Dukkansu a nan asibitin suka yi sallar Isha'i. Don Khateeb ma Dawud ya je ya ɗauko shi daga makaranta ya kawo shi nan asibitin. Har lokacin zulfa ba ta tashi ba.
Ko likita bai shigo ba Dawud kan duba ya ga komai stable. Hutu ne kawai take samu. Hira suke abinsu, don kallo ɗaya za ka yi musu kasan suna cikin nishaɗi da su kaɗai suka san ma'anar shi.
"Dare na yi Dawud. Ka je ka ɗauki Yumna ku tafi gidanku."
Cewar Mami tana kallon shi.
"Don har da ni za ka tafi. . .