Hidimar su suka ci gaba da yi da Mamdud kamar komai bai faru ba. Sai dai su duka babu wanda ya sake zuwa wajen wani partyn.
Daga wajen aiki hotel ɗinsu suke yi, kwanan Mamdud huɗu ya juya abinshi don ya ce ma Labeeb yana da test dama. Don haka shi kaɗai ya ƙarasa kwanakin shi.
Wanda duk yadda kewar Zulfa ke ci mishi rai baisa ko ɗaya ya ɗaga wayarta ba balle ya amsa saƙonninta da ke shigo mishi babu adadi a rana.
Suma yakan karanta su rage mishi damuwarta. Ranar Zafira tai. . .