Skip to content
Part 47 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Sa’adda ya fito daga wanka yana jin wayarshi na ringing bai bi ta kanta ba. Yasan su Asad ne za su azalzale shi. Shikuma sai ya gama shirin shi. Wani sama-sama yake jin shi. Ga wani sanyi da ke ratsa shi da bai da alaƙa da AC ɗin da ke kunne. 

Nishaɗi yake ji da ya jima bai ji irin shi ba. Ya kasa daina murmushi har ya gama murza wa jikinshi mai. Nan da awanni da basu shige biyu ba Zulfa za ta dawo ƙarƙashin kulawarshi. 

Ba zai iya misalta yanayin da tunanin hakan yake jefa shi ba. Kayanshi da ke ajiye kan gado ya ɗauka yana warwarewa. Ya ji an turo ƙofar, juyawa ya yi yana sauke idanuwan shi kan Ateefa da ke riƙe da plate a hannu ɗayan hannun kuma mug. 

Jikinta sanye da riga da wando na pakistan, kanta babu ɗankwali, a nutse take takowa har ta ƙaraso inda yake. Muryarta a dakushe ta ce, 

“Kar ka fita ba ka ci wani abu ba…”

Plate ɗin da soyayyen dankali da ƙwai ke ciki ya karɓa ya ajiye ƙasa, tukunna ya karɓi mug ɗin shi ma ya ajiye. Hannunta ya kama ya rungume ta a jikinshi saboda baisan me ya kamata ya ce mata ba. 

Duk yadda ta so danne mishi damuwarta yana gani. Yadda ba ta yi bacci ba jiya haka shima. Duk wani motsi da za ta yi zai sake gyara mata waje a jikinshi ya sumbaci ko ina ya samu a jikinta. Yasan kuka ta yi sosai, ko da bai ji a muryarta ba fuskarta a kumbure take. 

Zagaya hannuwanta ta yi ta riƙe shi sosai kamar za ta koma cikinshi. A hankali kuka ya ƙwace mata. Ita kaɗai tasan abinda take ji, nan da awanni kaɗan za ta koma ita da Zulfa suke da shi.

Za ta ci gaba da raba duk wani lokaci da yake da shi, soyayyarshi, komai nashi zai zama nasu su biyu. Ƙara maƙale shi tayie tana jin ɗuminshi da ƙamshin shower gel ɗinshi da ya hadu da man da ya shafa. 

Duk da ƙamshin ba baƙonta ba ne sai take jin shi daban yau. Ko don tana tattara duk wani abu da za ta iya nashi kafin ta soma rabawa da Zulfa ne oho. Kishin da take ji ba kaɗan ba ne. 

Tana jin yadda yake sumbatar kanta da gefen fuskarta yana ƙara riƙeta a jikinshi. 

“Ina sonki Tee… Ina sonki sosai.”

A zuciyarta take mishi ihu in har yana sonta kar ya raba mata zuciyarshi da Zulfa. Sai dai ko da wasa ba za ta bari bakinta ya furta abinda take ji ba. Ba za ta so kanta da yawa haka ba. 

Tana ta addu’a Allah ya sauƙaƙa mata zafin kishin da take ji. Tana kuma tuna wa zuciyarta kalar soyayyar da Labeeb yake mata daban da ta Zulfa. Bai musu iri ɗaya ba. Kowa tashi daban, tasan zai yiwu tunda zuciyarshi kashi huɗu ce. 

Ɗagowa ta yi daga jikinshi, hannunta ta sa tana goge fuskarta. Kamun Labeeb ya kama hannuwan ya sauke yana goge mata da kanshi. Kamata ya yi suka zauna a ƙasa tare. Yasan ita ma ba ta ci komai ba. 

Plate ɗin dankalin ya ɗauka ya & ɗibo yana miƙa mata. Buɗe bakinta ta yi tana karɓa, haka ya dinga yi, in ya ba ta shi ma sai ya ci. Haka har suka gama, da kanshi ya fita da plate ɗin da Mug ya dawo. 

Kayanshi ya ɗauka zaisa Ateefa ta miƙe tana faɗin, 

“Ina zuwa…”

Kafin ya amsata ta fita. Tun jiya da aka kawo kayan ba ta haura saman ba don gudun halin da zuciyarta za ta shiga sai da dare da ta je saboda Labeeb. Ta kuma ji daɗin yadda ɗakin shi yake ba a taɓa komai ba. 

Gaba ɗaya gani take kamar ba a cikin gidan take ba da ta fito daga ɗakinshi har sai da ta sauka ƙasa ta ɗauko abinda za ta ɗauko. Dawowa ta yi da farar shadda a hannunta. Ta ƙaraso inda yake tan miƙa mishi. 

