Skip to content
Part 12 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Da ƙyar Labeeb ya samu Dawud ya bashi Khateeb. Yadda ya ga ya goya shi ta gaba haka yayi shima.

Wani shaƙiƙin Ummi ne zai mata wanka. Babu ‘yan uwanta ko ɗaya. Don basu sani ba. Mamdud Dawud yasa ya shiga kiran mutane yana faɗa musu jana’iza.

Dawud shi kaɗai yaima Ummi wanka, shi ya haɗata, zuciyarshi a bushe yake jinta cikin ƙirjinshi har ya gama. Zuba wa gawar Ummi idanuwa yayi naɗe cikin likkafani.

Tunanin yadda take ji yake yi. Tunanin yadda shima wata rana zai buƙaci haka. Tunanin ko a wanne hali tashi mutuwar zata zo masa yake yi.

Ya zai ji lokacin da ranshi ya bar jikinshi. Wane abu zai samu a nashi kabarin, Ummi kenan, mai haƙuri da kawaici, in har tata mutuwar ta zo a haka ba tare da mijinta ba, shi baisan a yadda tashi zata zo mishi ba. Su Labeeb ya ji sun shigo da makara. Miƙewa ya yi ya kama musu suka shigo da ita suka ajiye.

Hannu ya kai yana taɓa bayan Khateeb da alamar yana son Labeeb ya bashi shi. Bai musa ba ya kai hannu bayanshi ya kwance towel ɗin ya miƙa mishi Khateeb.

Tallabe shi yayi a ƙirjinshi ya saka towel ɗin ya juya baya Labeeb ya ɗaure mishi shi. Yana jin ya motsa kafin ya ci gaba da wani irin kuka.

A haka Labeeb da Dawud suka kama Ummi suka sakata a cikin makarar. Su uku har da Mamdud suka kamata suka fito da ita. Waje suka samu suka ajiyeta.

Suna fitowa waje Dawud ya kalli tarin al’umar da ke wajen. Ba zai ce bai yi mamakin yawan su ba. Don baya iya hango iya inda suka tsaya. Gaba daya area ɗin wajen shaƙe yake da mutane.

Tayyab ne ya ƙaraso wajen su. Har lokacin kuka yake sosai.

“Ina su zulfa?”

Dawud ya tambaya cikin wata murya da ya kasa gane tashi ce.

“Gida nasa aka kaisu.”

Kai kawai Dawud ya iya ɗaga mishi. Suka ɗan taka suka ɗauki ruwan da ke ajiye a wajen suka yi alwala.

****

Kamo Tayyab Dawud yayi, amma yaƙi tasowa. Durƙushe yake kan kabarin Ummi yana kuka kamar ƙaramin yaro.

“Shikenan ko yaya? Rayuwar mu haka zata zo ƙarshe wata rana….”

Dawud da bai ma san sa’adda Khateeb ya bar kuka ba ya saki hannun Tayyab. Ya rasa abinda ya kamata yayi. Labeeb ne ya zo ya ɗago Tayyab ya janyeshi daga wajen. Ƙura wa kabarin Ummi idanuwa Dawud yayi. Addu’a ya sake yi mata kafin ya juya yana bin bayan su Labeeb.

Gida suka je, har an kafa canopies. Kallon su kawai Dawud yayi don shi bai ga amfaninsu ba. Kowa ya yi wa Ummi addu’a ya tafi abinshi zai fi mishi.

Kanshi na riƙe cikin hannuwanshi, har lokacin rasuwar Ummi bata samu wajen zama ba. Yawo kawai take mishi. Ba zai ce ga tsawon lokacin da ya ɗauka ba ko ga kalar tunanin da yake. Kawai ya daina gane meke faruwa da rayuwar su ne. Yana nan zaune Labeeb ya zo ya zauna a gefenshi.

Feeders ne guda biyu a hannunshi cike da madara. Miƙa wa Dawud yayi.

“Na je na ga likitan yara ne don ya bamu shawara kan kula da Khateeb, shi ne na biyo ta gida na faɗa wa Zainab yadda zata haɗa.

Ka riƙe, in ya farka ka bashi. Nasan yanajin yunwa, bari in koma mutane na ta zuwa.”

Kai kawai Dawud ya ɗaga mishi ya karɓi feeders ɗin guda biyu. Sake kallonshi Labeeb yayi, har kasuwa yasa aka je a dubo abbansu ba a ganshi ba.

