Skip to content
Part 41 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Kallon Ateefa yake yi, tun da suka tashi sallah da Asuba suka koma suka sake tashi yanzun yake kula da idanuwanta da yanayin fuskarta babu komai sai rikici fal a cikinsu.

“Menene?” Ya buƙata.

“Bakomai…” Ta amsa tana kauda kai.

“Um um ban yarda ba…” Kallon shi ta yi tana turo laɓɓanta da suka yi mishi kyau. “Don Allah mu tafi gida… Ni lafiya ƙalau nake jina… Ba inda yake min ciwo…” Tunda ta fara maganar yake girgiza mata kai. “Kin ji abinda Doctor ya ce… Sati biyu. Yau kwananki nawa? Takwas ko tara?” Yamutsa fuska ta yi tana shirin sa mishi kuka.

“Karki fara da hawayen nan Tee. Bana son ganin su… Ba inda za ki je!” Ya ƙarasa maganar yana kallon idanuwanta don ta ga da gaske yake yi. Ba inda za ta je ta ja mishi asarar baby. Za ta yi magana Doctor ya shigo suka gaisa da Labeeb.

“Doctor bana jin ciwon komai… Na gaji da zaman asibitin nan…”

Ateefa ta faɗi, Labeeb ya sauke numfashi, a kwanakin nan tana son yi mishi musu. Ya kuma san dalili shi yasa yake ƙyaleta.

“Zan iya sallamar ki in dai ba za ki yi wani aiki ba a gidan. Za ki kwanta ki dinga hutawa…ko da kwanakin sun cika banda aiki mai yawa.” Labeeb Ateefa ta kalla ya kauda kanshi gefe. Tunda bata ji maganarshi ba, na menene za ta nemi izinin shi yanzun? A sanyaye ta ce wa likitan, “Eh… Ba zan yi komai ba.” Murmushi ya yi ya kalli Labeeb. “Za ku iya tafiya gida. Amma ko yaya ta ji wani abu ku taho asibiti.” Hannu Labeeb ya ba likitan tare da yi mishi godiya. Ko da ya fita Labeeb bai motsa daga inda yake ba. Yana kallon Ateefa ta sakko tana haɗa komai nasu, har ta gama ta saka hijabinta.

“Mu tafi…” Ta faɗi, miƙewa yayi ya ƙarasa ya karɓi jakar da ke hannunta yana kama hanya. Yana jinta tana binshi a baya har suka fita daga asibitin suka ƙarasa wajen motarshi, buɗe mata yayi ya zagaya ya jefa jakar a baya tukunna ya shiga. Yana jin tana kallonshi har ya kunna motar ya ja su zuwa gida. Ko da suka ƙarasa jakar kawai ya ɗauka bai ce mata komai ba har suka shiga ciki ya hau sama yana nufar ɓangaren su ita da shi. Jakar ya ajiye mata yana juyowa da shirin fita daga dakin suka ci karo.

“El-labeeb…” Ateefa ta fara ya raɓata ya wuce, ta runtsa idanuwanta ta buɗe su. Bata ga abinda tai mishi da zai ɗauki fushi da ita ba. Asalima ita ya kamata ace tana fushin nan da yake yi. Tunda ba shiryawa suka gama yi ba. Akwai bayanan da zai mata bai mata su ba. Takalmanta ta cire tana shiga cikin ɗakin sosai. Duk da ta yi wanka a asibiti bai hanata sake shiga banɗaki don ta sake yin wani wankan ba. Tana fitowa mai ta murza ma jikinta ta shafa powder. Jikinta ta feshe da turaruka tukunna ta ɗauko riga da skirt na atamfa ta saka wa jikinta. Simple ɗauri ta yi wa ɗankwalin a kanta. Fita ta yi zuwa ɗakin Labeeb.

Da sallama ta tura ɗakin ta shiga. Yana tsaye yana waya, abu ɗaya ta ji, “Ko wani a sa ya kawo ta Mummy. Ko Mardiyya ce ko Uzzain.” Kafin ya ƙarasa wayar da faɗin, “Tam shikenan. Be safe.” Yana sauke wayar daga kunnenshi ya kasheta ta ɗora kan mirrow inda yake tsaye. Vest ɗin saman kayanshi ya soma cirewa. Tukunna ya soma ɓalle maɓallan rigarshi kamar Ateefa bata shigo ɗakin ba.

