Skip to content
Part 16 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

“Khateeb wa ya baka chocolate haka?”
Dawud ya buƙata yana kamo Khateeb ɗin suka zauna waje ɗaya. Sajda ya kalla, ta ɗan ɗaga mishi kafaɗa cewar itama da chocolates ɗinshi ta ganshi.

Karɓe wasu yayi, ya bar mishi guda biyu, dai dai shigowar Tayyab da ya zauna a gefen Sajda.

“Na ce ka daina ba yaron nan chocolates haka, sai yayi ciwon ciki ko?”

“Yazan mishi? Fita muka yi ya gani ya kama kuka shi yasa.”

Kallon Tayyab yayi sosai.

“Gara yai kukan ai, bana so, guda ɗaya ko biyu ya isa.”

Hannunshi Tayyab yakai yana saluting Dawud ɗin.

“An gama big Don.”

Hararrshi Dawud yayi tare da faɗin,
“Buzz off. Allah jikina ciwo yake min.”

Sajda dake zaune ta ce, 
“Ai na ma fi ku ciwon jiki.”

“Ke me kika yi? Ɗan zuwa makarantar sai Islamiyya.”

Gyara zama ta yi ta kalli Tayyab.

“Hu’un Yaya Tayyab, ga zuwa laboratory, ga zaman rubutu, ga cin abinci, ga…”

“Dalla rufe mana baki.”

Tayyab ya faɗi yana watsa mata harara, dariya Sajda tayi.

“Ka bari ka ji sauran mana, Yaya ai dai na fi shi yin aiki ko?”

Idanuwa suka zuba ma Dawud su duka biyun suna jiran amsar shi, murmushi yayi.

“Sajda bama za’a haɗa ba, Tayyab ƙyuya ta mishi yawa.”

“Ouchh……”

Tayyab ya faɗi yana dafe ƙirji.

“That hurt. M”

“Bani waje nikam, drama king.”

Dawud ya faɗi yana miƙewa, nan ya bar Khateeb wajen su Tayyab da Sajda, don su biyun ba gajiya suke da surutu ba ya wuce ɗakinshi.

Kwanciya yayi duk da ba wani bacci yake ji ba, ya lumshe idanuwanshi. Bai yi mamakin tunanin Yumna da ya lulluɓe shi ba. Yakan ji hakan lokuta da dama yanzun.

*****

Kuɗi ne masu yawa Mami ta fito da su ta miƙa wa tayyab ya karɓa.

“Ka bayar min sadaka.”

Dawud da ke kwance kan doguwar kujera ya ɗan ɗago kanshi ya kalli Mami tare da faɗin,

“Zakka aka fitar ga ‘yan gida Mami?”
Dariya tayi.

“Sadaka ce za a bayar min. Tunda kun gama jarabawa lafiya. Allah ya ƙara karemun ku.”

Tayyab ya amsa da,

“Amin Mami, Allah ya ƙara girma.”

Murmushi kawai tayi, don Dawud ne ya amsa mata. Sajda ce ta biyo zulfa da gudu.

“Don Allah Yaya Zulfa in ɗauka?”

Juyawa Zulfa tayi ta kalli Sajda sannan ta cika bakinta da iska tana fitarwa.

“Sajda karki dameni, wai ta ina rigata zata yi miki? Na ce ki bari muje tare inda aka ɗinka min, sai ai maki kema.”

Turo baki Sajda tayi.

“Ni wannan nake so.”

Girgiza mata kai tayi tana wucewa ta zauna kan hannun kujerar da Dawud yake kwance.

“Sake waje.”

“Haba Yaya, ɗan zama zan yi fa.”

“Ki tashi min a wajen nan, in zan miƙe ƙafafuwana fa?”

Miƙewa Zulfa tayi tana komawa wajen Tayyab tare da faɗin,

“Yaya Tayyab ka kalli Hunger Games?”

Girgiza mata kai yayi, ya karɓi wayarta da ta miƙa mishi. Ta yamutsa fuska.

“Yayi daɗi ne?”

Ya tambaya yana ɗorawa da,

“Ya dai?”

“Yayi daɗi sosai, ba komai wallahi gabana ke ta faɗuwa tunda na tashi da safe.”

“Yaya Zulfa in ɗauka?”

Sajda ta sake faɗi daga inda take tsaye, rolling idanuwanta Zulfa tayi, Mami tayi dariya kawai ta kama Khateeb suka wuce ɗaki abinsu.

“Yaya Zulfa….”

“O. M. G Sajda jeki ɗauka, ki zaɓi duk waɗanda suka yi miki na bar miki duka.”

Dariya Tayyab yayi, da gudu Sajda ta koma ɗakinsu.

“Allah Sajda sai ta sa maka hawan ruwa ba ma na jini ba, in ta nace magana ɗaya eyen.”

Zulfa ta faɗi a gajiye.

“Da gangan ma kike ce mata a’a, kinsan ƙarshe za ki mata yadda take so. Sajda ce fa, ba mai ce mata No. Ki yi ta faɗin Innalillahi….. Nima haka nake ji tun da safe.

