Bayan Yan Wasu Shekaru
Idan akwai abinda Labeeb zai ce ya sauya a rayuwar shi daga yadda yake guda biyu ne. Na farko canji ne mai kyau, saboda sana’ar shi na biya fiye da da.
Yanzun kuma da yake kula da su Dawud hakan na mishi daɗi, baya jiran Mummy ko Dady. Da sun bar mishi kuɗi da basu bari ba zai yi hidimarshi ba tare da shakkun komai ba.
Zai iya kiran wannan ci gaba mai kyau da sauyi mai inganci. Na biyu Mamdud. Ba dangantakar su bace ta canza. Mamdud ɗin ne ya canza ta yadda Labeeb a duk iya tunanin shi ya kasa hango meye sanadi.
Ya zama wani irin wild. Fiye da shi kanshi El-Maska. Ba yadda baiba su zauna su yi magana. Ko wanne lokaci maganarshi ɗaya ce,
“Abinda kake so ne. Stop faking cewar ka damu.”
Maganar Mamdud ɗin faɗa take kawo musu, saboda ɓata ma Labeeb ɗin rai yake. Don haka ya ɗauki idanuwa ya zuba mishi.
Tunda dai baya samun matsala a makaranta sai abin ya ɗan zo ma Labeeb da sauƙi. Amma can ƙasan zuciyarshi baya jin daɗin yadda Mamdud ya lalace. Ba yadda zai yi ne kawai.
Yanzun haka sanye yake da suspenders a jikinshi. Sai dai kanshi babu malfa. Kusan shekaru biyu kayanshi kenan, yana jin daɗin saka su saboda suna karɓar yanayin jikinshi.
Falo ya fito yana ɗaura agogo yana kiran.
“Zulfa! Zulfa!!”
“Gani nan zuwa fa!”
Ta faɗi daga ɗakin Zainab. Ya buɗe baki zai sake ƙwala mata kira ta fito daga ɗakin. Jikinta sanye da riga da wando ta ɗora jacket mai manyan maɓallai a sama ta yi rolling mayafi fari saman kanta. Sai takalma masu tudun gaske a ƙafarta.
Duk da jacket ɗinta ta kawo har gwiwarta bai hana Labeeb girgiza kanshi ba.
“Je ki sake kaya. Now!”
Buɗe baki tayi tare da faɗin,
“Me wannan suka yi? Allah zan fasa rakaka. Ka ce kayan ɗazu basu yi ba. Yanzun ma kuma.”
Kafa mata idanuwanshi yayi. Yana tunanin rashin hankalin Zulfa. Sam bata ganin kyan da take da shi da yadda maza ke binta da idanuwa duk inda zasu wuce. Tunanin shiga wajen party ɗin nan
cike da mutanen da rabi yasan halinsu, kamar yadda yasan halinshi. Idanuwansu akan Zulfa wani abu yake ji ya tsaya mishi a wuya.
“Ki sa atamfa, ko doguwar riga. Banda riga da wando.”
Yana rufe baki Mamdud na shigowa. Ɗan daga girarshi yai duka biyun.
“Kinyi kyau sosai Zulfa.”
“Na gode.”
Ta faɗi tana hararar Labeeb kafin ta juya ta nufi ɗakinta. Juyawa yayi wajen Mamdud.
“Kallon meye wannan? Ƙarya na faɗa. She is hot man. Ka bani ita please.”
“Mamdud bana son iskanci. She is off limit.”
Dariya Mamdud yayi.
“Sai a wajenka ko?”
Yamutsa fuska Labeeb yayi.
“Ewww. Meke damunka wai? Ƙanwata ce for goodness sake Mamdud.”
“Cousin. Cousin… Ka ji me nace ko saina matsa kusa.”
“Saika matso tukunna zan jika”
Da baya-baya Mamdud yake tafiya yana dariya kafin ya juya ya fice daga ɗakin. Zulfa ce ta fito jikinta sanye da doguwar riga ta material, kalar ruwan ƙwai.
Sai mayafin da ta yafa, jaka da takalminta suma kalar ne amma mai duhu. Sauke numfashi Labeeb yayi yana girgiza kai. Shagwaɓe fuska Zulfa tayi.
“Me nayi kuma?”
Girgiza mata kai yayi ya juya. Gara ma kayan ɗazu. Wannan gani yai sun fi mata kyau akan wanda yasa ta cire. Bayaso wani ya kalleta ya kawo wani abu a ranshi.
****
Gyara zamanta ta sake yi cikin motar sannan ta ɗan juya ta kalli Labeeb.
“Wai ina za mu je? Nifa bacci nake ji.”
Hankalinshi na kan tuƙin da yake yace mata,
“Birthday party ɗin Mukhtar Ahmad ake yi. Kin gane shi ai, wanda muka yi fim ɗin “Asalin Mu” tare?”
Ɗan ɗaga kafaɗa Zulfa tayi.
“Na gane shi. Ni nace maka zanje ne? I am not a fan.”
Ta ƙarasa a taɓare. Dariya ya ɗan yi.
“cewa akai kowa ya zo da budurwarshi. Ni kuma banda ita, shi yasa muka taho tare.”