“In ba ta kai taka tsada ba sai ka sa wannan… Ban faɗa maka ba ne saboda ina so in ba ka mamaki ne.”

Hannu ya sa ya karɓa yana rungume kayan a ƙirjinshi. Yana jin daɗin kyautar fiye da yadda zai iya faɗi. Ko da ta ɗari biyar ce sosai kyautar tai mishi daɗi. 

Bai damu da tsada ko rashinta ba. Zai sa su da kanshi a sama sanin ta danne duk kishinta ta ba shi su cike da ƙauna. Sumbatarta ya yi kamun ya ce, 

“Na gode sosai… Na gode Tee… Allah ya baki Aljanna…”

Murmushin ƙarfin hali ta yi mishi. 

“Amin… Tare da kai ma.”

Miƙa mata kayan yayi yana faɗin, 

“Ki taya ni shiryawa to…”

Ba ta yi musu ba ta karɓa tana taya shi ya shirya. Tana jin da duk wani abu da take mishi da yadda zuciyarta ke yin kamar za ta tsage saboda kishi. Ba ta san son da take mishi zai iya sa ta danne komai ba sai yanzun. 

Har turaruka ita ta fesa mishi tukunna ta kama hannunshi tana kaishi bakin ƙofa. 

“Allah ya sanya alkhairi ya dawo da kai lafiya.”

Nazarin fuskarta yake. Baya son damuwarta ko kaɗan. Sai dai bai da abinda zai yi ya rage mata ita. Yasan ta fahimta, ta gane Zulfa na buƙatarshi. Ta kuma san girman zumunci da ƙaunar ‘yan uwanshi a wajenshi. 

“Amin. Na gode sosai.”

Kai kawai ta ɗaga mishi tana kallon yadda ya yi kyau. Sai take ganin kamar ma yafi kyau cikin shaddar yau fiye da ta ranar auren su. Kuma tasan sharrin zuciyarta ne kawai. 

Don auren su babu wannan ramar a fuskarshi. Kuma bai yi duhu sosai ba. Tana tsaye a bakin ƙofa har ya fita. Sai da ta ga saukarshi da fitarshi daga gidan tukunna ta tura ƙofar bedroom ɗin. Zuciyarta gaya mata take yi ta kwanta kan gadon ta buɗe sabon shafin kuka. 

Sai dai wannan karon ba ta saurareta ba. Banɗaki ta wuce ta ɗauro alwala ta fito. Darduma ta shimfiɗa ta ɗauko Hijab ta saka tukunna ta fiddo da Ƙur’ani ta ajiye. Kuka take tana sallah. Tun babu nutsuwa tattare da ita har ta samu. 

Lokacin da ta zauna ta buɗe Ƙur’an wani sanyi take ji da miƙa lamurranta wajen Allah ne kaɗai zai samar mata da hakan. Wata nutsuwa take ji kamar za ta iya fuskantar ko ma menene ya taso mata saboda tasan Allah na tare da ita.

****

Washegari a cikin harabar gidan su suka yi walima daga ƙarfe huɗu zuwa shida. Duk da ba a daɗe ba ta ƙayatar da duk wani wanda ya samu halarta kafin Labeeb ya samu waje jikin motarshi ya kame yana jiran a sauko mishi da zulfa su tafi gida. 

Ita kuwa tunda Mami da Nabila suka gama shiryata. Mami ta kama hannunta ta kaita ƙofar ɗakin Abba ta samu waje ta tsaya zuciyarta ke rawa. Da ƙyar ta iya tura ƙofar ɗakin ta shiga. 

Tsugunnawa ta yi a gaban Abba kanta a ƙasa. Kallonta yake yana rasa abinda zai ce. Kallonta yake komai na yanayin na jefa shi cikin kewa da jin ciwon lokacin da ya yi asara a tare da su. 

Ƙasan zuciyarshi yake jin yadda ba zai taɓa iya yafewa Hajiya Beeba ba. Muryarshi na rawa ya ce, 

“Allah ya miki albarka a rayuwar Aurenki… Allah ya sa fitarki daga gidan nan ya zama matakin hawanki hanyar da za ta kai ki Aljanna… Har abada ba zan cike lokacin da na yi asara tare da ku ba. 

Bazan iya sake wa ba… Yadda nagan ku… Tarbiyarku… Addu’a kawai zan iya miki Zulfa… Wallahi ina ƙaunarku sosai.”

Hawayen da ya taru a idanuwan Zulfa ya samu damar zubowa. Ko bai faɗa ba tana jin yadda ya yi kewar Ummi a muryarshi. Kuka take sosai, sai da Abba ya tashi ya kamata ya ɗago ta. Jikinshi ta faɗa tana wani irin kuka. 