Tayyab ya faɗi yana maida hankalin shi kan wayar zulfa da ke hannun shi. Dawud kam jinsu yake, shi ba gabanshi bane yake faɗuwa, gaba ɗaya jikinshi ne a mace. Zuciyar shi tai wani irin sanyi.
Sai ya bar hakan da komawa wajen Abban da za su yi gobe, ƙila duk shi ne yake taɓasu su duka, banda Sajda da murna kawai take yi. Sai kuma Khateeb da bai ma san meke faruwa ba balle abin ya dame shi.

Ƙwanƙwasa ƙofa suka ji.

“Turo….”

Cewar Zulfa. Turo ƙofar aka yi da sallama, murmushin da ke fuskarshi yasa su gane Anees ne. Cikin nutsuwa ya ƙaraso falon ya samu kujera ya zauna suna gaggaisawa.

Zulfa ta miƙe ta ɗauko mishi ruwa da lemo da kofi ta kawo.

“Na gode.”

Ya faɗi yana ɗorawa da,
“Na shigo area ɗin ne nace bari in biyo mu gaisa.”

“Kaga ka samu ladar zumunci, ina stubborn yaron nan.”

Dawud ya faɗi, dariya Anees yayi. A kunyace ya ce,

“Ina su Mami?”

Gyaran murya Tayyab yayi, zulfa tai dariya ta miƙe ta nufi ɗaki, tasan Sajda yake son tambaya kunyar Anees har mamaki take bata.

Bata yi mintina biyu ba, sai ga Sajda ta fito da hijab har ƙasa, a kunyace suka gaisa da Anees ɗin, ya miƙe.

“Nikam zan wuce.”

Sallama suka yi, ya nufi ƙofa, da ido Tayyab ya nuna ma Sajda ta raka Anees ɗin. Kanta a ƙasa ta bi bayanshi.

Jikin motarshi suka jingina.

“Gobe in Allah ya kaimu za ku dawo ko?”

Kai ta ɗan ɗaga mishi.

“In sha Allah.”

“Na ji ina son ganin ki ne Sajda shi yasa na zo.”

‘Yar dariya tayi a kunyace.

“Yaya Anees ai gobe kamar haka muna maƙwaftan juna.”

Shima dariyar yayi.

“Zan ji daɗi, kullum zan ga ƙanwata ko?”

Juyawa tayi ta kalle shi, a karo na farko da ta yarda idanuwan ta suka sauka a nashi, ta kuma riƙe su na’ yan mintina, kafin ta yi murmushi.

“Ina ka bar Yaya Asaad?”

“Baisan na fito ba, yanzun haka yana can yana ta nema na.”

“Da ka taho dashi ai.”

Girgiza mata kai yayi.

“Kinsan Asaad, damuna zai yi, bari in zo in wuce.”

Gyara tsayuwarta tayi, tana tashi daga jikin motar, hannayenta ta fito da su daga cikin hijab ɗin, kanta na ƙasa ta ce,
“Yaya Anees ka ga na siyo maka, bansan ko zai maka dai-dai ba.”

Karɓa yayi, zoben azurfa ne, murmushi ya bayyana a fuskarshi, ganin yanayin kwalliyar da ke jiki, har stone din pink ne. Na mata sak amma ya mishi kyau.

Ya mishi kyau sosai, saboda sajda ce ta siyo, ya mishi kyau saboda ita ce ta bashi, gwadawa yayi, bai zauna ko ina ba sai ƙaramin ɗan yatsan shi.

Ya jujjuya hannunshi, yana ganin kamar anyi zoben ne don ya zauna a wajen.

“Kinsan Yayan nan na son ƙanwarshi ko?”
Dariya ta yi tana rufe fuskarta da hijabinta.
“To buɗe fuskar mu yi sallama, in kun dawo gida dai, tunda kina ganina kullum kin daina wannan kunyar ai.”

Dariyar dai ta sake yi, tana sauke hijab ɗin ba tare da ta ɗago kanta ba.

“Sai kunzo sajda, ki kula da kanki.”

“In shaa Allah. Allah ya tsare ya mayar da kai lafiya

“Amin. Na gode da kyauta.”

Murmushi kawai tayi.

“Ki fara wucewa, in ga kin shiga gida tukunna.”

Bata yi musu ba ta wuce, dai dai ƙofa ta sake juyawa ta kalle shi, murmushi ta yi a kunyace ta tura kofar tana shiga ciki.

“Wannan murmushi haka Sajda, ko mu ba samun irin shi muke yi ba ai.”

Zulfa ta faɗi tana dariya. Da gudu Sajda ta wuce saboda ganin Dawud ya ɗago ya kalleta, ita kunya take ji. Ko mintina sha biyar ba a yi ba da tafiyar Anees.

Sai ga Asaad, shi ko ƙwanƙwasawa ma bai yi ba, kawai turo ƙofar yayi da sallama.

“Nan ya zo ko?”

Ya buƙata.

“Baka iya ƙwanƙwasa ƙofa bane?”

Dawud ya faɗi l, ƙare wa kowa kallo Asad yayi, Ya ga Mami bata nan, juya idanuwanshi yayi.

“I know you are all fully dressed.”