Ɗagowa ta yi daga jikin kujerar ta juya jikinta gaba ɗaya ta fuskanci Labeeb, hannu ta sa ta nuna kanta tare da yin dariya.
“Kowa yasan ƙanwarka ce ni. Duk ina ‘yan matan ka?”
“Ni na faɗa miki ina da ba ma mace ɗaya ba har ‘yan mata?”
Kai ta ɗaga mishi tana zuba mishi idanuwanta.
“Ko last zuwanka da ka je ɗauko ni school da wata mai kama da zabiya ka zo. Ka biya ka sauketa gidanka sannan muka wuce gida. Wacece ita? Ka tuna rannan da muka fita cin abinci. Wadda tai kissing ɗinka and wa…”
Sauke numfashi yayi. Yana kai hannu wajen makunnin radio ɗin motar tare da katse ta da faɗin,
“Karki dameni da surutu Zulfa. Ba daɗewa za mu yi ba. Minti sha biyar ya isa.”
Zata yi magana ya kunna radio ɗin motar yana ƙure volume ɗin. Hannu ta kai zata kashe ya doke hannun. Dariya tayi ta sake kai hannu ta kashe.
“Kina son ranki ya baci ba?”
“Labarai fa ake. Kana jin labarai ne. Beside hiran ‘yan matanka ne baka so ko kuma maganar abinda kake yi da kasan bai kamata ba?”
Gudu ya ƙara ma motar har saida zulfa ta ƙume kai don ba zaune take sosai ba kan kujerarta.
“Yi haƙuri rage gudu. Wallahi nayi shiru.”
Zulfa ta faɗi tana gyara zaman ta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi-karfi. In akwai abinda ke tsoratata bai wuce gudu da mota tana ciki ba.
Ba yadda Labeeb baiyi da ita ba kan tuƙi ta ƙi ko da gwadawa. Don Allah yai mata tsoro, lokaci ɗaya ya so koya musu ita da Zainab. Ga Zainab nan babu inda bata shiga da mota.
Rage gudun yayi, yana dariya ƙasa-ƙasa.
“Yaya labeeb wall…”
“Shiru nake son ji Zulfa.”
Shirun kuwa tai mishi har suka ƙarasa inda ake party ɗin. Motoci ne birjik da mutane da yawa suna ta shiga wajen. Kamar yadda Labeeb ya faɗi bata ga kowanne namiji shi kaɗai ba. Gift ɗin da ya siya yasa akayi wrapping ya ɗauko ya ba Zulfa ta riƙe m.
Kowa da budurwa tare da shi. Jerawa suka yi ita da Labeeb suka shiga. Taron wajen bai sa ta jin komai ba don sun saba zuwa wanda ya fi wannan da Labeeb ɗin.
Gaggaisawa yake tayi da mutane kamar ko da yaushe, Zulfa na tsaye a gefenshi. Sai dai duk wanda ya haɗa idanuwa da ita sai yayi mata murmushi, ta mayar mishi, tana ganin yadda ‘yan matan suke watsa mata kallo.
Dariya ma suke bata, gaba ɗaya mazan wajen bata ga wanda yai mata ba. Don bata ga mai aji kamar Labeeb ba. Wata ce ta tako inda suke, hannu ta miƙa ma Labeeb suka gaisa.
Zulfa ta bi hannuwansu da kallo, ƙirjinta ya soma irin zafin da yake yi inhar ta ga wata da ba ita ba a kusa da shi m. Ta rasa me yasa ranta yake mugun ɓaci.
“Kwana biyu. Ka ɓoye abinka.”
“Ina nan. Zulfa, Samira. Samira, Zulfa.”
“Sannu.”
Zulfa ta faɗi tana jin kamar ta kwaɗa ma Samira mari saboda kalar kallon da take ma Labeeb ɗin.
“Sannunki, finally El-Maska yayi budurwa.”
Girgiza mata kai yayi.
“ƙanwata ce.”
Wani murmushi Samira tayi.
“Oh. Zamu yi magana, any party a gidanka soon?”
“Umm Mamdud zai aiko muku da invite in akwai.”
Jinjina kai tayi. Tai mishi sallama sannan tai gaba.
“Mtsww sai kace zata mayar da kai cikinta.”
Dariya Labeeb yayi.
“She is nice. Tana mana background waƙoƙi haka.”
“Bance ina son sanin kowacece ba. Ni batai min ba.”
Murmushi Labeeb yayi, indai rikicin Zulfa ne kan ‘yan matan da suke mishi magana ya saba.
“Chill nima batai min ba. Muje mu lalubo Birthday guy ɗin nan mu bashi gift mu tafi gida.”
“Da ya fi. Don bacci nake ji.”
Tare da Zulfa suka tafi har ya hango Mukhtar a cikin taron mutane. Karɓar gift ɗin yayi ya je ya bashi. Yana dawowa ya samu Zulfa tsaye da wani producer suna hira.
Ƙarasawa yayi. Fuskarshi a haɗe.
“Aminu sannu fa. Zulfa mu je.”
“El-Maska. Oh tare kuka zo kenan.”