“Ya isa Zulfa… Allah ya sanya miki alkhairi…”

Da ƙyar ya samu ta yi shiru ya kama hannunta yana buɗe ƙofar ɗakin. Mami da ya gani tsaye ya miƙa wa ita yana rufo ɗakin ko zai samu sauƙin yanayin da yake ciki. 

Kallonta Mami take yi cike da alfahari, cike da ƙara yarda da cewar akwai ƙarshe a duk abinda yake da farko. Wa zai ce ƙaddarar da ta faɗa wa Zulfa za ta wuce da sauri haka har ta kawo su yau. 

“Duk wani shafi da ƙaddara ta buɗe miki daban yake da wannan Zulfa. Daban yake da rayuwar aure. Rayuwa ce da take cike da duk wani abu da kike tunani da wanda ba kya tunani. 

Banda haufi kan son da Labeeb yake miki. Sai dai soyayya kaɗai ba ta isa ta riƙe aure ba. Har yanzun babu wanda zai ce miki yasan duka abubuwan da ake buƙata a cikin zama na har abada. 

Zan ce miki, haƙuri, amana da yarda na ciki. Haka ma kau da kai musamman da yake ba ke kaɗai bace ba. Kar ki zama cikin mata masu yawan kai ƙara hakan na rage kima. Kar ki zama mai yawan tsegumi da mita yana dakushe ƙauna a wajen miji. 

Ki taƙaita ɗaga muryarki akan ƙananan abubuwa. Gidan aure ba waje bane na dauwamammen jin daɗi. Kamar yadda akwai ɓacin rai a cikin komai na rayuwa haka ma a zaman aure. 

Ki zama mai haƙuri da kau da kai.”

Kai Zulfa kawai take ɗaga wa Mami hawaye na zubar mata. 

‘Duka duniyar kwana nawa ce? In lokacin nan shi ne abinda ya rage muku fa? Kun yi asararshi wajen ɓacin rai kan abin duniya… Ku zama masu haƙuri da kau da kai. Ya fi ɓacin ran nan sauƙin yi.’

Nasihar Ummi wa su Tayyab wani lokaci ya dawo mata. Maganganun Mami na mata shige da na Ummi a mafi yawancin lokuta. Hannunta ta sa tana share ƙwalla, har Mami ta kama hannunta tana janta. 

Ba ta samu kyautar yaran da suka fito daga cikinta ba. A tare da su Dawud ta samu duk wani abu da Uwa take ji akan ‘ya’ yanta. Ta samu ƙaunarsu, ta samu jin daɗin da ke cikin kulawa da yara, ta samu ɗacin da ke cikin sallamar ƙarshe da yara akan Sajda. 

Ta koyi darussan da ke cikin samun ‘ya’ya ta kowanne fanni. A tare da su ta ƙara imani mai yawa. A tare da su yau ta samu farin cikin aurar da yara har biyu. A cikin rashin kyautar ‘ya’yanta Allah ya zo mata da hanyar da ba ta ji rashin yara ba ko kaɗan. 

Hamdala take har suka ƙarasa inda Dawud da Tayyab suke tsaye. Zulfa da ke kuka ta kama tana sumbatar goshinta. 

“Allah yai miki albarka. Allah ya ba ki dukkan farinciki da ladan da ke cikin aure… Allah ya ba ki haƙurin jarabawar da ke cikinsa.”

Tana ƙarasawa ta saki Zulfa ta juya don ba ta son su ga hawayenta. Tabbas akwai kewa mai yawa a lokacin da uwa za ta yi bankwana da ‘yarta duk da farin cikin da ke cikin hakan mai yawa ne. 

Dawud ne ya matso inda take tsaye yana tallabar fuskarta cikin hannuwanshi. Kuka take sosai har jikinta ɓari yake yi. 

“Amarya da kuka? Duk kin ɓata kwalliyarki…”

Cikin kuka ta ce, 

“Ina kewar su Ummi Yaya…”

Kai ya ɗaga mata don ya fahimta. Har abada za su kasance cikin kewar su Ummi. 

“Mu duka muna yi… Suna wajen da ya fiye musu nan. Ƙaunar mu a gare su na cikin addu’ar mu ta kullum. 

Ke da kin girma yanzun….manya ba sa kuka. Aure fa kike da…”

Ture hannuwanshi da ke fuskarta ta yi tana ci gaba da kuka. Tayyab da ke tsaye ta kalla, ya kasa ƙarasowa don haka ta ƙarasa inda yake. Kau da kanshi ya yi gefe. 

“Ya.. Yaya Tayyab…”

Ta kira muryarta na sarƙewa. Ya kasa juyowa, ya kasa yarda shi kaɗai za su bari a gidan nan sai Khateeb. Ya kasa yarda har sun yi girman da kowa zai yi gidanshi. Bai juyowa ba sai da ta riƙo hannunshi. Idanuwanshi cike taf da hawaye ya ce 

“Yaushe muka zo nan? Yaushe rayuwa ta kawo mu nan?”

