Skip to content
Part 17 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

“El yumna….. Bansan ya take ba, bata numfashi….”

Dawud yake faɗi yana dafe kanshi cikin hannayenshi. Miƙewa Labeeb yayi daga tsugunnen da yake ya kama hannun Dawud yana taimaka mishi ya miƙe. 

Yana kallon jirin da yake ɗaukar shi, dam ya riƙe shi, ya fito da shi daga cell ɗin, ‘Yansandan da ke wajen ya kalla. 

“In wani abu ya same shi…… I will see you in court, zan tabbatar babu wanda ya ƙara saka uniform a cikinku!”

Yana jin yadda idanuwansu ke yawo a jikinshi har suka fice daga Police Station ɗin. Mota ya buɗe ya saka Dawud sannan ya zagaya ya shiga. 

Ko ta ina yake jin rayuwa kamar tana janshi, ko wanne ɓari na son samun nashi kason. Kai tsaye asibiti Labeeb ya nufa da Dawud. 

Suna shiga Dawud ya ce mishi,

“Wayata….. I need to know yadda Yumna take….”

Hannu Labeeb yasa a aljihunshi ya zaro wayar tare da faɗin, 

“Gata nan na karɓo maka.”

Hannu yasa ya karɓa ya cire ta daga key. Lambar Anty ya lalubo ya kira. Zuciyarshi dokawa take kamar zata fito daga ƙirjinshi. 

Tana ɗagawa ko sallama bai bari ta ƙarasa ba ya katse ta da faɗin, 

“Anty yumna…….”

“Gamu nan tare Dawud, muna asibiti ma….”

Numfashi Dawud ya sauke ya miƙa ma Labeeb wayar, saboda ba ƙaramin ƙarfin hali yake ba, ko ina na jikinshi ciwo yake. 

Musamman kanshi da yake jin kamar ya cire ya ajiye gefe ɗaya ya ɗan huta, sama sama yake jin Labeeb da Anty suna magana, don ya daina fahimtar abinda ake faɗi. 

Koya ya lumshe idanuwanshi sai ya ga wani haske-haske na gilmawa. Yana jin Labeeb ya riƙo shi yana faɗin, 

“Dammit! stay with me Dawud…..”

Komai jujjuya mishi yake, so kawai yake ya rufe idanuwanshi ko na mintina biyu ne ya ɗan huta, hakan kuwa yayi, yana rufe su ya ji komai shiru.

Ba cikin idanuwan nashi ba kawai harma kanshi, gaba ɗaya komai na duniyar ya tsaya cak. 

BAYAN AWA UKU 

Sallar Magariba ma Labeeb bai sameta cikin jam’i ba. Sa’adda ya ƙarasa masallaci an idar mutane ma har sun soma fitowa. 

Don haka yayi tashi shi kaɗai, bayan ya idar ne ya fito tunanin ya kira Ateefa ya faɗo mishi, don haka ya ɗauko wayarshi. 

Dialing ya sake yi a karo na huɗu, har tai ringing ta gama bata ɗauka ba, ya dafe kanshi. Text ya tura mata 

“Tee ya kike so inyi? In zaki hora ni ban ƙiba, karki haɗa min da kanki da baby. Stay safe, bansan ko ƙarfe nawa zan dawo ba. Love you.”

Sai da ya ga ya shiga sannan ya mayar da wayar aljihunshi ya komawa cikin asibitin. Har lokacin Dawud bai tashi ba, don likita ya ce ma Labeeb ɗin ya samu concussion a kanshi. 

Amma in dai ya samu wadataccen hutu babu wata matsala da za a samu. Kujera Labeeb ya ja ya zauna, yana dafe fuskar shi cikin hannuwanshi. 

“Ciki gare ni wata uku!!!”

Maganar Zulfa ta doki kunnuwanshi, da sauri ya buɗe fuskarshi yana jan numfashi, lokaci ɗaya iskar dake ɗakin ta daina wadatar da shi. 

Yanzun kalamanta guda biyar suke mishi yawo, nauyinsu da komai nasu ke ziyartarshi. Ciki Zulfa take da shi. Ciki gareta har wata uku! 

Da sauri-sauri yake fitar da numfashi yana rasa kalar abinda yake ji, ya dai san kowanne kala ne yana da alaƙa da zuciyarshi saboda ƙunar da take yi.

Ya ga abubuwa da dama, ya ji abubuwa kala-kala, da yawan su sun faru akan shi, amma bai taɓa sanin tashin hankali irin wannan ba. 

Dawud da ke kwance yake kallo, daga haihuwarshi zuwa yanzun Labeeb zai iya cewa kwanciyar hankali na ƙasa da shekara sha shida Dawud ya gani. 

Sauran cike suke da jarabawa iri-iri. Tun daga kan zuri’ar su har zuwa matar da za a ɗaura musu aure da ita cikin awannin da basu shige 28 ba. 

Har yanzun rayuwa bata barshi ya huta ba, wannan karon har da gudummuwar Labeeb ɗin a ciki, sake dafe kanshi yayi da hannuwa. 

Dawud baya nan lokacin da yake aikata zunubanshi, Dawud bai taɓa sanin yana aikata su ba, amma yanzun dole su raba wani kason tare akan abinda ke faruwa da Zulfa. 

