Skip to content
Part 2 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Ya kai mintina sha biyar a ƙofar gidan su Yumna yana kiran wayarta bata ɗauka ba. Hankalinshi ya soma tashi. 

Wata yarinya ya gani. Ya aiketa cikin gidan ta kira mishi ita. Sai ta dawo ta ce an ce bata gidan. Yasan ƙarya ne. 

Wayar El ya kira. Not reachable. 

“Damn…”

Ya faɗi yana mai saka hannunshi cikin sumar kanshi. Ya sake gwada lambar Yumna ɗin. Wannan karon ɗagawa ta yi. 

“Kin san me kika yi kuwa? Kin san in na shigo cikin gidan nan abin ba zai kyau ba. Ki fito in kaiki gidan Aunty Binta.”

Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Sun tafi ma. Maybe kawai na tsorata ne. Ka koma in sha Allah ba abinda zai faru.”

Girgiza mata kai yake kamar tana ganinshi. 

“Ki fito Yumna. Ban yarda da zamanki a gidan nan ba. Ban ma san me yasa kika dawo ba.”

Muryarta a tausashe ta amsa shi da, 

“Ya zan yi to? Ina buƙatar albarkar Baba ko ya take a auren nan. Na san kome yake faruwa ba laifinshi bane ba.”

Sauke numfashi yayi. Ji yake kamar ya janyo goben ta zo ya ɗauketa daga wannan ƙangin da take ciki. Don ya fi kowa fahimtar halin da take ciki. 

“Rayuwar mu kenan Yumna. Tamu ƙaddarar da wannan kalar ta zo.”

Da yarda da abinda ya faɗi a muryarta ta ce, 

“Allah Ya san da mu. Ya san zamu iya ɗauka shi yasa ya ɗora mana. Kwana ɗaya ai ya rage.”

Fara’a wahalar bayyana take a fuskarshi saboda dalilai da yawa. 

“Allah ya kaimu goben. Ki kula da kanki please. In kinga abinda baki yarda da shi ba ki kirani.”

Saida tai alƙawarin ko ya wani abu ya faru zata kira shi tukunna sukai sallama ya shiga mota ya juya. 

****

Ta ji wani iri da ta taso Dawud. Tasan ba zai rasa hidimar da yake yi ba ya ajiyeta ya taho. Ita kanta bata san dalilin tsoron ba. Ƙawayen Mami ta ga sun zo suna kallonta ta zo wucewa. 

Ta sake fitowa ta ga sun miƙe suna nufo ta. Mami zata iya komai don ganin auren nan ya fasu. Don gara ta ga mutuwar Yumna da ta ganta nutse a gidan Dawud kuma ta san hakan. 

Jin shiru hayaniyarsu da take ji a falo ta yi shiru yasa ta miƙewa ta kasa kunnenta a jikin ƙyauren ɗakin. Still babu wani motsi. Sauke ajiyar zuciya ta yi. Wata irin azababbiyar yunwa ke addabarta. A hankali ta buɗe ɗakin ta fito. Cikin sanɗa take takawa zuwa kitchen. 

Yanayin shirun gidan kamar ba gobe ɗaurin aurenta ba bai dameta ba. Ba taron biki bane a gabanta. Ta zama mallakin Dawud shi ne buƙatarta. 

Tana shiga plate ta ɗauka ta buɗe warmer ta soma zuba shinkafar da ke ciki. Kamar daga sama ta ji muryar mami. 

“Munafuka. Uwarki ta dafa min abincin?”

Tsoratar da ta yi har murfin warmer ɗin na suɓucewa daga hannunta. Inda sabo ta saba. Bata juyo ba. Ba ta kuma ci gaba da zuba abincin ba. Tsaye take a wajen kamar an dasa ta . Zata rantse tana jin hararar da Mami take mata a bayan kanta. 

“Wai ke aure ko? Kina tunanin don kin bar gidan nan hutu kika samu? Wallahi ko komai nawa zai ƙare sai na hanaki zaman lafiya a rayuwarki.”

Juyowa Yumna ta yi. Idanuwanta cike taf da hawaye. Wannan wane irin bala’i ne. 

“Wai Mami me na tsare miki a rayuwarki? Me kuma kike so da ni? Wadda kike kishin da ita hotonta kawai kika taɓa gani. 

