Tuna Baya (Rayuwar Dawud)
Da zai iya ɗora kalmar ‘Perfect’ zai kira ahalin shi da haka. Tun tasowarshi bai san wani tashin hankali ba balle ɓacin rai.
Ba masu kuɗi bane su. Sai dai suna da rufin asiri dai dai gwargwado. Don babu abinda suka nema suka rasa ta ɓangaren abinci, sutura da makaranta me kyau dai dai ƙarfin Abbansu.
Yakan yi mamaki in ya ji an ce mata da miji na faɗa. Don bai taɓa gani a nasu gidan ba. Maman shi Aisha da suke kira da Ummi mata ce mai hakuri da kauda kai a al’amura.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu da sauyi na ci gaba har lokacin da Dawud ya shiga aji biyar Secondary. Ba zai manta ranar talatar da ta zo musu a hargitse ba. Talatar da tai ɗigo a rayuwar su da yai sanadin canza musu komai. Kamar yadda ya saba.
Da sallama ya shiga gidan nasu yana ɗorawa da,
“Sajda….”
Bai ji motsinta ba. Takalman shi ya cire ya ajiye gefe. Ya taka zuwa cikin folonsu. Ummi ya samu zaune da alama ko shigowar shi bata ji ba saboda zurfin da ta yi cikin tunani. Jakar makarantar shi ya ajiye ya zauna gefenta. Hawaye ne a fuskarta abinda bai taɓa gani ba. A tsorace ya dafa hannunta yana faɗin,
“Ummi?”
Sai lokacin ta ji shi. Hannu ta sa da sauri tana goge fuskarta. Kafin ta ɗora murmushi a fuskar ta kalle shi sa cewa,
“Dawud. Har an dawo. Ya makarantar?”
Sam bai yarda da murmushin ta ba. Yasan akwai matsala.
“Ummi me yake faruwa ne?”
Girgiza mishi kai ta yi.
“Ka je kitchen ka ɗauki abincin ka.”
Gyara zama yayi. Yunwar da ya shigo da ita ta ɗauke gaba ɗaya. In akwai abinda ya tsana a zuciyarshi bai wuce ganin Ummi cikin damuwa ba.
Muryar shi da rauni a cikinta ya ce,
“Ummi ki faɗa min ko menene. Bazan iya cin abincin nan ba bayan na san da damuwa a tattare da ke.”
Wani numfashi ya ga ta ja tana fitar da shi. Kafin ta ce,
“Na faɗa maka za a rage ma’aikata a kamfanin Abbanku ai ko?”
Kai ya ɗaga mata. Ya tuna amma sam abin bai dame shi ba. Don bai kawo ma ranshi zai shafe su ba. Abba na komai babu ha’inci a cikinshi.
“To har da shi aka sallama a cikin su. Tun jiya abin ya faru. Ban faɗa maka bane saboda muna tunanin wasu cikin manyan wajen da suke mutunci za su taimaka mishi.
Sai dai mutane basu da tabbas Dawud. Sun yi kamar basu ma taɓa haɗa hanya da shi ba….”
Ta ƙarasa hawaye na zubo mata. Ta kai hannu ta goge su. Shiru Dawud yayi yana tauna maganganunta da jinjina ma’anarsu a wajen su.
Komai yake hangowa. Hakan na nufin komai zai canza musu. Makarantar su. Lokaci ɗaya ya ji komai baya mishi daɗi.
Dafa kafaɗarshi Ummi ta yi.
“Ka ga abinda yasa ban faɗa maka ba ko? Bana son ka ce za ka ɗora ma kanka damuwa. Addu’a za mu ci gaba da yi.
Allah kaɗai yasan abinda ya ɓoye mana a wannan jarabawar da yai mana. Ka tashi ka je ka ɗauko abincin ka.”
Hannuwanshi ya ɗora kan kujerar da yake jingine da ita ta baya. Yunwar ta riga da ta ɗauke kuma. Sai dai ya ci abincin haka nan.
“Zan ci Ummi. Sai ma na watsa ruwa tukunna. Bana jin yunwa. Ina su sajda? Gidan yayi shiru da yawa.”
Wannan karon murmushin ta har zuciya yakai. Tana jin daɗin ganin ƙaunar da ke tsakanin ‘ya’yanta. Dawud na son su sosai. Sai dai kowa zai kula shaƙuwarsu da Sajda mai girma ce.