“Yeah. Tare muke.”
Labeeb ya faɗi yana zuba mishi idanuwanshi cike da yanayin da ke nuna baya buƙatar shi a wajen.
“Um… Sai mun haɗe.”
Ko amsa Labeeb bai bashi ba. Idanuwan dai ya kafa mishi. Har ya bar wajen, juyawa yai kan Zulfa.
“Meye kashedi na in mun zo waje irin haka? Bana so kina magana da kowa. Na tafi for like mintina biyar har kin yi magana da shi.”
“Kai kowa kake kulawa. Don mun gaisa. He is nice, na bashi address ɗina ma”
“What? Kinsan waye Aminu kuwa? Zulfa kina son ɓata min rai ba. Idan na ga ƙafarshi a area ɗinmu gaba ɗaya …as in kusa kusa da Area ɗinmu… Mtsww”
Ya ƙarasa yana juyawa ya kama hanyar da zata fitar da shi daga wajen. Da murmushi a fuskar Zulfa ta bi bayanshi. Don kawai ta ga faɗanshi yasa ta ce ta ba Aminu address ɗinta.
Kyau yake ƙara mata in yana faɗa. Musamman in ita yake ma wanda lokuta kaɗan kaɗan hakan ke faruwa. Amma ta tabbata tafi sauran ‘yan gidansu ganin ɓangarori da yawa nashi.
Bakin mota ta same shi yana magana da wata yarinya.
“It was one night…me yasa ba zaki gane hakan ba? Bana budurwa, ko zanyi bazan fara dake ba.
Ki kalle ki mana.”
Dariya yarinyar tayi.
“Ban kai matsayin budurwa ba, amma na kai na abokiyar iskanci ko?”
“Watch yadda harshenki yake yawo!”
Zulfa ta faɗi ranta a ɓace. Kallonta Labeeb yayi.
“Ki shiga mota Zulfa.”
“Ita kake screwing kenan ‘yan…”
Bata ƙarasa ba ya ɗauketa da mari.
“Believe me bakya son sanin El-Maska. Wannan shi ne last time da zan ganki taku ashirin kusa da ni.. In kin shiga ciki ki tambaya waye El-Maska kafin ki sake gwada wannan shirmen.”
Yana ƙarasa maganar ya buɗe mota ya shiga.
“Kai kake ja mana wannan abin kunyar. Da kaza da agwagwa duk naka ne. Ka kalli yarinyar da ke faɗa maka magana…”
“Zulfa.”
Ya faɗi cike da kashedi. Bata saurara ba, don ta gama harzuƙa. Ga ƙirjinta da ke mugun zafi.
“No ka barni in faɗi abinda ke raina. Kai aure mana. Da wannan zunuban da kake ɗauka.”
Motar ya fizga ba tare da ya ce komai ba. Gudu yake sharawa da su, Zulfa kuma bata mishi magana ba har suka kai gida. Buɗe murfin motar tayi.
“Kai aure zai yi saving mana stress da yawa.”
Ta faɗi tukunna ta fice daga motar tana shigewa cikin gidan. Haɗa kanshi yayi da gaban motar yana sauke numfashi. Sam baya son Zulfa na ganin gifcin El-Maska.
Babu yadda zaiyi ne. Indai yana gari suna tare, in sun fita kuma da wahala inda za su je baiga wata da mu’amala ya haɗa su ba.
Fitowa yayi daga motar ya shiga cikin gida, bai samu kowa a falon ba. Kanshi tsaye ɗakin Zulfa ya nufa. Ya ƙwanƙwasa tare da kiran sunanta. Yasan tana jinshi tai shiru.
Don haka ya tura ɗakin. Tana tsaye tana cire ɗan kunnayenta, ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon.
“Zo mu yi magana.”
“Bacci nake ji. Ka tafi abinka.”
Miƙewa yayi. Ya ƙarasa inda take ya kamo hannunta ya jata ya zaunar sannan ya zauna. Cikin fuska ya kalleta.
“I am sorry.”
Sauke numfashi ta yi tana jin ɗaci da zafin da zuciyarta tai mata har lokacin yana mata yawo.
“Ba ni zaka ba haƙuri ba. Abinda kake yi bashi da kyau, yana ci min rai. Gara kayi aure.”
Kai ya ɗaga mata.
“Zanyi ƙoƙari. Bari in barki ki huta. I love you okay.”
“I know. Love you more.”
Ta faɗi tana hamma. Miƙewa yai, ya ranƙwafa ya sumbaci kuncinta yai mata saida safe sannan ya fice. Zuciyarta ta ji ta kumbura da wani yanayi. Ita take matsa mishi yai aure. Amma tunaninshi da wata kawai yana sata jin numfashinta na shirin ɗaukewa. Kome take ji akan Labeeb tasan ganinshi da wata tsaf zai illatata.
****
Bacci yake ya ji wayarshi na ringing. Da ƙyar ya lalubota ya amsa ya kara a kunnenshi.
“Emergency 606.”
Mamdud ya faɗi ta cikin wayar. Baccin da ke idanuwan Labeeb ne yaji ya nema ya rasa. Dirowa yai daga kan gadon babu shiri.