Kin raba ni da mahaifina. Kin raba ni da dangin mahaifina da na mahaifiyata. Duk bai ishe ki ba? 

Ga gidan nan zan bar miki. Da Baba duk ki haɗa. Bansan me kuma kike nema ba.”

Sakin baki Mami ta yi tana kallon Yumna. 

“Oh ni Asiya. Yumna ni kike faɗa wa maganganu haka? Ko ubanki ya isa ya faɗa min magana?”

Mami ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin kaima Yumna mari. Hannunta Yumna ta riƙe dam. 

“Da kenan mami. Wallahi hannunki na sauka kan fuskata zan rama. Na gaji da jarabarki…..”

Kafin ta rufe bakinta. Mami ta rarumo muciyar dake gefe da ɗayan hannunta ta maka mata ita akai. Wata ƙara Yumna ta saki tana dafe kanta da dukka hannuwanta. 

Azabar dukan har ranta ta ji shi. Tana jin ɗumi a inda ta dafe ta san jini ne. Kafin ta gama fahimtar me ke faruwa Mami ta sake dukanta da muciyar a ciki. 

Tsugunawa Yumna ta yi don azaba. Ƙafa Mami ta sa ta kai mata harbi da dukkan ƙarfinta a haƙarƙari har sai da ta faɗi. 

Muciyar ta ci gaba da buga mata ta ko ina har saida ta ga ta daina motsi tukunna. 

“Jarababbiya. Ki bi uwarki da ɗan uwanki kowa ya huta. Mayya kawai!”

Da hanzari Mami ta ɗauki wuƙar da ke ajiye cikin cokula a kitchen ɗin. Hannunta ta yanka da ita. Sai da ta kai ta kawo saboda azaba. 

Sannan ta sake yankar gefen wuyanta da wuƙar kafin ta ajiye tana maida numfashi. Hannu ta sa ta yaga rigar dake jikinta sannan ta kwance dankwalin dake kanta tana yamutsa gashin kanta. 

Dai dai ƙofar kitchen ɗin ta ƙarasa. Gefen jiki ta buga kanta da bangon. Wani jiri take ji yana ɗibarta. Wannan ƙaramar azaba ce ta wucin gadi. In dai buƙatarta zata biya. 

Tsaye tai na mintina ta huta sannan ta wuce daga kitchen ɗin zuwa falo tana ɗaukar wayarta. Lambar Dawud da ta ɗauka a wayar Yumna saboda irin wannan ranar ta lalubo. Dialing ta yi . Sai da ta kira sau huɗu bai ɗaga ba. In bai ɗauka ba plan ɗinta ba zai yiwu ba. A karo na biyar ɗin ne ya ɗaga. 

**** 

Oasis ya tsaya ya siyi ko shawarma ne saboda yunwar da ke damunshi ya ji wayarshi na faman ruri. Dubawa yai ya ga baƙuwar lamba ce. Ƙaramin tsaki ya ja ya saka wayar a key ya ajiyeta ya buɗe motar ya fita abinshi. Sa’adda ya dawo yana zama ya kullo motar wayar shi na sake ɗaukan sabon ruri. Ba daga baƙuwar lambar yake ba. Ba ma kowa yake da tashi lambar ba. 

Ƙyaleta ya yi har ta yanke. Sannan ya ɗauki lambar ya sake dubawa. Ya ga kira har huɗu. Scowl ɗin da ke fuskar shi ya sake zurfafa. 

Wata zuciyar ta ce ya ɗauka. Tunda ana ta kira maybe cikin su Tayyab ne don ba duka lambobin su yake da shi ba. 

Ana sake kira ya ɗaga ya kara a kunnenshi yai shiru. Muryar mace ya ji. 

“Dawud ne?”

Da mamaki ya amsa da, 

“Shi ne lafiya?”

“Uhum. In kana son Yumna ka zo ka ɗauke ta. In da sauran rai a jikinta kenan.”

Wani haske ya ga ya gilma ta cikin idanuwanshi kafin zuciyarshi ta doka da wani irin ƙarfi . Girgiza kai yake yi kawai.

Ba zai sake iyawa ba. Zuciyarshi ba zata iya ɗaukar wani rashin ba. Banda Yumna. Bazai iya ɗaukar wani abu ya same ta ba. 