Da murmushi a fuskarta har lokacin ta ce mishi,
“Sunje gidan su Labeeb.”
Ba don baya son zuwan su can ɗin ba ya ce,
“Islamiyar fa Ummi? Ai da sun bari sai ranar Alhamis in Allah ya kai mu.”
Miƙewa Ummi ta yi tana ‘yar dariya.
“Na haɗa musu da uniform ɗinsu. Daga can za a sauke su Islamiyya. In sun taso su yo gida.”
Murmushi yayi kawai. Har Ummi ta fice daga ɗakin sannan ya miƙe shi ma. Ɗakin shi ya wuce ya cire uniform ya watsa ruwa. Alwala yayi don lokacin sallar Asr ya gabato ya fito. A kitchen ya samu Ummi tana ɗora abincin dare.
“Sannu da aiki Ummi. Me zan taya ki da?”
Amsawa tayi da,
“Yawwa. Ba komai. Ka je hidimar ka. “
Girgiza mata kai yayi. Ba shi da wata hidima da ta wuce taya Ummin shi aiki. Koda na kitchen ne kuwa. Sai dai in baya gidan take abinta. Indai yana nan tare suke komai. Girgiza mata kai yayi.
“Banda wata hidima Ummi. Don Allah ki kawo in taya ki wani abun.”
Ta san Dawud ba tafiya zai yi ba. Don haka ta bashi albasa da magi ta ce ya ɓare mata. Hira suke abinsu suna aiki tare da zai burgeka. Daga nesa in kana kallon su za ka ga tsantsar ƙaunar da ke tsakanin Dawud da mahaifiyarshi.
****
Bayan Wata Ɗaya.
Abubuwa sun fara canza musu a kwanaki talatin bayan korar mahaifin Dawud daga aiki.
Idan Auwal mahaifinsu ya ce yana tara wani abu ƙarya yake. Don albashin shi ba wani mai yawa bane ba. Ga iyali. Su ne ake amfani da su koyaushe.
Sai kaɗan da yake warewa saboda tsaron lalura ko rashin lafiya. Yanzun kuma da baya saka ran samun wasu kuɗin a wata na gaba sune yake ta amfani da su.
Banda Dawud da Tayyab cikin yaran babu mai hankalin fahimtar wani abu ya canza musu. Zaune Auwal yake a falo da matarshi suna tattauna halin da suka tsinci kansu a ciki.
“Wai tun yanzun kenan. Diploma ta fara zama bakomai ba ina ga nan gaba.”
Jinjina kai Aisha ta yi.
“Abin nan har mamaki yake bani wallahi. Ba fa ku kaɗai bane Abban Sajda. Samun aiki yanzun mai degree ɗin ma sai yana da hanya.”
“Hmm hakane. Amma su Alhaji Abdulhadi sun bani mamaki. In kin ga yadda ya ɓata rai dana shiga office ɗinshi. Da ƙyar ya amsa gaisuwa ta.”
Girgiza kai Aisha ta yi.
“Ka bar mutane. Inda Aljannah a hannun su take da an sha wahala. Allah ba zai hana mu yadda za mu yi ba.”
Gyara zama ya sake yi sannan ya ce,
“Hakane kam. Amma ina jin takaicin a koro min yaran nan kuɗin makaranta. Bana son zuwa ma su Yaya da koke na.
Suna yin iya yinsu. Tun da suka ji abin nan. Kina gani dai.”
Maganarshi gaskiya ce. Yayan shi na ji duk da baya gari haka ya aiko mishi da kuɗi. Duk sati kuma yakan aiko mishi da su.
Haruna ƙaninshi ma duk da ta san halin matarshi ba kirki gareta ba. Ya kawo musu taliya kwali biyu harda cous-cous da cefane mai yawa sau biyu.
Abinda take ta tunanin yi jiya take juyawa a ranta kafin ta ce,
“Abban Sajda da za ka yarda. Tunda takarduna suna ajiye tun aurenmu. Da na ɗauko su na gwada neman aiki.”
Ware idanuwa yayi. Tana karantar rashin amincewar shi tun kafin ya furta.
“Aiki? Gaskiya abin bai zauna min ba. Kina ganin ina ta fama nima da nake namiji inaga ke kuma?”
Murmushi ta yi mishi ta ce,
“Ka ga ni NCE ne. Ba wani aiki bane mai wahalar samu. Koyarwa ce. Ka barni Abban Sajda in gwada ko makarantun kusa da mu ɗin nan ne.