Yasan dadynshi ba ya gari, amma ya kira dai ya sanar da shi rasuwar. Babu wanda ya samu sai kawu Haruna. Da shi aka kai Ummi, kuma da shi suke ta karɓar gaisuwa yanzun.

Miƙewa Labeeb yayi yana barin wajen. Motsi Dawud ya ji khateeb yayi, ya kai hannu ya kwance towel ɗin yana riƙe shi a hannunshi.

Madarar ya soma bashi a hankali, yadda ya ga yana sha yasan yunwa yake ji. Sosai yake kallonshi, shi ko Ummi ba zai samu damar sani ba. Yawon da rasuwar Ummi ke mishi ya ƙara sauri.

Sai da ya gama ba Khateeb madara tukunna ya ajiye feeder ɗin gefe ya sake mayar dashi kan ƙirjinshi ya goya.

Miƙewa yayi, ga mamakin shi baisan inda zai nufa ba. Baisan ta ina zai fara ba. Komai ya dawo mishi sabo, bashi da wata makama.

Yana ɗaga idanuwanshi ya sauke su kan Abba, wani abu ne ya taso mishi tun daga ɗan yatsan kafarshi har cikin kanshin inda yai tsaye yake jin kama ya kurma ihu.

Baisan ƙafafuwanshi na ɗaukarshi ba har sai da ya ƙarasa inda Abban yake, gabanshi ya sha yana mishi wani kallo mai cike da fassara kala-kala.

“Dawud……”

Yanajin labeeb na kiranshi ko juyawa bai yi ba. Hannunshi tallabe da bayan Khateeb.

“Me kake anan?”

Ya tambayi Abba da ke kallon shi, yana kuma kallon Khateeb da ke riƙe a jikinshi. Yana jin labeeb ya dafa shi.

“Dawud please…..”

Muryar Dawud can ƙasa ya ce,

“Bama buƙatarshi, Ummi ma ta tafi, sai me don shi baya nan? Bana son ganin shi a wajen nan.

Kamar yadda ya faɗa, babu abinda zai ma Ummi, bamu da wata alaƙa da shi. Bai bamu zaɓi ba ya yanke alaƙar da ke tsakaninmu. Ya bar wajen nan kawai…..”

Kallon shi Auwal yake yi, ya rasa me yasa yake ganin komai kamar a mafarki, har yanzun abinda yake ji akansu bai ko motsa ba balle ya canza.

Ya zo ne saboda yaya ya kirashi ya faɗa mishi, kuma yana jin tunda rasuwa ce ya kamata ya zo bawai don yanajin wani kusanci game da su ba.

Juyawa Dawud yayi ya kalli Labeeb, sauran control ɗin da yake da shi yanajin yana ƙwacewa. Bai kuma san me zai iya faruwa ba.

“Ya bar wajen nan….!”

Yanayinshi Labeeb ya kalla, sannan ya maida hankalinshi kan Abba yana ɗan ɗaga mishi kafaɗa alamar bashi da wani zaɓi.

Juyawa Abba yayi, Dawud bai san me yasa hakan ya ƙara mishi tsanar abban ba.

“He is a coward, ka gani ko? Saboda me ba zai yi fighting ba, i hate him!”

Sauke numfashi Labeeb yayi.

“Na sani dawud, for what it’s worth, am sorry.”

Cikin idanuwa Dawud ya kalle shi.

“Ba laifinka bane ba, ka dawo min da su Zulfa.”

Yana karasa maganar bai jira amsar Labeeb ba ya juya. Cikin gidan ya shiga, ta bayan kujerun ya bi , yanakin kallon inda aka shimfiɗar da gawar Ummi ɗazu.

Ɗakinsu ya wuce, ya tura ya shiga, kwanciya yayi akan bayanshi saboda Khateeb. Ya lumshe idanuwanshi yana rasa abinda yake ji.

****

Sai da Labeeb ya biya Stop ‘n’ Shop ya ce su haɗa mishi kayan babies da duk ake buƙata, daga kan socks zuwa kayan sakawa, zuwa pampers da komai.

Haka suka haɗa mishi aka shaƙe bayan mota, ya biya kuɗin tukunna yakoma gida. Gidan ya ji yayi wani irin shiru, yasan su Anees na wajen zaman makokin.

Zaune ya samu Zulfa a ƙasa kan kafet da sajda kwance jikinta, wani tausayinsu ya cika mishi zuciya. Zainab na takure can ƙarshen kujera.

