Skip to content
Part 40 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Dukkansu a nan asibitin suka yi sallar Isha’i. Don Khateeb ma Dawud ya je ya ɗauko shi daga makaranta ya kawo shi nan asibitin. Har lokacin zulfa ba ta tashi ba. 

Ko likita bai shigo ba Dawud kan duba ya ga komai stable. Hutu ne kawai take samu. Hira suke abinsu, don kallo ɗaya za ka yi musu kasan suna cikin nishaɗi da su kaɗai suka san ma’anar shi. 

“Dare na yi Dawud. Ka je ka ɗauki Yumna ku tafi gidanku.”

Cewar Mami tana kallon shi. 

“Don har da ni za ka tafi ko?”

Khateeb ya faɗi tun kafin Dawud ɗin ya amsa yana ƙara maƙalewa a jikin shi. Dan sadda kai dawud yayi yana jin kunyar Mami ɗin. 

“Da na bari sai gobe in Allah ya kai mu.”

Girgiza mishi kai Mami ta yi. 

“Ɗawainiyarta duka ta dawo hannunka… Iya ƙoƙari Antynta ta muku ai. Ko kwanciyarta asibiti mu ya kamata mu kula da ita… Yanzun za ka tashi ka tafi.”

Mami ta ƙarasa babu wajen musu a muryarta. Khateeb ya ci gaba da tsalle-tsalle a jikin Dawud yana faɗin zai bishi. 

“Zo nan… Ba yau ba”

Mami ta faɗi, shagwaɓe fuska Khateeb ya sake yi yana kallonta. Girgiza mishi kai ta yi. Dole ya sauka daga jikin Dawud yana komawa inda Mami ta nuna mishi a gefenta ya zauna yana turo baki. 

Miƙewa Dawud ya yi

“Sai da safenku Mami. Zan kira anjima… In dai kuna buƙatar wani abu ku kira ni.”

“Allah ya tashemu lafiya. Babu ma abinda muke bukata. Ka kwanta ka huta din Allah.”

“In sha Allah…”

Tayyab ne ya miƙe yana binshi suka fita tare. Har sai da suka je wajen parking ɗin cikin asibitin tukunna Dawud ya zaro mukullai daga aljihunshi yana ware na motar ya miƙa wa Tayyab. 

“Ka riƙe wannan a hannunka. Sai in je gida in ɗauki ɗayar…”

Karɓa Tayyab ya yi. 

“In sauke ka gidan mana Yaya.”

“A’a ka zauna ko za a siyo wani abu. Zan hau mashin.”

Jinjina kai Tayyab ya yi, fuskarshi ɗauke da wani yanayi ya ce, 

“Allah ya sanya maka albarka da alkhairi a rayuwar aurenka Yaya. Allah ya kula da kai fiye da yadda ka kula damu. Allah ya baka farin ciki fiye da yadda ka bamu.”

Lumshe idanuwa Dawud ya yi yana buɗe su tare da sauke numfashi mai nauyi. Addu’ar da Tayyab yai mishi na nutsar da zuciyarshi. 

“Amin tayyab… In dai kuna sona a kusa da ku… Faɗa min kawai za ku yi. Kasan hakan ko?”

Murmushi Tayyab ya yi. 

“Kana tare da mu a zuciyar mu ko yaushe Yaya. Da Tafiyar Haji Beeba nake jin komai zai dai-dai ta…”

Murmushi Dawud ya yi da yake ji har cikin zuciyar shi. Ko ya ya tuna Hajiya Beeba bata gidan nan sai ya ji wani farin ciki a zuciyarshi. Don ya tsani ya ko ga inuwarta balle ita da kanta. 

Sai da Tayyab ya ga ya hau mashin tukunna ya juya. Yana zuwa gida kanshi tsaye ɗakinshi ya wuce ya ɗauko mukullin ɗayar motar. Tukunna ya fito, duka akwatunanshi na nan falo inda suka barsu da safe. 

Ɗauka ya shiga yi yana kaiwa mota. Sai da ya gama tukunna ya shiga motar. Ya kunna yana juyawa da motar ya fita daga gidan. 

Wakar (Free by Zain Bhikha) ya kunna yana kure volume ɗin. Waƙar na sa shi shiga wani yanayi mai wuyar fassara. Ita ya bari on repeat har ya ƙarasa gidan su Yumna tukunna yai parking yana kiranta a waya. 

Cawa ta yi ya shigo. Shigar kuwa ya yi da sallama suka gaisa da Anty tana tambayarshi mai jiki. Akwatinan lefen Yumna ɗin anty ta ɗauko musu Dawud ya ɗiba ya kai mota duka tukunna ya dawo. 

Anty ya kalla. 

“Bansan kalar godiyar da zan miki ba Anty. Bansan me zan ce ba… Allah ya shirya miki yaranki… Allah ya baki dukkan farin ciki…”

“Amin Dawud… Ba sai ka gode min ba… Ka riƙe Yumna amana… Shi kaɗai ne godiyar da za ka yi min. Kai alheri ne a rayuwarta. Don Allah karka sauya hakan.”

