Skip to content
Part 49 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Yana fitowa wanka wannan karon da towel ɗin a jikinshi ya fita zuwa ɗakinshi ya sako kaya tukunna ya dawo ya ɗauki wayarshi da ke gefen Zulfa da ke bacci. Sumbatar ta ya yi sannan ya fita daga ɗakin zuwa falon da ke saman ya zauna. 

Ateefa ya kira har sau shida ba ta ɗauka ba. Ya duba agogo ya ga takwas da kwata. Text yai mata yana rasa kome zai ce banda, 

‘Ya kuka tashi?’

Zama ya yi yana jiran tara ta ƙarasa ya sauka kasan ya dubata. Lambar Asaad ya kira, bugu ɗaya ya ɗaga da faɗin, 

“Ango…”

Runtsa idanuwa yayi yana buɗe su, Asad ya raina shi, in ya nuna baya so ci gaba zai yi. 

“Ya kuka tashi? Ya jikin Mamdud?”

“Alhamdulillah… Da sauƙi sosai. Na san dai yau ba za mu ganka ba ko?”

Ɗan jim Labeeb yayi. Baya jin zai fita ko ina. Dariya Asaad ya yi. 

“It’s ok… A gaishe da ‘yan gidan duka. In Yaya Mamdud ya tashi zan faɗa mishi ka kira…ga Anees.”

“Hello Yaya ina kwana?”

“Lafiya ƙalau Anees… Ya gajiya?”

“Babu fa… Zee Zee tace za ta kira ka da sun sauka…da sassafe suka tafi tasan ba ka tashi ba.”

Jinjina kai Labeeb ya yi. 

“Zan yi mata text yanzun nan In sha Allah…”

“Chaii Asad…ba kai ya kira ba ne wai?”

Labeeb yaji Anees na faɗi a tsawace. 

“Kaji… Maza ku tashi ‘yan asibitin da safen nan. Ka ga sai su tattara su sallame ku ba shiri.”

“Asad ne fa…wai zai yi magana da kai. Shi ne zai cire min kunne…ba zai bari in gama magana in ba shi wayar ba.”

Dariya Labeeb ya yi, sarai yasan kaɗan da aikin Asad ne, kafin ya yi magana ya ji muryar Asad na cewa, 

“Wayata ce dai ko? Nawa ka cika aka siya? Da na ce kaban sai ka bani abu na ai.”

“To rasa kunya… Ba ka san ya girmeka bane ba?”

“Mummy ta ce minti sha biyar ne tsakanin mu.”

“Ko ma minti ɗaya ne…”

“Umm me ma zance maka ne?”

“Ni kake tambaya?”

Labeeb ya faɗi yana girgiza kanshi. Asad sai addu’a.

“Ba ma zai yi a waya ba… Idan ka zo gobe in Allah ya kai mu na faɗa maka.”

“To… Allah ya kai mu. Ku kula da kanku.”

Kafin ya kashe wayar yana jin Asad na faɗin, 

“Yaya yace ka kula da ni… Ka koma gida ka ɗauko min takalman nan kuma… Yaya ne ya faɗa.”

Dariya kawai yayi ya kashe wayar. Yana miƙewa, a hanyar shi ta sauka ƙasa ya yi wa Zainab text. 

‘Allah ya kai ku lafiya. Banda rigima, kuma kar in ga ƙafarki sai nan da wata shida. Yawon ya yi yawa.’

Kafin ya sa wayar a key har ta yi reply. 

‘Amin. Wata shida? Hu’um…’

‘Gidan ku Zee Zee.’

Dariya ta turo mishi. Ya sa wayar a key ya mayar aljihunshi ya ƙarasa sauka kasa ya nufi ɗakin Ateefa, ya ƙwanƙwasa kafin ya tura tare da yin sallama. 

***** 

Da ƙyar ta iya saukowa daga kan gado saboda ciwon kan da rashin baccin da ba ta yi ba jiya ya saukar mata. Tunda ta yi sallah ta watsa ruwa take nan kwance kan gadon. Sauke numfashi ta yi tana miƙewa tsaye. 

Doguwar rigace a jikinta ta naɗe kanta da mayafin rigar. Ko mai ba ta shafa wa jikinta ba ballantana kwalliya. Fuskarta fayau haka ta fito daga bedroom ɗin ta nufi kitchen. Mai aiki ta samu tana fere dankali. 

“Ina kwana…”

“Ina kwana… Sannu da aiki.”

Ateefa ta amsa tana ƙarasawa cikin kitchen ɗin. Ƙara ɗibar dankalin ta yi ta ƙara yawanshi tun da har da Zulfa. Sannan ta bar mata tana ƙarasawa ta buɗe fridge ta ɗibo naman da za a yi farfesu da shi ta ajiye. 