Zafi ƙirjinshi yake yi sosai. Tari ya sarƙe shi. Duk da numfashin shi da yake ji baya kaiwa inda ya kamata bai hana shi murɗa key ɗin motar ba. Ko ganin titi baya yi sosai ya ƙarasa U-turn ya juya ya nufi hanyar gidan su Yumna da wani irin duhu cikin kanshi. 

**** 

Da murmushi a fuskarta ta sauke wayar jin yayi shiru. Ta san ya ji me ta faɗa. Saura abu ɗaya. Ta san Dawud zai riga su shigowa. 

Ta yi dialing lambar. Tana jin ya ɗaga ta saki wani kukan munafunci tana faɗin, 

“Alhaji kai sauri. Za su kashe ni wallahi. Yumna da saurayinta za su kashe ni…… Alhaji na shiga uku…”

A ruɗe yake kiran sunanta. Ta saki wata irin gigitacciyar ƙara ta kashe wayar. Ta jefar da ita kan kujera ta samu waje ta zauna tana kallon ƙofa. 

******

Kallon ta yake kamar bai taɓa ganinta ba. Kallonta yake yana jin yadda maganarta take yawo tana neman wajen da zata tsaya a kanshi. Maƙoshin shi yake ji kamar ya kwana biyu bai sha ruwa ba saboda bushewar da yayi. Malfar da ke kanshi ya cire yana fifita fuskarshi da ita. 

A tsorace Zulfa ta ce, 

“Ka ce wani abu. Don Allah ka ce wani abu.”

Fifita fuskarshi yake yana jan numfashi. Amma sam ya ƙi jin iskar. Ta ƙi kai mishi inda yake so ta je. 

Abinda yake gudu ne ya faru. Taka tsantsan ɗin da yake yi ya tashi a banza. Ya ɗauka abinda ya akaita ba zai same shi ba. Ya ɗauka ya tsallake wannan tashin hankalin da ya aurar da Zainab. Sama-sama zuciyarshi ke yi mishi. Ba yanzun ya kamata yai tunanin nan ba. 

Muryarshi a dakushe idanuwanshi kafe a ƙasa ya ce, 

“Ƙarya kike. Ki ce min wani bad joke ne wannan.”

Hawaye masu ɗumi ne suka zubo mata. Tunda suka fito saga asibiti ita da Nabila take so da fatan ace ta farka daga mafarkin nan.

Ta kasa farkawa. Da duk mintinan da suke wucewa take ƙara ganin gaskiyar abinda yake faruwa. Kallon El take ya ƙi ɗagowa ya kalleta kamar yana tsoron yin hakan. 

“Who?”

Tasan ma’anar tambayarshi. Ƙara karyar mata da zuciya ta yi. Ta ɗauka fuskantarshi zata fi mata sauƙi. Sai ta ga in ma akwai wanda ya kamata tafi jima nauyi shi ne. Ta ya ma zata fara faɗa mishi ko wanene. Bayan duk abinda ya faru. Ina ma hankalinta yake. Numfashinta ta ji yana barazanar ɗaukewa. 

Maganar El ta sake dawo da ita. 

“Waye?”

Ba ita kaɗai tambayar take tsoratarwa ba. Harda shi kanshi. Yana tsoron amsar da zata fito daga bakinta. Yana tsoron jin abinda yake gudu. 

Ganin ta yi shiru yasa ya matsa jikin motar da take jingine. Hannuwanshi ya raba gefe da gefe na jikin motar yana sata a tsakiya. 

Yana kallon yadda ta runtse idanuwanta tana haɗe jikinta kamar tana son shigewa cikin motar. Can cikin jikinshi yake jin inda ya ɓoye El-Maska yana yawo. 

Inda ya ɓoye asalin El-Maska yana barazanar fitowa. Kanshi yake girgizawa kamar hakan zai sa abinda yake jin tasowarshi ya koma. 

Wannan shi ne maganar da Ateefa take faɗa ɗazun kafin su fito. Ya yarda da tsoronta yanzun. Zaman lafiyarsu yana fuskantar barazana. 

“Zulfa…..”

Ya kira da kashedi a muryarshi. Gab abinda yake ji yake da ɓallewa. A hankali ta buɗe idanuwanta ta sauke su kanshi. 

Yana ganin nadamar da ke cikinsu. Yana ganin dana sanin da take yi. Amma babu ɗaya daga ciki da yai tasiri a zuciyarshi. 

“Forgive me…..”