In na samu nima ai na dinga taimakawa. In kuma ka riga ni samun aiki shikenan.”
Sauke numfashi mai nauyi yayi. In dai zata samu aikin kamar yadda ta faɗa zai taimaka musu ta wani fannin. Suna buƙatar kuɗin sosai.
“Shikenan. Allah yai mana jagora.”
Da farin ciki ta ce,
“Hakan na nufin ka amince kenan?”
Kai ya ɗaga mata yana murmushi. Da sauri ta tashi ta ƙarasa kujerar da yake zaune ta zagaya hannuwanta tana mai rungume shi.
“Na gode sosai. In sha Allah komai zai zo mana da sauƙi.”
Hannuwanta ya kama ya ɗago da ita. A wasance ya ce,
“Sai yara sun shigo? Baki san mun girmi wannan abubuwan ba.”
Ɗan haɗe fuska ta yi.
“Shekaru basa hana ƙauna in dai akan gaskiya aka gina ta.”
Hannu yakai ya kama nata cikin nashi.
“Wasa nake. Ina ƙaunarki Aisha. Aurenki babban rabo ne da bazan taɓa da na sani da shi ba.
Ke mace ce da kowane namiji zai so samun irinta.”
Sadda kanta ƙasa ta yi tana murmushi. Hakan ya bashi dariya sosai. Shekarun su sha takwasa kenan da aure. Ko Dawud shekararshi shi shida amma yakan yi mamakin yadda Aisha bata daina jin kunyar shi ba.
Ita kam ta dabance ko a cikin mata. Yana son komai nata. Haƙurinta da kauda kanta. A shekarun nan bai taɓa ganin ɓacin ranta ba. Yasan kuma ba don baya mata laifuka ba. Ita mace ce da bata son tashin hankali. Ko ita ce da gaskiya takan bashi haƙuri don a zauna lafiya. Darajarta a idanuwanshi ba zata misaltu ba.
****
Kamar yadda Auwal ya bar Aisha ta nemi aiki. Haka ta fita makarantun da ke kusa da unguwarsu ta nan Kabalan Doki da ma ƙetarenta neman aiki.
Sati ɗaya tsakani ta samu a nan wata private da ke kusa da su. Don tafiyar bata wuce mintina sha biyar ba. Ko abin hawa bata buƙata. Duk da aji ɗaya zuwa uku suka bata. Zata dinga koyar da Islamic Studies, Social Studies da Hausa. Hakan yasa suka ƙara mata albashi tunda ayyukan da yawa kuma da alamun da ta nuna musu na zata jima.
Ranar da farin ciki ta wuni. Dubu ashirin ba kuɗi bane masu yawan gaske. Amma a halin da suke ciki za su canza musu abubuwa da yawa. Kuma daga ita har Auwal sun ji daɗi. Sun kuma gode ma Allah. Koda ya jarabce su. Ta wasu fannin da suka lura yana sama musu mafita a hankali a hankali.
****
Kasancewar ranar Lahadi ce. Zaune suke a falo su dukkansu bayan sallar Isha’i suna hira.
Dawud na zaune kan kafet da litattafai a gabanshi yana assignment. Tayyab da Zulfa hankalinsu na kan T.V suna kallon wani Indian film.
Sajda kam na maƙale kusa da Dawud. Hannu ta sa ta ɗauki littafi ɗaya ya ƙwace yana faɗin,
“Kin kusan tashi ki bar wajen nan tunda hannunki baya zama waje ɗaya.”
Turo baki ta yi.
“Karantawa zan yi.”
Harararta ya yi. Ko a jikinta, sai ma ƙara matsawa da ta yi ta kwantar da kanta a jikin hannun shi.
“Sajda tashi ki ban waje.”
Maƙale kafaɗa ta yi. A tsawace ya ce,
“Ki tashi ko!”
Da gudu ta miƙe tana komawa wajen Abbansu. Kuka ta sa.
“Dawud ka sa min yarinya kuka ko?”
Ɗagowa yayi.
“Abba bata ji. Bansan me zata karanta a chemistry ba. Zata daƙuna min littafi ne kawai.”
Kallonshi Abba yayi.
“Iyye. Ka raina min yarinya ko. Sajda karɓo littafin mu bashi mamaki.”