“In sha Allah…”

Dawud ya faɗi yana ƙara yi wa Anty godiya. Tukunna ya basu waje ita da Yumna ɗin. Kallon Yumna da ke zaune kanta sadde tana kallon ƙasa Anty ta yi. 

“Ba komai yake da tabbas ba a rayuwa. Zan iya cewa kin samu mijin da zai yi iya yinshi wajen ganin farin cikin ki. Don Allah ki riƙe shi da ‘yan uwan shi amana. 

Ki koyi danne ɓacin ranki a gabanshi in ba ya kama dole ba. Mahaifiyar ki macece mai haƙuri. Ki yi koyi da hakan, ki guji zugar kowaye akan mijinki

Duk wanda zai ce miki rayuwar gidan aure da sauƙi ƙarya yake yi. Duk wanda zaice miki cike take da farin ciki ko da yaushe yaudararki yake yi. 

Rayuwa ce da soyayya kaɗai ta yi kaɗan ta riƙeta, rayuwa ce da take buƙatar fahimta, haƙuri, yafiya da kauda kai da abubuwa da a hankali za ki fahimta. Duk idan kina bukatar wata shawara ki kirani”

Yumna da tunda Anty ta fara magana take zubda hawaye ta ɗago tana share kwalla tare da miƙewa. Mayafinta ta ɗauka ta yafa a kanta. Mata da yawa dangin su ke kaisu gidan mazajen su. 

Nasihar da Anty tai mata, mahaifiya da mahaifi ne suke maka ita. Duka biyun bata samu ko ɗaya ba. Har soro Anty ta rakata tana ƙara yi mata addu’a sosai kafin ta koma. 

Kanta a ƙasa yake, haka take tafiyar a hankali tana zubda hawaye. Don haka ba ta ga tahowar Dawud ba sai karo da ta ji ta kai mishi. Hakan ya sata ɗago da kanta da sauri. 

Hawaye ne shimfiɗe akan fuskarta da bai hana Dawud ganin kyan matarshi ba. A idanuwan mutane da yawa. Cikin kashi uku na kyawawa ko na biyu ba za ta zo ba. A idanuwanshi kyawunta mai yawa ne, a zuciyarshi kyawunta ba zai taɓa misaltuwa ba. 

Tashi ce ita, zaɓin shi ce, kyanta ya ishe shi. Komi nata ya mishi dai-dai. Yasan damuwarta, yasan dalilin hawayenta. Idanuwanshi cikin nata, muryarshi cike da ƙaunarta da yake ji ya ce, 

“Ba ki samu kalar bikin da mata da yawa suke samu ba… Tare da ni za ki samu abinda ba kowacce mace take samu ba Yumna. 

Ba zan miki alƙawarin farin ciki tare da ni ko da yaushe ba. Zan miki alƙawarin baki farin ciki duk sa’adda Allah ya bani ikon yin haka. 

Mu je inda za mu fara rayuwa ta daban. Inda za mu fara haɗa duniyar mu waje ɗaya…”

Dawud ya ƙarasa maganar yana miƙa mata hannunshi, idanuwanshi take kallo inda wani abu ke fisgarta kamar zai haɗiye dukkanta, kafin ta sauke su kan hannunshi da ya miƙo mata. 

Zuciyarta na sake karyewa. Son shi na sake zauna mata, wasu sabbin hawayen na zubo mata, hannunta ta kai cikin nashi, da sauri kamar yana tsoron in ya ɓata lokaci za ta fasa ya kama hannunta tsaf cikin nashi. 

A hankali ya kamata suna takawa har inda motar shi take, yana jin hannunta kamar dutse mai nauyin gaske cikin nashi. Yana jin yadda igiyar aure ta ɗaure su waje ɗaya. Yana jin yadda lokaci ɗaya ya shiga rayuwarta. 

Ta yarda da shi, ya aureta, yanzun kuma ta miƙa mishi dukkan zuciyarta cike da yarda. Yana mamakin yadda wasu mazan ke manta duk wannan karamcin su wulaƙanta matansu. 

Yana rasa dalilin da zai sa ka karɓi kulawar yarinyar mutane in har kasan ba za ka iya ba, yana jin gara ka barta a gidansu, gara ka bar wa iyayenta ita in har kasan in ka aureta za ka wulaƙantata. In har kasan ba za ka darajtata ba in ka aure ta. 

Da tunanin nan fal a zuciyarshi ya buɗe mata mota ta shiga. Sai da ta zauna sosai tukunna ya rufe murfin motar ya zagaya ya shiga yana jansu a hankali.

Sai da ya biya da su ta Chicken Republic ya siya musu kaji da kayan ciye-ciye kala-kala tukunna ya kama hanyar zuwa gidan da Abba ya bashi da ke Malali. 

***** 

A ƙofar gidan yai parking, ga mamakin shi maigadi ne ya buɗe mishi gate, don haka ya sake kunna motar yana shiga gidan. Tun satin bikin da Abba ya zo da shi don ya shiga ya ga ko yana buƙatar a ƙara ko a sake wani abu. 