Ta furta a hankali. Space ɗin da ya rage a tsakaninsu ya ƙarasa haɗewa. Yana jin hucinta kan fuskarshi. Saura ƙiris ta taso da abinda ya jima yana lallaɓawa yai barci. 

“Waye?”

Ya sake tambaya. Cikin kanta take tunanin illar da kuskurenta zai yi. Shekaru biyu kenan rabon da ta ganshi haka. Duk da bata son Ateefa ta san alheri ce ita a tattare da El. Ta canza shi ta fanni me kyau. Ga kuskurenta zai lalata komai. 

Wannan karon tana jin yadda idanuwanta suka bushe. Ta nemi ɗigon hawaye ko ɗaya ta rasa. Sai dai wani nauyi a ƙirjinta. 

Gara ya ji daga bakinta. Ita ya kamata ta faɗa mishi da kanta. Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Mamdud.”

Matsawa El yayi da sauri ya sa hannu yana kare fuskar shi kamar ta watsa mishi wuta. Zamewa ta yi daga jikin motar ta zauna a ƙasa tana haɗe jikinta da ƙafafuwanta. 

Idanuwanta akanshi suke tana ganin yadda yake maida numfashi. Tana kallon illar abinda tai mishi. Kanshi ke sarawa. 

Dariyar Mamdud yake ji cikin kanshi. Fuskar shi yake gani tana mishi yawo. Muryarshi yake ji yana faɗin, 

“I am going to hit you hard El-Maska. Zan lalata abinda yake da kusanci da kai. Ka rubuta ka ajiye. Zan taɓa zuciyarka kamar yadda ka taɓa tawa. I will destroy you!!!”

Sam bai ga Tayyab da ke gabanshi ba. Balle kiran da yake mishi. Hankalinshi yai nisa duniyar daya zaci ba zata taɓa dawowa ta taɓa shi ba. 

Sai ji yai ya girgiza shi. 

“El…….”

“Uhmm.”

Ya faɗi yana kallon Tayyab. Fuskar shi kawai ya kalla ya san wata matsalar ce ta ɓullo. Da ƙyar ya iya saita kanshi ya ce, 

“Inajin ka”

Zulfa da ke miƙewa Tayyab ya kalla. Kafin ya maida dubanshi zuwa El ɗin. 

“Meke faruwa?”

Ya tambaya cike da shakku da rashin yarda. Girgiza mishi kai El yayi. 

“Ba matsalarka bane ba. Ya akai?”

Yasan tsakanin El da Zulfa dangantaka ne da bazai taɓa fahimta ba. Don haka ya share kawai. 

“Dawud na hannun Yansanda. It’s very bad.”

“Wonderful”

El ya faɗi don bai ga wani abu da zai sake faruwa da zai girmi wannan biyun ba yau. Kafin ya ɗora da, 

“Ina su Asaad? Ka je ku sallami kowa. Act normal. Zan ji da komai.”

Kai Tayyab ya ɗaga mishi ya kalli Zulfa na tsawon mintina biyu sannan ya juya ya tafi. Numfashi El ya sauke sannan ya maida hankalinshi kan Zulfa. 

“Karki faɗa ma kowa komai. Za mu yi magana.”

Bata ce komai ba. Bata san me ya kamata ta ce ba. Har ya wuce ya juyo ya kalleta. 

“Ya sani?”

Ya buƙata. Ɗan yatsina fuska ta yi kafib ta ce, 

“Mamdud?”

Irin abinda yai ɗazu ya sake yi. Ya ɗan ja da baya. Kamar kiran sunan Mamdud ɗin da ta yi wani abu ta watsa mishi a fuska. 

Da ƙyar ya iya ɗaga mata kai alamar eh. Ita ma da kai ta bashi amsa da A’a. Wani numfashi ya ja ya sauke shi tukunna ya taka a hankali. Hannunta ya kamo a hankali ya jata jikinshi. So yake ya faɗa mata zai gyara komai. Saboda laifin shi ne. Zunuban shi ne suke rarrabuwa kan mutanen da ya fi kusanci da su. 

Komai ya tsaya mishi. Baisan ta inda zai fara ba. In ya ce yana da plan ƙarya yake. Sumbatar goshin ta ya yi. 

“it’s going to be ok.”

Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Ka yi haƙuri. Don Allah ka yi haƙuri.”