“Me nai maka?” Ta buƙata don gara ya mata faɗanshi da ya dinga yin kamar bata wajen. Abin ciwo yake mata. Bai amsata ba ya cire rigarshi yana yaddarwa a ƙasa, ya shige toilet ya ƙyaleta. Ko da ya fito wanka, kayanshi ya ɗauko irin wanda ya cire sai dai kalar ta banbanta. Ya sa a jikinshi yana ƙarasawa wajen mirrow ya ɗauki turare ya fesa wa jikinshi. Ta riga ta taɓara shi ta tayashi shiryawa in ya fito wanka. Miƙewa ta yi daga inda take zaune a gefen gadonshi tana ƙarasawa inda yake ta tsaya.

“Ni ban yi fushi ba kai ne za ka yi. Bayan ban maka komai ba.” Ba tare da ya kalleta ba ya ce, “Bana son yin faɗa. Ki ƙyaleni.” “Ni ina son yin faɗan.” Ta ce tana shan gabanshi tare da kallon fuskarshi. Sauke numfashi ya yi. “Kinyi abinda kike so… Wallahi idan na rasa babyna…idan na rasa babyna…” Kallon da take mishi ya sa sauran kalaman suka maƙale mishi. Hawaye cike fal a idanuwanta. “Ka ƙarasa mana… In ka rasa babynka sai me zai faru? Me yasa kake yi kamar kai kaɗai ka damu? A jikina cikin nan yake… A jikina yake girma… Babu kalar son da za ka yi mishi da zai kai kusancin da ni nake da shi. Bayani ya kamata kai min, ba wannan faɗan ya kamata mu yi ba. Ka daina kauce wa ɗayan…”

Waje Labeeb ya samu kan gadon ya zauna. Sannan ya bubbuga gefenshi yana ma Ateefa nuni da ta zauna ita ma. Ƙarasowa ta yi ta zauna tana kallon shi. Muryarshi a sanyaye ya ce, “Me kike son ji? Me kike so in faɗa miki Tee? Ya kike so in yi? Kan ƙafafuwana zan tsugunna in roƙeki kafin ki yafe min? Don Allah ki faɗa min ko me kike so zan miki…maganar nan ta ƙare iya yau. Duk minti ɗaya na kowacce rana da tunanin manne a ƙirjina. Ban taɓa manta na yi hurting ɗinki ba… Na tsani kaina da abinda na sa kika ji. In har akwai yadda zan gyara komai ki faɗa min. Kawai so nake mu koma normal… Mu koma yadda muke kafin wannan abin… Na gaji… Na gaji sosai…” Ya ƙarasa maganar yana sadda kanshi ƙasa. Yanayin muryarshi, maganganun shi duk sun kashe mata jiki. Tana ganin yadda yake nadamar abinda ya faru ko da bai furta ba. Tausayin shi ya kamata, duk da inta tuna abinda ya faru, ta tuna yana shirin auren Zulfa sai ta ji kamar za ta haɗiye zuciyarta take ji. Kamar numfashinta zai tsaya. Ba ta san yadda za ta danne kishin shi ba. Duba zuciyarta take yi, me take son sani? Me take son Labeeb ɗin ya faɗa mata? Kamar wanda yasan abinda take tunani. Batare da ya ɗago ya kalleta ba ya ce, “Cikin jikin zulfa ya zube.” Sai da zuciyarta tai wani irin dokawa. Cikin tashin hankali ta ce, “Karka ce min kun zubda cikin nan… Karka ce min kun ƙara wa kanku wasu sabbin zunuban…” Ɗago kai ya yi yana sauke idanuwanshi cikin nata. Yana tabbatar ta ga yadda kalamanta suka yi mishi zafi ba kaɗan ba. Ya zaɓi ya faɗa mata cikin Zulfa ya zube ne saboda zai aureta da wuri. Ba sai ya jira ta haihu ba. “Ki kalleni Ateefa…Ba El-Maska bane ba. Ya Rabb… Me ma zai sa ki yi tunanin zan yi wannan irin ɗanyen aikin? Zulfa ce… Zulfa ce fa.” Ta so da na sanin abinda ta faɗa. Amma maganar da ya yi ta ƙarshe ta sa ta fasawa. Wani irin kishi ne ya turnuƙeta.