Three quarter ne a jikinshi don haka riga kawai ya saka. Ya shiga toilet ya sake wanke fuska ya ɗauki mukullin mota ya fita.
Da gudu ya ƙarasa gidanshi. A ƙofar gida ya samu Mamdud da wata yarinya a tsaye. Ya fito daga mota, kallonta yake yana tunanin ya taɓa ganin fuskarta koma a ina ne.
“Gashi nan ya zo.”
Mamdud ya faɗi yana shigewa cikin gidan. Yarinyar ta ɗago ta kalli Labeeb idanuwanta sun rine saboda kuka, yanzun ma hawaye ne cike taf a idanuwanta.
Muryarta na rawa ta ce,
“An…an kawo kuɗin neman aurena. Ciki gareni wata ɗaya.”
Runtsa idanuwa Labeeb yayi yana jin duniyar tayi tsaye cik. Yanzun ya tuno yarinyar. Ta kai sati tsaye a ranshi saboda shine namiji na farko da ta sani.
Ya manta fuskarta amma sanadin abinda yai mata na adane a zuciyarshi. Baisan rayuwa nawa zai lalata kafin ya gyara tashi da ta lalace ba.
“Me kikeso inyi? Bazan iya aurenki ba kiyi haƙuri.”
Hawaye ne suka zubo mata.
“Ban tsammaci hakan ba nima. Matsayinmu ba ɗaya bane ba. Na zo ne saboda banda halin kuɗin da zan zubda cikin.”
Jikinshi babu ƙwari ya koma wajen motar shi ya buɗe, gaba ɗaya kuɗin da ya zuba da bai san yawansu ba ya kwaso. Yasan ko dubu nawane ba zasu taɓa gyara ɓarnar da yayi ba.
Komawa yayi inda yarinyar take tsaye, sai yanzun yake kallonta sosai,yake ganin talauci da halin rayuwar daya sata yin abinda tayi.
“Allah ka yafe min.”
Ya faɗi yana jin tsanar kanshi. Kuɗin ya miƙa mata.
“Ki yi haƙuri. In kina son wani abu, ko wasu kuɗi ki zo.”
Girgiza mishi kai tayi, hawaye na zubo mata.
“Wannan ma kan dole zan karɓa . Haka kuke, masu kuɗi da yaransu, babu wanda zai taɓa taimaka maka don Allah, a ranar in da kuɗi na roƙeka ba zaka bani ba.
Saina baka abinda yafi komai daraja a tare da ni. Na koma gida kuɗin basu min amfanin komai ba. Ƙanina za aima tiyata na koma ya rasu. Hanyoyin Allah yawa gare su, inka kuskure saiya kama ka inhar baka tuba ba.
Bana son sake ganinka a rayuwata, saɓo mai girma na aikata tare da kai, zan kuma sake aikata mafi girma da hannunka a ciki. Ina fatan za ka ji abinda na ji wata rana El-Maska.”
Ta ƙarasa tana saka hannu ta goge fuskarta. Kallonta yake har ta tafi. Kalamanta na mishi yawo, suna taɓashi. Girman maganarta na zauna mishi.
Zuciyarshi ce tai wani irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjinshi. Girgiza kai yake yi.
“Allah karka ɗora min. Allah ka kare min zainab. Allah ka yafe min…..”
Addu’ar da yake kenan, har ya koma motarshi ya ja ta zuwa gida. Saboda ba abinda yake so illa ya ga lafiyar ƙanwarshi. Babu wanda zai taɓa mishi Zainab.
*
Baccin da ta yi da wuri ne yasa ta tashi da wuri, tunda tai sallah ta koma ta kwanta. Wanka ta shiga ta fito, kwalliya ta gama. Zaka rantse da Allah wani gagarumin biki zata je.
Doguwar riga ta saka ma jikinta cikin wanda Mummy takan ɗauko daga Dubai, ta ɗaura ɗankwali akanta, ta yi kyau sosai. Sallama ta ji anayi.
Ta daƙuna fuskarta jin an ci gaba, kuma babu wanda ya amsa. Ko ina su Asad suka shiga oho. Fitowa tayi daga ɗakin fuskarta ɗauke da scowl saboda ba ƙaramin shiga rayuwarta koma waye yayi ba.
Idanuwanta ta sauke kan kyakkyawar fuskarshi, kafin su soma yawatawa kan kayan da ke jikinshi da suke kira designers.
“Wa’alaikumus Salam. Hi.”
Ta faɗi tana sake daƙuna fuska saboda kyan da ta ga yai mata. Murmushi yayi da ta ji ya tsaya mata a rai.
“Shoot me now.”
Ta faɗi ƙasa-ƙasa.
“Magana kika yi?”
Girgiza mishi kai tayi.
“Ba da kai nake ba. Yaya Labeeb ɗin baya nan.”
Don ta ɗauka abokin Labeeb ne. Dariya yayi da sautin muryarshi da yai mata lulluɓi.
“Wai ba Zainab bace?”
“Yeah ni ce.”
“My God kin girma. When last na ganki, shekaranki biyar ne or more.”