Dariya Tayyab da Zulfa suka yi, ƙarasowa yayi ciki, lemon da Anees bai taɓa ba ya ɗauka yana buɗewa.

“Ai dama nasan nan ya zo, in zance ne ba sai ya bari in rako shi ba…”

Ya faɗi yana kurɓar lemon.

“Tayyab na ga ka yi fari.”

“Bleaching nake yi.”

Tayyab ya bashi amsa yana dariya.

“Don yaron nan ya raina ni.”

Ya faɗi yana hararar tayyab. Ko kallonshi Dawud bai yi ba.

“Come on Don, nifa in law ɗinka ne. Very rude of you ina magana ka share ni…..”

Amsa zai bashi Sajda ta fito.

“Ina wuni. M”

Ta ce ma Asad.

“In-law, kina lafiya?”

A kunyace ta amsa shi ta shige kitchen. Da hannu ya nuna ma Tayyab.

“Haka ya kamata, kana jin kunyata.”

Wani abu Tayyab yayi, kamar mai shirin amai, dariya sosai Asad yake yi.

“Meye haka ɗin ?”

“Ni zanji kunyarka? Allah ya kiyaye.”

Miƙewa Asad yayi yana komawa kan kujerar da Dawud yake kwance yana danna wayarshi. Babu shiri ya miƙe.

“Asad ka ga ka sama min lafiya.”

Sajda ce ta fito daga kitchen.

“Yaya kamar gas ya buɗe”

“Tayyab shiga ka gani.”

Dawud ya faɗi, miƙewa Tayyab yayi ya bi Sajda kitchen ɗin. Bai jima ba ya fito.

“Me ya samu gas cooker ɗin?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Tayyab yayi.

“Na ƙasan ne, kamar ya kwance, na ɗaure nace kar tai amfani da shi ta kunna wancen sai ankai an duba.”

Kai kawai Dawud ya ɗaga mishi, yana ture Asaad.
“Ka tashi ka bani waje, wai me ma ya kawoka?”
“Taya ku haɗa kaya, i can’t wait ku dawo, me ma kuke yi yau ne?”

“Tare zamu tafi.”

Zulfa ta ce,

“Zulfa aike dama ta gidanmu ce, ko kun koma kina gidan mu right?”

“Right.”

Ta amsa shi.

“Don?”

Da sauri Dawud ya ce,

“Karma ka fara Asad, ni da kai, Atleast tafiyan awa ɗaya tsakanin mu.”

Dariya suka yi su dukkansu. Kafin wata irin ƙara kamar an fasa bom ta cika falon har sai da ƙasar ɗakin ta girgiza.

Kallo ɗaya za ka yi wa gaba ɗayansu kasan ba ƙaramin girgiza da tsorata suka yi ba, an rasa mai motsi a cikinsu saboda abin duka ya faru ne cikin ƙasa da minti ɗaya, kafin wani hayaƙi ya ci gaba da fitowa daga kitchen ɗin haɗe da wani irin ƙauri, daga ɗaki Mami ta fito da gudu da Tayyab ta janyo shi, sai da Dawud ya ganta tukunna yake tunanin akwai abinda ya kamata yayi.

Sai dai kamar wanda paralyze ya kama ma ƙwaƙwalwa haka yake jinshi. Wani gunjin kuka Zulfa ta saki tare da faɗin,

“Sajda…..”

Tana nufar hanyar kitchen ɗin da wuta ta soma ci, dam Tayyab ya riƙeta yana jin wani tashin hankali da zai rantse da Allah ko mutuwar Ummi bai ji kalar shi ba.

Da gudu dawud ya mike, Sajda da zulfa ta kira ya dawo da shi hayyacin shi, Sajda na kitchen! Sajda na kitchen!! Sajda na kitchen!!! Shi ne abinda ƙwaƙwalwar shi da komai na jikinshi yake faɗa mishi.

Hanyar kitchen ɗin ya nufa, tafiya yake ba tare da yana jin ƙafafuwanshi na taka wani waje ba, bai taɓa sanin kitchen ɗinsu na da nisa haka ba sai yau, don gani yake gudu yake amma ya kasa ƙarasawa kitchen ɗin.

Ga hayaƙi da wani irin ƙauri da yake neman saka numfashin shi tsayawa, baya jin komai cikin kunnuwanshi sai gunjin da Zulfa take yi tana kiran Sajda.

Tari ya soma sarƙe shi, ga idanuwanshi da suke raɗaɗi saboda zafin hayaƙi.

“Sajda! Sajdaa!!…..”

Yake faɗi muryarshi cike da wasu emotions da bai taɓa sanin ɗan Adam zai iya samu a lokaci ɗaya ba sai yau.

In ya ce ga kalar addu’a ko tunanin da yake yi ƙarya yake, zuciyarshi yake ji ta kasu wajaje da dama na jikinshi saboda tashin hankali, ga zafin wutar na huro shi, amma ba ta shi yake ba.
Ya kasa ganin sajda sam. Ya kasa hangota.

“Sajdaaaaa!!!”

Ya kira muryarshi na sarƙewa tare da wani irin tari da yake jin kamar huhun shi zai fashe.

