Kallon Ateefa yake yi, tun da suka tashi sallah da Asuba suka koma suka sake tashi yanzun yake kula da idanuwanta da yanayin fuskarta babu komai sai rikici fal a cikinsu.
"Menene?" Ya buƙata.
"Bakomai..." Ta amsa tana kauda kai.
"Um um ban yarda ba..." Kallon shi ta yi tana turo laɓɓanta da suka yi mishi kyau. "Don Allah mu tafi gida... Ni lafiya ƙalau nake jina... Ba inda yake min ciwo..." Tunda ta fara maganar yake girgiza mata kai. "Kin ji abinda Doctor ya ce... Sati biyu. Yau kwananki nawa? Takwas ko tara?" Yamutsa fuska ta yi. . .