Hararar shi tayi. In akwai abin tafi tsana bai wuce ka nuna kasan yarintarta ba.
“I like you kafin ka buɗe bakinka.”
Dariya ya sake yi.
“Anty Habiba bata nan?”
“Waye kai ɗin wai?”
Waje ya samu ya zauna don ya ga Zainab bata da niyyar bashi wajen zama.
“Ishaq…”
Maimaita sunanshi tayi. Ba mutane ta cika shiga ba ko a family ɗin Dady. Balle kuma na Mummy da suke ji da kansu.
“Zo ki zauna sai in faɗa miki ko ni waye.”
Ya faɗi yana zuba mata idanuwanshi. Akwai wani yanayi tattare da shi da yasa ta kasa yi mishi musu. Ƙarasawa tayi ta zauna kan hannun kujerar da yake.
“Kin girma sosai.”
“Another comment akan yadda kasan yarintata zaka tashi ka fita tunda wadda ka zo wajenta bata nan.”
Murmushi yayi yana daring ɗinta da idanuwanshi.
“Attitude, attitude ɗinki babu inda yaje tun yarinta.”
Dafe kai Zainab tayi, yanayin yadda yake magana kawai burgeta yake a lokaci ɗaya kuma yadda yake ji da kanshi na bata haushi.
“Na gama yanke hukunci ba kai min ba. Ko kaɗan.”
Ɗaga girarshi yayi.
“Zamu gani.”
Dai dai sallamar Labeeb. Idanuwa ya kafa musu, da ‘yar tazara tsakaninsu da Zainab. Amma idanuwanshi gani sukai jikinta na kusan gogar nashi.
“Ishaq”
“El-labeeb ko na ce El-Maska.”
Zainab Labeeb ya kalla.
“To your room.”
Wani ja fuskarta tayi. Ta buɗe baki tana kallon Labeeb da mamaki.
“Really? Yaya mana.”
Ta faɗi tana son ya ga yanda ya gama yaga mata a gaban ishaq. Sai ka ce wata yarinya ‘yar shekara biyu.
“Now! Bana so in sake maimaitawa.”
“This is so embarrassing!”
Ta faɗi tana miƙewa tai ɗakinta. Inda ta tashi Labeeb ya zauna.
“Ban yarda da yaron London kusa da ƙanwata ba.”
Sosai Ishaq yake dariya.
“Anty fa?”
“Bata nan. Ya gida, ya kowa?”
“All good. Sauri nake, na bi tanan ne nace bari in shigo mu gaisa.”
“Ka kyauta, tun yaushe aka ce ka dawo. Last month, ka zo da wuri gaskiya.”
Kallon shi Ishaq yayi.
“Ni na zo ai El-labeeb. Na taɓa ganinka a gidanmu kuwa? Oh yeah a TV in an saka fim ɗinka.”
“Fine. Ka kawo point, zan zo in sha Allah.”
Miƙewa Ishaq yayi. Ya jinjina mishi kai kawai ya fice. Labeeb ya sauke ajiyar zuciya. Ɗan wan Mummy ne amma in za a yanka Labeeb ba zaice ga su nawa bane a gidansu.
Balle sunayensu. Abu ɗaya ya sani, suna da kuɗi kamar sauran ‘yan uwan Mummy. Kuma duk ƙasar waje suke karatun su. Ishaq ya gama amma baisan me ya karanta ba.
Miƙewa yayi yana gyara numfashi ya nufi ɗakin Zainab don yasan ya gama ƙuleta. Yana tura ƙofa ta juya kanta tare da fadine,
“In ka ce ba ka yarda da guys around me ba one more time amai zanyi. Ka tafi kawai Yaya.
Ka ƙyale ni.”
Sauke numfashi yayi yana kallonta. Ba zai taɓa yarda da maza a kusa da ita ba. Saboda duk wanda zai gani shi yake gani a fuskarshi.
“I love you.”
Ya faɗi muryarshi na fitowa a dakushe.
“Thanks. Kana nunawa sosai. Ka ja min ƙofar.”
Ja mata ƙofar yayi. Gara ta ji haushin shi da ya bari wani ɗan iska ya je kusa da ita.
******
Wannan karon Mamdud ya rasa me ya samu Labeeb, har suka je Bauchi suka gama aikin da za su yi acan party ko ɗaya Labeeb bai je ba.
Sai dai Mamdud ya je shi kadai. Shi kam baya cikin yanayin yin party. Gaba ɗaya yarinyar nan ta tsaya mishi a zuciya. Ba ita bace ta farko da ta fara zubda cikin shi ba.
Amma itace ta farko da alhakin ɓacinta yake gaba dayay akanshi. Sauran duk rabawa suke. Kuɗinshi suke so, shi kuma jikinsu yake so. Wannan karon ɓarnar da ya yi babbace.
Cikin ɗakinsu na Salama Hotel Mamdud ya shigo wajen ƙarfe uku na dare ya samu Labeeb yana haɗa kayansu cikin jaka, zama yai gefen gadon.
“Wai meke damunka ne? Baka da lafiya ne ko tsufa ne ya fara kamaka?”