“Oh hakane… Zulfa daban take da duk sauran mata… Duk soyayyar nan da kake mata… Duk kariyar nan sai kuma gashi ka mata tabon da ba zai taɓa gogewa ba..fentin…” Shi kanshi labeeb mamaki ne a fuskarshi, har lokacin ƙarar da yake ji cikin kunnuwanshi na amsawa ‘Tassss’ a hankali, balle Ateefa da ta ware idanuwanta tana son fahimtar me ya faru. Me ya katse mata maganar da take yi, ƙwaƙwalwarta da zuciyarta sun kasa fahimtar cewar Labeeb ne ya ɗaga hannunshi ya mare ta. Shi kanshi baisan ya akai ba. Abu ɗaya ya sani. Da na sanin da ya lulliɓe shi kamar ƙaton bargo. “Tee… Oh my God! I am so sorry…” Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata. Ba na ciwon marin da Labeeb yai mata ba. Sai na akan dalilin da ya mareta ɗin. Miƙewa ta yi, tana jin kiran da yake mata ba ta ko saurare shi ba sai gudu da ta ƙara wa tafiyar ta tana barin ɗakin. Dafe kai Labeeb ya yi kafin ya sake hannayenshi yana ɗaukar pillow ɗin da ke kan gadon yai jifa da shi. Baisan ya akai ya kasa controlling kanshi ba. Ranshi bai da wahalar ɓaci akan Zulfa ba tun yanzun ba. Mari abu ne mai sauƙi da zai yi wa duk wanda ya faɗi maganganun da Ateefa ta faɗi. Sai dai Ateefa ce, ta yaya hannunshi zai sauka a kan fuskarta. Miƙewa ya yi yana fita daga ɗakin ya nufi ɓangarenta. Ba bugawar da bai yi ba ta ƙi buɗe mishi. Yana da mukullan dukkan ɗakunan, sai dai yasan ba ta son ganin shi, ko shi baya son ganin kanshi balle ita kuma.

Juyawa ya yi da niyyar ya koma ɗakin shi ya ji sallama. Don haka ya sauka daga benen zuwa falon ƙasa. Mardiyya ce da wata mata mai matsakaicin shekaru. “Yaya ina kwana…” “Lafiya ƙalau Mardi. Ya su Mummy?” “Duka suna lafiya. Mummy ta ce in kawo ta.” Matar Labeeb ya kalla. “Sannu…” Ya faɗi, ta amsa shi tana kallon yanayin gidan. “Ki shigo mana ko lemo ki sha.” Girgiza kai Mardiyya ta yi. “Makaranta zan wuce yaya. Wani lokacin… Ka gaishe min da Anty.” “Za ta ji. Bacci take… Na gode. Zan ba Jarood saƙo ya baki.” Murmushi Mardiyya ta yi sosai. Tana mishi godiya tukunna ta fita. Matar Labeeb ya kalla. “Ba wani aiki ba ne ba, sharar gida ne da goge goge. Sai wanke-wanke da girki…In kin gama sai ki tafi abinki. Kullum in kika gama za ki tafi… Nawa zan biyaki?” Ɗan jim ta yi kafin ta ce, “Hajiya daga can ta ce dubu ashirin za a ba ni.” Kallonta Labeeb ya yi yana daƙuna fuska. Da ka ga yanayinta kasan tana cikin halin rayuwa. In tana da iyali bai ga me dubu ashirin za ta yi mata ba. “Nasan ba hurumina bane… Amma shin kina da yara?” Kai ta ɗan ɗaga. “Yarana shida…” Sauke numfashi ya yi. “Inkin tashi dafa abinci kullum ki yi da yawa sosai, wanda zai isa har da su. Zan baki dubu hamsin duk wata… Ya miki?” Yana kallon yadda idanuwanta suka cika da hawaye, tukunna ta durƙusa har ƙasa.

“Na gode… Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta min. Allah ya taimakeka kamar yadda ka taimake ni… Na gode.” Ta ƙarasa muryarta na karyewa. Ba ta san yadda addu’arta tai mishi daɗi ba. Sosai yake buƙatar taimakon Allah a cikin lamurranshi. Musamman yanzun da komai ya cakuɗe mishi. “Kin ga hanyar kitchen can…ƙofar store ɗin na daga cikin kitchen. Komai yana ciki…abinda babu sai ki faɗa… A gyara falon a goge komai.” Kai ta ɗaga mishi alamar ta fahimta, tukunna ya bar mata ɗakin yana hawa sama. Ɗakin Ateefa ya sake zuwa ba yadda bai yi ba ko magana ba ta mishi ba. Don haka ya koma ɗakinshi ya ɗauki wayarshi da mukullin mota. Text ya tura wa Ateefa: ‘Don Allah ki yi haƙuri… Please… Ki yafe min… Don Allah. Bansan ya akai ba. Zan fita. Ina ƙaunarki sosai. Har cikin zuciyata… Don Allah ki yi haƙuri.’ Sannan ya fita yana ɗaukar motarshi. Gidansu ya nufa kai tsaye.