“Zulfa ku taso mu tafi……”

Ba musu suka miƙe dukansu, Zainab ya kalla da ta sake gyara kwanciyarta cikin kujerar. Sai ya ga bambancinta da su Zulfa a yanzun ba shi da yawa.

Sai dai ita tata mahaifiyar na da rai, lokacin su ne kawai bata da shi.

“Zeezee mu je in sauke ki gidan su Jarood.”

Kai ta girgiza mishi tare da faɗin,

“Ku je abinku, zan yi kallo.”

Bai ce komai ba. Ya wuce ya ɗauki ledar madarar jariran da ya siyo ɗazun, ya buɗe ya ga instructions ɗin da likita ya rubuta yana ciki sannan ya juya, ya kama hannun su Zulfa da sajda ya fice da su. Suna mota yake tunanin ko me ya kamata ya siya da za su buƙata kuma.

Amma ya rasa, don haka ya ƙarasa da su gida kawai, yana buɗe motar suka fito suka yi ciki. Shi kaɗai ya dinga kwasar kayan babies ɗin da ya siyo yana shiga da su ciki.

Sai da ya gama tas sannan ya dawo ya rufe motar ya koma wajen karɓar gaisuwa, Tayyab ya gani ya haɗa kanshi da gwiwa. Zuwa yayi wajen shi ya ce mishi ya tashi ya shiga gida ya ɗan huta.

Bai musa ba, don jinshi yake kamar ba shi da lafiya, a falo ya samu su Zulfa a zaune, zuciyarshi ta ƙara karyewa wasu hawaye masu ɗumi na zubo mishi.

Kama su yayi yaja su ɗakinsu ya zaunar da su, sannan ya zauna shima, sai lokacin Dawud ya ɗago ya kalle su. Agogon shi da ke gefe ya ɗauka ya duba.

Har ƙarfe uku tayi, ko sallar Azahar bai yi ba. A hankali ya kwance Khateeb yana ɗan gyara towel ɗin kan gado sannan ya kwantar da shi.

Toilet ya shiga ya ɗauro alwala ya fito. Muryarshi a dishe ya ce,

“Ku tashi ku yi alwala mu yi sallah.”

Miƙewa suka yi, Sajda ta ce,

“Yaya ina Ummi?”

Zafi ƙirjinshi yake yi. Kafin ya bata amsa muryar Tayyab a dakushe ya ce,

“Ta yi tafiya sajda, mu je mu yi alwala….”

Bata ce komai ba ta wuce.

*****

Nan suka zauna cikin gida. Gaba ɗaya a nan suka yi sallolinsu, sai dai in Khateeb ya farka Dawud ya bashi madara ya sake komawa bacci.

Ba wanda yake shigowa sai Labeeb, don shi ya zo ya kawo musu abinci, daga zulfa sai Sajda suka ci. Dawud kam bai da zuciyar da zai matsa ma Tayyab.

Nan suka yi Isha’i kafin Labeeb ya shigo ya samu Dawud m.

“Gobe in Allah ya kaimu zan samo wadda zata dinga taya ku aiki, saboda babyn nan.”

Miƙewa Dawud yayi ya raɓa Labeeb yana ficewa daga ɗakin, da sauri labeeb ya bishi yana faɗin,

“Dawud….”

Kai kawo yake yi a cikin ɗakin. Bakinshi Labeeb ke ganin yana motsi amma baisan me yake cewa ba. Ƙirjinshi yake ji yayi wani irin nauyi kamar an ɗora mishi dutse.

Kafin ya tsaya hannunshi ɗaya kan ƙugunshi ɗayan kuma cikin sumar da ke kanshi.

“Da gaske duk abin nan ya faru ko? Ummi ta rasu?”

A hankali kamar wanda baya so Labeeb ya ɗaga mishi kai. Wani irin numfashi Dawud ya ja. Ƙirjinshi kamar an zuba garwashi saboda zafin da yake yi.

Numfashi yake ja sama-sama. Ummi ta rasu, ya ma zai ɗauka mafarki yake yi bayan shi da kanshi ya yi mata wanka? Da kanshi ya kama aka saka ta a makwancinta.

Ya zai yi da Khateeb bayan ko yadda zai mishi wanka bai iya ba. Ware idanuwanshi yayi.

“Khateeb El, bansan ya zan yi da shi ba, ko wanka ban iya mishi ba. Yazan kula da su ba Ummi? Ta ina zan fara?”