Ita ta haɗa komai na farfesun daidai taste ɗin da Labeeb ya fi so tukunna ta bar wa mai aikin don ta ƙarasa. Tana komawa ɗakin ta hango wayarta na haske kan gado. Sa’adda ta ƙaraso ta yanke. Missed call ɗin Labeeb har guda shida. Murmushi ta yi kafin wani abu ya soki zuciyarta sanin daga inda yake kiranta ɗin. 

Sai ta tsinci kanta da kasa mayar mishi da kiran, wayar ta jefa kan gado ta koma ta kwanta abinta. Ganin ta sake yin haske ya sa ta ɗaukowa ta duba. Text ne ta buɗe:

‘Ya kuka tashi?’

Key kawai ta sa wa wayar ta sake mayarwa ta ajiye. Ko sallar Subhi ba ta ji ya fito ba. Ta san bai je masallaci ba, amarci na mishi daɗi balle ya yi tunanin tashin ta ita ma kamar yadda ya saba. Har ƙasan zuciyarta take jin canjin da ya shigo musu. 

Ƙwanƙwasa ƙofa ta ji an yi, kafin ta buɗe baki Labeeb ya turo tare da yin sallama. Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi, sanye yake da wando baƙi, rigar shi ta ciki blue mai cizawa sai vest baƙa daga sama. Yayi wani irin fresh da shi. 

Tunanin komai ta ji ya ɓace mata, zuciyarta babu komai sai son shi da kewarshi da ta yi jiya. 

“Ina kwana.”

Ta faɗi a sanyaye. Tsare ta ya yi da idanuwan shi ba tare da ya ce komai ba. 

“Yanzun zan maka reply dama…”

Ɗaga girar idanuwanshi ya yi duka biyun, sauke numfashi ta yi. 

“Ok ban yi niyyar reply ba”

“Ko kefa…”

Ya faɗi yana ƙarasawa ya zauna a gefenta. Kallonta ya yi cikin fuska

“Ya kuka tashi?”

“Alhamdulillah… Kai fa? Ku fa?”

Hannunshi ya sa kan cikinta madadin amsar tambayar da ta yi mishi. Kamar zai ji motsin babyn shi a cikinta. 

“Yaushe zai fara motsi?”

Ware idanuwanta ta yi. 

“Ni ma bansani ba fa.”

Har lokacin hannunshi na kan cikinta yana jin sonta da na abinda yake ciki na ƙara zauna mishi a zuciya. 

“Ku zo mu karya…”

Ateefa ta faɗi tana kallonshi. Kai ya ɗaga mata yana miƙewa.

“Barin kira Zulfa…”

Ba ta ce komai ba har ya fice daga ɗakin. Miƙewa ta yi ta nufi dressing mirror ɗin . Kwalliya ta yi sosai sannan ta miƙe ta sake kaya zuwa doguwar riga ta less, milk da ya karɓi jikinta tukunna ta nufi kitchen, da kanta ta shirya komai a dining area ɗin falon ƙasan. 

Tana zama Labeeb da Zulfa suka ƙaraso, hannun Zulfa da ke cikin nashi ta fara sauke idanuwanta akai. Wani abu na mata tsaye a wuya. Ba yau ta fara ganin hannunshi cikin na Zulfa ba, ba dai za ta daina jin abinda take ji ba, ƙaruwa ma ya yi. 

Da kanshi ya janyo ea Zulfa kujera ta zauna, sannan ya zauna shi ma. 

“Ina kwana…”

Zulfa ta gaishe da Ateefa da sai lokacin ta kalleta, banda pink ɗin jan baki babu wata kwalliya a fuskar Zulfa ɗin, amma tai wani irin kyau. Ta san kyau halitta ne, wani ya fi wani dama, amma ba ta zaton a duk family ɗin su Labeeb akwai wanda ya kai Zulfa kyau. Sai dai ko Zainab.  

“Lafiya ƙalau… Ya kika tashi?”

“Alhamdulillah… Sannu da aiki.”

Ɗan ware idanuwa Ateefa ta yi. 

“Ba ma ni na yi ba kam.”

Ita ta miƙe ta zuzzuba wa kowa. Zulfa yunwa take ji sosai dama. Tas ta cinye dankalin da Ateefa ta zuba mata da tea. Labeeb ma ya ci sosai, yana kallon Ateefa da ke wasa da cokalinta cikin shayin. 

“Baki ci komai ba Tee.”

Ɗagowa ta yi ta girgiza mishi kai. 

“Wallahi ɗanwake kawai nake son ci.”

Murmushi Zulfa ta yi tana kurɓar tea ɗinta, don yanayin da Ateefa tai maganar kamar ɗanwake ya fi komai muhimmanci yanzun a wajenta ya ba ta dariya. Kofin ta ajiye ta kalli Labeeb. 

“Yaya jifan ɗanwake ya kamaka…”

Ta ƙarasa maganar tana dariya. Harararta Labeeb ya yi, yanayin fuskarshi ya sa Ateefa yin dariya ba ta shirya ba, abinda ta kwana biyu ba ta yi ba. 

