙaddararshi ma haka… Ba komai ba ne alkhairi a rayuwar mutum. 

Wani rashin yaran shine alkhairin shi.. Akwai masu yaran da suke jin dama basu da saboda ƙaddarar da ta zo musu tare da yaran…”

“Bazan iya rasa shi ba Tee… Ƙaunarshi ta gaskiya ce a zuciyata… Akwai lokacin da na tsane shi… Akwai lokacin da na ji kamar ace ban sanshi ba… Yau.. Ranar nan ta nuna min abubuwa da yawa.

Kamar wasa na rasa Arif… Ba zai dawo ba. Bazan sake asarar lokaci na ina faɗa da wani ba… Bamu da su da yawa… Babu… Babu lokaci mai yawa a rayuwarmu.”

Tana jin yanayin damuwar shi har zuciyarta, hannun da ke fuskarshi ta cire ta goge hawayen da suka zubo mata. 

“Bansan me zan ce maka ka ji sauƙi ba…bansan me zan maka ba.”

“Hmm…”

Labeeb ya iya furtawa kawai yana zame hannun shi da ke cikinta tare da miƙewa. Sumba ya manna mata a goshinta. 

“Ki kula min da kanki. Zan je gida.”

Saukowa ta yi daga kan gadon tana kuka. 

“Mu tafi tare…”

Girgiza mata kai yayi. 

“Don Allah ka tafi da ni.”

Hannuwanshi ya sa ya tallafi fuskarta. Yana kallonta cikin idanuwanta. 

“Tee in wani abu ya same ki ko abinda ke cikinki bansan ya zan yi ba. Ki rage min nauyi… Ki zauna inda na san za a kula da lafiyar ki… Don Allah ba don ni ba.”

Kai take ɗaga mishi kawai kuka ya hanata magana. Sumbatarta ya sake yi a kuncinta, yana rungumeta a jikinshi. Yana jin kamar ya dawo da duk wani lokaci na baya dabai nuna mata ƙauna ba ya nuna mata. 

Zai iya rasa ta. Ko ita ta rasa shi, komai na duniyar nan tasu zai iya ƙarewa, komai babu tabbas a cikin shi. Zai sota iya yadda zuciyar shi za ta iya. 

“Ko wani abu ya same ni ki riƙe a ranki. Ina sonki… Ina son ki har cikin zuciyata…”

Sosai ta matse shi a jikinta

“Ka daina… Babu abinda zai same ka… Ina sonka sosai… Wallahi ina ƙaunarka har raina El-Maska… Komai zai yi dai-dai.”

Abinda yake so ya ji ne. Sai dai ya ji ɗin, babu abinda ya ƙara mishi, ko ya sa shi ji a zuciyar shi. Da ƙyar ya zame jikinshi daga nata yana nufar ƙofa ya buɗe ya fice daga ɗakin. 

A hanyarshi ta fita yake jin wasu na kiran sunan shi. Ko ta kansu bai bi ba ya fice daga asibitin. Mashin ya tare ya hau ya kai shi gida. Aljihunshi ya laluba, naira dubu ya ɗauko ya ba mai mashin ɗin. 

“Jeka kawai…”

Ya faɗi yana shiga cikin harbar gidan da ke maƙare da mutane, gaisawa yake da su yana amsa ta’aziyar da suke mishi da Alhamdulillah ba don yana tsayawa gane fuskokinsu ba. 

Sam ba shi da wannan nutsuwar. Ɓangaren su Dawud ya nufa. Zulfa yake son gani da duk wani abu na jikinshi. 

****

Bacci ta tashi ta ji gidan yayi wani shiru. Jikinta da nauyi sosai ta miƙe ta shiga wanka ta fito. Mai ta shafa wa jikinta, ta samu wata doguwar riga ta zura, hular rigar ta saka. 

Fuskarta ta kalla a mudubi, ta ga idanuwanta sun faɗa kamar wadda tai jinyar watanni, hakan yasa ta murza wa fuskarta powder, ta ɗauki kwalli ta ɗan saka wa idon ko za ta ga ya ciko. 

Dawowa ta yi ta ɗauki wayarta, ta zauna a ƙasa tana jingina bayanta da gadon ɗakin. Tun da suka karya ɗazu ta kwanta take bacci. 