Lokacin ko fitowa bai yi ba daga mota, don gani yake babu yadda za a yi ya zauna a nan gidan. Bai ga dalilin da zai sa Abba ya ce inda ya bashi a nan zai zauna ba. Bayan yana da nashi gidan. 

Mami da Labeeb suka tausasa shi. Don haka da ya fito daga motar kallon gidan yake. Ba wani girma gare shi ba, Abba ya ce 3 bedroom flat ne. Amma ya ƙayatu sosai tun daga waje. 

Don har ya fi nashi ma. Kamar an ce ya kalli gefen haggun shi. Jeep ce babba, baƙa sabuwa dal da ita, da mamaki bayyane a fuskarshi ya ƙarasa. Wani ɗan rubutu da ke maƙale a jikin motar na jan hankalin shi. 

Ƙarasawa ya yi yana ganin ɗan kati ne, ya ɗauka yana duba jikin shi. 

‘Fatan alkhairi a rayuwar aurenka. Na rasa abinda zan baka. El-labeeb.’

Numfashi dawud ya ja yana fitarwa. Ba lokacin da zai tsaya tunani bane ba, mukullin da ke jikin murfin motar ya zare yasa a aljihunshi yana komawa wajen motar da ya bar Yumna a ciki ya buɗe mata. 

Ta fito tana kallon yanayin gidan, hannunta ya kama suka taka steps biyun da zai hau da su inda ƙofar gidan yake. Har suka ƙarasa, ya saki hannunta ya zaro mukullan gidan, ya saka da bismillah yana buɗewa. 

Hannunta ya kama yana faɗin, 

“Bismillahi walajna wa bismillahi kharajna wa alallahi rabbina tawakkalna.”

A hankali itama cikin zuciyarta ta maimaita addu’ar shiga gidan da ya yi. Suka saka ƙafafuwansu na dama a tare. Falon Yumna take ƙare wa kallo. Ba kyawun shi ba ne a zuciyarta. 

Farin ciki ne na cimma nasara. Farin ciki ne na bayan duk wahalhalun da suka sha. Yau su ne ƙarƙashin rufin gida ɗaya a matsayin mata da miji. 

Da sauri Yumna ta juya ta rungume shi tare da zagaye hannunta a baya ta riƙe shi dam, tana kuka take faɗin, 

“Da gaske mune a matsayin nan…”

Dariya Dawud ya yi yana ɗora hannunshi a bayan kanta, ya kwantar da kanshi a kafaɗarta. 

“Shhh… Mune Yumna. Mata da miji… Mune a matsayin nan.”

Dariya ta yi ita ma, tana ƙara ɓoye kanta a ƙirjinshi. 

“Ina sonka sosai.”

Lumshe idanuwanshi ya yi, yana barin yadda zuciyar shi take dokawa akan fuskarta ya bata tashi amsar. Sai da ya tabbata ta nutsu tukunna ya jata ya zaunar kan kujera. 

Ya koma ya dinga shigo musu da kayansu, nan falon ya barsu. Ko yaushe suka samu nutsuwa sun shirya su. Tukunna ya ɗauki ledojin kayan ciye-ciyen da ya siyo ya miƙa wa Yumna, hannunshi ta kama tana miƙewa. 

Ɗaya daga cikin bedrooms ɗin suka shiga. Kallon komai Dawud yake yi na cikin ɗakin da yake na baƙin silver. Komai na ɗakin baki da fari. Murmushi ne ya ƙwace wa Dawud. 

Ƙarasawa ya yi kan gadon inda ya hango wani kati a ajiye, ya ɗauka. 

‘Bansan me zan baka ba Yaya. Hope za ka so ɗakunan da kalar da na zaɓa. Tayyab.’

A ko ina yake jin ƙaunar Tayyab ɗin. Yana can yana fushin Abba ya sa shi zama inda baya so. Su kuma suna nan suna ƙoƙarin ganin komai na gidan ya mishi yadda zai so shi. 

Cikin manyan kyautuka da za ka yi dace da su a duniya har da ƙauna irin wadda ke tsakanin su da Tayyab. Ƙauna ta tsakani da Allah babu gauraye a cikinta. 

Da bashi da Mami a rayuwar shi zai ce ɗan uwanka da kuka haɗa jini da shi ne kawai zai so ka har haka. Sai ta fahimtar da shi ƙauna ta gaskiya Allah ne yake dasa ta. Ya ke bada kyautarta a tsakanin Al’umma ko da babu haɗuwar jini. In kana da rabo za ka dace da irin ta. 

Yumna ya kalla da take tsaye. 

“Kin yi Isha’i?”

Ya buƙata, kai ta ɗaga mishi. 

“To… Mu je mu yi alwala.”

Ba Ta yi musu ba ta nufi inda ya nuna mata, banɗaki ne. Alwala ta yi ta fito tukunna shi ma ya shiga. Falo ta koma ta buɗe cikin wata jaka ta ɗauko hijabinta da sallaya ta koma musu da shi.

Dawud ya ja suka gabatar da sallar nafila raka’a biyu. Suna idarwa ya juya ya ɗora hannunshi na dama a saman kanta yana karanta, 

“Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi… Wa’auzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi.”