Inda ance mishi ta wannan ɓangaren zunubanshi za su kamo shi daga gudun da ya jima yana musu zai ƙaryata.

“Ya Allah….”

Ya faɗi yana sauke ajiyar zuciya. Ta ina zai fara? Me yasa kuskurenshi zai taɓa Zulfa. Wayar shi da ke ringing ta katse mishi tunanin da yake. 

Tun bai zaro ba yasan ɗaya daga cikin ƙannen shi ne, saboda kalar ringtone ɗinsu daban yake. Yana ɗaukowa ya duba ya ga Anees ne. 

“Anees lafiya dai ko?”

Ya buƙata. A nutse Anees ya amsa shi da,

“Kawai zanji ne if all is well, tunda Tayyab ya faɗa mana na jika shiru kuma, shi ne na ce bari in kira in ji.”

“Muna asibiti ne Anees, karka faɗa ma kowa for now. Zan kira su da kaina.”

Da sauri Anees ya ce, 

“Ko in zo? I mean ko kuna buƙatar wani abu”

Girgiza kai Labeeb yayi kamar Anees na ganin shi. Abu ɗaya da yake so da shikenan, yana da hankali sosai. 

“Ba sai ka zo ba. Ka tabbatar komai is under control. Kuna wajen party ɗin har yanzun ne?”

“Eh, amma an sallami kowa, mu kaɗai muka rage, yanzun zamu koma gida.”

Sauke numfashi Labeeb yayi. 

“Ba matsala. Ku kula da kanku.”

Ya ƙarasa yana katse wayar ba tare da ya jira amsar Anees ba. Yasan Tayyab ya kamata ya kira ya kwana a wajen Dawud ya tafi gurin Ateefa. 

Ko magana baya son yi a yanzun nan, baya son yin komai da ya wuce komawa rayuwar shi ta baya don ya goge abubuwa da yawa. Amma yasan abu ne da ba zai yiwu ba. 

Don haka ya sake fito da wayarshi, text yai ma Tayyab na asibitin da suke da Dawud ɗin , da kuma cewar yazo ya kwana wajen shi. 

Ko mintina ashirin ba a yi ba sai ga Tayyab. Kallo ɗaya zakai mishi kasan cikin tashin hankali yake. 

“Ya jikin nashi?”

Ya tambaya. 

“Calm down Tayyab, lafiya ƙalau, kawai hutu yake buƙata.”

Kai Tayyab ya jinjina mishi ba don maganganun shi sun bashi wata nutsuwa ba, don ba zai taɓa ganewa ba. 

Yana ce mishi suna asibiti sai da hanjin cikinshi suka yamutsa, tunanin wani abu zai iya samun Dawud kawai yasa zuciyarshi barazanar tsayawa. 

Kujera ya ja gab da gadon Dawud ɗin ya zauna yana kallon shi, da ciwukan da ke fuskarshi da ta kumbure. Wani abu ya tsaya mishi a wuya. 

“Waya basu right ɗin mishi wannan dukan kamar ɓarawo?”

“Ka bari kawai Tayyab, bansan me ke damun Nigeria ba, kwata-kwata ‘Yansandan mu basa aiki da doka da tsari.”

A ƙufule Tayyab ya ce, 

“Ban damu da doka da tsari ba, wannan dukan da suka yi mishi ne matsala ta. For goodness sake gobe in Allah ya kaimu ɗaurin auren shi….. I feel useless…”

Ya ƙarasa yana sauke muryarshi, dafa kafaɗarshi Labeeb yayi. 

“Ba laifinka bane Tayyab, ka sani kuma.”

Jinjina kai yayi. 

“Gaba daya rayuwar shi akan kula damu ne, bai taɓa tambayar wani abu da ya wuce mu kasance cikin farin ciki ba, kana ganin bai yi deserving farin ciki ko na rana ɗaya ba?”

Sosai maganganun shi suka taɓa Labeeb, wani abu ya tsaya mishi a maƙoshi ya hana shi magana, hango wutar da take ci a hankali da tayyab da dawud basa hangowa yake yi. 

Ji yake dole ma ya samu ruwan da zai kashe musu ita. Baya so ko inda ta ci su gani sam. Da ƙyar ya iya cewa. 

“Take care Tayyab, ka kirani in kana buƙatar wani abu.”

Kai kawai ya ɗaga mishi ba tare da ya ce komai ba har ya fice daga ɗakin. Har inda yai parking ɗin motarshi ya ƙarasa ya buɗe ya shiga. 

Zama yayi ya haɗa kanshi da steering wheel ɗin motar yana maida numfashi. Har ƙasan zuciyarshi yake addu’ar Allah Ya sa Ateefa ta yi bacci. 

Baya jin yana da ƙarfin yi rigima da ita a daren nan. Abubuwa sun mishi yawa, da wannan tunanin ya ja motar a kasalance kamar wanda baya son tuƙin ya nufi gida.

**** 

Har wata ajiyar zuciya ya sauke da bai ga Ateefa a babban falo ba, sama ya hau, bai nufi part ɗinsu ba, nashi shi kaɗai ya wuce. 

Yau ya fi gode ma Allah fiye da koyaushe da yadda suka tsara gidansu, yadda suke da part guda ɗaya a ciki da suke sharing. Sannan kowa na da nashi part ɗin.