“Seriously? Ni ban iya wani ɗanwake ba…”

“Ba wuya zan koya maka…”

Zulfa faɗi tana ci gaba da dariya. Ateefa ya kalla da ta tsura mishi idanuwa. Cikinta ta kalla tana maida hankalinta kanshi. 

“Baby ɗanwaken ka yake jin ci.”

Dariya zulfa ta ci gaba da yi. 

“Ki fita idona zulfa… Ni ba ɗanwaken da zan yi. Kisa mai aiki ta dafa miki.”

Ya ƙarasa maganar yana ɗaure fuska. Shagwaɓe tata fuskar Ateefa ta yi. 

“Ta je gida ta dawo…”

Zulfa da ke dariya ya kalla yana daƙuna mata fuska. Miƙewa ta yi har lokacin dariya take yi. 

“Ina kitchen ɗin in dafa miki?”

Ware idanuwa Ateefa ta yi. 

“Kai… A’a wallahi. Kina son a cini tara ko? Wa ya ce amarya na aiki.?”

Cikin fuskar da babu alamar wasa ta ce, 

“Yaya ya ce an hanaki aiki… Duka minti nawa ne…Zan yi.”

Labeeb Ateefa ta kalla don ya kawo mata ɗauki. Ita kam ba da ita za a yi wannan ɗanyane aikin ba, amarya da shiga kitchen washe garin daren aurenta. Ɗan ɗaga kafaɗa ya yi yana shan tea ɗin shi. 

Juyawa Zulfa ta yi. 

“Yaya ina kitchen ɗin?”

Nuna mata hanyar ya yi ta wuce abinta. Kallon shi Ateefa ta yi. 

“Me na yi?”

Ya tambaya yana turo mata laɓɓanshi da suka yi mata kyau. 

“Da na kalle ka ina nufin kai mata magana ne. Bawai ka nuna mata hanyar kitchen ba.”

Daƙuna mata fuska kawai ya yi. Shi bai ga komai a ciki ba. Ita kam Ateefa da sam ba haka ta hango yau za ta tafi ba. Ba shiri suke da Zulfa ba tun da ta auri Labeeb, banda gaisuwa babu abinda yake haɗa su, sai tai watanni ma ba ta saka ta a idanuwanta ba. 

Duk kallon mai jin kai take wa Zulfa, amma yanzun ta soma ɗiga ayar tambaya akan hakan, duk da tasan kissa ta mata za ta iya yin abinda ta yi yanzun saboda Labeeb, amma yanayin Zulfa bai nuna za ta yi wani abin da ba ta yi niyya ba. 

In ma Labeeb ne ba sai ta yi wani abu ba, son da yake mata ko ita kanta Ateefa tana jinjina mishi. 

“Don Allah ka je ka ce ta fito… In wani ya zo ya ganta fa?”

“Ki yarda in na ce miki ba ta damu ba… Zulfa ba ta da matsala da wannan… Ina sonki ta sani… Za ta taya ni kula da ke ne.”

Kamar za ta yi kuka ta kalli Labeeb. 

“Ina son ka… Sosai. Amma ba na jin zan iya danne kishina in mata abinda take shirin yi min yanzun… Ba na so mu fara abinda dukkan mu ba za mu ɗore da shi ba.”

Kujerar shi ya ja ya matsa dab da ita sosai. Sai da ya sa hannunshi ya goge jan bakin da ta saka yana kallon kwalliyar da ke fuskarta.

“Ba sai kin yi ba… Ba na so ki yi duk wani abu da zai takura ki a zamana da ke ko zaman ki da ita… Ba na son ki yi komai banda zaman lafiya da ita daidai iyawarki. Shi kaɗai na ce ki yi Tee… Kin ji ni?”

Kai ta ɗaga mishi, wani abu ya tsaya mata a wuya. Tana addu’ar Allah ya rage mata kishin nan ko ya yake. Hannu ya sake sawa yana ƙara goge mata laɓɓanta. Ta ture shi. 

“Ka daina goge min kwalliya.”

“Nafi son ganinki a haka.”

“Me yasa baka goge na Zulfa ba… Sai ni da kwalliya ba ta ma kyau ko?”

Dariya yake sosai, kau da kai ta yi gefe don takaici. Da ƙyar ya iya controlling ɗin kanshi. 

“Ba… Ba haka ba ne…”

Ya faɗi, fushin da take na ƙara ba shi dariya. 

“Tee… Na fi son ganinki a haka… Ba kwalliya bace ba ta miki kyau… Kyanki ne yafi ƙarfin kwalliyar… Bansan ya zan ce ki gane ba. Tun da Zulfa ta tashi ta soma wayau nake ganin fuskarta da kwalliya. 