Yana sauke hannunshi tana ɗora nata saman nashi kan ta karanta. Murmushi Dawud ya yi. 

“Allah ya bani ikon zama dake cikin aminci.”

“Ya bamu ikon zama da juna cikin aminci.”

Ta Faɗi da sauri, ya amsa ta da amin. Ya janyo ledojin da ke gefensu ya fito da fresh milk, ya buɗe kaza guda ɗaya. 

“Mu ci…”

Girgiza mishi kai ta yi.

“Na ci abinci a gidan Anty. Bana jin yunwa.”

Kallonta yake yi, hakan yasa ta sauke idanuwanta daga cikin nashi. Bai ce komai ba ya kama ledar ya rufe yana ajiyewa gefe ɗaya. 

“Me ya sa za ka rufe. Me ka ci?”

“Ban ci komai ba.”

Ya amsa ta. 

“Don Allah ka ci…”

Idanuwanshi ya sauke cikin nata

“Kinsan halayena da yawa. Kinsan abubuwan da bana so da yawa Yumna. Cikin su har da yawan magana. 

Mu ci ko mu barshi dukkan mu.”

Bata ce komai ba ta janyo ledar gabanta tana buɗewa, da kanta ta dinga raba kazar da ƙasusuwan tana tara mishi. Sai da ta gama, kamar yadda ya faɗa tasan da yawa cikin halayen shi. 

Cikin su har da yadda damuwa ke hana shi zama ya ci wani abu, da kanta ta sa hannu ta ɗibi kazar ta miƙa mishi. Buɗe bakin shi ya yi ta saka mishi. Sosai take bashi, babu abinda Dawud ke tunawa sai Umminshi. 

Da kewarta da ta mamaye ko ina nashi. Ummi ce kaɗai ta ke bashi abinci da hannunta duk idan baida lafiya ya ƙi ci. Ko wani a gidan baida lafiya ya kasa cin abinci. 

Tunda ta rasu ya rasa wannan kulawar sai yau. Ya manta yaushe rabon da ya nutsu ya ci abinci haka. Sai da ya ji ya ƙoshi tukunna ya girgiza mata kai, kaɗan ta ɗauka ta sa a bakinta. 

Ta ɗauki fresh milk guda ɗaya ta buɗe ta miƙa mishi. Karɓa ya yi ya sha fiye da rabi ya miƙa mata ta karɓa ta ajiye. 

“Nagode…”

Ya furta a hankali saboda baisan me zai ce mata ba don ta san ya ji daɗin abinda tai mishi. Murmushi kawai ta yi bata bashi amsa ba. 

Gyara zamanshi ya yi yana jingina bayanshi da bangon wajen kamar yadda take zaune ita ma. Kanta ta kwantar jikin hannunshi wata gajiya na saukar mata. 

Sun jima a haka shiru, kafin Dawud ya kalleta. 

“Tashi mu kwanta.”

Miƙewa ta yi tana wucewa kan gadon. Dawud kam banɗaki ya shiga, tana jin ƙarar ruwa alamar wanka yake, fitowa ya yi ɗaure da towel a jikinshi. Ta sauke idanuwanta har ya fita daga ɗakin. 

Ya dawo jikinshi sanye da riga mai yankakken hannu da wandon ta. Farare ne ƙal, hannunshi riƙe da riga da ya miƙa mata, karɓa ta yi tana rasa inda ya samota don kala ɗaya na kayan lefenta bata gani ba. 

Wanda duk ta sa da bikin daban ya kawo mata su, karɓar rigar ta yi ta miƙe ta shiga banɗaki. Wankan ta yi ita ma ta sako rigar ta fito tana zagayawa da sauri ta kwanta. 

Ƙwan ɗakin Dawud ya kashe musu yana kai hannu ya riƙo Yumna jikinshi. Cikin kunnenta yake faɗa mata kalaman da sirri ne a tsakanin su. Kafin ya fara nuna mata kalar son da yake yi mata. 

**** 

Sa’adda Dawud ya shiga su duka ukun a zaune suke kan gadon asibitin suna ta hira. Ya manta last da ya gansu cikin walwala haka. 

“Mami ina kwana…”

“Lafiya ƙalau. Ya kuka kwana?”

Ta buƙata, a kunyace ya janye fuskarshi daga ta Mami. 

“Alhamdulillah…”

Gaishe da shi Zulfa da Tayyab suka yi. 

“Ya kuke? Zulfa ya jikin?”

“Na ji sauƙi. Anjima ma ƙila a sallame mu.”

Murmushi Dawud ya yi yana neman waje ya zauna. 

“Zaman me za ka yi kuma ka bar ‘yar mutane ita kaɗai? Ba mun gaisa ba ka ganmu?”

Daƙuna fuska Dawud ya yi. 

“Kai Mami… Ko zama ba zan yi ba?”

Dariya su Zulfa suke mishi, ya harare su. 

“Ina Khateeb?”

Ya buƙata.

“Yana makaranta. Kasan Khateeb in bai je ba zai fara tambaya me ya sa.”