Dan ɗaga mishi kafada ta yi, hawaye na zubo mata ta ce, 

“Nima ban sani ba…”

“Haka duk za mu rarrabu ko? Lokaci ya zo da ba ma buƙatar kulawar junan mu… Yaya ya samu nashi gidan… Yanzun kuma ke ce… Ni da khateeb ya za mu yi to?”

Ya ƙarasa maganar yana sa ɗayan hannunshi ya goge hawayen da suka tarar mishi da ke ƙara sa na Zulfa su fito. 

“Wa ya ce ba ma buƙatar kulawar junan mu? Nisan mu ba zai hana hakan ba… Nisan mu na nufin rayuwarmu na canzawa ne kamar yadda takan yi… Kaima nan da ɗan lokaci za ka yi naka gidan. 

Baya nufin mun daina ƙaunar juna… Baya nufin ba za mu ga juna ba… Yana nufin za mu buɗe zuciyoyinmu ƙaunar wasu ta shigo… Yana nufin za mu ƙara yawan zuri’ar mu…”

Hawayen da suka zubo wa Tayyab ne ya sake gogewa yana ɗago hannunta da ke cikin nashi ya sumbata. 

“Yaushe kika yi hankali haka?”

Dariya ta yi cikin kukan da take yi. 

“Aure akai mun…”

Shima dariyar ya yi yana hugging ɗinta. Yana jinjina wa rayuwa da ta kawo su inda suke. 

“Allah ya sanya miki albarka. Ina ƙaunarki sosai Zulfa…”

“Nima haka… Kai sauri kai ma mu yi maka aure….”

Dariya ya sake yi. Kafin ya ɗago Zulfa daga jikinshi. Shi kam aure da saura, sai ya gama jin komai ya tsaya mishi tukunna zai gayyato wata cikin rayuwar shi. Hannunta Dawud ya kama na dama, Tayyab ya kama ɗayan suka kamata suna fitar da ita daga cikin gidan. 

Sakin hannunta Tayyab yayi yana tsayawa a wajen. Yana kallon takun tafiyar su har Dawud ya ƙarasa da ita wajen Labeeb. Hannun Labeeb ya kamo ya saka na zulfa a ciki. 

“Allah ya sa aurenku ya zama sanadin ƙaruwar zumuncin mu da ƙaunar mu…ka riƙe ta da amana…”

Babu alamun wasa a fuskar Labeeb ya kalli Dawud ɗin. 

“Allah Ya bani iko…”

“Amin…”

Sai da ya sumbaci Zulfa a saman goshinta tukunna ya ɗan matsa yana kallon yadda take kuka sosai. Yana kallo Labeeb ya buɗe mata motar ta shiga. Ya zagaya shi ma ya shiga. 

Yana tsaye har sai da ya ga motar su ta juya tana fita daga cikin gidan. Ya sauke wani numfashi, a ƙasan zuciyarshi yake mata addu’ar alkhairi a sabuwar rayuwar da za ta tsinci kanta.

***** 

Fuskarta har ta kumbura saboda kukan da tayi. Idanuwanta zafi suke mata, ga kanta da take ji kamar ana buga ganga a ciki saboda ciwon da yake yi, ta kuma san kukan da ta yi ne. Zazzaɓi ruf a jikinta, ba ta damu da ta nemi ko panadol ta sha ba don ta san zazzaɓin ta ba na asibiti ba ne. 

zazzaɓin ta kishi ne kawai da yake cinta. Duk yinin ranar wankanta ɗaya, yanzun ma da ƙyar ta ja ƙafafuwanta zuwa toilet ta yi wanka ta fito, rasa kayan da za ta saka ta yi. Idanuwanta suka tsaya kan wata doguwar riga baƙa, plain ce, Labeeb ya siyo mata da suka je aiki Ghana. 

Fito da ita ta yi ta saka wa jikinta, mai ta shafa sai powder, ta naɗe kanta da siririn mayafi fari, ta sa hannunta kan cikinta tana kallon yadda fuskarta ta kumbura ta cikin mudubin. Kafin ta maida dubanta zuwa siririyar chain ɗin da ke wuyanta. 

Hannunta ta sa ta taɓa tana lumshe idanuwanta, tana jin komai na ranar da Labeeb ya saka mata sarkar na dawo mata, a irin lokacin nan ne, da bayan isha’i haka. 

*

Wanka ta fito jikinta ɗaure da towel ta zauna a gaban mirror tana shafa mai Labeeb ya turo ƙofar da sallama, a hankali ta amsa mishi. Kafin ya tako ya ƙaraso inda take, ta cikin mirror ɗin ta sauke idanuwan ta cikin nashi. 

“Sannu da zuwa…”

“Ke ce da sannu da zaman gida.”