Bawai ba ta kyau in babu ba… Amma kwalliyar ya zama wani ɓangare ne nata. Babu kwalliya zuciyata ta buɗe ido dake… Like kyan da kike min a hakan ba zai faɗu ba… Naturally… Ba kwalliyar bace ba ta miki kyau. 

Rashin yinta ɓangarene a tare da ke da bana so ya canza… Kin gane?”

Murmushi ta yi tana kallon shi da sauke ajiyar zuciya. 

“El-Labeeb kalaman ka ko? Hmm ko bangane ba zuciyata ta gama yarda ai.”

Ja mata hanci ya yi ta ture hannun shi. Hira suke Zulfa ta ƙaraso da sallama. Plate ɗin ɗan waken da ke ta jamshin soyayyen mai da ya sha albasa ta ajiye wa Ateefa da har miyanta ya soma tsinkewa. 

“Sannu da aiki… Na gode sosai wallahi.”

“Kar ki damu… A ci lafiya.”

Zulfa ta faɗi tana ɗorawa da, 

“Bari in je… Ban gaisa da su Mami ba.”

Ta ƙarasa maganar tana fita daga falon, kai kawai Ateefa ta ɗaga mata don ta cika bakinta da ɗanwaken da take jin daɗinshi kamar ta yi tsalle. Hannu Labeeb ya kai zai ɗauki cokalin ta janye plate ɗin. 

Miƙewa ya yi ya zagaya, itama ta miƙe tsaye tana rugawa ɗayan ɓangaren. Sai da ta haɗiye na bakinta tukunna ta matsa tana janye plate ɗin ganin ya taho

“Kai ka dafa min? Ka ga ka barni in ci abina cikin kwanciyar hankali… Ka tafi wajen matarka.”

Ware idanuwa Labeeb ya yi. 

“Lallai Tee… Korata kike saboda ɗanwake… Don Allah bani…guda biyu kawai zan ɗauka.”

Girgiza kai ta yi ta sake ɗiba ta zuba a bakinta. Zagayawa ya yi ya riƙeta dam ya kama plate ɗin. 

“Wayyoo… Allah ka sake ni. Wai ka ji ba kwaɗayi fa…”

Ɗiba ya yi ya sa a bakin shi. Taunawa ya yi tare da daƙuna fuska. 

“Babu daɗi ma…”

Ture shi ta yi tana ƙwace plate ɗin ta zauna. Hannu ya sake kawowa ta janye.

“Ba cewa ka yi ba daɗi ba?”

Dariya ya yi. 

“Yi haƙuri…”

Saboda fitinar Labeeb zama ya yi suka ci tare. Kuma ya riƙe ciki yana yamutsa mata fuska. 

“Cikina ya cika da yawa…”

“Madalla… Ba yunwa kake ji ba ai”

Miƙewa ya yi yana turo ciki tare da daƙuna fuska. Ba za ta iya taɓarar Labeeb ba. Plate ɗin ta ɗauka ta wuce kitchen tana barin shi a wajen. Ko da ta kai ta ajiye ɗakinta ta wuce. 

Ɗan zama ta yi ta huta tukunna ta kwanta, har ranta tai wa Zulfa addu’a don ta ji daɗin ɗanwaken. Rabon da ta ci ta ƙoshi haka har ta manta. 

“Allah ka ba ni ƙarfin danne kishi mu zauna lafiya… Kai ka halatta auren mata ba ɗaya ba har huɗu… Allah ka ba mu haƙurin zama da juna.” 

Lumshe idanuwanta ta yi, bacci mai karfi na ɗaukarta.

Labeeb ma sama ya hau ya samu Zulfa zaune kan gado, gefenta ya zauna. 

“Cikina kamar zai fashe…”

Kallon shi Zulfa ta yi. 

“Ɗanwaken ka cinye mata ko?”

“Ni ki barni… Cikina ya cika da yawa.”

Girgiza mishi kai ta yi tare da kai hannu tana ja mishi kunne. Ture ta ya yi ta sake binshi, pillow ya ɗauka ya kwaɗa mata yana yamutsa fuska. 

“Ki barni na ce ko?”

Dariya ta yi ta sake ja mishi kunne, ganin ya juya kanta gaba ɗaya ya sa ta yin ihu. 

“Yi haƙuri… Wallahi na bari.”

Girgiza kai yake yi. 

“Ba ki isa ba kuma…”

Janyo ta ya yi tana ture shi tare da yin dariya. Dole ya saketa dln cikin shi ya cika da yawa. In ya biye Zulfa wahala zai sha. Kwanciya ya yi yana shafa ciki, gefenshi ta kwanta, suna hira. Har bacci ya ɗauke su. 

Bayan Sati Biyu

Wani irin kwanciyar hankali suke ciki da ba zai faɗu ba. In Ateefa ta ce kishinta da minti ɗaya ya ragu ƙarya take. Sai dai ta canza akalar kishin zuwa ganin ta yi abinda shi wanda take kishin akanshi yake so. Wato zaman lafiyar su. 