Kai Dawud ya jinjina. Wani lokacin Khateeb na tuna mishi Sajda. Ita ce ko kaɗan bata son abinda zai hanata zuwa makaranta. Addu’a yai musu ita da Ummi yana jin kewarsu da take manne da zuciyar shi ko da yaushe. 

Kallon Tayyab da Zulfa da suke hira abinsu yake yi. Sosai yai kewar ganinsu haka, ko bai yi magana ba hirarsu na mishi daɗi in suna yinta.

Sallama suka ji ana turo ƙofar. Labeeb ne ya shigo bayan sun amsa mishi sallamar. Idanuwanshi cikin na Zulfa suka sauka. Ganinta zaune haka ya sa shi yin ɗan murmushi da ta mayar mishi. 

Mami ya fara gaishewa ta amsa shi tukunna ya miƙa wa Dawud da Tayyab hannu. Ledar dake ɗayan hannunshi ya miƙa wa Mami ta karɓa. 

“Sannu da hidima… Allah ya yi albarka.”

“Amin Mami. Zulfa ya jikin?”

“Na ji sauƙi. Alhamdulillah.”

Zama Labeeb ya yi kusa da Dawud. 

“Ya Mamdud da Ateefa?”

Dukkansu idanuwa suka zuba mishi. Zulfa da saida cikinta ya yamutsa da aka kira sunan Mamdud. Fuskarta na canzawa lokaci ɗaya, hankalin su nakan Labeeb shi ya sa basu kula ba. 

“Tee na gida. Ɗazun aka sallame mu. Mamdud sai godiyan Allah….bai tashi ba har yanzun…”

Ya ƙarasa cike da damuwa a muryarshi. Kallonshi Dawud yayi, har yanzun akwai haushin shi a zuciyarshi, hakan bai hana damuwarshi taɓa dawud ɗin ba. 

“Komai zai yi dai-dai In sha Allah, zai tashi.”

Kai Labeeb ya jinjina yana jin ya ɗan rage damuwar kaɗan. Kamar ya rabata da Dawud ne, tunda ya ga Zulfa haka hankalin shi kuma ya koma gida wajen Ateefa. Don haka ya miƙe yana faɗin, 

“Mami na tafi. Allah ya ƙara sauƙi. Sai can da yamma in sha Allah zan sake dawowa.”

“To shikenan ka gaishe da Ateefa. In kuma an sallame mu kafin yamma zansa a kira a faɗa maka.”

“Allah ya kaimu yamman…”

Ya faɗi, Dawud miƙewa ya yi yana bin bayan Labeeb tare da jan ƙofar. 

“El…”

Ya kira, juyowa Labeeb ya yi, tsaf Dawud yake kallonshi, sai yanzun motar da ya gani jiya ta faɗo mishi a rai. Ya kuma rasa me zai ce ma Labeeb, karamcin shi a gare su mai girma ne. 

Har ƙarshen rayuwar su yasan ba za su taɓa iya biyanshi ba ko yanzun za su fara ɗaukar nauyinshi da na ‘ya’yanshi, har jikokin shi. Don ya taimaka musu lokacin da suke cikin tsananin buƙata. 

“Motar da na gani… El ya yi yawa…bazan…”

Hannu Labeeb ya ɗaga mishi yana katse shi da faɗin, 

“In har ba laifina bane zai shafi kyautar da na yi maka don Allah karka sa mu yin gardama akan ƙaramin abu irin wannan. 

Meye amfanin abinda na tara in har bazan iya muku abinda nake so da shi ba? Meye wannan motar? A’a Don karka ɓata min rai.”

Sauke numfashi Dawud ya yi yana jin nauyin girman Labeeb ɗin ya sake danne shi. Ɓangaren da ya kasa yarda ya wa Zulfa abinda yai mata na ƙara girma a zuciyarshi. 

“Na gode… Allah ya ƙara buɗi… Jiya kuma tare da Zulfa. Da ba ka nan bansan me za mu yi ba… Kamar ko da yaushe.”

Ɗan dafe kai Labeeb ya yi yana kallon Dawud da ke mishi godiya don ya yi abinda shi ne ya kamata. Ko da jinin shi bai zo ɗaya da na Zulfa ba duk inda zai nemo shi sai ya nemo. 

“Wai me ke damunka? Me ya sa kake min abu kamar baƙo?Rayuwarmu duka a haɗe take…”

Labeeb ya ƙarasa maganar yana juyawa ya tafi abinshi ya bar dawud tsaye yana kallonshi har ya sha kwana. Tukunna ya koma ɗakin. 

“Mu je ka sauke ni a gida in ɗora girki. Sai ka tafi.”

“Mami ki barshi a siyo abinda za a ci mana.”

Girgiza kai ta yi. 

“Bana son ina nan suna cin abincin waje kamar basu da kowa….Mu je kaima sai ka zo ka ɗaukar muku.”

Ba zai iya wa Mami musu ba, don haka ya kalli su Tayyab. 

“Ku kula da kanku sosai. Kirana kawai za ku yi in kuna buƙatar wani abu.”