Shiru ya yi kawai. Duk amsar da zata fito daga bakin shi yanzun ƙarya zai zama.

“In kun gama ina son magana da kai.”

Da sauri ya saki zulfa jin muryar Ateefa. Ya ɗauka yammacin nan ba zai sake zuwa da wani rikici ba. 

Ta gefenta Zulfa ta raɓa ta wuce. Ba ita bace a gabanta. Buɗe baki ya yi zai yi magana ta ɗaga mishi hannu. Muryata na rawa ta ce, 

“Yaushe kaina zai daina ciwo akan zulfa?”

Ƙarasowa yayi ya kama hannunta ta fisge. Wasu hawaye masu zafi na zubo mata. 

“Ba abinda kike tunani bane Tee. I can explain.”

“Idan a cikin gida kuke zagin zai zo da sauƙi. Ba akan titi ba. Cikin taron jama’a na wucewa. Me kake tunanin zasu ɗauke ni? I’m the stupid wife da ba ta iya ganin abinda ke gabanta saboda idanuwanta sun rufe da son kuɗi da kasancewa da mutumin da mata da yawa za su bayar da hannunsu na dama don su kasance da.”

Hannu ya kai yana murza goshin shi. Ciwon kan da yake ji yana ƙaruwa da duk second ɗin da ke wucewa. Maganganunta na mishi zafi. 

“Tee….. Ba a nan ya kamata ba. Ki je gida please. Zanyi wani abu. Idan na dawo za mu yi magana.”

Wata dariyar takaici Ateefa ta yi. Muryarta ɗauke da wani yanayi ta ce, 

“Oh hakane. Ba wajen da ya kamata kai magana da matarka bane. Wajen rungume-rungume ne da ‘Cousin Zulfa’.”

Tana ƙarasawa ta juya abinta. 

“Tee….. Tee!”

Ko juyowa bata yi ba. Ƙara sauri ta yi ma tana nufar inda motarta take ajiye. Ya dafe kanshi yana faɗin,

“Damn it!”

Wayarshi ya ɗauko a aljihu. Yana tafiya yana lalubar lambar Tayyab don bai ma tambayi wani station Dawud ɗin yake ba. 

****

A falo ta ajiye komai. Kan kafet ta zauna ta ɗora kanta akan kujera. Kuka take marar sauti. Zuciyarta zafi take na gaske. Ko ya ta rufe idanuwanta Labeeb da Zulfa take gani a tsaye. Ba shi bane na farko. Amma wannan ɗin ya fi taɓata fiye da sauran. 

Akwai wani abu a yanayin su da ta kasa tantancewa a yau ɗin nan. Ko wata huɗu ba aiba da sukai rikicin gaske da Labeeb akan Zulfa. 

Ta ɗauka komai ya wuce. Sake kifa kanta ta yi hawaye na ziraro mata. Tana tuna ranar da suka je asibiti sati biyar da suka wuce. 

Abinda ta gani a idanuwan Labeeb bayan likita ta faɗa musu tana ɗauke da cikinshi ya sake wanke mata duk wani shakku da take ciki. Wunin ranar murna suka wuni yi. Yana nuna mata ƙaunar shi mai tsaya mata a zuciya. Exact maganganun su suka fara dawo mata. 

***** 

Kwance take kan cinyarshi yana zaune kan gadon ya kama hannunta yana wasa da yatsunta. 

“Bazan iya faɗan abinda nake ji ba Tee. Na ji tsoro sosai. Na ɗauka bazan taɓa ganin wannan ranar ba.”

Dayan hannunta takai ta rufe mishi baki tana murmushi cike da ƙaunar shi. 

“Babu tuna baya. Wannan shi ne alƙawarin mu.”

Cizon yatsunta yayi ta janye tana yarfe hannu. Fuskarta a taɓare take kallonshi. 

“Saina rama.”

Dariya yayi cike da nishaɗi kafin ya ɗora da faɗin, 

“Na gode Tee. Na gode da za ki ƙarasa cika min rayuwata.”

Miƙewa ta yi zaune. Tana son ganin fuskarshi sosai. Tana so ta saka idanuwanta cikin nashi kafin ta faɗa mishi maganar nan. 

Zuciyarta ta mata nauyi. 