*****

Asad kanshi tsaye yake hannunshi ɗaya kan ƙugunshi ɗayan kuma yana saka shi cikin sumar kanshi, tun tasowar shi wannan ne tashin hankali na farko da ya taɓa gani.

Kallon su Tayyab yake yi, da yake ta ƙoƙarin riƙe Zulfa tana ƙwacewa, so take ya barta ta nufi hanyar kitchen ɗin, yanayin su kawai ya ƙara karya mishi zuciya.

Mami ta ƙaraso ta miƙa ma Asad Khateeb da ya karɓa m, yaron yai luf a jikinshi ya riƙe shi gam, da alama shi kanshi a tsorace yake.

Hanyar kitchen ɗin mami zatayi, muryar Tayyab na rawa ya ce,

“Mami ina zaki je?”

Hawaye na zubar mata ta ce,

“Yarana har biyu suna ciki Tayyab, bazan iya jira ba, ku kira mana taimako daga maƙota.”

Kai Tayyab ya ɗaga mata yana jan Zulfa suka buɗe gidan, Asad ma bayansu ya bi. Mami kam ta nufi kitchen ɗin.

Tun kafin ta ƙarasa take jin zafin da tiles ɗin ya ɗauka a tafin ƙafarta, ga hayaƙi yayi yawa.

“Dawud! Sajda!”

Take kira tana tari saboda hayaƙin da take shaƙa, numfashinta na barazanar ɗaukewa.

*****

Baya ganin hanya ko kaɗan, ji yayi kaman ƙafarshi ta zunguri wani abu, da sauri ya tsugunna, yana tari, hannunshi ya kai yana murza idanuwanshi.

Wani abu daya taka yasa shi ɗauke ƙafarshi babu shiri yana jin azaba har tsakiyar kanshi data saka shi tuna Allah babu shiri.

Zafin wutar duniya kenan, amma ya jita har ranshi, tabbas ba zamu iya jure azabar Allah ba. Hannunshi ya kai inda ya ji ya ci karo da abu, sajda ce.

“Sajda! Sajda!!”

Yake kira yana girgiza ta, shiru ya ji babu amsa, da hannuwanshi yake lalube, idanuwanshi hawaye kawai ke zuba saboda hayaƙ. Ɗago Sajda yayi yana miƙewa da ita.

Tari yake yi har ƙirjinshi na wani irin ciwo, laluben hanya yake, baya ganinta, hayaƙin ƙara yawa yake, yana jin numfashin shi na ƙoƙarin ɗaukewa.
Kanshi ya ɗauki zafi saboda iskar da ta yi mishi yawa, jiri ya soma ɗibar shi, hannunshi ya kai guda ɗaya, ɗayan na riƙe da Sajda gam, yana neman wajen dafawa, inda ya ɗora hannunshi yai saurin ɗaukewa babu shiri.

Runtsa idanuwanshi yayi, ga azaba ga hayaƙi, ga tashin hankali. Duniyar yake jin gaba ɗaya wani duhu na tahowa yana shirin lulluɓeta, sake riƙe Sajda yayi dam a jikinshi, sama-sama can nesa yake jin maganganun mutane.

Kafin ya ji saukar ruwa mai sanyi a jikinshi da na Sajda, wani numfashi ya ja yana jin samuwarshi a inda ya kamata kafin ya fito da shi, yana ware idanuwanshi, ji yayi an kama kafaɗarshi ana janshi.

Baya gane komai a yanzun, baya fahimtar komai banda iskar da ta dan soma samuwa cikin kanshi da sauƙin da ya ke ji a ƙirjinshi, jan shi ake amma Sajda na manne da jikinshi gam.

Har suka fito falon, yana jin yadda aka ruƙunƙume shi, ta ko’ina akai mishi rumfa shi da sajda. Runtse idanuwanshi yayi yana buɗe su, dishi-dishi ya soma gani kafin ya fara gane mutane.
Ya gane wasu cikinsu, maƙwaftansu ne, bakin su ya ga yana motsi, yasan magana suke amma bata zuwa kunnenshi. Don haka ya sake juyawa, Mami ya gani tsaye idanuwanta sun yi ja.
Fuskarta har ta kumbura, kafin ya maida hankalinshi kan jikinshi, Zulfa ne da Tayyab ruƙunƙume da shi, su dukkansu kuka suke yi, ko ina na jikinsu na ɓari.

A hankali yasa hannunshi ɗaya yana tutture su, sannan ya tsugunna ƙasa da Sajda a hankali, su dukkansu suka bishi, Mami, Asad, da Khateeb suka rufe su suma.

A hankali Dawud ke girgiza Sajda, wani irin yankane a gefen fuskarta, babu ƙonewa ko kaɗan a jikinta, ko dai Dawud zai iya cewa bai gani ba.
Su duka kowa da inda ya kama a jikin sajda, musamman Zulfa da Dawud , don shi a jikinshi take kwance, sai dai ko motsi bata yi ba.

Hannun Tayyab dake tallabe da kanta ya ciro yana son gyara mata wuyanta, jini ya gani jikin hannunshi, cikin tashin hankali yake kallon hannun, kafin ya mayar da idanuwanshi dai dai inda kan Sajda ɗin yake.