Ya amsa yana murmushi tare da zura hannunshi a aljihu ya ɗauko wani ɗan akwati ƙarami, tana kallonshi ya buɗe, sai dai ba ta ga me ya ciro a ciki ba ya mayar da akwatin a aljihunshi yana saƙalo hannauwanshi duka biyun a wuyanta. 

Ware idanuwa ta yi da ta ga siririyar sarƙar da ya ɗaura mata yana dafa hannuwanshi kan kafaɗar ta, kamo hannunshi ta yi ta sumbata. 

“Ta yi kyau….nagode sosai.”

Harararta ya yi ta cikin mudubin. 

“Ba wani… Ban taɓa ganin ki da sarƙa ko ɗaya ba. Kawai wannan ya min kyau ne na siyo…. Na san ba kya so.”

Miƙewa ta yi tsaye ta fuskance shi, hannuwanta ta saka cikin nashi ta dumtse sosai. 

“Ban ɗauka kana lura ba…”

Goshin su ya haɗa waje ɗaya. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Ina lura da komai naki Tee… Ƙarami da babba… Komai ina lura. Nasan duk idan kika sa red janbaki fushi kike min saboda kin san bana son ganin komai a laɓɓan ki. 

Ba kya haɗa ido da ni in kin min laifin da kika san zan yi faɗa… Ranar na fi ganin ƙaunarki don a rikitani ko?”

Sakin hannunshi ta yi tana ja mishi hanci tare da yin dariya. Waɗannan ƙananan abubuwa ne da ba ta za ci yana kula ba. 

“Banda sharri… Ko yaushe ma ai ina nuna maka ƙauna.”

Turo leɓen shi ya yi gaba yana ɗaga mata gira. 

“Bana gani ni kam…”

Hannuwanta ta zagaya kan kafaɗarshi tare sa sumbatar shi a ko ina na fuskarshi. 

“Um ba laifi…”

Ya faɗi yana daƙuna fuska, kyau yai mata ba kaɗan ba, dariyar da ta yi ta sa shi dariya shi ma, kafin ya rungumeta a jikinshi yana shaƙar ƙamshinsabulun da ta yi wanka da shi. 

**** 

Buɗe idanuwanta Ateefa ta yi saboda zafin da take ji a ƙirjinta, kafin ta soma jero Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Duk soyayyar nan ta Labeeb, duk wannan kulawar daga yau raba su za ta yi da Zulfa. 

Sam hawayenta sun ki fitowa wannan karon, don ma tana ta jero Innalillahi wa inna ilaihir raji’un dano Allah ya kawo mata ɗaukin duhun kishin da take ji. Turare kawai ta iya ɗauka ta fesa wa jikinta. Ta samu waje ta zauna a gaban mirrow ɗin tana dafe kanta da ke dokawa da hannuwan ta duka biyun. 

Kamar cikin zuciyarta aka buɗe kofar, bata san ya akai ta ji buɗewar ƙofar ba. Haka sallamar da Labeeb ya yi ta iso cikin kunnuwanta. Sai yanzun take jin idanuwanta na ƙara mata zafi da wasu hawaye masu ɗumin gaske da suke tarar mata.

Zuciyarta na wani irin tafasa. Hawayenta nata ne ita kaɗai, hawayenta da Labeeb kawai za ta iya raba su. Shi kaɗai za ta iya bari ya gansu a fuskarta banda Zulfa. In ba tsautsayin da ba ta fata ba, Zulfa ba za ta taɓa ganin wannan ɓangaren nata ba. 

Don haka ta ja wani irin numfashi tana fitar da shi tare da blinking idanuwanta ta mayar da hawayen da ke gab da zubo mata. Za ta jira su, Labeeb zai shigo da kanshi ya sameta. 

**** 

Tunda suka taho bai ce mata komai ba, yana jin sautin kukan ta ƙasa-ƙasa. Waje ɗaya ya tsaya ya siya kaji. Tukunna ya sake komawa sai kuma yanzun da suka shigo gida. 

Ledojin ya riƙe da ɗayan hannunshi ya zagaya ya buɗe wa Zulfa ƙofar. Hannunta ya kamo, ba ta yi musu ba ta fito daga motar ta tura murfin ta rufe. Hannunta na cikin nashi ya jata suka nufi cikin gidan. 

Wani irin dokawa zuciyarta take kamar za ta fito daga ƙirjinta. Ba wannan ba ne karo na farko da ƙafafuwanta suka tako gidanshi, amma yadda take jin sautin takunta a cikin shi yau ya sha banban da na ko yaushe. 

Har hannunshi dake riƙe cikin nata ya mata wani ɗumi na daban. Gidanta ne nan, gidan mijinta, ba hannun Labeeb ba ne kawai cikin nata, ba hannun yayanta da ta girma da dakon soyayyarshi ba ne kawai yake riƙe cikin nata, hannun mijinta ne. 