Zulfa kam ko da ba ta so ba ta san yadda za ta ji haushinta ba. Sati biyun nan da suka yi ta fara gane halayyarta, ko kaɗan ba ta da matsala kamar yadda Labeeb ya faɗa mata. 

Tun bata sakewa su yi magana har ta ɗan fara, don Zulfa ita za ta ja ta da hira. A ɓangaren Labeeb da Zulfa wata irin soyayya suke mai nutsuwa. Shi kanshi sai yanzun yasan hankalin shi ya kwanta. 

Sai yanzun yasan ya nutsu ta fannoni da dama, yana jin ya fi kowanne namiji sa’ar samun mata biyu da suke matuƙar son shi. Ƙarin kwanciyar hankalin shi na tare da samun sauƙin da Mamdud yake yi, duk da ba a sallame shi ba har yanzun amma yana takawa da sanduna guda biyu. 

Su kansu su Asad akwai nutsuwa da kwanciyar hankali, duk da ƙasan duk wannan akwai kewar ƙaninsu da za ta zauna tare da su har ƙarshen rayuwarsu. 

A sati na uku Zulfa ta koma makaranta. Kasancewar Labeeb ya tafi Abuja za su ƙarasa wani shooting da ɓangaren shi kawai ake jira a ƙarashe fim ɗin, ita kuma ba tuƙi ta iya ba, ya sa Tayyab yake zuwa har gida ya ɗauke ta. In an tashi ya dawo da ita. 

***

Kallon Dawud da Tayyab Mami take da zuciyarta ke dokawa tun da Dawud ɗin ya kirata a waya ya ce zai zo akwai maganar da yake son su tattauna. 

“Ka min magana mana Dawud.”

Sauke numfashi Dawud ya yi ya juya ya kalli Tayyab, kai ya ɗan ɗaga mishi alamar ya yi magana. Duka hankalin shi Dawud ya nutsar akan Mami kafin ya soma cewa,

“Mami a duk lokacin nan kina tare da mu… Lokutan damuwar mu da suka fi nutsuwarmu yawa… Ba ki taɓa gajiyawa ba. Kin so mu, kina kan son mu da ina tunanin Ummi jininta dake yawo a jikin mu kawai za ta nuna miki…”

“Dawud…”

“Mami dan Allah ki bari in gama… Muna ƙaunarki… Dukkan mu muna son ki sosai. Na yi magana da Zulfa… Haka ma Tayyab… Mami don Allah kar ki ce a’a. Komai da kanki kike mana… Ban taɓa roƙon alfarma a wajen ki ba. 

Ki auri Abba!”

Kallon Dawud mami take zuciyarta na ƙara dokawa, kunnuwanta na amsa kalaman shi na karshe. Da sauri Tayyab ya ɗora da, 

“Don Allah mami kar ki ce a’a… Ki auri Abbanmu…ba mu yarda da kowa tare da shi ba sai ke…wata zai auro… Ba mu jima da samun kwanciyar hankali ba. 

Ba za mu bari wata ta sake shigowa ba.”

Hawayen da suke cike da idanuwan Mami suka zubo. Ta rasa ko me take ji, ta rasa ko me za ta ce wa su Dawud da suke kallonta kamar amsarta na tattare da farin cikin su. Kamar yadda suka faɗa, Allah ne kaɗai ya san kalar ƙaunar da take musu. Don Shi ya haɗa ta a zuciyarta. 

Sai da ta sa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata tukunna ta ce 

“Ya zan yi da ku? Me zan ce?”

“Kice Eh… Ki ce kin amince za ki auri Abba.”

Dawud ya faɗi yana murmushi don yasan sun ma gama samun nasara. 

“Shi Abban naku ne ya ce aure zai yi?”

“Mamii mana… Ke dai ki ce kin yarda.”

Tayyab ya faɗi fuskarshi ɗauke da fara’a. A hankali Mami ta ɗaga musu kai. 

“Yes!”

Tayyab ya faɗi, Dawud na murmushi ya miƙe. 

“Bari in je wajen Abba….ya ce min zai fita.”

Kafin su amsa shi ya wuce. Zuciyarshi a nutse yake jinta, rayuwar shi yake jin ta kowanne fanni a nutse take tafiya. Ko a mafarki bai taɓa sa ran irin wannan kwanciyar hankalin ba. Duk da yasan ba dawwamamme ba ne, don akwai jarabawa a kan kowanne ɗan Adam. 

Da sallama ya ƙwanƙwasa ɗakin Abba. Ya ce mishi ya shigo, turawa ya yi ya samu kujera ya zauna suna gaisawa da Abba. 

“Ba ka je aiki ba?”

“Sai ran Monday ɗin nan mai zuwa in sha Allah zan koma. Hutun bai ƙare ba Abba…”

Kai Abba ya jinjina. Sakkowa Dawud ya yi daga kan kujera yana tsugunnawa a gaban Abba. 