Kunna wayar ta yi tana ganin yadda cajin yai ƙasa sosai. Ta manta yaushe ne karshen saka wa wayar cai. Rasa me za ta yi da wayar ta yi, ta miƙe ta ɗauko charger ɗin wayar Mami. 

Ta dawo ta zauna tana saka cajin. Shiru ta yi tana jin kewar Labeeb, bata san inda ya shiga ba tun shekaranjiya rabon da ta sa shi a idanuwanta. 

Ko kiranta bai yi ba, duk da wayarta ba a kunne take ba, inda ya kira ya ji a kashe ko text zai mata. Babu ko ɗaya, ta ja numfashi ta sauke. Bata san dalilin shi na ƙin kiranta ba. 

Amma abin ya tsaya mata a rai. Har yanzun bata san me ya yanke a kanta ba, ko yana jin haushinta, duk bata sani ba, banda son kareta babu abinda ta gani. 

Dole ma zai ji haushinta, ta yi shirme da abokin da ta san ya ɗauka ɗan uwa. Ta yi kuskure babba, ta ja mishi ɗaukar lefin da ba nashi ba. Komai ya hargitse mishi kamar yadda ya hargitse mata saboda laifinta.

Hawaye masu zafi ne suka zubo mata, ta sa hannu ta goge su. Mami na iya ƙoƙarinta, tana mata abinda ko ita ta haifeta sai haka, sai dai ta kasa jure kewar Ummi. 

Ko Sajda da tana nan abin zai zo mata da sauƙi. Kanta a kasa yake, tana jin wani zazzaɓi-zazzaɓi . 

“Zulfa…”

Ta ji muryar Labeeb can ƙasa, ta ɗauka kunnuwanta ne. Kewar shin da take ne ya sa muryarshi ke mata yawo. Sai da ya sake kiran sunanta tukunna ta ɗago idanuwa. 

Kayan jikin shi. Rigarshi da ta ke da jini, har da wasu wajaje a wandonshi ta fara kallo, kafin ta soma yawo da idanuwanta ko ina tana neman ciwon da ya ji ta rasa. 

Jikinta yai mata nauyi sosai, ta kasa tashi ma. Takalmanshi ya cire a bakin ƙofa, yana takawa ya zauna a gabanta. Idanuwanshi cikin fuskarta yana ganin yadda ta rame tai wani haske na ban mamaki. 

Muryarta na rawa ta ce, 

“Me ya same ka? Jinin meye a jikin ka?”

Sai da ya haɗiye abin da ya tsaya mishi a wuya tukunna ya kalli rigar shi, ya sake kallon ta. 

“Arif… Jinin arif ne… Ya rasu.”

Maganar ta ji ta zo mata kamar daga sama, kafin ta gane ma’anar ta, girgiza mishi kai take, fuskar Arif na mata yawo, yanayin dariyar shi da komai nashi. 

“Don Allah ka faɗa min wani abu banda wannan…”

Ta ƙarasa maganar kuka na ƙwace mata, kallonta yake wani abu na taso mishi. 

“Mamdud yayi accident…”

Hannu tasa ta goge hawayenta, kiran sunan Mamdud da yayi yana ƙara mata ciwo. Muryarta ɗauke da wani nisantaccen abu ta ce, 

“Ya mutu?”

Kai Labeeb ya girgiza mata. Ba ta taɓa yi wa wani fatan mutuwa ba. Saboda ba wanda ya taɓa bata dalilin yin hakan. Amma Mamdud, abinda take ji a kanshi ba zai taɓa misaltuwa ba. 

Ko sunanshi ta ji sai wani abu ya ƙara rugujewa a zuciyarta. 

“Abinda ke jikin ki… Cikin da ke jikinki shi ne ƙarshen yaron da Mamdud zai samu a rayuwar shi.”

Cikin tashin hankali take kallon Labeeb, abinda duk zai fito bakin shi na ƙara mata yanayi mai wahala. Mutuwar Arif da ya faɗa mata ta taso mata da abubuwa masu yawa. 

Ba sai ya gaya mata abinda ya fi komai birkita rayuwarta ba. Kuka take mai sauti. 