Jini ne, tun daga kan farin yadin wandon da ke jikin Dawud har ya taru a ƙasa, ɗayan hannunshi ya kai kan kafaɗar Dawud, zuciyar shi na soma daskarewa a ƙirjinshi ya girgiza shi.

Dagowa Dawud yayi, Tayyab ɗin ya nuna mishi hannunshi, da kuma ƙasa, da sauri Dawud ya juyo da Sajda, ɗankwalin kanta ya jiƙe sharkaf da jini, zame shi Dawud yayi.

Mami da ke wajen, tana tayashi juyo da kan Sajda, huda ce a bayan kanta dake fitar da wani irin jini haɗe da wani abu da su dukkansu ba zasu so faɗi ba.

Numfashi Mami ta ja tana sakin kan Sajda tare  da matsawa baya wani irin kuka na kubce mata, matsawa da kanta Zulfa tayi tana son ganin me suke gani haka.

Babu shiri ta miƙe, baya-baya take tana girgiza kanta, hannu Asad ya kai ya taɓa wuyan sajda, sam bai ji nerve ko ɗaya ya harba ba.

Da sauri ya cire hannunshi, wani cikin maƙwaftan su Dawud ne ya ƙaraso inda suke, ya samu sun gama kashe wutar.

“Ku ɗaukota a tafi asibiti mana.”

Da sauri su dukansu suka miƙe banda Dawud da kanshi yake kafe a ƙasa, idanuwanshi na kan Sajda yana tallabe da ita a jikinshi.

“Yaya ka taso mu tafi.”

Tayyab ya faɗi. Kai ya ke girgiza musu, mami da ke tsaye ita ma ta riƙe Khateeb daya kasa fahimtar ko me ke faruwa ta ce,

“Dawud ka taso.”

Wani mutum dake tsaye shima ya ƙaraso inda Dawud yake, hannun Sajda ya kama, ya sake riƙewa a hannunshi.

“Allahu Akbar. Wannan ai ta rasu!!!”

Riƙe baki Mami tayi tana son toshe kukan da ya ƙwace mata.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Suke faɗi ita da Asad. Yau ya taɓa ganin rasuwa muraran, baisan hawaye na zubar mishi ba, babu abinda ke mishi yawo cikin kanshi sai Anees.

“Yaya ka ji fa, wai ta rasu. Duka mintina nawa muka yi magana da ita! Saboda me za a ce wai ta rasu?!”

Tayyab yake faɗi yana ƙarasa maganar cikin hargowa, Dawud dai bai ko ɗago ba balle ya kalle shi, Zulfa dake jingine da bangon ɗakin ji take kamar zuciyarta zata faɗo daga ƙirjinta.
Cikin karfin hali ta tako, Tayyab ta kalla.

“Yaya Tayyab wai ta rasu?”

Juyowa yai, cikin hargowa ya ce,

“Ƙarya ne! Bata rasu ba!”

Kai ta ɗaga mishi tana yarda da abinda ya ce. Su dukkansu suka zuba ma Dawud idanuwa suna jiran shi. Sai lokacin ya ɗago ya kalle su.

Idanuwansu na kan fuskarshi, yana jin nauyin su har bayan zuciyarshi da ke wani irin tafasa, tun da ya sauke Sajda a ƙasa yasan babu rai a jikinta.
Baisan me zai faɗa musu ba, a karo na babu adadi kenan yana kasa cika musu alƙawarin da ya ɗaukar musu, su dukkansu huɗun.

Wani abu daya tsaya mishi a wuya yake son haɗiyewa ya kasa, numfashi yake ja sama sama.
“Yayaa…”

Zulfa ta kira shi, yanayin muryarta kawai yasa shi jin kamar ƙirjinshi zai buɗe. Hankalin shi ya mayar kan Sajda, ya saukota daga jikinshi ya shimfiɗe ta a ƙasa akan tiles ɗin ɗakin.
Don babu kuma wani sauran gata da zai nuna mata, babu rai a jikinta.
“Bata son sanyi, ka sani, saboda me zaka ajiye ta ƙasa?”
Tayyab ya faɗi ranshi a ɓace kamar zai rufe Dawud din da duka, baice komai ba dai, ya fi kowa sanin Sajda bata son sanyi. Amma yau shi da kanshi ya shimfiɗar da ita akan tiles.

Kallonta yake, duk da ciwon dake fuskarta zai iya rantsewa ya ga murmushi, da murmushi a fuskarta duk da babu rai a jikinta.

Cikin muryar da bai gane tashi bace ya ce musu,
“Ta rasu!!!”

Da mamaki Tayyab yake kallonshi kamar wanda yai mishi magana da wani yare da baya fahimta, dafe kai Zulfa tayi kafin ta tafi ƙasa luuuu…..!

Da hanzari Mami ta rarrafo ta yo kan Zulfa tana girgizata tana kuka, Khateeb ma kuka ya soma mai cin rai duk da baisan abinda yake faruwa ba.
Dawud Tayyab yake kallo, ɗagowa yai suka haɗa ido, cikin idanuwan shi Tayyab ke karantar gaskiyar maganar da ya faɗa. Sajda ta rasu itama. Sajda ta bi Ummi.