Goge fuskarta ta yi tai tsaye tana kallon Dawud ɗin. Tsoron zuwa kusa da shi take. Ummi da ke gefe kallonsu kawai take yi.
Bamai yawan magana bace ita. Sai su kusan tayar da gidan da hayaniya ba ka ji muryarta ba. Littafin Dawud ya ɗauka ya miƙa mata. Sannan ta ƙarasa ta karɓa. Tsoronshin da yake gani a fuskarta ne baya so. A hankali yadda ita kaɗai zata ji ya ce,
“Sorry.”
Murmushi ta yi tana jin daɗi. Kafin ta juya wajen abbansu da littafin. Shima murmushin yayi yana maida hankalinshi kan calculations ɗin da yake.
Kan cinyar Abban su ta zauna. Ta buɗe littafin. Sajda akwai tambaya. Tun tana tambayarshi abinda bata iya karantawa yana faɗa mata har ta soma tambayarshi abinda shi kanshi baya ganewa.
Don ɗan Accounting ne. Wannan kuma tarkacen ‘yan science ne.
“Dawud meye wannan kam?”
Abba ya tambaya yana ɗaga ma dawud littafin. Ɗago kai yayi ya kalla. Da murmushi ya ce,
“Abba ya haka kuma. Ku da za ku bani mamaki kai da ‘yarka.”
Ummi da ke zaune dariya ta kufce mata. Hararrta Abba yayi yana sake gyarama Sajda zama a cinyarshi.
“Ke rabu da su. Yanar gizo ce mai ‘ya’ya….”
Dariya Dawud yake yi sosai. Shi kanshi Abba abin dariya ya bashi.
“Yanar gizo fa Abba…..”
Dawud ya faɗi yana dariya.
“Organic Chemistry ne.”
Da murmushi Abba ya ce,
“Oho dai. Mu abinda muka gani kenan ko Sajda.”
Kai ta ɗaga mishi tana faɗin,
“Kuma wallahi Abba abin yai kama da yanar gizo ɗin. Irin ta cikin cartoon.”
Dariya Dawud ya sake yi yana maida hankalinshi kan aikin da yake yi. Indai ta Sajda da Abba ne zai kwana bai gama aikin shi ba.
“Yawwa my daughter. Maza ku tashi a je a kwanta. Akwai makaranta gobe in Allah ya kai mu.”
Sai lokacin Zulfa da Tayyab suka kalli Abba. Zulfa ta soma cewa.
“Wayyo Abba. Faɗan ƙarshe za ayi wallahi.”
Kallonta ya yi.
“Au ashe kuna jinmu kuka yi shiru. To tashi za ku yi ku kwanta goma saura.”
“Abba da an kashe boss ɗin nan zamu tashi.”
Cewar Tayyab. Girgiza kai Abba ya yi.
“Ku riƙe sunan fim ɗin. Na siyo muku. Amma kwanciya za ku yi. Balle ma kai Tayyab da sai ai maka tashi goma kana komawa.”
Miƙewa suka yi su dukkansu banda Dawud. Ummi ta kalle su ta ce,
“Ku yi brush dai. Ku yi addu’a Zulfa ki yi ma Sajda ita ma.”
“Ummi na iya fa.”
Sajda ta faɗi cike da rigima.
“Na sani ai Sajda. Zata ƙara yi miki ne.”
Kai Sajda ta ɗaga su duka suna musu sai da safe. Zulfa ta kama hannun Sajda ɗin suna nufar ɗakin su.
Abba ya ɗora da faɗin,
“Ku yi min addu’a zan je wata interview gobe in Allah ya kai mu.”
“Allah Ya bada sa’a Abba. Allah Ya tabbatar da alkhairi.”
Tayyab ya fadie yana ɗorawa da,
“Saida safenku.”
Suma su Sajda ɗin addu’a suka yi mishi. Da gudu Sajda ta rugo ta ruƙunƙume wuyan Dawud.
“Yaya saida safe.”
Kai ya iya ɗaga mata, yadda ta shaƙe mishi wuya ba zai iya magana ba. Sannan ta sake shi ta ruga suka wuce ɗakinsu. Murza wuyanshi yayi da hannu sannan ya tattara litattafan shi.
“Ummi…. Abba…. Saida safenku. Allah Ya bada sa’a Ya tabbatar da alkhairi.”
Su duka suka amsa da amin. Ummi na ɗorawa da,
“Karka manta da Addu’a dai.”