Ba ta yi ƙoƙarin tsayar da hawayen da suka zubo mata ba, don ba na baƙin ciki ba ne ba, na farin cikin da mamakin matsayin da yau ta taka a rayuwa ne. A bakin ƙofa yasa hannu ya murɗa handle ɗin ya tura tare da yin sallama. 

Shiru ba a amsa ba, ba ta kuma ga Labeeb ɗin ya jira a amsa sallamar ba, don ƙafa ya sa ya mayar da ƙofar ya tura, ya ja hannunta suka nufi sashin da ƙafafuwan benen suke, kafin ya taka yana ɗan juyowa ya ga ta hau. 

Sai da ta sauke ajiyar zuciya tukunna ta bi shi suka soma hawa, don ba sosai take ganin komai ba ta cikin mayafin daya rufe mata fuska. Har suka ƙarasa can sama ya ja ta zuwa bedroom ɗinta ya tura ƙofar da Sallama nan ma. 

Shiga suka yi , sai lokacin Labeeb ya saki hannun Zulfa yana kallon tafin hannunshi kamar hakan zai sa shi fahimtar abinda ya banbanta da riƙe hannunta da ya yi yau. Abinda ya banbanta a yanayin tun ɗazu da Dawud ya sa hannunta cikin nashi. 

Takalmanshi ya cire, ya ajiye ledojin kan kafet yana murza goshin shi da yatsun hannunshi. Ya kasa gane yanayin da yake ji, ya kasa fahimtar abinda ya canza daga ɗaura aurenshi da zulfa zuwa yanzun. 

Sautin ajiyar zuciyarta ya sa shi juyawa da sauri, tana tsaye a bayanshi. Hannu ya sa yana ɗaga abinda ya lulluɓe masa fuskarta tun ɗazu. Idanuwanshi yake yawatawa kan fuskarta da hawayen da suka jiƙa bai hana ta yi mishi kyau ba. 

Wasu hawayen suka sake zubo mata, da sauri ya kai hannunshi yana goge mata su. 

“Bana son kukan nan… Na bar ki ne tun ɗazu saboda na ga it’s normal mata su yi kuka in za su bar gida… In ba ciwon kai kike son yi ba ya isa haka.”

Ba ta san me yasa maganar shi ta sake ba hawayenta damar zubowa ba. Ta kasa tsayar da su duk da tana son yin hakan. Runtsa idanuwanshi ya yi ya buɗe su akanta, kukan ta ba tun yanzun ba tsaya mishi yake a rai. 

Fuskarta ya tallaba yana son idanuwanta su sauka cikin nashi amma sam ta ƙi yarda, tana tsoron yadda take jinta cike da rauni haka ba za ta iya ɓoye yanayin son shi ba. Sirrinta zai iya nunawa cikin idanuwanta. 

“Ki kalleni Zulfa… Ni ne fa. Ba baƙon waje kike ba… Babu abinda ya canza. Dan Allah ki yi shiru kar kanki ya yi ciwo…”

Maimakon ta kalle shin yadda yake so sai ma lumshe idanuwanta da ta yi tana ba wasu hawayen damar zubowa. Sakin fuskarta yayi yana ja ta ya rungume a ƙirjinshi. Sosai take kuka tana riƙe shi kamar zai ɓace mata. 

Burin zuciyarta ya cika, sai dai rayuwarta ta samu gurgunta. Ba ta da abinda kowace macce ke tinƙaho da shi. Ba ta da abinda kowace macce ke alfaharin zuwa gidan mijinta da shi. Jin yadda kukan ta ke tsananta ne yasa shi ƙara riƙe ta sosai yana jin kamar ya maida ta cikin jikinshi in har hakan zai sa ta daina kukan nan da take yi. 

“Komai zai yi daidai zulfa… In sha Allah komai zai yi daidai…”

Sun kai mintina goma a haka yana maimaita mata abu ɗaya kafin ya samu ta yi shiru. Har ƙofar toilet ya rakata ta wanke fuskarta ta fito tukunna cikin sanyin murya ya ce, 

“Za ki iya zuwa mu je wajen Ateefa ku gaisa ko zamu zauna ki ɗan ƙara hutawa?”

Muryarta a dishe ta amsa da, 

“Mu je.”

Leda ɗaya ya ɗauka ya nufi ƙofa ta bi bayanshi suka sauka ƙasa. Abinda ya sa bai tsaya da ita ba don kukan da take ne ɗazu. Sai da ya rakata ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon da ke ƙasa tukunna ya taka ya ƙarasa bedroom ɗin da Ateefa take ciki da sallama. 