Shi kanshi Labeeb baisan me zai faɗa wa Dawud ɗin ba. Ba kuma shi da yadda zai ya taimaka mishi. Mai aiki kaɗai zai iya ɗaukar mishi.

Kujerar da ke wajen Dawud ya kama kafin ya zauna a ƙasa, haɗe jikinshi ya yi waje ɗaya yana rocking gaba da baya.

Tashin hankali ne yake ciki da babu kalaman da za su misalta shi. Rashin da yake ji baya zaton akwai wanda zai fahimta.

Ruɗani ya shiga da baida wanda zai juya wajenshi don ya samu sauƙi. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un ya ji cikin kanshi da muryar Ummi na ɗorawa da,

“In kana cikin matsala ba tunanin mafita za ka yi ba, saboda ba kai ka ɗora wa kanka ba. Allah za ka miƙa wa dukkan lamurranka. Don Shi ya ɗora maka, Shi kuma zai baka mafita……”

Innalillahi ya ci gaba da jerowa cikin kanshi kafin Labeeb ya zauna kusa da shi.

“Banda kalaman da zan taimaka maka da su don ka samu sauƙin abinda kake ji.

Sai dai ina nan idan kana buƙatata Dawud. Kuɗi kaɗai nake da shi, su kuma ba sa maganin baƙin ciki balle dawo da wanda ka rasa.

Banda abinda zan baka.”

Dafa hannunshi Dawud yayi yana dumtsewa.

“Kana nan lokacin da mutumin da na ɗauka zai iya min komai ya guje mu. Kana nan lokacin da muka fi buƙatar tallafi, rayuwar mu ta zo da sauƙi ne saboda da kai a cikinta…..”

Kai labeeb ya ɗaga mishi yana kasa cewa komai na wani lokaci.

“Zan kwana a nan tare da ku.”

Kai Dawud ya girgiza mishi.

“Karka damu. Zan kiraka in ina buƙatar ka.”

Sai da ya kalle shi ya tabbatar zai iya ɗin tukunna ya ce,

“Allah ya tashe mu lafiya.”

Da kai Dawud ya amsa shi. Yana binshi da kallo har ya fice. Kayan da ke ajiye a falon ya kalla. Net ya ɗauka mai haɗe da katifa a jiki ya wuce ɗaki da shi.

Khateeb ya ɗauka ya ce ma Tayyab ya ɗauko mishi net ɗin su biyo shi. Haka suka wuce har ɗakin Ummi. Khateeb ya saka cikin net ɗin ya tofa mishi addu’a tukunna.

Da kanshi ya kama Sajda ya ɗora ta kan gadon Ummi ya kwantar da ita, ya nuna ma Zulfa da ta zo ta kwanta gefen Sajda ɗin.

Shima hawa yayi ya zauna daga can ƙarshe. Yana janye net ɗin da Khateeb zuwa gabanshi. Bubbuga gefenshi yayi yana kallon Tayyab.

Babu musu ya zo ya kwanta gefenshi. Addu’a Dawud ya tofa musu. Yana kallon su. Sai lokacin yake jin hawaye na bi mishi fuska.

Yana sake ganin yadda komai ya dawo mishi sabo. Ba kukan rasuwar Ummi yake ba. Saboda yana mata kyakkyawan zato. Kukan rashinta a tare da su yake.

Kukan maraicin da ƙannenshi suke ciki yake yi. Musamman Khateeb da ba zai samu soyayyar Ummi ba. Yana jin Tayyab ya kama hannunshi ya dumtse.

Muryar Dawud na rawa ya ce,

“Tayyab Ummi ta rasu, yau babu Ummi a rayuwar mu………”

shima Tayyab ɗin kuka yake yi. Su duka biyun kuka suke na rashin da suka yi. Kuka suke na makomar rayuwar su a yanzun.

*****

Da wani irin yanayi ya buɗe ido, kiran sallar Asuba yake ji. Bayanshi ya ji ua riƙe saboda yanayin yadda yai bacci a kishingiɗe.

Zuciyarshi ta doka cike da fargaba kafin lokaci ɗaya komai ya soma dawo mishi, cikin hanzari ya miƙe yana duba Khateeb.

Hannu ya sa saitin hancin shi, ya ji yana numfashi, ya taɓa jikinshi ya ji komai lafiya ƙalau. Numfashi mai nauyi ya saki.

Goshinshi dafe da hannu ya ɗan koma yana kishingiɗa tare da miƙe bayanshi da wuyanshi da suke a riƙe. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un ya ci gaba da jerowa don ƙirjinshi ya yi nauyi.