Ware mishi idanuwa Zulfa tayi.

“So kake Anty Yumna ta cire mana kawuna muna ƙwace mata kai ko?”

Daƙuna fuska Dawud ya yi. Yana jin wata kunya da bai zata ba. 

“Gidan ku Zulfa…”

Ya faɗi yana juyawa, dariya suke mishi ita da Tayyab. Sam har ya fita ya ƙi yadda su haɗa idanuwa da Mami saboda kunya. Zulfa ta maida shi kamar kakanta yake faɗi a zuciyarshi sa’adda ya buɗe wa Mami mota ta shiga. 

***** 

Ƙarfe uku da ‘yan mintina aka sallame su daga asibitin. Su duka cikin farin ciki da godiyar Allah suke har suka ƙaraso gida. Ɗakin Mami Zulfa ta kwanta tana shaƙar ƙamshin ɗakin. 

Tayyab kam har zai wuce ɗakinshi. Baisan abinda ya ja shi zuwa ɓangaren Abba ba. Ƙwanƙwasa ɗakin ya yi zuciyarshi na wani irin dokawa. Shiru ya ji don haka ya tura da sallama. 

Zaune ya samu Abba ya haɗe kanshi da gwiwa. Takalman shi Tayyab ya cire yana shiga cikin ɗakin har inda Abba yake zaune ya tsugunna yana dafa shi, ɗagowa ya yi a hankali. 

Yanayin shi sai da ya ɗan tsorata Tayyab ɗin, gaba ɗaya ya fita hayyacin shi, kayan jikinshi sun yi cukwu-cukwu kamar an tauna su an fiddo. Da gani a cikinsu ya kwana ya kuma tashi bai canza ba. 

Hannu Tayyab ya kai zai taɓa jikin Abba ya janye da sauri. 

“Zan ji jikinka ne…”

Tayyab ya faɗi a sanyaye. Kai Abba ya ɗaga mishi, yana taɓawa ya ji zazzaɓi rau. 

“Zazzaɓi ne a jikinka… Tashi mu je asibiti.”

Tayyab ya faɗi yana miƙewa. Can ƙasan maƙoshi Abba ya ce, 

“Babu inda za ni. Ka barni ni don Allah… Ka je abinka.”

Girgiza mishi kai Tayyab ya yi, ba inda zai barshi a haka. Banɗaki ya shiga ya haɗa mishi ruwan wanka mai ɗumi sosai ya fito yana kama hannunshi. 

“Tashi ka yi wanka ko daɗi sai kaji. Ka ci abinci?”

Kallonshi Abba ya yi, hawaye masu ɗumi suka zubo mishi. 

“Ya kuka yi da rashin Aisha?”

Abba ya faɗi yana sa hannu ya goge fuskarshi, wasu hawayen na sake zubo mishi. Zuciyarshi kamar ta tsage yake jinta saboda ciwon da take mishi. 

Shigowar Tayyab ta sake fama mishi ciwon da yake ji. Hawaye Tayyab ya ji cikin idanuwanshi shi ma, baisan ya suka yi da rashin Ummi ba, kawai dai yasan Dawud ya riƙe hannayen su ya ɗago su daga faɗuwar da suka yi. 

Hannunshi ya miƙa wa Abba. Baisan me yake ji akanshi ba har yanzun. Amma ba zai iya jure ganinshi a haka ba, kamawa Abba ya yi Tayyab ɗin ya miƙar da shi tsaye. 

Har bakin toilet ya kai shi, sai da ya shiga ya ja mishi ƙofar ya dawo yana fito mishi da kayan da zai canza ya ajiye kan gado ya fita daga ɗakin zuwa kitchen. Abinci ya zubo a plate ya sako cokali ya ɗauko robar ruwa ya dawo. 

Yana nan tsaye don ya kasa zama saboda dokawar da zuciyarshi take yi har Abba ya fito daga wanka. Muryar Tayyab har wani rawa take. 

“Ga abinci nan… Don Allah ka ci… Zan dawo anjima in zazzaɓin bai sauka ba asibiti zamu koma.”

Don ko Abba bai dawo abbansu ba, ba zai jure wani rashin ba. Ba zai iya ba, kai Abba ya ɗan ɗaga mishi, har ya kai ƙofa ya ce, 

“Tayyab…”

Juyowa Tayyab ya yi, rasa abinda zai ce mishi ya yi. Juriyar da Tayyab yayi yana mishi duk wannan abin yake mamaki. 

“Jeka kawai…”

Sai da Tayyab ya dan yi jim kafin ya fita daga ɗakin. 

****** 

Kwance Zulfa take har lokacin, Allah ya rabata da ƙaddarar da ke jikinta, har ƙasan zuciyarta take jin abinda ya kamata ta yi . Wannan karin ba ta buƙatar shawarar kowa. 

Ta gama yanke hukunci, ta kuma san mutum ɗaya ne zai iya hanata in har ta ce zata nemi shawarar shi, miƙewa ta yi daga kwanciyar da take tana dudduba wayarta, can ta hangota gefen gado a ajiye a ƙasa. 