Sai da ya watsa ruwa ya fito sannan yayi sallar Isha’i. Dogon wandon da yayi salla da shi ya cire ya ɗauki gajere ya saka. 

Ya bar farar rigar da ke jikinshi tunda ba wani nauyi gareta ba. Ko gashin shi bai taje ba ya fito daga ɗakin ya nufi ɓangarensu shi da Ateefa. 

Bai damu da knocking ba ya tura, wani ƙamshi mai sanyi ya daki hancin shi yana jin yadda lokaci ɗaya damuwarshi ke ɗan yin sauƙi. 

Kwance ya hango Ateefa kan ƙaton gadonsu, jikinta sanye da doguwar riga fara. Kanta babu ɗankwali, kanta babu kitso. 

Duk da ba gashi gareta ba sosai, yana parking, kuma tana kula da shi sosai, wani kyau tai mishi, yadda duk halin da yake ciki baya hanashi jin son Ateefa har mamaki yake yi. 

Silifas ɗin da ke ƙafarshi ya cire a bakin ƙofar ya ƙarasa har inda Ateefa take kwance, ko ɗagowa bata yi ba balle ta nuna alamar ta ji shigowarshi. 

Remote ɗin da ke hannunta ta ci gaba da dannawa tana flipping tasoshi ta kasa tsayawa waje ɗaya, zama yayi gefenta, yasa hannu ya karɓi remote ɗin ya ajiye gefe. 

Gyara kwanciyarta tayi ta juya mishi baya, kanshi ya ɗora akan hannunta, ya lumshe idanuwanshi. 

“Bana son yin rikici da daren nan, na gaji sosai.”

Matsawa ta yi gefe, ta ja mayafi ta rufe jikinta da shi. Sauke numfashi Labeeb yayi. 

“Tee please….”

Shiru tayi ta ƙyale shi. Gyara zamanshi yayi ya ja ƙafafuwanshi ya ɗora kan gadon kafin ya janyo pillow. 

Kwanciya yayi ya ja duvet ɗin da ta rufa da shi yana lulluɓewa, hannunshi ya zagaya ya riƙota jikinshi ya lumshe idanuwanshi. 

A karo na farko tun auren su, da tashin hankalin da yake ciki ya rinjayi abinda yake ji kan Ateefa, sam nutsuwar da yake ji in yana kusa da ita haka ya nema ya rasa yau. 

Maganganun Zulfa sun ƙwace mishi wannan, duk da ƙarshen abinda zai yi tunani a daren nan Mamdud ne. In ya ce zai yi tunanin abinda yayi ba zai kai safiya da sauran nutsuwa a jikinshi ba. 

Yanajin ateefa ta sa hannunta cikin nashi. Da sanyin muryarta da yake so ta ce mishi, 

“What is wrong?”

Yana jin ƙaryar da ta yi saurin zuwa mishi. 

“Babu komai.”

“Hmm….”

Yasan fassarar hmm ɗinta, na farko shi ne bata yarda babu komai ba, na biyu shi ne zata bar maganar saboda tasan bai shirya faɗa mata ba. 

“Ka ci abinci?”

Ta buƙata a taƙaice. 

“Bana jin yunwa….”

Ya amsa ta. 

“Nima haka.”

Shiru yayi, kafin ma’anar maganarta ta ziyarce shi. Da sauri ya miƙe zaune. 

“Tee baki ci abinci ba kike nufi? Kina son ɓata min rai ne ko menene?”

Tashi zaune ta yi itama. Ta sauke idanuwanta cikin nashi. 

“Bana jin yunwa, kamar yanda baka ji, saboda me nawa dalilin zai maka zafi?”

Runtsa idanuwanshi yayi ya buɗe su. 

“Tashi muje mu ci abinci.”

Babu musu ta miƙe. Tare suka sauka har dining area ɗin gidan. Ta jera komai ma. A plate ɗaya ta zuba musu soyayyen dankalin turawa sai farfesun kayan ciki. 

Ci yake ba don yana gane daɗinsu a bakinshi ba, sai don yasan Ateefa na buƙatar abincin, kuma in baici ba ba zata ci ba. Taurin kanta har mamaki yake bashi.

Cokalin ya ajiye, kallonta yake, yanayin yadda take tauna abincin, yadda take haɗiye shi, komai natan nan da yake tsaya mishi a zuciya. 

Yana jin yadda zuciyar shi ke ƙoƙarin tattara duk wani memories da zata iya ɗauka tana adana mishi, yanajin har cikin tsokar jikinshi yadda agogon ƙarshen zaman su da Ateefa yake harbawa. 

Abincin daya ci ya ji yana jujjuya mishi a cikinshi yana barazanar fitowa waje, ba shiri yakai hannunshi ya ɗauki ruwa ya buɗe, ba tare da ya zuba a kofi ba ya kafa baki yai mishi wani irin sha. 

Zufa yake ji da bata da alaƙa da zafin gari, don AC ɗin wajen a kunne take, yasan wannan zufar ta dabance. 

“Ka faɗa min ko me yake faruwa.”

Ateefa ta faɗi kamar zata yi kuka, muryarta cike da tsoro, tasan me take gani a gabanta, wannan ne karo na uku da ta taɓa ganin wannan yanayin a fuskarshi. 