*****

Tana jin duk maganar Labeeb. Kuka take sosai. Cikin ɓacin rai ta faɗa mishi maganganun da ta faɗa. Sai yanzun take jin nauyinsu, wacece ita da za ta jefe shi da kalamai irin wannan. Har a wajen Allah laifin shi mai yafuwa ne in har ya cika sharuɗɗa wajen tuba, ita kanta tana ganin nadamar da yake ciki. Sai dai har yanzun marin da yai mata na mata wani irin ciwo. Ba tun yanzun tasan Zulfa na da matsayi babba a wajen Labeeb ba. Amma bata taɓa hango ranar da zai ɗaga mata hannu zai zama akan Zulfa ba. Ba ta haufi akan soyayyar da yake mata. Sai dai yanzun tana jin ba za ta taɓa hango inda zulfa take ba. Tun kafin igiyar aure ta haɗa su da Labeeb ma kenan. Ta ina za ta fara? Ta tuna wani lokaci suna zaune a motar Labeeb ɗin.

*****

“Daddy ya amince da maganar aurenmu. A karo na farko Dady ya goyi bayana… Bansan me ya sa na kasa yin farinciki da hakan ba.” Labeeb ya ƙarasa maganar yana kallonta. Jin ta yi shiru ya sa shi ci gaba, “Ina sonki sosai… Ina son kowa nawa ya tayani sonki. Musamman Mummy… Ban taɓa mata musu ba… Ban taɓa yin abinda ba ta so ba…” Tana kallon yadda yake kokawa. A ɓangare ɗaya soyayyarta ce. A ɓangare ɗaya soyayyar mahaifiyarsh ce da son yi mata biyayya. Muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,

“Mu haƙura kawai… Auren mu zai yi wahala in ba albarkar Mummy.” Da sauri ya girgiza mata kai. “Ki kalli yadda soyayyarki ta gigitani… Ku duka ina ƙaunarku… Wajen Mummy ne ba zai taɓa haɗuwa da komai ba… Ita ta min alƙawari, duk matar da nake so… Za ta haƙura… Za ta haƙura in sha Allah.”

*****

Wannan karon hannu ta sa ta share ƙwallar ta. Bayan auren ta da Labeeb ta ga kalar yadda yake ƙaunar ‘yan uwanshi. Ta ga girman matsayin su a wajen shi, hakan ya sa ta gane ba ƙaramin so yake mata ba in har zai ɓata ran Mummynshi akanta. Amma yanzun tana kokwanto, tana shakku da shigowar Zulfa rayuwarsu komai zai canza. Wani irin tsoro take ji, duniyarta a yanzun ba komai bace in babu Labeeb. Bai taɓa ɗaga kai akan asalinta ba, bai taɓa ko da wasa ya tada maganar asalinta ba. Sai yanzun take ƙara ganin munin kalaman da ta jefe shi da su. Kowanne ɗan Adam a rayuwarshi ba zai rasa abu ɗaya mummuna ba. Ba zai rasa wani laifi ko aibu babba ba. Saboda me zaka danne naka ka nuna wa wani ɗan yatsa? Kishin labeeb ne ba ta san yadda za ta ko da rage shi ba ballantana ta daina. Yanzun banda kishin har da tsoro, sosai zuciyarta take cike da tsoron rabuwa da Labeeb. Tana tsoron abinda zai faru da soyayyar su in Zulfa ta shigo tsakiya. Kwanciya ta yi akan gadon, hawaye wani na bin wani. Ga zuciyarta ta mata wani irin nauyi. Ba ta san yadda rayuwarsu za ta kasance ba, a kowanne yanayi in dai Labeeb na kusa da ita za ta iya wucewa.

*****

Zaune yake a gefen gadon ya zuba wa Yumna da ke bacci idanuwa ko ƙiftawa baya son yi. Kallonta yake, daraja, kima da ƙaunarta na ƙaruwa a zuciyarshi. Bacci ko na minti ɗaya bai samu ba. Ko da suka gama raya darensu, ƙyaleta ya yi tai baccinta, salloli yai ta yi yana addu’a da godiya ga Allah da ni’imomin da ya yi mishi har aka kira Asuba. Ba don ya so ba ya tashe ta tai sallah. Yanzun kam zai barta tai baccinta don tana buƙatar hutun. Ranƙwafawa ya yi ya sumbaci kuncinta, tukunna ya tashi ya koma falo ya kwanta kan doguwar kujera. Agogon jikin wayarshi ya duba. Ya ga ƙarfe bakwai da ‘yan mintina. Text yai wa Tayyab don ya ji ya suka kwana. Yana dawo mishi da reply cewan komai lafiya ya ajiye wayar gefe. Lumshe idanuwanshi ya yi, bacci mai ƙarfi ne ya ɗauke shi. Bacci ne ya samu irin wanda duk wani ɗan Adam da ke cikin kwanciyar hankali zai samu. Baisan iya lokacin da ya ɗauka yana baccin ba. Motsin da ya ji ne ya sa shi buɗe idanuwanshi. Yumna ya gani ta ajiye plate da soyayyen dankali da ƙwai a ciki. Miƙewa ya yi babu shiri yana kallonta. Hakan yasa ta faɗin, “Ina kwana. A kitchen na ga komai…bansan me kake so ka ci ba…”