Ɗauka ta yi ta ga cajin saura 5%. Lambar Tayyab ta duba tana tura mishi text:

‘Yaya Tayyab ka tara min kowa a gidan su Yaya labeeb. Kowa nake nufi har da kai da su yayan…in mun haɗu zan muku bayani gaba ɗayanku… Don Allah karka tambayeni komai yanzun… Ka haɗasu kawai…bazan iya tambayar kowa ba… Yana da muhimmanci duk su haɗun…’

Yana shiga ta ji cikinta ya ƙulle, tsoronta za ta fuskanta. Ƙarshen komai za ta kawo yau.

**** 

Abu ɗaya Abba zai iya tunawa a halin da yake ciki. Bai fito daga tsohon gidan su ba sai bayan Magariba. Sa’adda ya dawo gida har an yi Isha’i. Sai lokacin ya haɗa duka sallolin ya yi su. 

Ya ja jikinshi ya kwanta, zazzaɓi mai zafi yake ji a jikinshi. Tashin hankali ya sa baya jin yunwa balle ƙishin ruwa. Shi kaɗai yasan abinda yake ji. 

Koya ya rufe idanuwanshi babu abinda yake gani sai fuskar Aisha da ta Sajda. In ya juya kwanciyarshi ya sake rufe idanuwanshi su Dawud yake gani suna ƙanana da kuma yadda suke da girma yanzun. Babu tunanin komai a zuciyarshi sai na yadda suka yi rayuwa duk shekarun nan kamar marayu. Babu kulawar mahaifi bayan sun rasa mahaifiyarsu. 

Baya ganin komai sai Khateeb da a idanuwanshi baida mahaifin da ya wuce Dawud, ta inda zai fara yake nema. Shekarun da ya yi asara da ba zasu taɓa dawowa ba. 

Soyayyar yaranshi da baida tabbas zai sake samu. Yafiyar su akan zaluncin da ya yi musu. Haƙƙin Aisha da ƙasa ta rufe ma idanuwa balle ya roƙi yafiyarta ita da Sajda. 

Hawaye ko kaɗan sun ƙi zubo mishi balle ya samu sauƙi don wuni ya yi yana zubda su yau. Har sai da kanshi ya soma sarawa. Duk juyin da zai yi ya buɗe idanuwanshi da kalar tunani da kuma abinda zai gani. 

Yadda ya ga rana haka ya ga dare. Kwana ya yi cikin mawuyacin yanayi. Kwana ya yi yana tsine wa Hajiya Beeba da yi mata Allah ya isa akan cutar da ta yi mishi. Kan kunnenshi akai sallar Asuba. 

Da ƙyar ya iya miƙewa ya shiga banɗaki ya ɗaura alwala ya dawo ya yi sallah. Nan ya zauna yana kuka yana roƙon yafiyar Allah da kuma sakayya akan Hajiya Beeba. 

***** 

Tun jiya da Auwal yai mata korar kare duniyar ta soma birkice mata. Hankalinta bai sake tashi ba sai da ta nufi gidan Huzai ta samu baƙon maigadi yake shaida mata ai an siyar da gidan jiya. 

Maigidan aka ce tai hatsarin mota ta mutu gawarta ma da mutanen da suke cikin motar aka haɗa aka binne don sun yi raga-raga. 

Da ƙyar ta kawo kanta gidanta. Kwana ta yi tana kuka don ji take ta ko ina duniyar ta haɗu ta mata zafi. Don haka a birkice ta tashi safiyar yau ɗin nan. Ga rashin bacci, ga tashin hankali, ga tsamin jikin dukan da Auwal ya naɗa mata. 

Ga wata irin yunwa da take addabarta. Kitchen ɗin gidan ta shiga. Duk da takan leƙo gidan wani lokaci. Da ƙyar ta samo wata tsohuwar taliya, electric ta kunna ta ɗora ruwa a tukunya ta fito tana komawa bedroom ɗinta. 

Kwanciya ta yi akan gado. Sallah ba damunta ta yi ba dama. Rashin baccin da bata samu ba ya sa bacci mai ƙarfi ya ɗauketa ta manta ma da ta ɗora girki. 

Ba ta farka ba sai da ta ji ɗakin ya ɗumame da wani irin zafi na tashin hankali. Buɗe idanuwan da za ta yi ta shaƙi hayaƙi mai kaurin gaske da ya sa ta jin kanta ya ɗauki zafi kamar zai fashe. 

Kafin tari ya turnuƙe ta. Miƙewa ta yi ba shiri, hayaƙi ya turnuƙe ɗakin, fitowa ta zo yi tana buɗe ƙyauren zafin wutar da ya laso ta ya sa ta komawa tana kurma ihu. 

Ganin yadda ko ina na falon ke ci da wuta kamar ana zuba mata fetir. Tunda Hajiya Beeba take bata taɓa sanin me ake nufi da asalin tashin hankali ba sai yau. Ihu take amma babu wanda zai kawo mata taimako. 