“Abba alfarma na zo roƙa… Don Allah kar ka ce min a’a.”

Da mamaki Abba yake kallon Dawud da ya ci gaba da faɗin, 

“Ka auri Mami…”

Sai da Abba ya ji zuciyarshi tai wani irin dokawa. Har ƙasan zuciyarshi tsoron kalmar da Dawud ya furta yake yi, ɗagowa Dawud ya yi yana nazarin fuskar Abba da bayyanannen tsoro yake a shimfiɗe. 

“Mami kaɗai muka yarda da ita a tare da kai. Mami ce za ta riƙe ka kamar Ummi… Ta riƙe mu kamar ‘ya’yanta Abba… Don Allah kar ka ƙi.”

Ya kai mintina goma yana tauna maganar da Dawud ɗin ya yi. Ya manta rabon da ya yi musu wani abu, ya manta rabon da ya sa su farin ciki, rabin rayuwarsu bai yi ta tare da su ba. In har auren Mamin su shi ne farin cikin su zai yi. 

“In har aurenta shi ne farin cikin ku na amince Dawud…”

“Kaima naka farin cikin ne in sha Allah…Na gode Abba… Cikin satin nan fa za a yi bikin.”

Kai kawai Abba ya iya ɗaga wa Dawud saboda kewar Aisha da ta lulluɓe shi, da girman laifin da ya yi mata, da lokaci ya riga ya ƙure balle ya roƙi gafafarta. Addu’a yake jero mata cikin zuciyarshi, kafin Dawud ya sa hannu a aljihunshi ya zaro wata takarda ya miƙa wa Abba. 

Cikin mamaki Abba ya karɓi takardar yana juyawa. Ganin ‘Auwal’ rubuce a jiki cikin rubutun Aisha da ko daga bacci ya tashi zai gane shi ya sa zuciyarshi dokawa kamar za ta fito daga ƙirjinshi. Jikin shi babu inda ba ya ɓari. 

Hannunshi na rawa ya soma warware takardar. Miƙewa Dawud ya yi, bai tsaya yi wa Abba sallama ba don ya san ba ma jinshi zai yi ba ya ja mishi ƙofar. AC ɗin ɗakin bai hana zufa keto wa Abba ba. Buɗe wasiqar ya yi, hannunshi da ke ɓari ya hana shi karantawa don haka ya hau kan gadon sosai ya buɗe ta akai ya soma karantawa:

Assalamu Alaikum. 

Banda tabbas sa’adda za ka karanta wasiƙar nan ina nan a raye. Banda tabbas cewar wasiƙar za ta sameka kaima. Abu ɗaya nake da tabbas akai; rayuwarmu ba komai ba ce face tarin lokuta masu iyaka. 

Mutuwa bata jiran mu sai mun gama abinda za mu yi kafin ta riske mu, ko sallamar ta ba za mu ji ba. In wasikar nan ta same ka zan ji daɗi. In ba ta same ka ba rubutata na rage min yanayin damuwar da nake ciki. 

Zuciyata ba ta son komai a yanzun da nake rubutun nan da ya wuce sake ganin fuskarka ko na mintina biyar ne, bana jin son komai da ya wuce sake jin ɗumin mijina a kusa da ni. Na yi kewarka a duk wani numfashi da zan ja ba tare da kai ba. 

Kasancewarka mijina na ɗaya daga cikin abubuwan da suka yi min daɗi a zamana na duniya. Ƙaunarka na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da nake alfahari da su. Abinda ya faru bai canza yadda nake ji akanka ba. 

Ba zai taɓa canzawa ba. Ina son ka, kuma zan so ka har ƙarshen rayuwata. In kana karanta wasiƙar nan, ina ji sosai a jikina ba na tare da ku, kai kaɗai ka ke tare da yarana. Na san Dawud ya ba ka sa’adda ya dace ya ba ka ita. 

Na san kana tare da su a yanzun. Na ji daɗi, na yi farin ciki, ka kula da su. Kar ka dinga duba abinda ya faru, ba zai taimake ku ba. Ba ku da wani wadataccen lokaci, ka ƙaunace su dai-dai iyawarka kafin rabuwa da su ta har abada ta riske ka. 

Ka yafe min duk wani abu da na yi maka a zaman mu wanda na sani da wanda ban sani ba. Na yafe maka duk wani abu da kai min wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Ba lallai in iya maka magana ba bayan ka gama karantawa. 

Ba lallai ka sake jin muryata ba, ba lallai ka sake jin ɗumina a kusa da kai ba. Amma ni zan ji muryarka, zan ji ƙaunar ka, zan ji kusancinka ta cikin addu’arka. Kar ka bari har acan in ji kewarka, babu daɗi ko kaɗan. 