Ta ƙarasa tana sauke kanta a kunyace. “Ina zuwa…” Dawud ya faɗi yana miƙewa ya nufi bedroom ɗin da suka kwana. Yasan ba zai wuce aikin su Mami ba. Su tabbatar har kayan da za su buƙata akwai a cikin gidan. Sake brush ya yi ya wanke fuskarshi tukunna ya fito, hannuwanshi ya ɗora kan ƙugunshi yana kallonta da fuskarshi jiƙe da ruwa. “Waya sa ki yin girki? Kin taɓa ganin amarya na girki washegarin tarewarta?” Hannuwanta duka biyun tasa tana rufe fuskarta da su, ƙarasawa Dawud ya yi ya haɗe space ɗin da ke tsakanin su. Ya sa hannuwanshi ya sauke nata, sannan ya haɗa fuskarshi da tata.

“Ya kika tashi? Sannu da aiki.” Ya faɗi. “Alhamdulillah. Kai fa?” “Cikin farin ciki.” Murmushi ta yi tana runtse idanuwanta. Haka yasa shi yin dariya yana sumbatarta, kafin ya kama hannunta ya zaunar da ita. Kitchen ɗin ya nufa, har ta dafa ruwan zafi, don haka ya ɗauko musu da cups ya dawo. Ya koma ya ɗauko musu kayan haɗawa. Da kanshi ya haɗa musu tea ɗin ya miƙa mata nata kofin. Karɓa ta yi. “Sannu da aiki.” “Ke kikai aiki ai.” Ya amsata, tare suka karya har suka gama. Hanata ya yi tai wani abin, shi ya kwashe komai ya maida kitchen ɗin ya dawo ya zauna kusa da ita. Hannunta ya kama yana dumtsewa cikin nashi kamar wani zai ƙwace mishi ita. “Ba za mu je mu ga Zulfa ba?” “Zan je.” Ya amsata. “Za ka je ko za mu je?”

“Zan je dai. Ke kam ina za ki fita? Bakisan amare sai sun yi shekara ɗaya basu je ko ina ba?” Numfashi Yumna ta ja tana kallon fuskarshi da ya tamke babu alamun wasa. “Don Allah da gaske kake?” Da wasa yai niyyar maganar, sai daya faɗe ta yake jin ta zauna mishi. Yanzun yake sanin yana da kishi ba ɗan kaɗan ba. Tunanin za ta fita wasu su kalle mishi mata kawai ya sa kanshi na ɗaukar zafi. “Za mu je ba yau ba.” Ya faɗi, ko bata shekara ba, in ba wani babban dalili ba. Baya jin akwai inda za ta je. Gyara zamanta ta yi tana ɗora kanta a kafaɗarshi. Sun ɗan jima a haka kafin ya ji za ta zamo daga jikinshi. Bacci ta yi, gyara mata kwanciya yayi kan jikinshi sosai yana mamakin nauyin baccinta.

Ko gifta mishi kai yana bacci sai ya buɗe idanuwanshi. Yanayin yadda suke na mishi daɗi. Ƙyaleta ya yi ya juya ya ɗauko wayarshi da ke ajiye kan kujera yana duba agogo. Duka ƙarfe goma saura minti biyar. Ƙyalewa yayi. In Yumna ta tashi daga baccin ya tafi asibiti. Yasan Mami sai ta yi faɗa ta ce ya bar ‘yar mutane a baƙon waje, yanzun kam duk hankalin shi yayi wajen su. Yana son ya ga ya suka kwana.

*****

Da sallama ya shiga cikin gidan. Ga mamakin shi Mummy ya samu a falo zaune. Cikin sanyin murya ta amsa sallamar shi. Gaba ɗaya bayason yanayin da ya ganta a ciki, damuwa ce shimfiɗe a fuskarta tun rasuwar Arif, ta rame, ta kuma yi duhu sosai. Ga fuskarta na mishi wani iri saboda bai saba ganinta babu kwalliya haka ba. Musamman yau da ko ɗan kunnayen gwal ɗin da takan yi wa kunnuwanta da hannayenta ado da su duk babu. Idanuwanshi ya sauke gefen ɗanshi da ke bacci kan kujera kusa da Mummy.