“Me kake son faɗa min? Ban zaɓi abinda yake cikina ya kasance a ciki ba… Duk da ina da laifi… Wallahi ban zaɓa ba Yaya Labeeb…”

Da sauri ya kama hannunta cikin nashi yana son gaya mata ya fahimta, amma babu maganar da ta iya fitowa daga bakinshi saboda abinda yake ji ya girmi duk wata kalma. 

Kula ta yi da yanayin shi, da abinda ta san yana ji. Da girman ƙaunarshi ga ‘yan uwan shi. Hannu ta sa ta share nata hawayen. 

“Ya su Zainab?”

Kai ya ɗan langaɓar gefe. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Suna asibiti… Can na barsu… Banda ƙarfin lallashin su… Yanayin su na ƙara min damuwa… Cikin kwana biyu komai ya hargitse min.”

Ya ƙarasa maganar yana sadda kanshi ƙasa. Tausayin shi ya tsaya mata a zuciya. 

“Shikenan ko? Iya shekarun da za mu yi da Arif… Ya tafi kenan. Zulfa haka ake ji dama?”

Ya tambaya yana sauke idanuwanshi cikin nata, rashin Arif yake ji har a ƙasusuwan jikin shi, ba abinda yake gani sai Arif a hannun shi. Sai lokacin da suka ɗauki gawar Arif. 

Komai dawo mishi yake, da ƙyar yake jan numfashi. Mamdud da halin da yake ciki yake gani. Bai kamata ace baya kusa da shi ba, ko me Mamdud yai mishi. 

Ya bashi shekaru masu yawa na rayuwarshi, ya taya shi kula da ƙannen shi, tunda Mamdud ya shigo rayuwarshi ya daina sanin ƙananan matsalolin su Zainab. 

Ya daina shakkun barin su a hannun ‘yan aiki. Rayuwa ta mishi sauƙi da Mamdud a kusa da shi. Hannun shi yasa ya rufe fuskar shi. 

“Bazan iya rasa Mamdud ba… Bazan iya ba.”

Yake faɗi, hannun shi da ke cikin na zulfa ya ji ta ƙara damtsewa. 

“Ba za ka rasa shi ba in sha Allah…”

Ta faɗi , bude fuskarshi yayi

“Ba ki ganshi bane ba… Ba ki ga halin da yake ciki ba…ya yi kuskure Zulfa… Amma bana son in rasa shi.”

Ya ƙarasa cikin sauke murya. Kallon shi kawai take, tana rasa abinda ya kamata ta yi ko ta ce. Yanayinta yake nazari da ciwon gaske. 

“Ba don bana sonki ba… Ba don bana jin zafin abinda yai miki ba… Laifina ne… Waye ni da zan lalata yaran mutane in ce zan tuba lokacin da na ga dama… Ni na ja miki…”

Girgiza mishi kai ta yi 

“Ka daina… Don Allah ka bari…abubuwan za su yi maka yawa… Ka daina ɗora laifin da babu ruwanka… Me yasa za ka ɗauki cikin jikina? Bayan ba naka bane?”

Sauke numfashi Labeeb ya yi. Sosai zuciyarshi ke mishi zafi, lallashi yake so. Wajen Zulfa ma ba zai samu ba, ita ma nata ciwon babba ne. 

Hannunta da nashi ya ɗago ya sumbata. 

“Komai zai yi dai-dai in sha Allah. Ki daina tunanin na ɗora wa kaina laifi. Ki daina tunanin dalilin da ya sa nai haka… Abu ɗaya nake so ki yi tunani… Komai zai yi dai-dai.”

Kai ta ɗaga mishi hawaye na zubar mata, miƙewa yayi ya kama hanyar fita. Kukan ta na ƙara mishi damuwa. Yana fita daga gidan ɓangarensu ya wuce. 

Gidan cike yake da mutane, ɗakin Arif ya nufa. Ya tura a hankali, ya cire takalman shi. Kan kafet ɗin ɗakin ya taka ƙafarshi yana ƙare mishi kallo. 

Sai yake ganin Arif a ko ina na ɗakin. Inda yakan zauna ya yi zanen shi. Kan gadon shi. Komai na rayuwar yaron tun daga yarinta na dawo mishi. 

Akwatin shi ya gani ajiye akan gado. Ya ƙarasa ya zauna akan gadon. Hannun shi na rawa ya kwantar da akwatin yana buɗewa. 

