"Khateeb wa ya baka chocolate haka?"Dawud ya buƙata yana kamo Khateeb ɗin suka zauna waje ɗaya. Sajda ya kalla, ta ɗan ɗaga mishi kafaɗa cewar itama da chocolates ɗinshi ta ganshi.
Karɓe wasu yayi, ya bar mishi guda biyu, dai dai shigowar Tayyab da ya zauna a gefen Sajda.
"Na ce ka daina ba yaron nan chocolates haka, sai yayi ciwon ciki ko?"
"Yazan mishi? Fita muka yi ya gani ya kama kuka shi yasa."
Kallon Tayyab yayi sosai.
"Gara yai kukan ai, bana so, guda ɗaya ko biyu ya isa."
Hannunshi Tayyab yakai yana saluting. . .