Ɗan da har yanzun ko sunanshi bai sani ba. Bin inda idanuwan Labeeb ɗin suke Mummy ta yi. Tukunna ta maida dubanta kan fuskar Labeeb ɗin, yakai mintina biyu yana nazarin yaron kafij ya samu waje ya zauna. “Ina kwana Mummy.” “Lafiya ƙalau. Mardiyya ta kai maka ‘yar aikin ko?” “Eh can ma na barta. Ya…yake?” Ya tambaya a ɗan daburce. Gyara zama Mummy ta yi, muryarta ɗauke da wani yanayi ta ce, “Nasan ɗanka ne Labeeb. Wacece babarshi?” Ta ƙarasa tana zuba wa Labeeb ɗin idanuwa. Cikin kwanakin nan ta gama gane rayuwa ba komai bace ba. Ɗan da ke gefenta kaɗan ne daga cikin rikicin da rayuwa ta ƙunsa. A yanzun matsayin yaron, yadda aka same shi bai dame ta ba. Sama mishi rayuwa me kyau ita ce damuwarta.

“Ban sani ba… Wallahi bansani ba. Ko sunanshi ban sani ba… Abu ɗaya nasani. Ɗana ne… Ina jin hakan har a zuciyata ko da kamannin shi basu nuna ba…” Labeeb ya faɗi muryarshi na rawa. Jin mummy ta yi shiru ya sa shi sakkowa daga kan kujerar, gwiwoyin shi ƙasa yana ɗorawa da, “Na san kuna fushi da ni ke da Dady… Akan Zulfa… Akan yaron nan…don Allah ki yafe min Mummy. Na kunyata ki…na…” Katse shi Mummy ta yi, hawaye sirara na zubo mata. “Ka tashi Labeeb, ko da ka min laifi na yafe maka. Yaushe na zauna rayuwarka balle har in nemi yanke maka hukunci akan abinda ka aikata? Har in tuhumi tarbiyarka bayan ban baka ita ba.” Yasan gaskiya Mummy take faɗi. Amma bayason damuwarta. Ganinta a wannan yanayin ba ƙaramin nauyi yake ƙara wa zuciyarshi ba. Tashi ya yi ya koma kan kujera. “Na biyo in gaishe da ke ne. Zan je in duba Zulfa tana asibiti ita ma. Sai in biya wajen Mamdud” “Oh Allah… Me ya sameta?” “Miscarriage…” Labeeb ya faɗa don kalmar da turanci ta fi mishi sauƙin faɗi a gaban Mummy. Yana kallon murmushin da ya ɗan bayyana fuskarta kafin ya ɓace. “Allah ya basu lafiya… Ka gaishe da su.” “In sha Allah” Ya faɗi yana miƙewa.

Har ya kai ƙofa ta ce, “Labeeb…” Juyowa yayi. “Ya Ateefa?” Da mamaki Labeeb yake kallon मम्मी. Karo na farko da ta kira Ateefa da sunanta ba da asalinta ba. Karo na farko da ya ji damuwa a muryarta kuma akan Ateefa. Abin mamaki yake bashi, matar da ke zaune yake kallo. Komai nata ya sha bamban da na Mummyn da ya sani. “Ko ba ka ji ba? Na ce ya jikin Ateefa?” Sauke numfashi ya yi. “Da sauƙi sosai. Ɗazu aka sallame mu.” “Allah ya ƙara sauƙi. Kai mata sannu… In ka koma ka kirani mu gaisa… In na ji dama-dama zan zo har gida in duba ta.” Wani mamakin ya sake kama Labeeb. Saboda Ateefa ya sa bata taka gidanshi ba. Tun ana gininshi, shi ma da ƙyar lokacin a hanyarta ta zuwa airport ta biya ta sa mishi albarka. Amma da ƙafarta ba ta sake zuwa ba tunda ya kawo Ateefa gidan. Asalima in ba dole ta kama ba, ba za ka ji maganar Ateefa a bakin Mummy ba. In ko har ta furta to ba magana bace mai daɗi. Amma yau ita da kanta take cewa a kira waya su gaisa da Ateefa. Da kanta take faɗin za ta taka gidanshi. Murmushi ne ya ƙwace mishi. “Na gode sosai Mummy.” Murmushin ta ɗan mayar mishi, tukunna ya fice daga ɗakin yana nufar wajen gidan inda motar shi take. Kila labarin da Ateefa za ta ji na Mummy zai sa ta yafe mishi marin da ya yi mata.

*****

Zuciyarshi na dokawa ya shiga gida. Ateefa ya gani ta fito daga hanyar kitchen. Ɗan ware idanuwa ya yi yana kallonta.