Ya kasa faɗin kalmar da ita kaɗai zai furta ya samu sauƙi a ƙirjinshi, fuskarshi ya saka cikin hannayenshi yana jan numfashi da sauri da sauri, ko’ina na jikinshi yana ɓari.

“Ni nace mata ta yi girkinta babu abinda zai faru! She was so scared! Ni nace mata babu abinda gas ɗin zai yi! Yaya ni na kashe ta! Ni na kashe Sajda da kainaaaaa!!!”

Tayyab ya ƙarasa yana durƙushewa ƙasa kan gwiwoyinshi yana sakin wani gunjin kuka kamar mace, faɗi kawai yake,

“Ni na kasheta yayaa….. Sajda ta rasu….. Kuma nine sanadi.”

Dawud ya kasa motsi daga inda yake balle yai comforting ɗinshi, shi kanshi baisan abinda yake ji ba, baisan me ya kamata ya ji ba, kawai ƙirjinshi yake ji zai iya buɗewa a kowane lokaci.

Yana kallon Asad da Mami da wasu mutane na ta shafa ma Zulfa ruwa amma ta ƙi miƙewa, ya sake maida hankalinshi kan Tayyab, wani irin numfashi yake ja kamar wanda asthma attack ya kama.

Miƙewa yayi, yana ci gaba da numfashin, Dawud dai da ido yake binshi, kamun yaja numfashi ya kasa fito dashi, shi ma luu ya tafi yana faɗuwa ƙasa a sandare.

Dawud na kallon mutane sunyi kan Tayyab wani na kiran a kawo ruwa, Mami sakin Zulfa tayi tana yin wajen Tayyab.

Haka in ta yi nan ta jijjiga wannan sai ta koma nan, ta rasa abinda zata yi, kallonsu kawai Dawud yake. Ya sake kallon sajda da ke shimfiɗe, ko ya ce gawar Sajda da ke shimfiɗe a gabanshi.

Inda yana tunanin rayuwa babu komai sai wahala a cikinta, abinda yake gani, kuma yake experiencing a yanzun ya sake tabbatar mishi da babu abinda kowa yake da rayuwarshi sai asara.
Sai lokacin da mutuwa ta sameka babu shiri za ka gane kalar asarar lokuttanka da kayi wajen gina rayuwar da babu abinda ke da tabbas a cikinta face riƙe Allah da hanyoyin Manzon Shi.
Baisan me yake ji ba a yanzun, Khateeb da ke ta kuka ya ƙaraso wajen Dawud, zagayawa yayi ya kwanta kan bayan Dawud yana saƙalo hannunshi kan wuyanshi. Ajiyar zuciya kawai Khateeb yake yi.

Dawud baisan me zai mishi ba, baisan me zai ma Sajda ba, babu sauran wani gata ko kariya da take buƙata a wajenshi, tayyab ya kalla da yake kwance ana ta shafa mishi ruwa.

Sannan ya sake kallon Zulfa itama hakan take, wani abu yake jin yana kwancewa cikin kanshi da baisan ko menene ba, baida tabbacin me ke faruwa cikin kan, abu ɗaya yake ji, ko memene ya kwance a yanzun bazai taɓa komawa dai dai ba.
Abinda yake faruwa a yanzun ya canza rayuwar shi ta fannin da ba zata taɓa komawa kusa da daidaituwa ba. Bazai ce ga yadda lokaci yake wucewa ba.

Yasan dai yana zaune a wajen ne, yana kallon yadda har lokacin da ga zulfa har Tayyab babu wanda akai nasara ya farka, yana nan zaune ya ga shigowar su Labeeb da mutanen daya jima bai saka su a idanuwan shi ba.

Yana nan zaune ya ji Labeeb ya ɗauke Khateeb daga kan bayanshi yana miƙa ma Zainab da ke kuka, yana kallo suna ta magana amma babu sautin da ke zuwa kunnen shi balle ya fahimci me suke cewa.

Yana kallo aka ɗauke Tayyab aka fita da shi, sannan Zulfa ma, yana kallon Mami na kuka kamar ranta zai fita. Yana kallo ta miƙe ta ƙaraso inda yake.

Sajda ta kai hannu zata ɗauka, dawud ya kama hannun ya ture ta, kamo Sajda yayi jikinshi yana riƙeta gam, yana jin yadda jikinta yayi sanyi ƙarara.

Girgiza wa Mami kai yayi, Labeeb ne ya ƙaraso wajen.

“Dawud…….Dawud ka basu ita wanka za a yi mata.”

Hannunshi ɗaya yasa ya hankaɗee Labeeb yana girgiza mishi kai.

“No….. Babu inda zata je, tana nan.”

Dafe kai Labeeb yayi, yasan Dawud baya cikin hankalinshi, shi kanshi yanzun gani yake ko ta’ina rayuwa bata zuwa ma Dawud da sauƙi. Ummi, yanzun kuma ga Sajda.