Na gode da ƙaunarka, na gode da kasancewa tare da kai. na gode da karanta wasiƙar nan, na gode da addu’ar da na san zan samu in har wasiƙar nan ta sameka. Ka kula min da yarana. Ina ƙaunarku fiye da yadda kalmar za ta taɓa fassaruwa. 

Matarka a Aljanna In sha Allah. 

Aisha. 

**** 

Hannuwa Abba ya sa ya dafe fuskarshi ciki yana wani irin kuka kamar ƙaramin yaro. Yana jin yadda wasiƙar Aisha ta ɗage mishi wani irin nauyi da tunda ya dawo hayyacin shi yake jinshi a tare dashi. 

Yafiyarta na nufin komai a wajen shi. Yafiyarta ta canza komai a tare da shi. Ya jima yana kukan rashin ta, kalamanta kamar ko da yaushe suna taɓa shi. Kafin ya ninke wasiƙar ya sumbaceta, ya tashi ya adanata inda wani abu ba zai same ta ba. 

Rayuwa kenan, haka take wucewa da saurin gaske, sai ka ga tamkar kana rufe idanuwanka ka buɗe ne ka ganka a wani lokaci da yanayi da zai saka mamakin yaushe ka zo nan? Yaushe rayuwa ta kawo ka nan? Kamar yadda Aisha ta faɗi, duka rayuwar cike take da tarin lokuta masu iyaka. 

Da duk numfashin da yake ja yana fitarwa da kusancin da lokacin nan yake zuwa iyakarshi. Canji yake ji ya sami sauran rayuwar da yake ciki ta fannin da yake nutsar da shi. 

“Allah ya jaddada Rahma a kabarinki Aisha. Kin kasance mace mai haƙuri da yafiya… Allah ya jiƙanki… Kewarki za ta kasance da ni har in riske ki.”

Abba ya faɗi yana jin wasu hawayen na sake zubo mishi da bai san ranar da za su daina zuba ba. Abinda ya sani shi ne yana ƙaunar Aisha… Ba kuma zai daina ƙaunarta ba har zuciyarshi ta tsaya.

***** 

“Ki bari mu fita tare mana. Nima zan je gidan da mun dawo asibiti da Ateefa.”

Labeeb ya faɗi yana kallon Zulfa da take shafa powder. Juyowa ta yi tana ware mishi idanuwa. 

“Ni dai a’a…Za mu yi walima fa anjima da yamma.”

Don Labeeb ya hana ne ma, tun jiya ta so ya kaita ta kwana. Ba zai gane farin cikin da take ji ba. Ta daɗe tana jin ina ma Abba Mami ya aura. Yau da fatan ta zai zamo gaskiya babu abinda take so da ya wuce ta kasance cikin ‘yan uwanta. 

Su yi farin cikin tare su dukkan su. Shi ma Labeeb ɗin jiya da dare ya dawo daga Abuja. Yau kam lallaɓa shi za ta yi ya barta ta kwana a gida, tunda dama yau yana ɗakin Ateefa, ya ƙarashe mata cikon kwana ɗayan. 

“Sai fa ƙarfe sha biyu ma za a ɗaura auren. Kuma walimar ba ƙarfe huɗu na ji Don ya ce ba?”

Turo baki Zulfa ta yi tana ci gaba da shafa powder ɗinta ba tare da ta sake ce mishi komai ba. Yasan ma’anar shirunta, ko me zai ce ba canza komai zai yi ba. 

“Sai mu fita tare in na sauke ki mu wuce…”

Tashi ta yi daga gaban mirror ɗin. 

“Tayyab ya je karɓo ɗinki… Na ce ya biyo mu wuce…”

Ta faɗi tana wucewa don ta sa kaya. Fitowa ta yi sanye da atamfa, riga da zani, gashin kanta take gyarawa, Labeeb ya bi hannuwanta da kallo, yana son gashinta, Tee ɗinshi ba ta da gashi haka. 

Wayarta da ke kan gado ta soma ringing, kafin ta ƙarasa Labeeb ya ɗaga. 

“Ke gani nan ƙofar gidanku…”

“Ya yi kyau Tayyab… Ba za ka iya shigowa a gaisa ba ko?”

Yana jin dariyar da Tayyab yayi a kunyace. 

“Sauri nake ne Yaya Labeeb…”

“Ko ba ka sauri ba zuwa kake ba dama…”

Labeeb ya ƙarasa maganar yana kashe wayar tare da miƙa wa Zulfa da ke tsaye, kafin ta ɗauki ƙaton mayafinta ta yafa tun daga kanta, jakarta da ke ajiye kan gado ta ɗauka. Ta tsugunna tana sumbatar Labeeb. 

“Sai na dawo…”

“Ki kula da kanki… Zan taho nima.”

Ya ƙarasa maganar yana saukowa daga kan gadon, sai da ya ga ta fice daga ɗakin tukunna ya shiga wanka. Zulfa kam ƙasa ta sauka ta samu Tayyab da Ateefa da ke gaisawa. 