A zaune ya sameta, ta amsa mishi sallamar da ya yi. Murmushi ya ƙwace mishi ganin rigar da ke jikinta, ta mishi kyau duk da fuskarta da take a kumbure. Ƙarasawa ya yi inda take zaune. 

Ledar ya ajiye mata akan mirror ya kai hannunshi yana shafa fuskarta da ta ci kuka. Baice komai ba ya kama hannunta ya ɗagota ta miƙe tsaye tukunna ya rungumeta a jikinshi saboda bai da kalaman da zai faɗa mata. 

Bai da abinda zai rage mata zafin da yasan tana ji, sai kulawarshi da nuna mata cewar ƙara aurenshi bai canza matsayinta ba, tana sonshi, ya kuma san tasan yana sonta shi ma. Sai dai Shaiɗan zai fi samun damar ɗarsa mata wasiwasi yanzun da take cikin rauni. 

Shi ya sa sam baya son ba shi damar hakan. Sumbatar gefen fuskarta ya yi. Kafin ya kai hannunshi ɗaya kan cikinta yana shafawa. 

“Ina sonku sosai. “

Kasa amsa shi ta yi saboda yanayin da take ji da ba zai fassaru ba. 

“Zulfa na falo…”

Har lokacin ba ta ce komai ba, sai jikinta da ta zame daga nashi tana nufar ƙofa, binta ya yi a baya suka fito a tare suka ƙarasa falon, idanuwanta na kan Zulfa, wani kishi ne ya turnuƙe ta duk da ba ta ga fuskar Zulfar ba. 

Duk ta tsara har sannu da zuwa da Allah ya sa alkhairi za ta yi wa Zulfar, a cikin ranta ta gama misalta yadda za ta yi, amma kishin da take ji da ƙyar ta samu kujera za ta zauna nesa da Zulfa, Labeeb ya kama hannunta yana janta suka ƙarasa kujerar da Zulfa take. 

Shi ya fara zama sannan ya zaunar da ita a gefen shi. Yanayin yadda ta zauna kamar ƙiris take jira ta miƙe ya sa shi riƙe hannunta yana dumtsewa cikin nashi. Shi kanshi baisan me zai ce ba. Ya sha acting a films na mata biyu da nasihar da miji yake yi.

Amma yau ko maganganun da ya yi a fina-finan ya kasa tunowa, dama ba kalamanshi ba ne ba, hawansu ya yi. Wani irin shiru ya ziyarci falon kamar ka sa hannu ka dangwalo. Banda ƙarar tafiyar agogon da ke ɗakin da ke nuna musu cewar lokaci na tafiya ba ka jin komai. 

Sam ya rasa kalaman da zai amfani da su, ga shi zaune a tsakiyar matan da bayan mahaifiyarshi da Zainab suka fi kowa muhimmanci a rayuwarshi amma ya rasa abinda zai furta musu. Buɗe bakinshi ya yi kawai ba tare da ya san me zai faɗa ba, 

“Na rasa me zan ce muku… Bayan ina ƙaunar ku dukkan ku komai ya ƙi fitowa. Nasiha ya kamata in muku sai dai na rasa akan me…”

Jin ko motsi babu wadda ta yi a cikin su ya sa shi ci gaba. 

“Ina son Tee… Zulfa kin sani ina sonta sosai. Ko ba ta girmeki ba za ki girmamata saboda matata ce… Saboda ba zan ɗauki ki raina ta ba…. Saboda uwargidana ce…”

Ba sai ya maimaita mata ba, tambarin son da yake wa Ateefa na zuciyarta har ta mutu ba zai goge ba, din son Ateefa ya tarwatsa zuciyarta da ko shi da kanshi bai sani ba. Ba ta tsani Ateefa ba, don ko me Labeeb yake so ya girmi hakan a wajenta. 

Kishin Ateefa ba baƙo bane a wajenta, ba kuma zai zama abinda za ta ɓata lokacinta akai ba. Ta san raɗaɗin da ya fishi zafi, ta san rashin Ummi, ta ji rashin Sajda, ta ji zafin ƙaddarar rabuwa da darajarta da za ta mutu da shi. Kishin da ba zai canza komai ba shi ne ƙarshen abinda za ta ɓata lokacinta akai. 

Ba sai Labeeb ya jaddada mata ba, ko da wasa ba ta da niyyar raina mishi mata. Za ta bata girma daidai iyawarta. Tana jin Labeeb ya gyara zama.

“Ki riƙe girmanki Tee… Amanar gidana a hannunki take tun kafin ta shigo. Ba zai canza komai ba… Bana son tashin hankali…gidan nan ba zai samu zaman lafiya babu haɗin kanku ba. 