In shi ne a matsayin Dawud Allah kaɗai yasan haukan da zai yi. Tsugunnawa yayi ya kama Dawud ɗin.

“Dawud ta rasu, gatan ƙarshe da za ku yi mata shi ne gaggawar kaita makwancinta.”

Ɗagowa Dawud yayi ya kalli Labeeb, kafin ya kalli Sajda da ke hannunshi, ɗagota yayi sosai ya sumbaci goshinta da kuncinta da babu ciwo, kafin ya miƙa wa Mami ita.

Miƙewa yayi, jiri na ɗaukarshi, Labeeb ya riƙe shi da sauri.

“Sakeni kawai!”

Dawud ya faɗi, sakin shi Labeeb yayi, a hankali ya taka har sai da ya shige ɗakinshi, turo ƙofar yayi ya sa mukulli ya datse ta.

Kayan da ke kan mirror ya soma hankaɗowa ƙasa yana fasa su, kafin ya jijjigo madubin gaba ɗaya daga mazaunin shi yana hargitsa shi ƙasa.

Duk wani abu da hannunshi ya kai sama destroying yake, duk wani abu da yake cikinshi ne yake hucewa kan kayan da ke ɗakin.

Safe ɗin kayan shi ya buɗe ya shiga fito dasu yana watsarwa a tsakiyar ɗakin, yana jin Labeeb na dukan ƙofar kamar zai karyata yana kiran sunanshi amma a banza.

Sai da ya gama lalata gaba ɗaya kayan da ke ɗakin, inda na Ummi suke ajiye cikin akwati ne kawai bai taɓa ba, tukunna ya zagaya inda babu kaya sosai ya cire key ɗin da ke jikin ƙofar.
Ya buɗe ta.

“Dawud……”

Labeeb ya fara, katse shi yayi da faɗin,

“I am ok…. Mu je.”

Sosai labeeb ya kalle shi kafin ya juya, janyo ƙofar Dawud yayi ya bi bayanshi, suka fice waje, unguwar har ta soma ɗaukar mutane.

Alwala suka yi shi da Labeeb, yana kallon Abba da Dadyn su Labeeb, bai bi takansu ba. Ba su bane a gabanshi. Zama suka yi a nan har sai da Labeeb ya miƙe.

Ya dawo ya ce ma Dawud ɗin ya taso su fito da Sajda an gama haɗata, babu musu ya miƙe suka shige. Kallon makarar yake da sajda a ciki.

Har lokacin kanta baibar zubar jini ba, don za ka iya ganin inda ya ɓata jikin likkafaninta, tunani yake, ba Sajda bace abar tausayi.

Shine abin tausayi, shi da zuciyarshi take bugawa a ƙirjinshi, shi da babu tabbas a cikin kowace daƙiƙa na rayuwarshi, sajda ta huta.

Sajda na da tabbaci a yanzun, saboda gidanta na asali za akaita, shi ne abin tausayi da baisan yadda rayuwarshi zata ƙare ba.

Lumshe idanuwanshi yayi, yana jin har lokacin kamar ƙirjinshi zai buɗe, addu’o’in neman rahmar Ubangiji yake ma Sajda.

Dariyarta, yanayinta da komai nata ke dawo mishi, dafa shi yaji Labeeb yayi, ya buɗe idanuwanshi, ƙarasawa suka yi suka kama makarar.

Dawud ya ɗaga idanuwa ya sauke su cikin na Mami da har sun kumbura saboda kukan da take yi, hijabin jikinta ta ja ta rufe fuskarta, bata son ganin fita da gawar Sajda.

Haka suka fice da ita daga gidan. Kome Dawud yake, nauyin shi da na Tayyab yake haɗawa, ya ji Asad nace ma Labeeb suna asibiti shi da Zulfa.
Sallah akai ma sajda, Dawud zai iya cewa mutanen da suke wajen har sun fi na rasuwar Ummi, saboda Sajda har da Abba a wajen, yasan zata ji daɗin hakan inda zata buɗe idanuwanta ta gani.

Wani iri yake ji har suka ɗauki Sajda zuwa maƙabarta, hankalinshi bai ƙara tashi ba sai da suka sakata a kabari, wani tsoro mai tsanani ya shige shi.

Haka aka saka tukwane aka bi da ƙasa ana rufewa a gaban idanuwanshi, meye rayuwa banda tashin hankali, yana jinjina ma kwanan farko da Sajda zata yi yau a kabarinta.

Yana jinjina wahalarshi da ya zo a Hadisi, sai dai babu yadda zai yi, halayyarta da ibadunta da ba shi da shakku akai su kaɗai zasu iya taimaka mata.

Duk kalar ƙaunar da yake mata, ƙaunarta da ta kai su Tayyab asibiti bata isa ta taimaka mata a kwanan yau ba. Addu’o’in ya sake mata sannan suka juya.

Yana jin yadda ya bar wani ɓangare na rayuwarshi tare da ita, yadda aka haɗa aka rufe da shi har abada. Asad ya gani ya kama Anees da ke wani irin kuka.

Rayuwa kenan, babu komai cikinta sai rashin tabbaci, suna komawa, Dawud bai damu da mutanen da ke cike cikin gidan ba ya shiga. Ɗakin Mami ya wuce.