Ganin wutar ta soma turnuƙowa tana nufowa ɗakin ya sa ta tsananta ihun da take ga tari ga zafin wuta. Ganin babu wanda zai kawo mata ɗauki, ganin in ta tsaya nan ƙurmushewa za ta yi har tokarta yasa ta yin ta maza ta fito daga ɗakin. 

Sai dai me, tana jin yadda tafukan ƙafarta suka kware tunda ta ɗora su akan tile ɗin ɗakin. Numfashinta ke shirin ɗaukewa saboda azaba. A haka ta ci gaba da takawa tana kauce wa wutar da ke ƙoƙarin lasota har wajen ƙofa. 

Tana kamawa don ta buɗe tana ƙone hannunta har tsokar wajen kana hangowa. Azaba ta sa ko ihunta ba ya fita. Zanin da ke jikinta ne ya kama, bata gama tantance asalin inda ke mata zafi ba wutar da ke cin labulen da ke ɗakin ta ba narkarkakkar robar jiki ta zubo mata akan fuska. 

Azabar ta sa ta fisgar ƙyauren yana buɗewa. Rugawa ta yi waje tana mirgina tana ihu tana riƙe rabin fuskarta da robar labulen ta manne a jiki. Sama-sama take jin hayaniyar mutanen da suka shigo kawo ɗauki. 

Da tunanin duk wata dukiya da ta mallaka tana cikin gidan duhun gaske ya rufe mata ido. Komai na duniyar yai mata tsaye. 

**** 

Harmony ya fara isa ya samu Mamdud yadda ya barshi jiya. Anees zaune sai Asad can ƙarshen ɗakin yana waya. 

“Ina kwana…”

“Lafiya ƙalau Anees… Ya kuka tashi? Ya mai jiki?”

Labeeb ya faɗi yana samun kujera ya zauna. Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Anees ya yi. 

“Lafiya muka tashi. Mai jiki yana nan yadda ka barshi. Yaya ba zamu sake mishi asibiti ba? Ka kalle shi fa… Ni ko numfashi bana ganin yana yi. 

Banda canza mishi bandages da ake yi. Bana ganin wani abu na canzawa.”

Jan numfashi Labeeb ya yi yana saukewa. 

“Na yi wannan tunanin… Ka kalleshi Anees. Ina za mu motsa shi da karayar da ke jikinshi? Ko jiya na yi magana da likitan ya ce ana samun ci gaba. 

Mune kawai ba ma gane hakan…”

Yana rufe bakin shi Asad na dawowa ya kalle su. Sannan ya gaishe da Labeeb ɗin. Ya amsa shi yana ɗorawa da, 

“Dawa ake waya?”

“Mardi.”

Ya amsa. Ɗan ware idanuwa Labeeb ya yi bai ce komai ba. 

“Yaya wayar Zainab a kashe kuma wai Anees kar in kira Ishaq ko suna bacci ne. Ka kalli agogo fa…”

Kafin Labeeb ya amsa kira ya shigo wayarshi. Video call ne Zainab ta kira su. Amsawa Labeeb ya yi yana miƙa wa Asad da ya sauke ajiyar zuciya. 

“Karki ƙara kashe wayarki. “

Ya faɗi muryarshi cike da kashe di. 

“Yi hakuri Yaya Asad… Bansan cajina ya yi ƙasa bane na kwanta. Sa’adda na tashi empty yake shi ya sa. Ina kwana… Ya jikin Yaya Mamdud?”

Zainab ta faɗi. Ƙarasawa Asad ya yi inda Mamdud ɗin yake yana juya camera ɗin ya haska mata Mamdud na tsawon minti ɗaya. Kafin ya dawo da wayar saitin fuskar shi suka ci gaba da magana. 

Sai da suka gama tukunna ya ba Anees, gaisawa kawai suka yi ya miƙa wa Labeeb. Sun jima suna waya Zainab ɗin na shirin mishi kuka ita za ta dawo ta sake ganin Mamdud. 

Sai da ya buɗe mata idanuwa tukunna ta haƙura suka yi sallama. Ya mayar da wayar cikin aljihunshi. Kallon su Asad yayi. 

“Cikin jikin Zulfa ya zube.”

Wani irin numfashi Anees ya fidda yana runtsa idanuwanshi kafin ya buɗe su. Asad kam daina motsi yayi. Idanuwanshi kan Mamdud. Su dukkan su babu wanda ya ce komai. 

Labeeb bai tsammaci amsa ba. Amma yadda suka yi shiru ɗin da yadda iskar wajen ta canza sai yake jin duk wani iri. Basu lokaci ya yi su gama fahimtar maganar kafin ya ce, 

“Zan tafi… Ku kula da kanku.”

Muryar Anees can ƙasa ya amsa shi da,

“Allah ya tsare”

Duban Asad ya yi da har lokacin bai motsa ba. 

“Asad.”

“Ok”

Ya faɗi ba tare da ya ɗago kanshi ba. Wani abu yai tsaye a ƙirjin Labeeb. Bai ce musu komai ba ya fita yana jan ƙofar. Baisan me yake expecting ba. Yanayin su ya mishi wani iri. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 39Rayuwarmu 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×