Yana fitowa wanka wannan karon da towel ɗin a jikinshi ya fita zuwa ɗakinshi ya sako kaya tukunna ya dawo ya ɗauki wayarshi da ke gefen Zulfa da ke bacci. Sumbatar ta ya yi sannan ya fita daga ɗakin zuwa falon da ke saman ya zauna.
Ateefa ya kira har sau shida ba ta ɗauka ba. Ya duba agogo ya ga takwas da kwata. Text yai mata yana rasa kome zai ce banda,
'Ya kuka tashi?'
Zama ya yi yana jiran tara ta ƙarasa ya sauka kasan ya dubata. Lambar Asaad ya kira, bugu ɗaya ya ɗaga da. . .