Ta kowane fanni ƙaddara ta taɓa kowa a cikinmu. Ta kowane fanni rayuwa ta taɓa mu… Dukkanmu muna buƙatar zaman lafiyar. Muna buƙatar nutsuwar… Ba zan iya ni kaɗai ba… Ina buƙatar addu’ar ku Allah ya bani ikon riƙe ku da amana da kwatanta adalci a tsakanin ku…”

Yadda ya ƙarasa maganar yana sauke murya ne ya sa Ateefa kallonshi, ba ta son damuwar da take gani kwance a fuskarshi. Tana son mijinta, Labeeb shi ne komai nata. 

“In sha Allah…”

Ta furta, ɗan murmushi yai mata, tana kallon godiyar da yake mata cikin idanuwanshi duk da bai furta mata ba. Miƙewa ta yi tsaye ba tare da ta kalli Zulfa ba ta ce, 

“Sai da safe…”

Shi ma miƙewar ya yi don bai saki hannunta ba har lokacin. Tare suka wuce ya rakata. Ko ina jikinta ɓari yake don da ƙyar ƙafafuwanta suka kaita ɗaki, don ma Labeeb na riƙe da hannunta dam. Idanuwanta cike da tsoro take kallonshi. 

Muryarta na rawa ta ce, 

“Sai da safe…”

Girgiza mata kai ya yi yana janyo hannunta da take son ƙwacewa ya matso da ita dab dashi. 

“Karki fara… Please Tee… Karki kulle ni a waje…karki fara ɓoye min damuwarki…”

Wani irin kuka marar sauti ne ya ƙwace mata. Fuskarta ya tallaba yana sumbatarta tare da faɗin, 

“Wannan shi ne mu… Ni da ke… Tare muke raba komai. Karki ɓoye mun…”

Kuka take tana ɗaga mishi kai. Zafin kishi daban yake da komai. Wasu cikin matan da suka taɓa shiga halin da take ciki yanzun za su fahimci abinda take ji. 

“Ka barta ita kaɗai a baƙon waje… Ka tafi.”

Ta Faɗi hawayenta na sake zuba da ciwon gaske. Yana son tafiyar sai dai ba ya son barinta a wannan yanayin, sake rungumeta ya yi gam a jikinsa. 

“Ya zan yi? Kina kukan nan…hankalina ba zai kwanta ba Tee… In na barku a yanayin da kike ciki.”

Zamewa ta yi daga jikinshi tana kama hannuwanshi duka biyun ta kai bakinta ta sumbata. 

“Kar ka damu…komai zai yi daidai. Babu abinda zai same ni… Zai samu babynmu in sha Allah…”

“Kin tabbata?”

Ya buƙata yana tsare ta da idanuwanshi cike da damuwa. Sai da ta duba zuciyarta don bata son ta yi mishi ƙarya. Har cikinta take jin komai zai musu daidai. Kishin da take ji bashi ba ne ƙarshen duniyar su. Kamar yadda ba shi ba ne farkon ta. 

“Yau mun canza…duniyar mu ta canza. Saidai ba baƙon abu ba ne ba. Kullum canzawa muke ta fannin da muke ganewa da wanda ba ma ganewa… Karka daina sona… Please… Shi kaɗai ne canjin da bazan iya jurewa ba.”

Idanuwanshi ya sauke cikin nata, ya kamo hannunta ya ɗora kan ƙirjinshi.

“In dai tana dokawa… Da sonki za ta ci gaba da rayuwa tee… In sha Allah…”

Kai ta ɗan ɗaga mishi, sai da ya sake sumbatarta, zuciyarta na gaya mata inda bakinshi zai kai banda kan nata duk daren yau. Runtsa idanuwanta ta yi saboda ciwon da zuciyarta take yi. 

“Ina ƙaunarki sosai…ki kula min da ku… Sai da safe.”

Ya faɗi tukunna ya juya, da dukkan wani abu da take da shi ta samu ta jure fitarshi ba tare da ta riƙo shi ta roƙe shi da kar ya barta ba. Kar ya raba mata kanshi da wata, sanin ba don ita kaɗai aka halicce shi ba bai canza mata komai ba.

Kan gadon ta ta faɗa ta saki wani irin kuka mai cin rai. Bata san iya lokacin da ta ɗauka ba kafin ta miƙe tana goge fuskarta. Wayarta ta lalubo da earphones ta saka ta buɗe karatun Ƙur’an ta ƙure maganar. Tun tunanin inda Labeeb yake da abinda yake yi na tafasa mata zuciya da dukkan jikinta. 

Yana hanata fahimtar karatun da take saurare har ta samu ta soma nutsuwa tana jin karatun cikin muryar Sheikh Mahir da ke ratsa zuciya. Har ta samu komai ya fice mata a kai da zuciya banda karatun. Duk da bacci ko alamun shi ba ta ji balle ta sa ran zai ɗauke ta. 

<< Rayuwarmu 46Rayuwarmu 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.