Girgiza kai Labeeb yayi.
“Ka sama min lafiya Mamdud.”
“No, da gaske nake. Meke damunka? A waje muke fa, ina El-Maska? Nasan baka fitowa da El-labeeb.”
Jan numfashi Labeeb yayi, ya fitar da shi a hankali.
“Yarinyar nan ta tsayamun a rai Mamdud.”
“Mtsww shi ne me? Ita ce ta farko? Yara nawa ka zubda?”
Maganganun Mamdud ɗin sun ƙara saka shi jin ƙazanta da girman laifin da yake aikatawa. Laifin da baisan ta yadda zai yi ya bari ba.
“She is different. Ni ne na farkon ta.”
“No shit!”
Mamdud ya faɗi yana ware idanuwa. Kai Labeeb ya ɗaga mishi, yana tabbatar mishi da gaske ne abinda ya fada.
“Me yasa ba ka da kula ne? Ko yaushe sai kayi slipping?”
“Ta yaya zansan virgin ce? Ta yaya zan gane ba kamar sauran bace? Ya Rabb, na tsani kaina wallahi.”
Ɗan bubbuga mishi kafaɗa Mamdud yayi.
“Abinda ya faru ya faru. Just chill, ka daina ɗora ma kanka laifi, ita ta zo , ba dole kai mata ba.”
Kai labeeb ya ɗan ɗaga mishi, yasan ba zai fahimci yadda yake ji bane. Yanayin ta da komai zai jima bai mantu a wajen shi ba.
Maganganun da ta yi mishi sun tsaya mishi a rai ba kaɗan ba. Yana jin Mamdud yana ta kai kawo cikin ɗakin kafin ya shiga toilet. Zage zip ɗin jakarsu yayi ya hau kan gadon ya kwanta.
Har Mamdud ya gama wankan ya fito ya kwanta shima idanuwan Labeeb ko alamar bacci babu a cikinsu, wannan ne karo na farko da ya san wata damuwa banda ta family ɗinshi.
*****
Labeeb zai iya cewa a hankali a hankali, da duk ranar da zata wuce da yadda hoton yarinyar nan yake dishewa a zuciyarshi. Har ranar da ya wayi gari ya neme shi ya rasa.
Rayuwa ya ci gaba da yi abinshi kamar komai bai faru ba. Kamar yarinyar na ɗaya daga cikin abinda ya wuce a rayuwarshi da ba zai dawo ba balle kuma har ya gyaru.
Daga ɗakinshi ya fito ya kalli Asad dake kwance kan doguwar kujera, Anees kuma yana ƙasa ya jingina bayanshi da kujerar.
“Na fita, ku kira ni in kuna buƙatar wani abu.”
“A dawo lafiya.”
Suka faɗa a tare, ya ɗaga musu kai ya fice.
“Na rasa me zan saima sajda. Tun satin nan nake tunani, gobe ne ranar saukar su.”
Anees ya faɗi yana dafe kai.
Gyaran murya Asad yayi.
“How about ka faɗa mata kana sonta?”
Juyawa Anees yayi ya harare shi.
“Duka Sajdar nawa take? Kuma muna da sauran lokaci. I am fine da nuna mata ina sonta ba saina furta ba.”
“Bari wani ya ƙwace maka ita. Zaka ga ko nawa take.”
“Asad mana. Sai ka faɗa a bakin Mala’iku ka ja min ko?”
Dariya Asad yake mishi.
“Wasa nake. Amma da gaske ka faɗa mata ɗin zai fi. Kai kake kallon yarinya ce.”
“Shi yasa na ga ka faɗa ma zulfa…”
Bai ƙarasa ba zulfa ta fito ta katse shi da cewa,
“Menene za a faɗa min?”
Da sauri Asad ya miƙe yana faɗin,
“Ki ƙyale Anees, yayi shaye-shayen ruwanshi da lemuka ne kawai”
Dariya Zulfa tayi tana girgiza kai ta wuce kitchen. Asad ya bi ta da kallo, ba ko yaushe yake ganin fuskarta fresh haka babu kwalliya ba.
Sai ya ga ya fi son fuskarta a hakan, saboda yadda tai wani irin cool, sauke numfashi Asad yayi.
“Abinda nake cewa kenan.”
Gwiwar ƙafarshi Asad yasa ya harbi Anees a baya.
“Surutunka na tasowa ne sa’adda babu mai buƙatarshi.”
Dariya Anees yayi.
“Zaka tayani tunanin me zan siyan ma sajda ko kuwa ka fi son ayi maganar….”
Ya ƙarasa yana nuna hanyar kitchen, hararar shi Asad yayi. Baisan tun lokacin da ya fara son Zulfa ba. Sai dai zai ce ya wayi gari ne ya ganta riƙe da hannun Labeeb ya ji kamar an zuba mishi wuta a ƙirjinshi.
Lokacin ya gane zuciyarshi ta samu matsala sosai. Labeeb shi ne abinda ya hanashi tunkarar Zulfa. Zai iya haƙura da rayuwa gaba ɗaya don farin cikin Labeeb.