Ga ɗacin da zuciyarshi take yi, in ba wanda aka taɓa yi ma rashi ba babu wanda zai fahimci abinda yake ji. Ɗan gyara yanayin kwanciyarshi yayi, hannunshi na ɗan taɓa Tayyab.

Da saurin gaske ya janye hannunshi yana miƙewa zaune babu shiri. Sai lokacin yake jin nishi-nishin da Tayyab ɗin ke fitarwa. Hannunshi yasa yana feeling goshin Tayyab da wuyanshi.

Zafin zazzaɓin da ya ji sai da wani irin tsoro ya kamashi, ba shiri ya tsallake Tayyab ya sauka daga kan gadon. Toilet ɗin ɗakin ya shiga. Zuciyarshi ta sake dokawa.

Ganin toiletries ɗin Ummi da ke ajiye. Hannu ya sa ya dafe ƙirjinshi yana yamutsa fuska, raɗaɗi sosai wajen yake mishi. Ga kanshi yayi wani dumm kamar iska bata je mishi.

A daddafe ya fito daga toilet ɗin yana buɗe ɗakin ya fita, nasu ɗakin ya nufa ya shiga toilet ɗin ciki don in ya ce zai yi amfani dana Ummi matsala za a samu, zuciyarshi bata da wannan ƙarfin a yanzun.

Brush ya fara yi sannan ya ɗaura alwala, ya ɗauko ma Tayyab brush ɗinshi ya kuma ɗauko towel, kitchen ya biya ya haɗo da ƙaramar roba ya zubo ruwa a ciki.

Ajiye komai yayi, ya gabatar da sallar Asuba tukunna, ba zai ce ga kalar addu’ar da yayi ba. Yasan dai Ummi ce kaɗai a cikinta, don ba shi da wata wadatacciyar nutsuwa.

Tsugunne yake kan gwiwar shi, a hankali yake girgiza Tayyab wanda ya buɗe idanuwanshi da ƙyar.

“Yaya banda lafiya….”

Muryar shi a dishe ya faɗi. A sanyaye dawud ya amsa shi da,

“Na sani Tayyab, za ka iya tashi ka yi sallah?”

Yana kallo ya ɗan ɗaga mishi kai da ƙyar. Hannunshi ya kama yana taimaka mishi har ya miƙe zaune. Towel ɗin ya saka cikin ruwa ya matse ya soma goge wa Tayyab jiki da shi.

Muryarshi na rawa ya ce,

“Da sanyi sosai.”

“Ka yi haƙuri Tayyab, jikinka yai zafi sosai shi yasa.”

Shiru Tayyab yayi, ya bar Dawud ɗin yana kula da shi, bashie yake so ba, yasan yana da hankalin da ya kamata kar ya ji abinda yake ji a yanzun. Ummi yake so, wani karamin waje a zuciyarshi ya kwanta da fatan ya buɗe idanuwa ya ga duk abinda ya faru jiya ba komai bane sai mummunan mafarki.

Zazzaɓin da ya farkar da shi tsakiyar dare kawai ya tabbatar mishi da hakan abune da bazai yiwu ba. Ba abinda yake son gani sai ummi a yanzun.

Muryarta yake son ji, ruwa Dawud ya ji mai ɗumi ya ɗigo kan hannunshi, hakan yasa shi ɗago kai, runtsa idanuwanshi yayi yana buɗe su kan Tayyab ganin hawayen da ke zubo mishi.

“Kukan nan ya sa ka maka zazzaɓi Tayyab, gashi bansan yadda zan baka haƙuri ba…”

Dawud ya faɗi yana jin shi so helpless, kafin Tayyab ya amsa shi Khateeb ya tashi yana tsandara kuka. Cikin hanzari Dawud ya miƙe ya buɗe net ɗin ya ɗauko shi.

Yasan dole ya yi kuka, ya isa ace yana jin yunwa, ga wanka tun wanda akai mishi ne a asibiti, maganan wanka yasa Dawud tuna rabon su da wanka kwana biyu kenan.

Lallai ya yarda komai kwanciyar hankali ke baka damar yinshi, ba za ka gane kyautar da Allah yai maka ta nutsuwa ba sai lokacin da ka nemeta ka rasa.

Ƙoƙarin lallashin Khateeb yake yi, amma ina, kuka kawai yake yi, sai lokacin Dawud yaji laima a jikin wandon khateeb ɗin, da alama ya ɓata kayan jikinshi.