“Meke shirin tarwatsa auren mu?”

Ta buƙata tana wani sauke muryarta can ƙasa. Kai ya girgiza mata saboda bai yarda da kanshi da yayi magana ba. Ture plate ɗin dake gabanta tayi ta miƙe. 

“Tee…tee!”

Ko juyowa bata yi ba, da gudu take haɗa steps biyu na benen tana hawa, har ta kai ƙarshe, da gudu ta nufi ɓangarenta, har inda yake yana jin ƙarar dokowar ƙofarta. 

Kanshi ya ɗora kan table ɗin yana jin komai na hargitse mishi. Tunanin da baya son yi ne yake zuwa mishi. Kamar yanda Mamdud ya faɗa. 

Yayi nasara, gaba ɗaya rayuwarshi yake son lalatawa kuma ya samu nasara, sai dai bai hango abu ɗaya ba, zama El-Labeeb baya nufin El-Maska ya ɓace gaba ɗaya. 

Akwai traces ɗinshi har yanzun. Jikinshi babu ƙwari ya miƙe. Ɓangarenshi ya nufa, yana jin rashin dacewar hakan. Ba shi da wani zaɓi. 

Saboda ko ina na jikinshi yake jin abinda zai musu gobe. Bazai iya kallon fuskar Ateefa ba. Zai iya rasa courage ɗin daya samu. Family ɗinshi shi ne komai nashi.

Ateefa na cikin family ɗinshi, sai dai yasan in zaɓi ya zo, jinin dake yawo a jikinshi zai rinjayi abinda yake ji akanta a ko da yaushe. 

Kwanciya yayi, da tunani kala-kala a zuciyarshi, da shakku, ruɗani da tashin hankalin da yasan safiya zata zo mishi da shi ya rufe idanuwanshi ba don yana jin bacci ba. 

**** 

Da zazzaɓi mai zafin gaske ta shiga gida. Addu’a take kar ta ci karo da duk wani wanda magana zata haɗa su . Sai yanzun take da na sanin nufo gidan. 

Da ta sani part ɗinsu Labeeb tayi zai fi mata kwanciyar hankali a nan ɗin. Hajiya Beeba ta gani tana waya. Ko inda take bata kalla ba ta wuce ɓangaren su. 

Addu’a take kar ta ga Mami, aikam har ta shige ɗakinta ta kulle bata ga kowa ba, kayan jikinta ta soma ragewa sannan ta nufi banɗaki.

Alwala ta yi ta fito. Ta saka doguwar riga ta atamfa. Sannan ta shimfiɗa darduma. Idanuwanta ta ji sun ciko da hawaye. 

Kamar yadda takan yi a watanni uku da suka wuce. Duk lokacin da ta zo gabatar da kowacce sallah, jinta take da wata irin dauɗa a jikinta da babu kalar sabulun da zai taddo inda take balle ya wanke mata ita. 

Hijabi ta ɗauko ta saka, hannunta tasa ta shafi cikinta, hawayen da ke cikin idanuwanta suna zubowa da zafin da ya fi na zazzaɓinta ƙuna. Hannu ta sa ta goge su. 

Duk fitar da suke daga lokacin da ta bar asibiti ɗazu zafin zuciya yake ƙara mata. Abinda ta gani a idanuwan Labeeb kawai ya isheta har ƙarshen rayuwarta. 

Ba zata taɓa manta abinda ta gani ba, yadda ya kalleta……..da sauri ta hau dardumar ta tayar da sallah. Nutsuwar da take samu kenan a yanzun. 

Har ta idar da sallar hawaye ke zuba daga idanuwanta, durƙushewa tayi akan dardumar tana sakin kuka mai cin rai. 

“Allah kai ne shaida akan tarbiyar da na samu daga wajen Ummi, Allah karka riƙeta da laifina. 

Allah ka yafe min, ina mai kunyar haɗa idanuwa da kai a ranar da bani da wannan damar ta roƙon yafiyarka…….Allah ka bani mafita…”

Ta ƙarasa cikin kukan da take ji har ranta. So take ta ɗauki alhakin halin da take ciki ta ɗora akan Mamdud. Sai dai kwana 89 ta ɗauka tana ɗora mishi laifi. Yau ne cikon na 90 ɗin daya canza komai.

Cikin dake jikinta ya canza komai, su dukansu masu laifi ne. Ya kamata su raba dai-dai. Bata san ranar mutuwarta ba, bata kuma san yadda zata zo mata ba. 

Sai dai tasan har zuwa lokacin da zata zo ɗin, zata zama cikin dana sani da ƙuncin rana ɗaya tak da ta canza gaba ɗaya sauran ranakun rayuwarta da bata da tabbas a kansu.

Tasan sauƙi ne a wajen Ummi da ƙasa ta rufeta balle ta ga wannan ranar. Don bata san da idanuwan da zata kalli Ummi da ciki a jikinta ba. 

Tanajin hawayenta suna kafewa sai zafin da ƙirjinta yake yana ƙara mata zazzaɓin da take yi. Kuka take marar sauti marar hawaye.

Kuka take da yadda rayuwarta ta sauya. Kuka take da yadda tasan ba rayuwarta kaɗai bace ta canza, har da ta abinda ke cikinta da ko duniyar bai tako ba. 