“Labeeb……”

Gaba ɗaya hankalin shi ya bata. Yana ware mata idanuwanshi da alaman cewan ita yake saurare. Saida ta haɗiye yawu sannan ta ce mishi,

“Zan bar cikin nan Labeeb. Zan hada jini da kai da alkawarin ba zaka sake taɓa wata mace ba sai wadda take halattacciya a wajenka. Bana nufin ni kadail. In har bazan isheka ba. Gara ka auro min wata mu zauna da ita. Bazan iya haɗa jini da kai kana haɗa gado da wasu ba Labeeb…..”

Runtse idanuwanshi yayi ya buɗe su akanta. 

“Tee. Kin san ke kaɗaice yanzun. Babu kowacce mace a rayuwata sai ke. Saboda me hakan yake miki wuyar yarda?”

Da nisantaccen yanayi a fuskarta ta ce, 

“Ba haka bane. Zan iya zama da kai da dukkan halayyarka. Bazan iya kawo wani irina a rayuwar mu ba. Zunubinmu ba zai shafi wanda baisan sa’adda muka aikata ba.”

Kai ya ɗaga mata da cewar ya gane me take nufi kafin ya kamota ya kwantar da ita a ƙirjin shi. Ta lumshe idanuwanta tana shakar ƙamshin shi. 

“Zan cire cikin nan in ka karya alƙawarin mu Labeeb.”

Bai ce komai ba. Kawai sake riƙe ta yai a jikin shi yana nuna mata sonta ba tare da kalamai ba.

**** 

Hannu ta sa ta goge hawayen da suke zubo mata. Har ranta tana nufin maganarta. Da gaske take zata cire cikin jikinta in ya karya alƙawarin su. Ba ƙaramin mataki bane ta ɗauka a rayuwar ta na yarda ta haɗa iyali da Labeeb. Zuciyarta ta saba da karyewa akan shi. Ba zata bari ya taɓa abinda za su haifa ba. Rashin zuwanshi duniya zai fi mishi zuwanta sauƙi. 

****

Allah ne kawai Ya kai shi ƙofar gidansu Yumna lafiya saboda yadda baya ko ganin hanya. Yana parking ya kulle murfin motar. Yama manta da bai ko zare keys ɗin ba. Da gudu ya ƙarasa ƙofar gidansu. Wani irin duka yake ma gate ɗin. A rikice maigadi ya buɗe ƙofar. 

“Malam lafiya?”

Cakumo shi Dawud yayi ya ajiye gefe. Da gudu ya shiga gidan. Wannan ne karo na farko da ƙafarshi ta taɓa wuce ƙofar gidan su Yumna. Na farkon ba abu bane da yake da nutsuwar tunawa a yanzun. Wani sanyi-sanyi yake ji da alamar zazzaɓi ya saukar mishi saboda tashin hankali. 

Ƙofar falonsu ya kama. Yana turawa ya ji a buɗe take. A hankali ya shiga kamar me tsoron abinda zai iya gani in ya buɗe ɗakin. 

Asiya ya gani a tsaye. Yanayin ta kawai ya sa zuciyarshi sake wani irin tsalle. Da wata dakushe war murya ya ce, 

“Baki mata komai ba. Wallahi kuskuren da za ki yi shi ne taɓa min Yumna.”

Yanayin da ya ƙarasa maganar. Muryarshi a karye take. Ba faɗa yake ji ba a yanzun. Yumna yake son gani. 

Dariya Asiya ta kwashe da ita. Ta watsa ma Dawud ɗin wani kallo cike da tsana. 

“Me zaka yi? Kana tunanin lokaci dayae zaka zo ka ce za ka fitar da ita cikin tarkon da na gina shekaru masu yawa?”

Ba jinta yake ba. Yawo yake da idanuwanshi ko zai ga inda yumna take. 

“Yumna!”

Ya kira da ƙarfi. 

“Yumna!!”

Asiya ta maimaita tana kwaikwayon yanayin da Dawud ɗin ya kira sunan da shi. Fuskar shi da tsoro da tashin hankali ya ce, 

“Tana ina? Ina yumna?”

A wulaƙance take kallon shi. Idanuwanshi ta ga yabar kanta zuwa hanyar kitchen ɗin su. Da sauri ta juya. Yumna ce ta rarrafo. Jini ne wanke da fuskarta. Da alama ko hanya bata gani. Kallo ɗaya yai mata yasan jini ne ke ɗibar ta. 