Wani ƙaton drawing book ne a sama. Shi ya fara ɗaukowa ya buɗe, shafin farko zanen Labeeb ɗin ne da murmushi a fuskarshi. 

Hannun shi ya kai kan zanen yana shafawa. Hawaye ne ya ji suna bi mishi fuskarshi. 

“Innalillahi…. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un….Arif…. Ya Allah…. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shi ne abinda Labeeb ke faɗi kawai yana wani irin kuka da yake fitowa tun daga zuciyar shi, ya haɗa littafin da hannun shi yana kuka kamar ƙaramin yaro. 

Ji ya yi an dafa shi. Ya ɗago fuskarshi, Mummy ce ta ture akwatin ta zauna. Kan ƙafafuwanta labeeb ya dora kanshi yana sakin wani sabon kukan. 

“Mummy Arif ya barmu… Ya barmu…”

Ita ma kukan take yi, bayanshi take ɗan bubbugawa. Kamar ma ƙara mishi ciwon da yake ji take yi. Ɗago kai ya yi, ko ina na jikin shi kyarma yake. 

“Mu kaɗai ne… Ko ba kwa nan… Muna da junanmu… Ya zamu koma dai-dai? Ya zamu warke daga rashin Arif ?”

Hannu Mummy ta sa tana shafa gashin Labeeb ɗin, da na sani da yafda lokaci ya ƙure mata na mata wani irin raɗaɗi a ƙirjinta. Littafin da ke hannun Labeeb ta karɓa. 

Ta buɗe, shafin farko zanen Labeeb ne, haka ta dinga buɗewa har ta zo kan nata. Tai tsaye da idanuwanta akan zanen mamaki. Murya a sarƙe ta ce, 

“Wa ya yi zanen nan?”

Dariya Labeeb ya yi yana girgiza kanshi wasu hawayen na zubar mishi. Hannun shi mummy ta riƙo ya ƙwace, 

“Me za ki min yanzun Mummy? Ba ma ki san Arif na zane ba… In da za a ce ki faɗi abincin da ya fi so a dawo mana da shi ba za ki iya ba… Ba ki san komai akan shi ba… Ba ki san komai akanmu ba.”

Girgiza mishi kai Mummy take, gaskiya yake faɗa, ba ta san kalar abinda Arif yake so ba. Haka su dukkansu, sai yanzun da ya faɗa take ganin abin a idanuwanta. 

Me take da lokutanta haka? Zai zama abin kunya ace uwa bata san komai akan yaranta ba. To wa yake da haƙƙin hakan in ita bata zauna da su ba. 

Kallon Labeeb ta yi yadda hawaye ke bin fuskar shi, kamo shi za ta sake yi ya mike tsaye yana matsawa. 

“Bana so Mummy… Duka rayuwata ina yin abinda zan burgeki ko sau ɗaya ki zauna da mu… Kullum kika zo haka kowa a cikin mu yake binki… Ba mu tambayi komai daga gareki ba banda lokacin ki. 

Don Allah ki fita… Ki fita in ji da ciwon rashin ɗan uwa na… Ba ki saba kasancewa da mu a komai namu ba. Wannan ma na yafe… Wallahi na yafe Mummy.”

Mikewa Mummy ta yi, in akwai abinda mutuwar Arif ya nuna mata bai wuce bata da sauran lokaci ba. Ba zata bari kowa a cikin su ya sake kubce mata bata nuna mishi yadda take ƙaunar shi ba. 

Hannun Labeeb ta kama da yake kuka yana ƙwacewa kamar ƙaramin yaro, janyo shi ta yi tai hugging dinshi. Abinda ko da yana jariri bata tsaya ta bashi ba.

Goyo da iyaye suke don ya ji ɗumin su babu wanda yaranta suka samu tare da ita. Asalima suna wani ɗaki a kwace tana wani. Kuka Labeeb yake kamar ranshi zai fita. 

Yau ne karo na farko da ya san tallafin uwa. Ya san yadda ake ji in ana cikin damuwa mahaifiyarka na tare da kai. Wani sanyi-sanyi yake ji a raunukan da ke ƙirjin shi. 

“Kaina ciwo Mummy… Komai ciwo yake min.”