Akwatinan kayansu da suka haɗa ya shiga tattarowa, yana haɗa su waje ɗaya , Mami ce ta shigo. Muryarta a dishe ta ce,

“Dawud me kake yi?”

“Yau zamu koma, lokaci baya jiranmu, shine abu na ƙarshe da zan yi ma Sajda, a i zaman makokinta a gidan mahaifinta tunda ban mayar da ita da rayuwarta ba.”

Shiga ciki Mami ta yi, tana taya shi, don bata da zuciyar hana shi, in yana ganin yin hakan zai sama mishi sauƙi ko yaya ne, ita wacece da zata hana shi.

Bata haɗa jini da Sajda ba, mutuwarta na kaɗata, ba zata iya cewa ga yadda Dawud yake ji ba. Fita suka yi ta yi da kayan.

Har ɗakin Tayyab ya shiga ya ɗauko nashi don sun haɗa komai, Mami na ganin akwatunan Sajda hawaye sabbi suka zubo mata.

Da motar Dawud da ta Labeeb aka loda kayan, suka wuce tare suka kai. Sannan suka wuce asibiti. Ɗakin da Zulfa take suka fara shiga.
Tana ganin Dawud ɗin ta cire ƙarin ruwan da ke jikinta ta diro daga kan gadon, ƙarasawa ta yi inda yake ta faɗa jikinshi.

Wani irin kuka take kamar zata sake shiɗewa, bai yi ƙoƙarin hanata ba, nata hawayen suna zuba, shi ne sauƙinta. Tsaye yayi, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce mata,

“Mu tafi”

Ɗago jikinta tayi daga ƙirjinshi, jiri na ɗaukarta, Labeeb ya kama hannunta, kanta ta ɗora a kafaɗar shi ya kamata suka bar ɗakin, suka wuce inda Tayyab yake.

Kallo ɗaya Dawud yai mishi, ko rasuwar Ummi bai ga yai kuka irin wannan ba, fuskarshi har ta sake kala. Hawaye kawai ke zubar mishi yana sa hannu yana goge su.

“Taso mu tafi.”

Dawud ya faɗi yana miƙa mishi hannu, kama hannun yayi, ya taimaka mishi ya sauko daga gadon, daga shi har Zulfa babu mai takalma, hannun Tayyab na riƙe cikin nashi suka fita daga asibitin.

Bayan mota ya buɗe musu, suka shiga, sannan ya zagaya, Labeeb ma shiga yayi, shi yake tuƙin. Zulfa ta kwantar da kanta a ƙafafuwan Tayyab, kuka suke har suka kai gida.

Sai da labeeb yai parking suka fito sannan Tayyab ya ce,

“A ina muke?”

“Shi kaɗai zamu iya ma sajda, gidan abbanta, ayi zaman makokinta a nan.”

Hawaye na sake zubar ma Tayyab ya ce,
“Har an yi jana’iza?”

Kai Dawud ya ɗaga mishi. Girgiza kai yayi yana jingina kanshi da motar, ji yake kamar zai mutu shima, ƙirjinshi ciwo yake mishi.

Labeeb da ke tsaye ya kama zulfa, rungumeta yai a ƙirjinshi yana son comforting dinta, sai dai ya rasa kalaman da zai yi amfani da su.

Kallon gidajen Dawud yake yi, duk da ya zo, sai dai iyakacin shi ɓangaren su Labeeb. Sannan ya kalli Tayyab da ke jingine jikin motar yana kuka.

Babu Ummi, babu Sajda, su ukun nan suka rage mishi.

“Yaya kamar gas ya buɗe!!!”

Muryar sajda ta dawo mishi, sai yayi kamar ba wani babban abu bane, inda ya tashi ya duba ƙila da abinda ya faru bai faru ba.

Hannu yasa ya dafe ƙirjinshi da ke zafi, tari na sarƙe shi, yana ganin duniyar na wulwulawa da shi. Yana jin Labeeb ya kira sunanshi.

Yana jin ya tafi kamar mai yawo cikin gajimare, baisan hannuwan wa yake ji ba, Tayyab, Zulfa , ko Labeeb, sama-sama yake jin ana kiran sunanshi kafin wani duhu ya gilma mishi. Komai ya tsaya cik!

*****

Yana jin muryar Labeeb cikin kanshi, amma ya kasa buɗe idanuwanshi, ruwa ya ji an shafa mishi a fuska.

“Don….. Don!…Dawud!!”

Da ƙyar ya iya buɗe idanuwanshi, ya fara sauke su kan Labeeb, da ya ga ya sauke wani numfashin wahala, sannan ya mayar da su jikin bangon wajen.

Daƙuna fuska yayi, kamata yai ace ya ga gidaje ba baƙin fentin nan ba, da sauri ya miƙe daga jikin Labeeb. Kallon wajen yake yi, a zuciyarshi yake ganin cell ne.

Me suke yi a cell shi da Labeeb? Kamar wanda aka doka ma guduma komai ya dawo mishi. Cikin tashin hankali ya ce,
“Yumna…..

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 15Rayuwarmu 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×