Da ƙyar ta iya miƙewa ta mayar da sallar isha’i. Ta koma kan gado ta kwanta, sanyi take ji sosai. Ga zazzaɓi na ƙara rufeta tare da wani ciwon kai. 

Ko ya tai motsi sai ta sake jin laifinta na danneta da nauyin gaske. Inda tana ɗaukar kallon ‘yan gidansu cikin idanuwa bayan abinda ta aikata mai nauyi ne. Yanzun tasan wannan ya girmi wancan ba kaɗan ba. 

Tun bata haɗa ido da kowa a cikinsu ba tana fatan mutuwa ta risketa. Rufe idanuwanta ta yi ta ga wani irin duhu dunɗum. Babu shiri ta buɗe su, lokaci ɗaya tsoro ya ziyarce ta. 

Can ƙasan zuciyarta take jin raunin fatan mutuwar da take ma kanta. Masu tarin ayyuka na alkhairi ma ya suka ƙare da kwanciyar kabari ballantana ita da shakku da kokwanto ya shigo cikin nata kwanciyar kabarin. 

“Allah ka bani tsawon rayuwa da lafiyar da zan nemi gafararKa.”

Hakan take maimaitawa babu adadi. Tsoron haɗa idanuwa da ‘yan uwanta mai sauƙi ne akan tunanin azabar Allah da tayi. Bata san iya lokacin da ta ɗauka a hakan ba. 

Wayarta ta ji tana ringing. Da ƙyar ta iya miƙewa ta ɗaukota cikin jakar da ta dawo da ita. Kafin ta duba waye har ta yanke. Kiran ya sake shigowa. 

Ganin “Yaya” akan screen ɗin wayar yasa hanjinta wani irin yamutsawa da har saida ta jima abinda ke cikinta tsoro. Numfashi ta ja. Hannunta na rawa ta ɗaga. 

“Hello…”

Ta faɗi muryarta can ƙasa. 

“Na tashi ne yanzun, na ce bari in kira ku don hankalinku ya kwanta.”

Sai lokacin ta tuna abinda Tayyab ya faɗi lokacin da suke tare da Labeeb, cikinta ya sake yamutsawa. 

“Yaya…. Lafiyarka dai ko? Babu abinda ya sameka?”

Take tambaya muryarta cike da rauni, tana jin yacda hawayen da ta zata sun kafe suke cika mata idanuwa. 

“Lafiya ƙalau Zulfa. Ki yi bacci kema. Nima kwanciya zan yi.”

Kai ta ɗaga tana kai hannu ta goge hawayen da suka zubo mata, ta kasa cewa komai. 

“Love you sis. Kinsan haka ko?”

Kai ta sake ɗagawa, kuka na ƙwace mata. Inda yasan abinda ta yi, daya janye kalamanshi, tana jin yadda suka zauna mata fiye da ko yaushe saboda tasan ta kusan rasa su. 

“Zulfa….”

Ya kira, tanajin damuwa a muryarshi. Da ƙyar ta iya cewa, 

“Love you more yaya. Sai da safe.”

Bata jira amsar shi ba ta sauke wayar ba tare da ta kashe ba. Ta kwanta, sosai ta tisa sabon kuka. Duk halin da yake ciki, yana farkawa tunanin kwanciyar hankalinsu ne abu na farko da ya zo mishi.

Ta rasa inda nata tunanin ya tafi lokacin da ta aikata kuskuren da ta yi. Ta rasa inda ta ajiye ƙaunar ‘yan uwanta da abinda kuskurenta zai musu. 

Tana jin ciwon kanta na ƙaruwa, zazzaɓin da take ji yana tsananta, idanuwanta a buɗe, bata jin ƙarar komai sai na agogo da bugun zuciyarta. 

Babu tunanin komai banda lokaci da yake ƙure mata, bacci ko na minti ɗaya bai ɗauketa ba…. Kan kunnenta aka kira sallar farko.

**** 

Tana kallon wayarta na ringing, bata ɗauka ba, don tasan kiranta Mummy ke yi. Hula ta ɗauka ta saka ma kanta. Jikinta sanye da legins sai riga loose na vintage. 

Ta fito daga ɗakinta zuwa falo, a dining area ta same su. 

“Gani Mummy.”

Ta faɗi tana jan kujera ta zauna. 

“Your highness…..”

Aseem ya faɗi yana kallonta, rolling mishi idanuwa Mardiyya ta yi. Bata jin kula shi, asalima bata jin magana da kowa yau. Inda za su barta ita kaɗai shi ta fi so. 

“Dama abinci za ki ci.”

Mummy ta faɗi da murmushi. Sauke numfashi Mardiyya tayi. Ta ɗauki kofi ta zuba juice. 

“Bana jin yunwa. Na ci abu haka wajen party ɗazun.”

“Shi yasa gaki nan kamar tsintsiya. Ta yaya za ki yi ƙiba ba kya son cin abinci?”

Jarood ya faɗi hankalinshi kan abincin da yake ci. 

“Mummy ki ce su ƙyale ni.”

Mardiyya ta faɗi tana shagwaɓe fuska. 

“Surutunku ma ya isa ya hana min daughter ƙiba.”

Juice ɗinta ta shanye ta miƙe. 