Bubbuga bayanshi take, tana jin yadda yake ƙara riƙeta yana kuka, ita ma kukan take, tana jin ƙaunar ɗanta da bata taɓa sanin girmanta ya kai haka ba. 

“Ina ƙaunarka Labeeb… Ina ƙaunar ku fiye da zatona… Ku yafe min don Allah…”

Riƙeta Labeeb ya ƙara yi. 

“Ki daina barinmu Mummy… Don Allah ki daina barinmu.”

Kai kawai Mummy ta iya ɗaga mishi, sannan ta zame shi daga jikinta, sai da ta ɗaga kai take iya ganin fuskarshi don ya mata tsayi. Ta sa hannuwanta tana share mishi ido. 

Duk ƙasashen da take zuwa. Duk daular da take ciki, takan ji wani rami a zuciyarta, kamar komai na rayuwarta bai cika ba. Sai yanzun da fuskar ɗanta ke cikin hannunta tasan abinda ta yi missing. 

Akwai nutsuwa da ƙauna ta daban a tsayawa ka kula da yaranka da kanka da mahaifiyar da take kula da nata ne kawai za ta faɗi haka. 

Kamashi ta yi ta zaunar da shi akan gadon, ta ɗauki littafin tana mayarwa cikin awatin Arif ɗin. 

“Ban…ban gama gani ba Mummy… Karki rufe.”

Labeeb yake faɗi yana kai hannunshi zai ɗauki littafin, Mummy ta riƙe hannun tana janye akwatin tare da zuge zip ɗin. 

“Ba yau ba… Ciwon sabo ne. Ƙara musu girma za ka yi.”

Kai ya daga mata. 

“Ina su zainab?”

Ta buƙata tana goge fuskarta da hannuwanta. Wasu sabbin hawayen suka sake zubo ma labeeb. 

“Suna wajen Mamdud… Suna Harmony. Mamdud ya yi accident Mummy.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Mummy ke faɗi. Labeeb ya miƙe yana goge fuskarshi. 

“Can zan koma Mummy.”

Ya ƙarasa yana miƙewa, kasa ce mishi komai ta yi har ya fice daga ɗakin, ta koma kan gadon Arif ta kife kanta, ta buɗe wani sabon shafin kukan. 

Labeeb na fita daga gidan ya ƙarasa harabar da ake zaman makoki, Ishaq ya taso don ya ga fitar su. 

“El-Maska me yake faruwa? Ina Zainab… Ina ta kiran wayarta bata ɗaga ba.”

Murya a dakushe Labeeb ya ce mishi, 

“Mamdud ne ya yi accident. Suna Harmony.”

“Subahanallah…Mu je asibitin.”

Ba musu Labeeb ya bishi har wajen motar Ishaq ɗin, ya buɗe ya shiga ya zauna yana rufewa. Ishaq na shigowa ya ɗauko robar ruwa a bayan motar ya miƙa wa Labeeb. 

Karɓa ya yi ya buɗe, baisan yana jin ƙishirwa haka ba, don sai da ya ji cikinshi ya soma ƙullewa tukunna ya bar ruwan haka. Yana jin Ishaq ya tayar da motar ya kama hanya. 

***** 

Ishaq ya tura ɗakin suka shiga, Zainab na zaune kan kujera, ta haɗa kanta da gefen gadon da Mamdud yake kwance. Anees ma zaune yake kan kujera ya zuba wa Mamdud idanuwa. 

Kamar hakan ne zai sa ya tashi. Asad na zaune kan kujerar shi da ya haɗe da ta Anees, kanshi na kwance jikin kafaɗar Anees ɗin. Sai Dawud da yana ganin shigowar su ya miƙe. 

Mukullin motar da ke hannun shi na Labeeb ɗin ya miƙa mishi, ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fice daga ɗakin abinshi. A aljihu Labeeb ya sa mukullin motar. Ya maida hankalin shi kan ƙannen nashi. 

Zai ce Zainab ta fi kowa rikici a tasowar ƙannen nashi. Asad ya fi kowa buƙatar kulawa, zuciyar shi ta fi ta kowa rauni a cikinsu. Abu ƙarami ma taɓashi yake. 

Ko wani ya gani cikinsu kwance sosai tare za su yi jinyar, abinda yake saka shi kuka baida wahala. Wajen Zainab Ishaq ya ƙarasa ya dafa ta. 