Towel ya ɗauka ya ɗaure Khateeb a jikinshi ta gaba. Tayyab da ya miƙe yana dafa bango ya bi da kallo, kafin ya maida kanshi kan Khateeb, su duka buƙatar kulawarshi suke yi.

Baisan da wa zai ji ba. Abubuwan sun mishi yawa, Sajda ya ji tana faɗin,

“Ummi makaranta, baki tashe mu da wuri ba.”

Juyawa yayi yana kallonta cike da zafin zuciya, da alama bacci bai sake ta ba. Sajda kenan, ko da yaushe makaranta na ranta, Islamiyya ko boko, bata so ta ga sun makara.

Murza idanuwanta take yi kafin ta buɗe su kanshi. Da mamaki a Fuskar ta ta ce,

“Yaya ina ummi?”

Wani abu ne ya tsaya mishi a wuya da ya kasa haɗiye shi balle ya yi magana, yana kallon damuwar da ke mamaye da fuskarta, muryarta can ƙasa tace.

“Ba zata dawo ba ko yaya? Umm ta tafi kenan….”

Ya kasa magana, yana buɗe bakinshi ba shi da tabbas ɗin abinda zai fito, jin bai bata amsa ba yasa ta ce mishi,

“Mu ya za mu yi yanzun? Me muke yi a gidan nan? Ni ban sanshi ba, yaya mu tafi wajen Abba.”

Abban da ta kira ba abinda ya ƙara mishi sai zafin da zuciyarshi take yi. Tayyab ya fito daga banɗaki, da alama alwala yayi. Ƙarasawa Dawud yayi ya kamo hannun Sajda.

Har lokacin ita kaɗai ke ta surutun ta, ya kasa magana, brush ɗaya ya ɗauka cikin jerin da ya gani, ya miƙa mata yana ficewa daga banɗakin.

Tayyab ya sake kallo da ke sallah sannan ya buɗe ƙofa ya fita. Har lokacin Khateeb bai bar kuka ba. Kitchen ya wuce ya jona kettle ya ɗora ruwan zafi.

Kafin ya koma falon ya shiga buɗe tarkacen da ke ajiye har ya gano ledar da madararshi take ciki. Takardar da ya gani ya ɗauka, ya karanta abinda ke ciki sannan ya mayar.

Feeders ɗin Khateeb duk biyun ya ɗauka ya koma kitchen. Ya wanke su tas, ruwan ya tsiyaya ya haɗa wata sabuwar madarar ya cika duka biyu.

Ya sake cika kettle ɗin yana ɗan jijjiga Khateeb, amma ina, kuka kawai yake.

“Khateeb ba fa kai kaɗai kake rashin Ummi ba, don Allah ka yi haƙuri, ni bansan yadda zan maka ba, inata ƙoƙari, kai shiru don Allah…”

Yake faɗi yana kallon Khateeb da ke ƙirjinshi a ɗaure, kamar ma ba ya fahimtar abinda yake faɗa ɗin don kukan ya ci gaba da yi, kwance ɗaurin yayi ya sauko shi.

Ya taɓa madarar ya ji ta huce, a hankali yake ƙoƙarin bashi, da farko Ƙin sha yayi, sai a hankali tukunna, ya ga bayan awa bibbiyu aka ce ya dinga bashi madara, saboda cikinsu ɗan ƙarami ne za su ji yunwa da wuri.

Ga instructions nan birjik da ya haddace a karatu ɗaya. Yana gama bashi ya ga ya soma komawa bacci. Sake ɗaure shi yayi a jikinshi.

Ƙaramin bokiti ya gani, ya ɗauke shi ya juye ruwan zafin a ciki yana fitowa falo, ledojin ya sake buɗewa har sai da ya gano na kayan wankan Khateeb.

Wanka zai mishi duk da har lokacin baisan ta inda zai fara hakan ba. Ɗakinsu ya nufa da kayan ya kai banɗaki ya ajiye. Ya dawo ya ɗauki kayan sakawa da pampers.

Ya koma ya ajiye su gefe, famfo ya buɗe ya tari ruwa ya sirka na cikin bokitin kafin ya sauko da Khateeb. Ganin ba inda zai zauna yasa shi zama a ƙasa cikin banɗakin.

Don bai da wani zaɓi da ya wuce wannan ɗin. Kaya ya cire mishi da ƙyar, su duka biyun a wahale don Khateeb farkawa yayi yana ta kuka.