“Good night. Love you Mum.”

Ta faɗi tana wucewa ba tare da ta jira amsar su ba. 

“What is wrong with her?”

Aseem ya faɗi, yana kallon su dukkansu. Uzair da ba magana ta dame shi ba, kafaɗa kawai ya ɗan ɗaga ma Aseem. 

“Mardi ce fa, har sai ka tambaya meke damunta? Wani shirmen ne kawai.”

Jarood ya faɗi da murmushi a fuskarshi, duk da ya kula da canji ba kaɗan ba a watannin nan tare da Mardiyya.

Wannan shiru-shirun sam ba kalarta bane ba. Duk kauɗin nan da rawar kai, ta yi wani so cool da baya son gani. Ƙanwarshi yake so, can bayan zuciyarshi ya adana zai yi magana da ita. 

Mummy bata saka musu baki ba. Itama tana ƙarasa cinye abincinta tai musu sai da safe ta wuce. Aseem ya kalli Uzair. 

“Muje mu kalli film ɗin yau a ɗakinka mana.”

Ware idanuwa Uzair yayi. 

“No freaking way. Bacci zanyi, me TV ɗin falo da na ɗakinka suke yi?”

Dariya Jarood yayi. 

“Nima yau a ɗakin Uzair nake son yin kallo.”

Runtsa idanuwanshi Uzair yayi. Ya ɗan kalle su, ya ja kujerarshi baya, da gudu ya miƙe, suka rufa mishi baya. Aseem na riƙo mishi riga. 

“Aseem ranka zai ɓaci, wai ba yayanka bane ni. Ka raina ni ko?”

Dariya Aseem yayi. Jarood ya ce, 

“Oh fine, yanzun girma ake pulling kenan, to ai nima yayanka ne. So nace kallo a ɗakinka yau.”

Sauke ajiyar zuciya Uzair yayi. Yasan kawai son takura mishi suke yi. Sam baya son hayaniya da surutu. Hararrsu yayi ya kama hanya suna bin bayanshi. 

Aljihunshi ya lalabu. 

“Aseem key na baya wajenka?”

Girgiza mishi kai yayi. Ya ɗan dafe kai. 

“Na barshi a dining ina jin kuwa.”

Haɗa idanuwa Jarood da Aseem suka yi. Hakan ya ba Uzair damar tura ɗakin ya shige ya rufo shi, tare suka tura amma ya riga ya saka key daga ciki.

“I hate you both.”

Ya faɗi daga cikin ɗakin. Dariya suka yi. 

“We hate you more…”

Aseem ya faɗi yana dariya. 

“Nah, we love him more. L”

Jarood ya faɗi yana murmushi tare da ɗorawa da,

“Good night Auta.”

Haɗe fuska Aseem yayi. 

“Bana son Autan nan big bro.”

Dariya kawai jarood yayi ya wuce ɗakinshi yana jin ƙaunar da ke tsakaninsu na bin shi har ciki. 

**** 

Tana komawa dakinta ta kulle ta faɗa kan gadonta ruf da ciki. Tana jin ƙirjinta ya mata nauyi. Wayarta da ke hannunta tai swiping tana cire key ɗin jiki. 

Gallery ta shiga, ta buɗe hotonunan Danish, kwata-kwata baisan ta ɗauke shi ba, ɗaya dariya yake, tai zooming ɗin hoton saitin fuskarshi. 

Tana jin yadda wani abu ke matsewa a ƙirjinta, duk yadda ake faɗin soyayya, ake faɗin so, shirme take ɗaukar shi, ita gani take soyayya na marasa aikin yi ce. 

A wajenta, aji, kuɗi, matsayi, su ne tattare da soyayya. Bata taɓa zaton ta girmi tunaninta ba. Sai lokacin da ta wayi gari ta ganta a cikinta tsundum. 

Bata sake raina kanta ba sai da ta duba zuciyarta ta ga inda takaita, bata sake jin ta ƙasƙanta ba, bata sake ganin matsayi da kuɗi ba komai bane sai da ta karya ajinta ta nemi soyayya ta rasa. 

Babu wanda zai fahimci halin da take ciki sai wanda ya taɓa soyayya, soyayya da dukkan zuciyar shi ya kuma rasa wannan soyayyar. 

Kallon fuskar Danish na saka mata wata nutsuwa, ta wani ɓangaren kuma yana ja mata ciwo na daban. Maganganunshi na mata zafin gaske. 

Hawaye ta ji sun sake zubowa, ta ɗauka ta daina kuka akan son Danish, tasha yi wa kanta alƙawarin hawayenta sun daina zuba akanshi amma ina. Bata da iko da zuciyarta.

Bata da control kan abinda take ji. Ranar farko data fara ganin Danish na dawo mata kamar a lokacin komai ya faru. 

**** 

Birthday party ɗin babbar ƙawarta Yusra ake yi. Sun riga da sun gama shirya komai da yake cikin harabar gidansu Yusra ɗin za a yi ta dawo gida ta ɗauki kayanta da ta manta. 

Da sauri ta haɗa komai da take buƙata ta fito, jikinta sanye da farin less riga da skirt sai mayafin data yafa a saman kanta tai abaya dashi. 

Da heavy make up a fuskarta, sauri take ta yi, taci karo da Jarood a hanyarta ta fita. 