“Tayyab ashe ana ganinka.”

Dariya ya yi.

“Ki ji Anty fa… Duk saƙon gaisuwar da nake ba wa Yaya baya faɗa maki?”

Harararshi Ateefa ta yi. 

“Za ka faɗi gaskiya ne ma…”

Zulfa kam dariya take musu. 

“Sai kun taho.”

“In sha Allah. Na san ba wani jimawa za mu yi ba…ki gaishe min da Mami.”

Kai zulfa ta jinjina suka fita tare da Tayyab ɗin. A mota ne take ce mishi. 

“Allah raina ƙal nake ji.”

“Ni so nake kawai in ga an ɗaura. Ji nake kamar wani abu zai iya faruwa kafin lokacin nan ya cika.”

Ɗan kallon Tayyab da ke tuƙi Zulfa ta yi. Ba ta ga laifin shi ba. Ita ma can ƙasan zuciyarta tana wannan tsoron.

“Babu abinda zai faru sai alkhairi.”

Ɗan ɗaga kafaɗunshi ya yi. 

“Ko don ban saba abubuwa su tafi mana daidai na tsawon lokaci ba e… Kwanciyar hankalin nan har tsoro nake ji wallahi…”

“Zamu saba a hankali…babu abinda zai faru.”

Ta sake maimaitawa tana son tabbatar musu da hakan. Ba ta son nata tsoron ya bayyana. Bai sake ce mata komai ba har suka ƙarasa gida. Da sauri ta wuce tana barin shi nan. Sallama ta yi tana cire takalmanta tare da rugawa ɓangaren Mami. 

Tura ɗakin ta yi da sallama. Mami na zaune. Amsawa ta yi tana tafa hannuwa. 

“Zulfa?”

Da gudu ta ƙarasa tana faɗawa jikin Mami cike da jin daɗin ganinta. 

“Mami kike tafa hannu…”

“Ni ɗaga ni kar ki ƙarasa ni… Dole in tafa hannuwa… Me ya fito da ke?”

Dariya Zulfa ta yi tana ƙara maƙalewa a jikin Mami. 

“Kai mami? Kamar ba ki ji daɗin ganina ba.”

Zulfa ta faɗi tana turo baki. 

“Da gangan Labeeb ɗin ya barki ai. Duka duka kwananki nawa da za ki fara fita?”

Sosai Zulfa take dariya, mami ta ture ta daga jikinta. Har ƙasan zuciyarta ta ji daɗin ganin ‘yar tata cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka. Duk da ba ta yi ƙiba ba, ta ƙara wani irin haske. Kallo ɗaya za ka yi wa fuskarta kasan tana cikin farin ciki. 

“Na zama kakarki ko?”

“Ina fita fa mami… Ina zuwa makaranta. Kuma ya zan yi missing ɗin bikin nan… Ga walima zan sha.”

Ture ta mami ta sake yi tana girgiza kai. Ba ta san yadda za ta yi da Dawud ba da ya ce sai an yi wata walima, ita ba yarinya ba, ba ƙaramar kunya take ji ba. Don haka tai shiru ta ƙyale Zulfa ba ta ce mata komai ba. 

Mayafinta Zulfa ta cire tana ajiyewa gefe tare da hawa kan gadon sosai ta kwanta ta yi filo da cinyar Mami. Sauke numfashi ta yi ta riƙo hannun Mami da nata duk biyun. Muryarta ɗauke da wani yanayi ta ce 

“Mami gani nake kamar wannan kwanciyar hankalin ba mai ɗorewa bace…”

Kallon ta mami ta yi. 

“Bazan ce miki mai ɗorewa bace ba… Don bana son in miki ƙarya kan abinda banda tabbas akai… Sai dai bazan ce miki ko bai ɗore ba ba zai sake faruwa ba. Domin babu wani farin ciki ko baƙin ciki mai ɗorewa. 

Rayuwa gauraye take da duka biyun… Ya rage namu mu zaɓi me za mu yi a cikin kowanne… Kamar yadda nake so ki zaɓi more kwanciyar hankalin nan cike da godiya ga Allah… Yadda zai baki ƙwarin gwiwar cinye duk wata jarabawa da zai ɗora miki nan gaba…”

Sumbatar hannun Mami ta yi. 

“Ina ƙaunarki sosai Mami… Rayuwarmu ta zo da sauƙi da kika kasance a cikin ta.”

“Nima ina ƙaunarku… Tawa rayuwar ce ta zo da sauƙi da na same ku Zulfa…”

Mami ta faɗi tana jinsu har cikin ranta. Tana jin gaskiyar kalaman da ta furta har a zuciyar ta. Samun su na ɗaya daga cikin manyan kyautukan da ta samu bayan Imani da iyayenta.

<< Rayuwarmu 48Rayuwarmu 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×