Kafin ya cire mishi pampers ɗin da ya ɓata ya ajiye gefe. Baisan inda duk ƙyamarshi ta tafi ba lokaci ɗaya. Da hannu ɗaya ya riƙe Khateeb ya wanke mishi jikinshi.

Sanna ya durƙusa bisa bisa gwiwoyinshi ya zaunar da Khateeb yana riƙe da shi da hannu ɗaya, ɗayan kuma yana goga mishi sabulu yana wanke mishi jiki. Towel ɗin ya yii amfani da shi ya goge wa Khateeb fuska.

Don baisan yadda zai wanke mishi fuska ba, naɗe shi yai da towel ɗin yana kwaso kayan sakawarshi da baby oil din da ya ɗauko ya fito waje.

Da ƙyar ya ɗan shafa mishi saboda kukan da yake yi duk ya rikita shi, ba ƙaramin ƙoƙari iyaye mata suke yi ba, ko kwana biyu ba a yi ba ya fara gane hakan.

Ya saka mishi pampers ɗin, wannan ma don ba zai manta yadda yagae Ummi na yi ba lokacin Sajda na jinjira. Wajen sa mishi kaya yasan ya wahala.

Ƙafafuwanshi ya ji sun ɗauki sanyi, hakan yasa shi fita falo ya sake dudduba kayan ya ko yi sa’ar ganin socks ya saka mishi. Ya ɗauki sabon towel ya buɗe ya ɗaure shi a ƙirjinshi.

Kai kawo yake a falon yana jijjiga Khateeb a hankali har ya samu yai bacci. Sannan ya nufi ɗakin Ummi, Tayyab na zaune kan darduma yai shiru, Sajda ma na gefenshi, sai Zulfa da ke kwance, hijab ɗin da ke jikinta ya tabbatar mishi da ta yi sallah.

Katifar Khateeb ya ɗauko daga kan gado ya sauketa ƙasa, kafin a hankali ya sauko da shi ya saka shi ciki. Tayyab yace ma,

“Ka duba shi zanyi wani abu ne.”

Kai kawai Tayyab ya ɗaga mishi, sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Ɗakinsu ya koma ya shiga toilet, kayan da ya cire wa Khateeb da towel ɗin ya wanke ya shanya su.

Sannan ya wanke banɗakin, wanka yayo kafin ya fito, ya riga da ya jiƙa kayanshi wajen yi wa Khateeb wanka, farin yadi ya saka a jikinshi, ko mai bai shafa ba balle ya yi tunanin taje kai.

A kitchen suka haɗe da Zulfa, da sauri ya ce mata,

“Lafiya dai ko?”

“Zan haɗa kayan da za mu karya ne. “

Sauke numfashi yayi.

“Ki je kawai zan yi.”

Jingina bayanta ta yi da ƙofar kitchen ɗin tana kallonshi, a shekarunta kusan goma tana da hankali dai dai misali.

“Yaya ka bari in taya ka, ina taya Ummi ma.”

Ta ƙarasa maganar da sanyin murya, Dawud ya girgiza mata kai yana ɗorawa da.

“Ki wuce Zulfa.”

Baki ta turo sannan ta fice daga kitchen ɗin, ya ja numfashi ya fitar da shi. Shayi ya dafa ya fasa ƙwai ya soya. Yasan basudai biredi, kuma baisan wa zai barma su Tayyab ba.

Agogon da ke kitchen ɗin ya duba, har bakwai da kwata ta yi, ƙwanƙwasawa ya ji ana yi. Ya fito daga kitchen ɗin ya wuce ya buɗe ƙofar.

Labeeb ne tsaye, hannuwanshi riƙe da ledoji guda biyu. Matsa mishi Dawud yayi ya shigo ciki sannan ya kulle gidan.

“Ya kuka kwana?”

Labeeb ɗin ya buƙata yana neman kujera ya zauna, sannan ya ajiye ledojin da ke hannunshi.

“We are still alive cikin ikon Allah.”

Cike da tausayawa da fahimta Labeeb ya kalle shi.

“Sannun ku.”

“Kaima sannu da hidima da……”

“Shhhh!”

Labeeb ya faɗi da sauri yana girgiza mishi kai, kafin ya ɗora da,

“Da Asuba muka yi waya da dady, yana hanyar dawowa ma, ya ce in tafi gida tare da ku, kar abarku ku kaɗai.”