Shi yasa ya danne abin. Baisan yadda akai Anees ya gane ba. Hakan yasa ya faɗa mishi komai. Anees yaso ya faɗa ma Labeeb, amma ya ƙi . Don yasan yana furta wata kalma akan Zulfa Labeeb zai haƙura.
Baisan ya zai ɗauki hakan ba, musamman ita zulfan da yake kula da kallon da take ma Labeeb ɗin. Ba zai shiga tsakanin farin cikin mutane biyu da yake matukar ƙauna ba don nashi.
Yana jin ciwo da kishi duk in ya gansu tare da ko Anees bai sani ba. Don yanzun sun mayar da abin kamar wasa. Anees kan tsokane shi da cewar bai san so ba, baisan infatuation ba.
Fitowar Zulfa ya katse ma Asad tunanin da yake yi, idanuwanta ta sauke cikin nashi, zai iya rantsewa yana jin yadda zuciyarshi ta tsaya waje ɗaya.
“Yaya fa?”
Ta buƙata, sai da ya haɗiye abinda ya ji ya taso mishi tukunna ya amsa ta da.
“Yanzun ya fita.”
“Ohhhh my Goodness…Magana zanyi da shi kuma.”
Ta faɗi tana shagwaɓe fuska daya bayyana murmushi a fuskar Asad.
“Ƙila bazai jima ba.”
Kai kawai ta ɗaga ma Asad ta wuce ɗakinta. Gyaran murya Anees yayi. Asad ya kalleshi yana juya idanuwanshi.
“Ka tuna Ikram? Lokacin da muke SS1?”
Hannu Anees yasa yana rufe fuskarshi.
“I hate you.”
Ya faɗi, sosai Asad yake mishi dariya. Ikram ta wuce su da shekara ɗaya, ita ce yarinyar farko da Anees ke crushing akanta. Har ta window yake leƙawa in ta zo wucewa.
Lokuta irin haka da Asaad ke son ɓoye mishi damuwarshi ko kuma yake son gujema magana akan Zulfa sai ya faɗi sunanta.
Ita kam Zulfa anata ɓangaren tana shiga ɗakinta kwanciya tai, bacci ya ɗauketa, bata tashi ba sai bayan Azahar, banɗaki ta shiga tai alwala ta soma yin sallah kafin nan ta koma ta yo wanka.
Yunwa take ji cikinta har ƙara yake mata, don haka ta je kitchen ta zuba abinci, a nan ta ci shi a tsaye da murmushi a fuskarta, ɗabi’arta ne.
Ummi kanyi faɗa sosai tun lokacin. Murmushin da takan yi tayi yanzun tana jeroma Ummi addu’o’in samun Rahma a zuciyarta kafin ta koma ɗaki ta shirya kanta cikin riga da skirt na material.
Sosai tayi kyau. Mayafi zata ɗauko ta ga wani hijab milk kalar kayanta da Sajda ta ɗinka musu, murmushi ta yi ta fito da hijabin don ta tuna yadda ta gwale Sajda cewar itama ta zama matar liman ne da zata dinga yawo da hijab.
Sake ɗaurin ɗankwalinta tayi ta sanya hijabin da laushinsa ya burgeta. Wani irin kyau ta ga tayi fiye da inda mayafi ta saka, turarukan da Labeeb kan bata kyauta ta feshe jikinta da su.
Ta saka takalma ta ɗauki wayar daya bata gift ta saka a purse ɗin da zata fita dashi. Bata samu kowa a falo ba don haka ta fice kawai.
Gida zata je ko sajda na buƙatarta, wanda ba ko da yaushe bane tunda Mami na kusa. Wayar Labeeb ta kira bata shiga don haka ta yanke shawarar ta biya ta gidanshi.
Yace mata zasu fita amma bata san ko ƙarfe nawa ba koma ina zasuje ɗin.
*
Sam bai ji ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ba, don daga shi har yarinyar dake manne a jikinshi Shaiɗan na kaɗa musu ganga sunyi nisa sosai cikin duniyar saɓon da suke yi.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…!”
Da Zulfa ta faɗi ne ya daki kunnenshi, ta wuyan yarinyar dake jikinshi ya zuro kai, ya ware idanuwanshi ganin Zulfa da ke tsaye ta runtse idanuwanta tana karanto Innalillahi.
A karo na farko a rayuwarshi da asalin dana sani yake shigarshi, ba don Zulfa bata san abinda yake aikatawa ba. Sai don bai taɓa kawowa a ranshi zata kamashi dumu-dumu ba.
Ture yarinyar yayi gefe, ammanl yanayin da yake yasa ya kasa tashi, da baya baya zulfa ke tafiya, idanuwanta a rufe kafin ta juya, rawar da hannuwanta suke yi ne yasa buɗe ƙofar ke mata wahala.
“Zulfa! Zulfa!!”
Ko juyowa bata yi ba. Tana ficewa daga ɗakin ya ga ta ja ƙofar ya diro daga kan kujerar ya ɗauki kayanshi da ke watse a ƙasa, dogon wandon kawai ya saka da singlet, rigarshi a hannu ko takalmi bai saka ma ƙafarshi ba ya bita.