“Ba aiki na yi ba. Na shiga na duba ne kawai. Ko shima an hana?” Ta buƙata tana tsare shi da idanuwan ta. Kunyarta yake ji. Kunyar abinda yai mata yake ji. Girgiza mata kai yayi yana rasa ta inda zai fara magana. Ganin ta yi tsaye yasa shi takawa ya ƙarasa inda take tsaye. Idanuwanta sun kumbura sun canza kala. Wani abu yai tsaye a zuciyarshi yana mishi ciwo, bai sake jin ɗaci a maƙoshin shi ba sai da ya ga yatsun shi kwance a kan kuncinta. Kallonshi take tana ganin yadda marin a fuskarta yake amma shi yake nuna yana jin ciwon abin, da ƙyar ya iya ɗaga hannunshi ya kai wajen yana shafawa da yatsun shi. Yana ganin yadda ta runtsa idanuwanta da alamar zafin hakan take ji. Matsawa ya sake yi sosai, iskar bakinshi da ta ji yana hura mata a wajen ne ya sa ta buɗe idanuwanta. Kamar zai yi kuka ya ce, “Kiyi haƙuri Tee… Inda zan koma baya in goge da na yi. Banda kirki na sani… Ban kyauta ba… Kunyarki nake ji wallahi. Don Allah ki yi haƙuri…” Ya ƙarasa maganar yana tsugunnawa da shirin kai gwiwarshi ƙasa. Da sauri Ateefa ta rigashi kaiwa tana faɗin, “Me kakeyi haka? Don Allah ka tashi…”

Girgiza mata kai ya yi yana ƙarasa kaiwa kan gwiwoyin shi tare da sadda kanshi ƙasa. Ko a addini ba a ce ya ɗaga hannunshi a kanta ba don ta faɗa mishi maganganun da suka yi mishi zafi. Laifi ne babba da ba a wajenta kawai ya tsaya ba, ba ita kaɗai ya taba ba har da addininshi. “Don Allah ka tashi…” Ateefa ta faɗi tana ɗora hannuwanta kan damtsen nashi hannuwan tana ƙoƙarin miƙar da shi. Ko motsi bai yi ba. “Zan tashi in kin haƙura… In kin ce kin yafe min…” “Na haƙura… Na yafe maka.” Ta Faɗi da sauri, ɗagowa ya yi yana nazarin fuskarta kafin ya ce, “Ban yarda ba…” Tsayawa ta yi tana kallonshi, gaba ɗaya ya sa ta jin kunyar ita ma. Labeeb ne a kan gwiwarshi yana ba ta haƙuri bayan ita ma ta mishi laifi. Matsawa ta yi sosai ba tare da ta tashi ba tana tallabar fuskar shi cikin hannuwanta. Sumbatar shi ta yi, abinda tun kafin rigimarsu rabonta da yi. Sannan ta janye fuskarta. “Na haƙura…” Sauke numfashi ya yi yana ɗanɗana man leɓenta da ke kan nashi laɓɓan kafin ya miƙe yana ranƙwafowa ya kamata ya miƙar, janta ya yi jikinshi yana rungumeta. Sosai ta zagaya hannuwanta a ƙugunshi tana riƙe shi sosai itama. “Ka yi haƙuri… Na faɗi abinda bai kamata ba… Ina tsoron rasaka…

Bazan iya rasaka ba El-labeeb. Don Allah karka barni…” Ta ƙarasa muryarta na rawa saboda kukan da ta soma. Ƙara riƙeta ya yi yana rocking ɗinsu a hankali. “Shhhh… Wa ya ce miki zan iya barinki? Wa ya faɗa miki za ki rasa ni? Da ga ranar da na sauke idanuwana akanki na san ba zan iya barinki ki je ko ina ba Tee. Ina sonki sosai… Kar wani abu ya sa ki kokwanto kan haka…” Labeeb ya faɗi yana kamo hannunta ɗaya da ke kan ƙugunshi tare da turashi ta tsakanin su zuwa kan ƙirjinshi inda zuciyarshi ke bugawa kamar zata fito. “Ki ji me take cewa in maganganuna ba sa miki tasiri… Ki ji yadda zuciyata take bugawa akan hannunki…” Shiru Ateefa ta yi tana maida numfashi, ta yi luf a jikinshi. Sonshi na ƙara rufeta. Sun jima a haka kafin ya ɗago ta daga jikinshi yana jan hannunta suka ƙarasa cikin falon suka zauna kan kujera suna fuskantar juna. Ƙafafuwanshi duk biyun Labeeb ya ɗora kan kujerar yana gyara zamanshi, ya jingina kanshi da jikin kujerar yana kallon Ateefa kamar ba shi da wani aiki banda hakan. “Mummy ta ce ya jikinki?” Yana kallon yadda ta ware idanuwanta cikin mamaki, kafin ta kwashe da dariya tana kallon shi. “Ka sani dariya in hakan kake so…”