Sai lokacin Dawud ya samu waje ya zauna. A nutse ya ce,

“Ba wai na ƙi bane El, kai kasan ko da Ummi na nan rayuwar da muke ciki sabuwa ce, bamu ko fara sabawa da ita ba, gashi ta kubce mana.

Mun sake shiga wata daban da bansan ta inda za mu fara ba, i can’t snatch wannan ɗin ma daga wajen su. Zan kula da su, bansan ko ta yaya ba , amma zan yi wallahi, zan iya dakatar da komai na rayuwata indai tasu zata ci gaba.

Rayuwar Mu cike take da abubuwa kala-kala, kai kanka nauyin zai maka yawa.”

Dogon numfashi Labeeb ya ja ya sauke, yana karantar gaskiyar dake cikin zancen Dawud ɗin. Sai dai nauyinsu ba zai taɓa yi mishi yawa ba.

Idan akwai abinda ya sani a rayuwarshi bai wuce yadda zai kula da ‘yan uwanshi ba. Hakan na nufin ba wanda suka fito ciki ɗaya kawai ba.

“Nauyinku ba zai taɓa min yawa ba. Zaman gidanmu ba shi da bambanci da nan.

Da ace yana da shi bazan saurareka ba. Abinda zan maka acan shi ne iya wanda zan iya in kana nan ɗin ma…”

Labeeb ya ƙarasa maganar yana sauke numfashi. Su kansu maraici ba baƙon abu bane a wajensu. Bambancin kawai shi ne ƙaddara ce ta zo ma su Dawud da nasu maraicin ba tare da zaɓin komai ba.

“Zan yi magana da Dady in ya iso. Na kuma saka Mamdud ya taya ni nemo mai aiki….”

Kai Dawud ya ɗaga mishi yana ɗorawa da,

“Ba matsala, Tayyab ma baida lafiya, zazzaɓi yake sosai. Kuma har yau kuka yake. Bansan yadda zan mishi ba.”

Miƙewa Labeeb yayi yana faɗin,

“Ina tayyab ɗin?”

Hanyar ɗakin Ummi Dawud ya nuna mishi. Wucewa Labeeb yayi. Ko mintina biyar bai yi ba sai gashi ya fito riƙe da hannun Tayyab ɗin yana faɗin,

“Bana son gardama Tayyab, ba zaɓi na baka ba ai.”

“Ni ba sai na je asibiti ba, ku ƙyale ni kawai.”

Tayyab ya faɗa yana ƙwace hannunshi daga riƙon da Labeeb yai mishi. Dawud ya kalla.

“Tayyab ka je a duba ka mana, ba ka ji yadda jikinka yake bane?”

Girgiza kai tayyab yayi.

“Ku ƙyale ni, ni ba zazzaɓin asibiti nake ba, rashin Ummi ne, ba dawowa kuma zata yi ba na sani, ku barni in ji rasuwarta yadda ya kamata.”

Da sauri Dawud ya zagaya ya ƙarasa inda yake.

“Zama da zazzaɓin a jikinka shi ne jin rasuwar Ummi yadda ya kamata? Kana jin me kake faɗa ma kuwa?”

Jin rasuwar ummiy yana nufin ko yi da tarbiyarta, abinda hakan yake nufi shi ne karɓar hutun da ta samu koda hakan na nufin menene a wajenka.

Ka kalleni mana Tayyab! Ya kake so in yi? Hauka ko me? Ba kai kaɗai kake jin rashin Ummi ba…..ba zan iya ba…..”

Maganar ta cije mishi, zuciyarshi ciwo take yi, hannu ya ɗora kan kafaɗar Tayyab. Ya sauke muryarshi a ƙasa.

“Zuciyata ba zata iya ɗaukar wani abin ba, don Allah ka je a dubaka Tayyab.”

Hawayen da suka zubo ma Tayyab ya sa hannu ya goge su, amma wasu sabbi ne suke fitowa, hannun Dawud da ke kafaɗarshi ya dafa, cikin kuka ya ce,

“Am so sorry, zan je….. Zan je…. Ka yi haƙuri.”

Kai Dawud ya ɗaga mishi, shi kanshi hawayen ne yake jin na tarar mishi cikin idanuwanshi. Sauke hannunshi yayi ya koma inda ya ta so ya zauna.

Ya saka kanshi cikin hannayenshi ya dafe, yana jin fitarsu daga gidan suka ja mishi ƙofar, ya sauke ajiyar zuciya, duniyar gaba ɗaya ta birkice masa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 11Rayuwarmu 13 >>

1 thought on “Rayuwarmu 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.