“Ohhh Yaya mana.”

Ta faɗi tana wucewa, ya kamo hannunta ya janyota. 

“Mardi you bumped into me baki da manners ɗin bani haƙuri, kin wuce kina wani ohh yaya mana.”

Ya ƙarasa yana kwaikwayon yanayin maganarta, shagwaɓe mishi fuska tayi. 

“Yaya sauri nake wallahi, ka barni nikam.”

Haɗe hannayenshi yayi a ƙirjinshi, Jarood baida matsala ko kaɗan, don wani lokaci za ka ɗauka Uzair ne babba, amma baya bari wasan da yake da su raini na giftawa. 

Sauke muryarta tayi. 

“Ka yi haƙuri, yanzun zan iya tafiya?”

Kai ya ɗaga mata yana ɗorawa da, 

“A tsare mutunci dai, a kula Mardi.”

Waving hannunta ta yi mishi daga baya. Tana wucewa abinta, jeep ɗin Mummy da ta yi niyyar fita da ita ta ga Habule bai wanke ba. 

Tun shigowarta ta ce mishi yai sauri ya wanke mata ita, a ganinta mintina goman da tayi ya isa ya wanke mata motar. 

“Habule…. Habule!!!”

Take kira da ƙarfi ranta a ɓace, da gudu Habule ya taho da bokiti a hannunshi. 

“Hajiya ƙarama gani, yanzun zan ɗibo ruwan”

“Habule kai bagidajen ina ne? Wane part na cewa kafin in fito nake son ganin motar nan a wanke ne baka gane ba? 

Me yasa ku ‘yan ƙauyen nan baku san darajar lokaci ba?”

Girgiza kai Habule yayi, yasan ko bai haifi Mardiyya ba yayi ƙanwa ta wajen huɗu da ita. 

“Mtsswww dalla ni matsa ka bani waje, bagidaje kawai….”

Ta ƙarasa tana buɗe murfin motar, ta watsa kaya a ciki, sannan ta zagaya ta shiga. 

“I don’t know why some people are naturally stupid…”

Take faɗi tana kunna motar tai baya da ita sannan ta yi corner tana nufar gate ɗin da zai fitar da ita daga gidan. Ta kai mintina biyar a wajen tana danna ma maigadi horn alamar ya buɗe mata gate amma shiru. 

A fusace ta fito tana doka murfin motar da ƙarfin gaske. 

“Baba idi! Baba Idi!!……”

Take kira tana jin kamar zata fashe saboda ɓacin rai. Fitowa yai daga dan ɗakinshi, sarai ta ga yasa ‘yar rigar shi yana share ƙwalla. 

“Baba Idi don me ake biyanka? Sau nawa zan ma baba magana a sallameka ne? Ka buɗe min gate ya gagara?”

Take faɗi tana watsa mishi kallo a wulaƙance. Jinjina kai yayi. 

“Kiyi haƙuri Mardiyya, bana cikin hankalina. Wallahi yanzun aka aiko ƙanina ya rasu.”

“Mtswww…..meye haɗin buɗe min gate na fita da matsalarka? Malam ni ka buɗe min sauri…….”

Bata ƙarasa ba ta ji cikin wata murya da ta daki kunnenta an ce, 

“Da alama tarbiya bata wadace ki ba ko? Baba ka ga dalilin da yasa na ce ka ajiye aikin nan. Kana nan yara marasa kunya da basu san darajar ɗan Adam ba suna faɗa maka magana!”

Maganganun shi sun kunnata, juyawa ta yi ta ga waye ubanshi a garin Kaduna, ta ko sauke idanuwanta cikin nashi. A rayuwarta banda Mummy da Baba, sai Jarood. 

Babu wanda ya isa ya faɗa bata mayar ba, ko Jarood ɗin ma sai ta ga ranshi ya ɓaci ne take yin shiru. Amma ga mamakinta akwai wani abu tattare da fuskarshi da yai mata kwarjini.

Zata iya cewa ta ga ire-iren maza, masu aji na gaske. Sai dai babu wanda yayi intimidating ɗinta kamar wannan. Duk da jikinshi sanye yake da riga da ‘yar shara na yadi. 

Kallo ɗaya zakai mishi ka ga ƙauyancin da kyanshi bai hana shi fitowa ba. 

“Danish babu ruwanka, ka wuce ka tafi, nima yanzun zan taho.”

Saurayin da Baba Idi ya kira da Danish ya maida hankalinshi kan shi da faɗin, 

“Tare zamu tafi ai, zan jira ka.”

Ya ƙarasa yana juyowa ya watsa ma Mardiyya wani kallo cike da tsana. Muryarta da wani yanayi har lokacin ta kasa ɗauke idanuwanta daga kan Danish ta ce, 

“Ka buɗe min gate sauri nake yi.”

Danish ne ya juya, kamar wanda ya kama kwali haka ya tura gate ɗin ya buɗe shi. Ya dawo ya tsaya yana jingina bayanshi da ɗakin Baba Idi. 

Ta kasa ko ɗauke idanuwanta daga kanshi balle ta wuce. 

“Bana son kallo, musamman daga mutanen da basu san darajar na gaba dasu ba.”