Da murmushi ya ce,
“Ummi kamar su Sajda dai.”
Ta kalli Abba ta ce,
“Ka ji min yaron nan. Wai shi ya girma. Duka yaushe na daina yi maka addu’ar?”
Dariya Dawud yayi.
“Har yanzun ma ina buƙata Ummi. Addu’arki sabuwa ce a kullum.”
Abba ya ce,
“Dawud iya zaro zance a wajenka sai kace Labeeb.”
Dariya Dawud yayi.
“Shi acting yake. Ni kuma nawa daga zuciyata ne ko Ummi?”
Kai Ummi ta ɗaga mishi sannan ya sake musu sallama ya wuce ɗakinshi. Abba ya kalli Ummi.
“Yaron nan ke ya biyo. Kominshi irin naki ne.”
“Ba komai ba dai. Kamanninka ne sak. Kamar an tsaga kara. Kuma surutun ma naka ne.”
Pillow ɗin da ke gefenshi ya ɗauka ya jefa mata.
“Wato surutu ne da ni ko?”
Dariya take yi ta miƙe tana ƙarasa ta kama hannunshi tana taya shi miƙewa.
Hannunshi ya zagaya ya riƙo kafaɗarta suka wuce ɗakin su tare.
**
Yana kan mashin ɗinshi a hanyar zuwa kamfanin zuciyarshi na dukan uku-uku. Yana buƙatar aikin nan.
Kuɗin da Aisha zata ɗauka ba zai isa a biya ma Dawud kuɗin jarabawar shi ta aji shida ba. Yasan nan da watanni kaɗan za a buƙace su.
Komai ya sake tsinke mishi lokacin da ya shiga wajen ya ga jerin mutanen da ke neman aiki. Yasan samun shi sai wani rabo daga Allah.
Sallama yai musu da ba kowa bane ya amsa. Shi dai a addinance ya fita haƙƙinsu. Don amsa sallamar ce aka wajabta.
Waje ya samu a layin ƙarshe. Addu’o’i yake. Yana gaya wa Allah buƙatunshi duk da ya san su. Suna nan zaune ba akai ga kiransu ba wata Hajiya ta zo ta wuce.
A shekaru zai iya cewa ta girmi Aishar shi. Saboda yanayinta. Ta jima a ciki kafin ta fito. Idanuwanta ta tsayar a kansu ta ƙare musu kallo.
Kallon ne Auwal ya ji yayi yawa. Ya ɗago kanshi. Suka haɗa idanuwa kuwa. Ganin bata da niyyar sauke nata ne yasa shi sauke nashi ƙasa.
A ranshi yana mamakin rashin kunya ta wasu matan. Bai sake ɗago kanshi ba. Saida yaji wani ya taba shi.
“Da ni kake?”
Ya buƙata yana ɗagowa ya kalli mutumin da ke Sanye da uniform da ba zai ce ko na menene ba.
“Ka sauka ƙasa ana kira.”
Da mamaki a fuskar shi ya ce,
“Ƙasa kuma? Waye yake kirana?”
Da alamar ƙosawa a muryar mutumin ya ce,
“Hajiya Beeba ke kiranka.”
Ba tare da musun komai ba Auwal ya kalli sauran mutanen da ke gabanshi sannan ya miƙe. Da mamaki bayyane a fuskar shi har ya sauka ƙasa.
Matar da ta gama ƙare musu kallo ce. Wani shu’umin murmushi ta yi mishi tare da faɗin,
“Bisimillah. Mu yi magana mana.”
Cike da shakku da rashin yarda yake kallonta. Da komai na zuciyarshi tana gaya mishi kar ya je. Ya juya ya koma sama zaifi mishi kwanciyar hankali.
Sai dai da gani ba ƙaramar mace bace ba. Kallo ɗaya za kai mata ka fahimci hakan. Wani yawu ya haɗiya kamar me koyon tafiya ya ƙarasa inda take tsaye jingine da mota.
Bai ce komai ba har lokacin. Takardun shi dai na riƙe a hannunshi.
“Aiki kake nema ne?”
Kai ya ɗan ɗaga mata. Ta faɗaɗa murmushinta.
“Mu ga takardun naka.”
Miƙa mata yayi. Har lokacin bai san me zai ce ba. Yana kallonta ta buɗe ta dudduba. Kafin ta janye jikinta daga motar da suke tsaye.