Tana zaune a ƙofar gidan, fuskarta cikin hannayenta, ƙarasawa yayi ya zauna a gefenta, abinda bata taɓa yi ba tayi. Matsawa ta ƙara yi.
Da sauri sauri take fitar da numfashi don ƙirjinta da ya matse, zuciyarta na dunƙulewa waje ɗaya da wani irin ciwo da har mamakinshi take yi.
Cikin kanta da zuciyarta ta ga abinda tasan har ta mutu ba zai taɓa goguwa ba. Yau ta tabbatar da abinda take ji akan Labeeb bai tsaya ƙaunar ‘yan uwantaka ba.
Yau ta raina kanta da ta ganshi manne da wata, ji take kamar zuciyarta zata iya fashewa a kowanne lokaci. Muryarshi ɗauke da wani irin yanayi ya ce,
“Zulfa…”
Buɗe fuskarta tayi, ta juyo tana sauke masa idanuwanta da suka sake launi cikin tashi fuskar.
“Me zaka faɗa min wanda ban gani ba? Me za ka ce min wanda ban sani ba? Ba zaka taɓ canza halayyar ka ba. Ban isa in roƙi alfarma a wajenka ba Yaya.”
Girgiza mata kai yake yi yana jin yadda ƙirjinshi ke zafi, inda tasan matsayinta daban yake a wajenshi da bata ce haka ba. Yadda yake ji a yanzun tunda aka haife shi bai taɓa sanin kalar emotion irinshi ba.
Hannuwanta ya kamo, ta soma ƙoƙarin ƙwacewa amman ya riƙe dam. Idanuwanshi ya saka cikin nata yana tsanar hawayen da ke taruwa a cikin su. Yana tsanar shi ne sanadin abinda ke cikin idanuwanta.
“Ina son in canza, ina son in canza kar su Asad su ga halayyata da basu santa ba kamar yadda kike gani.
Bansan yadda zan yi ba. Banda abinda zan dafa in miƙe daga dannewar da ɗabi’una marasa kyau Sukai min. Karki tsane ni zulfa, don Allah karki tsane ni.”
Girgiza mishi kai take yi hawayen da suka taru suna zubo mata, bata san yadda zata tsane shi ba, ko da koya mata ake kullum zuciyarta ba zata fahimta ba.
Akwai inda yakai a cikinta da ita da kanta sai yau ta fahimta balle shi da bai sani ba. Kanta ta ɗora kan ƙafafuwanshi hawaye masu zafin gaske na zubo mata.
Lumshe idanuwanshi Labeeb yayi, kukanta na ƙara mishi zafin abinda yake ji. Mata kawai zulfa tasan yana bi. Yana jin daɗi da bata taɓa samunshi a daidan shi ba.
Akwai abinda baya son har mutuwarshi ta sani. Ba don tsoron karta tsane shi ba, sai din tsoron cutar da ita, abinda ya ji ya mishi tsaye a wuyanshi yake ta ƙoƙarin hadiyewa ya kasa.
Daƙyar ya iya samu ya ce mata,
“Yazan fixing yau? Me zanyi?”
Ɗagowa tayi daga jikinshi. Sosai take kallonshi, son da take mishi ya girmi komai a wajenta. Cikin muryar da bata gane tata bace ta ce,
“Kayi aure…”
Magana zaiyi tasa yatsun hannuwanta tana rufe mishi baki tare da girgiza mishi kai.
“In har ina da wani muhimmanci a wajenka. In har zan iya roƙar alfarma kai aure Yaya…”
Ta ƙarasa wasu sabbin hawaye na zubo mata da yanayin da zuciyarta ke ciki. Hannunta ya kama ya sauke.
“Zulfa…”
Ya kasa ƙarasawa don a tsarin rayuwarshi nan da wasu shekaru biyar ma bai hango kanshi da aure ba. Bazai iya ma yaranshi abinda Mummy da Dady sukai mishi ba.
Ya fi son ya ƙara tara kuɗi, ya samu yarinyar da zai so. Yarinyar da zata iya kwantar mishi da El-Maska. Yana jin zulfa ta zare hannuwanta daga nashi ta miƙe.
“Zulfa!”
Ya kira cike da wani irin yanayi. Girgiza mishi kai tayi tana ɗaga mishi hannu alamar ya ƙyaleta. Da sauri ta nufi titi ta tare mashin ta hau.
Miƙewa Labeeb yayi ya koma cikin gida, bai kula yarinyar da ke kwance tana mishi magana ba, kanshi tsaye kitchen ya wuce.
Kofi ya ɗauka, ya buɗe cabinet ɗin da yasan suna ajiye kwalaben giyoyinsu, zubawa yayi cikin kofin ya ɗura ma cikinshi ya ƙara cikawa ya shanye.
Ya jingina bayanshi da bangon kitchen ɗin ya lumshe idanuwanshi yana karɓar yanayin da giyar da ya sha yake samar mishi, fita yayi daga kitchen ɗin, ya ƙarasa ya kama hannun yarinyar yana janta bedroom.
Allah ya yafe mana baki daya, kuma ya jikan iyayen mu duka.