Hannunshi kawai ta ji ta gane shi ne, sai da ta ɗora nata hannun akan nashi tukunna ta ɗago da kanta. Fuskarta duk ta kumbure. 

Tsugunnawa Ishaq ya yi, muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Sannu…”

Kai ta ɗan ɗaga mishi. Tana jin daɗin zuwan da ya yi. Ganin shi na sata jin wani relief da bata zata ba. Hannun shi ta kai fuskarta tana sumbata. 

Ƙarasawa Labeeb ya yi gaf da gadon idanuwan shi akan Mamdud da baisan duniyar da yake ba. Rayuwa aikin banza, dubi yadda Mamdud ya koma lokaci ɗaya. 

Gaba ɗaya fuskar shi a kumbure take, kusa da shi Labeeb ya ƙara matsawa. Motsi yake so ya ga ya yi ko yaya ne, amma shiru kake ji. 

Hannunshi ya kai saitin hancin Mamdud ɗin don ya tabbatar da yana numfashi, a hankali ya ji hucin numfashin Mamdud ɗin yana dukan hannun shi. 

Ga abin abinci a hancin shi. Sauke numfashi labeeb yayi. Shi kaɗai ya juya ya koma office ɗin likitan ɗazu. Bills ɗin da aka kashe ya ji ko nawa ne. 

Faɗa wa likitan ya yi cewa sai ya koma gida don bai tare da master card ɗinshi. Su ba Mamdud duk kulawar da yake buƙata kafin yammaci. 

Fita ya yi, ya shiga neman wajen da ake saida wani abu, don yau ne rana ta farko da ya sakko ƙafarshi Harmony. Har ya gano wajen. 

Strawberry yoghurt ya siya da ruwa, ya biya kuɗin ya dawo. Zai danne abin da yake ji. Su Zainab na buƙatar kulawar shi a yanzun. 

Yadda ya barsu haka ya koma ya same su, ya buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin ɗakin ya saka strawberry ɗin yana barin robar ruwa guda ɗaya da ya rike a hannun shi ya buɗe. 

Asad ya ɗan taɓa, ya ɗago daga kan kafaɗar Anees. Ruwan ya miƙa mishi, ya girgiza kai. Shi ba ruwa yake so ba, Mamdud yake so ya tashi, ciwon da yake ji a ƙirjin shi yake son ya bari. 

“Ka sha ruwa ko yaya ne…”

Kallon Labeeb ɗin ya yi. 

“Ni ba ruwa nake so ba… Zuciyata ke min ciwo. Yaya Mamdud ko motsi bai yi ba.. Ba ruwa nake so ba yaya.”

Tsugunnawa Labeeb ya yi yana kallon Asad a cikin idanuwanshi. 

“It will get better… Ba za mu kasance haka har ƙarshen rayuwarmu ba. Mamdud ɗin na buƙatarku da ƙarfinku in ya buɗe idanuwanshi… Don Allah ka sha ruwa ko yaya ne.”

Sosai Asad ke nazarin fuskar Labeeb din kafin ya karɓi ruwan, sha ya yi sosai yana sauke ajiyar zuciya tukunna ya miƙa wa Anees shima ya sha. 

Ya ba Zainab da ta ƙarasa shanyewa tana kallon Labeeb. 

“In ƙaro miki?”

Ya bukata, kai ta ɗaga mishi alamar eh, fridge ɗin ya buɗe ya ƙara ɗauko mata ruwan, da kanshi ya buɗe ya miƙa mata, ta karɓa. Wannan karon da ta ƙara sha Ishaq ta miƙa wa. 

Tsaye Labeeb ya yi duk da akwai kujeru biyu ƙanana sai cushion doguwa a gefe. Babu wanda ya ce wa wani komai har aka kira Azahar. 

Duka cikin banɗakin da ke ɗakin suka yi i alwala. Su masallaci suka fita, Zainab kuma ɗankwalin ta ta cire ta shimfiɗa, ta naɗa mayafinta tai sallah da shi . 

Ko da suka dawo, kowa inda yake ya sake komawa ya zauna. Sai dai wannan karon Labeeb ya nemi kujera. Kowa da abinda yake ji a ranshi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 36Rayuwarmu 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×