Da hanzari yazo wuce wa. Asiya ta tare mishi hanya. Hannu yasa ya hankaɗeta ta faɗi. Tana tasowa ta kama mishi ƙafa ta riƙe gam. 

Miƙewa ta yi yana ƙoƙarin ɓanɓareta daga jikinshi. Rigarshi ta kama ta cukwikwiye ta cikin hannunta. 

“Sake ni! Wai ke wace irin mata ce?”

Ya faɗi a tsawace. Ai sai ma ƙara cakumar shi da ta yi. Wani irin mari ya kai mata cikin fuska ta saki ƙara amma ko alamar sakin shi bata yi ba. Kallon shi ya maida kan Yumna da ta faɗi a bakin ƙofar.

“Yumna!”

Ya kira ta yana sake jan jikinshi don ya ƙarasa inda take. Amma tamau Asiya ya riƙe shi. Hannunshi ya dunƙule ya kai mata duka a ciki. Ba shiri ta sake shi tai ƙasa tana dafe da ciki tana ihu. Da gudu ya ƙarasa inda Yumna take kwance ya tsugunna. Hannuwanshi rawa suke. 

Ya rasa ta inda zai fara. Da ƙyar kamar mai shirin taɓa wuta ya kai hannunshi kan wuyanta yana feeling pulse ɗinta. Shiru ya ji ba abinda ke harbawa. 

A tsorace ya ke kiran sunanta amma shiru yake ji. Ya sake taɓa jijiyar da ke wuyanta bata harbawa. Wani irin gunji yayi daya fito tun daga zuciyarshi. 

Miƙewa yai ya ƙarasa inda Asiya take. Gashinta ya kamo ya ɗago ta. Babu tunanin komai a zuciyarshi sai na aikata inda ta kai Yumna. 

Wata gabza ya kai mata a fuska. Hannu ya sake ɗagawa zai ƙara mata wata ya ji shigowar mutane falon. Bai damu da ya ko ɗaga kai ya ga me suke ba. 

Jijjiga Asiya ya yi. 

“Inda kika kai min yumna zan aika ki…..”

Duka ya ji a bayanshi ko ta ina ana faɗin,

“Sakar min mata ɗan iska. Mahaukaci kawai.”

Hannuwanshi duka biyu ya sa ya shaƙe wuyan Asiya da azaba ta hanata ko ihu. Babu yadda ba ayi ba. ‘Yansanda huɗu suka taru akan shi.

Dukanshi suke ko ta ina saboda ya ƙi sakinta. Sai da wani cikinsu ya doka mishi kulki akai tukunna ya saketa. Lokacin har ta suma. 

Hannu yasa bayan kanshi ya riƙe. Komai na jujjuya mishi. Sama-sama yake jin sun kama hannunshi sun saka mishi ankwa suna fita dashi. 

Da ƙyar bakinshi yake iya furta.

“Yumna…… Yumna…..”

Yana jin yadda suka ɗaga shi suka jefa bayan mota. Cikin kunnuwanshi yana jin tafiyar da suke amma yumna ce a tunaninshi da ko ina na shi. 

Suna ƙarasawa police station ɗin suka tura shi bayan cell suka kulle. 

Ɗaya daga cikin constable ɗin wajen yake ta kallonshi kamar ya taɓa ganin fuskarshi a wani waje. Miƙewa yayi ya ƙarasa ya ga inda yake a kwance. Ya kalle shi don ya tabbatar shi ɗin ne. Unguwarsu ɗaya. Duk majalisa ɗaya suke zama da Tayyab ƙanin shi. Fita ya ɗan yi daga wajen ya kira lambar Tayyab ɗin ya faɗa mishi. 

Shi ne kawai taimakon da zai iya masa a yanzun saboda zaman mutunci da suke da ƙanninshi. Yana gama wayar ya dawo ciki. 

Dawud kam kwance yake. Ga kanshi dake juyawa ga zuciyarshi da ke ta rawa. Babu yadda za a yi ace Yumna ta barshi. 

Ba zai yiwu ace duk haka zai sa ido yaita kallon su suna tafiya ba. Rufe idanuwanshi yayi gam. Zuciyarshi na ciwo. 

Ciwon da ba sabo bane ba. Fama shi yayi da tunanin rashin Yumna. Kamar wanda aka kunna ma film rayuwarshi take dawo mishi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 1Rayuwarmu 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.