Ta ƙarasa tana ci gaba da dariya. Murmushi Labeeb ya yi kawai yana zaro wayarshi daga aljihu ya cire key ɗin ya kira Mummy tare da sakawa a kunnenshi. “Mummy na dawo gida ne dama. Ga Ateefa ɗin…” Ya faɗi yana miƙa wa Ateefa da ke sake da baki wayar. Da ƙyar ta ɗago hannunta ta karɓa. Kamar mai tsoron wayar za ta cijeta ta kai ta kunnenta tare da yin sallama muryarta cike da tsoro. Amsawa mummy ta yi daga ɗayan ɓangaren tana faɗin, “Ya jikin naki?” “Alhamdulillah…” “Allah ya ƙara sauƙi. In sha Allah zan shigo in dubaki. Ku kula da kanku…” Kasa amsawa Ateefa ta yi tana cire wayar daga kunnenta ta miƙa wa Labeeb. “Hello… Mummy sai anjima… Love you.” Ya ce yana kashe wayar ya ajiye kan kujera.

Kallon shi Ateefa take tana son ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba. “Da gaske ne da Mummy ku ka gaisa.. Da gaske ne Mummy za ta tako ƙafarta gidanmu…” Cikin hanzari Ateefa ta faɗa jikinshi, bai yi tsammani ba don haka suka faɗa kan kujera. Sumba take manna mishi ko ina ta samu a jikinshi. “Mummy ta gaisa da ni! Mummy ta gaisa da ni!!” Take faɗi tana dariya, idanuwanta cike taf da hawaye. Riƙeta gam Labeeb ya yi don saura kaɗan ta faɗo da su daga kan kujerar. “Ki nutsu Tee…” “Um um… Mummy tai magana da ni.” Ta Faɗi tana sake maƙale mishi. Dariya suke su dukkansu. Farin cikinta na saka shi farin ciki shi ma. Haka yake son ganin fuskarta ko da yaushe. Haka yake son ganinta kullum. Sauka Ateefa ya yi daga jikinsu. “Bari in duba ya girkin can yake tafiya…” Kai ya ɗan daga mata, ta bar wajen. Wayarshi ya janyo yana ganin ɗaya saura minti biyar. Tashi ya yi ya hau sama yana ɗauro alwalar Zuhr ya sake saukowa yana fita daga gidan. Sa’adda ya dawo daga masallaci har Ateefa ta haɗa musu komai kan dining. Zama ya yi yana jiranta, yau yunwa yake ji har cikinshi na kara. Ta fi mintina goma sha biyar kafin ta fito. Doguwar riga ce ta atamfa a jikinta. Ta mishi kyau sosai. “Kin yi kyau…” Taɓe baki ta yi. “Ko ban yi kyau ba ma ba za ka faɗa min ba…” Murmushi ya yi. “Na ji… Zoki zuba min abinci yunwa nake ji.” Ƙarasawa ta yi tana zuba mishi komai ta miƙa mishi tukunna ta zuba. Sosai ya ci abincin, ita kam ɗan kaɗan ta ci, taliya da mai da yaji take son ci, ta ma sa a tafasa mata taliyar.

Kallonta Labeeb ya yi zai yi magana saƙon da ya shigo wayarshi ya katse shi. Ɗaukota ya yi, sai da zuciyarshi ta doka ganin Tayyab rubuce kan screen ɗin. Da sauri ya buɗe saƙon yana karantawa zuciyarshi na yo tsalle kamar za ta fito ta cikin idanuwanshi da ke karatun; ‘Ka zo gida… Komai lafiya dai. Zulfa ke son magana da kowa. Karka tambayeni akan me… Nima ban sani ba. Ta ce yana da muhimmanci kowa ya haɗu. Ka zo yanzun…mu ma gamu nan yanzun za mu shiga gidanku.’ Girgiza kai Labeeb yake zufa na keto mishi yana faɗin, “No… No… Zulfa no…” Tare da miƙewa. Ganin yadda ya rikice gaba ɗaya kuma ya ambaci Zulfa ya sa Ateefa cewa, “Lafiya? Me ya faru?” Hannu kawai Labeeb ya ɗaga mata yana nemo lambar Zulfa ya kira ya kara a kunnenshi. A kashe ya ji wayar, yasan rashin hankalin da Zulfa ke shirin yi, yasan wautar da za ta yi in har bai yi sauri ya je ya hanata ba. Da hanzari ya miƙe. Ateefa na tare shi. “Ina kake nufin zuwa? Ka faɗa min abinda ke faruwa.” Ɗan dafe kai Labeeb ya yi yana maida numfashi. “Zan faɗa miki in na dawo…” Ya ce yana raɓata ya wuce da gudu ya sauka daga benen. Ɗaki Ateefa ta nufa ta ɗauko mayafinta da mukullin mota. Ta gama zama Labeeb na barinta cikin duhu akan abinda ta san ya shafi rayuwarsu gaba ɗaya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 40Rayuwarmu 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×