Hannu ta zira ta glass ɗin. Sa’adda ta ɗago wani ɗan kati ne a hannunta. Ta miƙa mishi da faɗin,
“Ka zo nan gobe in Allah ya kaimu. Misalin ƙarfe goma na safe. Zan baka aiki.”
Karɓar katin yayi ba tare da ya duba ba. Cikin idanuwa ya kalleta ya ce,
“Akwai mutane sun kai arba’in a saman can. Saboda me kika zaɓe ni ni kaɗai?”
Yana kallon mamakin da ya bayyana a fuskarta saboda jin tambayarshi.
“Kana buƙatar aiki ko baka buƙata?”
Ta tambaya a maimakon amsa tambayarshi. Da gaske ne yana buƙatar aiki fiye da zatonta. Amma hakan bashie bane zai sa yayi abinda zuciyarshi bata nutsu da shi ba. Hannu ya miƙa ya karɓi takardun shi da suke hannunta. Ba tare da ya ce mata komai ba ya juya ya hau sama abinshi.
***
Lokacin da ya dawo gida wajen ƙarfe sha biyu ne na rana. Aisha bata taso ba sai ƙarfe ɗaya. Wanka yayi ya fito.
Da kanshi ya shiga kitchen ya duba ya ga akwai miya da yawa. Kasancewar da wuta yasa shi haɗa electric.
Taliya ya ɗora ya taya Aisha kafin ta dawo. Ya fito ya dawo falo ya zauna. Yana juya maganar Hajiya Beeba a ranshi.
Ga aiki ya samu. Amma na me zuciyarshi zata kasa nutsuwa waje ɗaya. Da wannan tunanin Aisha ta dawo ta same shi.
Kallo ɗaya tai mishi ta karanci damuwar da take fuskarshi. Sai dai ƙyale shi ta yi. Sai da ta watsa ruwa tai sallah suna zaune suna cin abinci tukunna ta tambaya.
“Ya interview ɗin?”
Cokalin shi ya ajiye cikin plate ɗin ya kalle ta sosai.
“Alhamdulillah. Sai dai akwai mutane da dama….”
Jin yai shiru yasata fadin.
“Allah ya bada sa’a. Ba dai damuwar rashin yiwuwar samun aikin bace a ranka ko?
Na ga kayi wani iri ne.”
Girgiza mata kai yayi. Cikin nutsuwa yake faɗa mata abinda ya faru tsakaninsu da Hajiya Beeba da yadda zuciyarshi bata nutsu da ita ba.
Dariya Aisha ta kama yi mishi.
“Abban Sajda. Kamar wanda zata sace ka.”
Kallonta ya yi fuskarshi babu walwala.
“Yanayin matar ne bai min ba. Kamar irin tsofin karuwan nan. Baki ganta ba fa.”
Sosai Aisha ta kalle shi.
“Ba kyau fa. Ka sani kuma. Daga ganin yanayinta bai kamata ka yanke mata hukunci haka ba.
Ƙasan abinda Allah ya ɓoye. Kai da kanka ka ce kunkai ku arba’in amma kai kaɗai ta sa aka kira.
Tunda ka fara neman aikin nan muke maka addu’ar samun mai alkhairi. Baka san ko dama bace Allah ya baka. Karkai wasa da ita.
Ka je kawai goben in Allah ya kai mu.”
Nisawa yayi ya kalleta da murmushi ya ce,
“Allah yai miki albarka Aisha. Ina ƙaunarki. Bazan gaji da gode wa Allah da kyautar mata irin ki ba.”
A kunyace ta amsa da amin tana mayar mishi da murmushin.
“Zanje goben. Allah yasa hakan ne mafi alkhairi a garemu gaba ɗaya.”
Dariya Aisha ta yi.
“Amin amin. Ko kaifa. Na ɗauka ka daina tsoron mata ashe har yanzun.”
Ware idanuwa yayi.
“In ji wa ya ce miki tsoron mata nake?”
Dariya take.
“Nake jin in ban manta ba. Sai da abokanka suka dinga turo ka kana tirjewa kafin ka iya min magana.”
Dariya yayi yana tuna lokacin.
“Wannan daban. Kuma kwarjini kike mun shi yasa.”
“Ahaf. Maganata dai zata fito ne.”
Dariya suka yi su duka. Suka ci gaba da cin abinci suna hira cike da nishaɗi da ƙaunar juna.