Ya faɗi ba tare da ya kalleta ba. Kunyar da ta ji ta rufeta ta sa ta faɗin, 

“Mtswww me zan kalla a jikinka? Bagidaje kawai…..”

Ta nufi motar ta, ta buɗe ta shiga, a jikinta take jin abinda ta kasa fahimta, a jikinta take jin yanayi da bashi da kalamai. 

Ba tare da tasan ranar zata canza komai na rayuwarta ba, haka ta fice daga gidan da haushin barin saurayin da aka kira da Danish ya faɗa mata maganar da ya so bata sauke mishi buhun rashin mutunci ba. 

**** 

Ji take kamar ƙirjin ta zai buɗe, da tasan komai zai juye haka da ko fita party ɗin ba zata yi ba, sai dai tunanin ƙin sanin Danish kawai a rayuwarta ya sa zuciyarta yin zafi na daban. 

Son shi take ji har wajajen da bata san ana jin soyayya da su ba. Ta rasa kalar wannan jaraba da zuciyarta ta ja musu. Duk mazan da ke mata layi. 

Me yasa Danish, me yake da shi har haka. Ta tabbata abin dariya zata zama, yau ita Mardiyya ce take son ɗan Maigadin su. Duk ajinta, duk ji da kanta, ɗan maigadi ya gigita mata lissafi. 

Ya canza mata rayuwa gaba ɗayanta. Lumshe idanuwanta tayi tana haɗa fuskarta da wayarta dake buɗe da shafin hoton Danish. 

A haka bacci mai wahala ya ɗauketa cike da mafarkin Danish da a wajen shi ita ɗin ba komai bace banda takura. 

**** 

Yana dawowa daga sallar Asuba ya kwanta, yana jin yadda zuciyarshi ke mishi ihu ya je ya duba ya Ateefa ta kwana ya shareta. 

Kwanciya yayi, rashin baccin dabai samu ba da dare yasa wani ya ɗauke shi, lokacin da ya farka takwas har ta wuce, toilet ya shiga yayi wanka. 

Ɗaure da towel ya fito, Ateefa ya gani tana ajiye mishi kayan sakawa akan gado, murmushi ya ɗan yi. Ya ƙarasa inda take, ta baya ya rungumeta. Ta ture shi. 

“Karka jiƙani, jikinka duk ruwa…..”

Sake matseta yayi.

“Ya kuka tashi?”

Ya tambaya a hankali cikin kunnenta. Taɓe baki tayi tana ɗora hannunta kan nashi da ke riƙe da ƙugunta. 

“Ya babynka dai. Ni faɗa muke ko ka manta? Bansan me yasa ma na zo ba, babu goodnight jiya…. Babu dubani yau….”

‘Yar dariya yayi. 

“Saboda yadda kike so na, kyauna baya barin ki zama nesa da ni for lon…..”

Bai ƙarasa ba ta naushe shi da gwiwar hannunta. Ba shiri ya sake ta. 

“Tee da zafi fa”

Ya faɗi yana murza gefen cikinshi. 

“Ka shirya ka zo mu karya. Nasan you can’t wait ka faɗi ma Zulfa abinda yake damunka jiya wanda ni nasan matsalata ne. 

Na kuma san ita zata riga ni ji. Am so not jealous El-labeeb……”

Ta ƙarasa tana tsare shi da idanuwanta kafin ta nufi ƙofa ta buɗe ta fice. Sauke numfashi yayi. Wannan matsalar ta girmi duk inda Ateefa take tunani. 

Kamar yadda ta faɗa ne, matsalar ta shafeta, ta shafe su gaba ɗayan su, kuma zata taɓa su ta fannin da baya tunanin zasu taɓa warkewa. 

3 pieces suit ne Ateefa ta fito mishi da su, suit ɗin ya ɗauka da rigar cikin ya mayar ya ɗauko wata blue mai haske, mai yankakken hannu.

Ya saka, ya ɗora bakar vest ɗin a sama, sannan ya feshe jikinshi da collection na white oud. A gurguje ya ƙarasa shiryawa, malfar shi da sun shade a hannu ya fita daga ɗakin yana sauka ƙasa. 

A dining area ya samu Ateefa zaune kan table tana zuba ma cikinta wainar ƙwan da ke gabanta da mug da ba zai ce ga abinda ke ciki ba. 

Yasan in tana fushi ne kawai bata jiranshi su yi breakfast tare. Tea ya haɗa shima da baya son doguwar magana ya fara sipping a hankali. 

“Tare zamu fita ne?”

Ya buƙata. 

“Ka biya ka ɗauki zulfa. Zan tafi ni kaɗai.”

Ajiye mug ɗinshi yayi kan table. Ta soma ɓata mishi rai. 

“Matsalarki da ni ne Tee, ki daina sako zulfa a ciki…”

“Oh really? Ranka ya ɓaci yanzun? Yaushe zan daina ciwon kai akan zulfa? Yaushe zan daina jin ta fini matsayi a rayuwarka?”

Miƙewa yayi, ya sauke idanuwanshi cikin na Ateefa yana son ta ga yadda ta ɓata mishi rai. 

“Lokacin da kika fara yarda da ni…”

Bai jira amsarta ba ya ɗauki malfar shi, sun shade da mukullan mota ya fice ya barta a nan cike da tashin hankali.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 16Rayuwarmu 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.