Skip to content
Part 5 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Sati biyu kenan. Ba Auwal kaɗai ba. Hatta ita Aisha zata iya cewa Allah ya sanya musu albarka a kasuwancin da ya fara. Kamar dama can duk wasu ƙofofin samun shi suna cikin kasuwancin. 

Gane hakanne bai yi ba. Kuma su duka sun ji daɗi da Yaya ya barshi nan garin Kaduna. Dama yana ta saka yara a harkar shi ta nan ɗin. Mutane ne yanzu babu amana. 

Sanin su Auwal ɗin basu da ra’ayi ne yasa shi bai neme su ba. Sai da yaje da kanshi yai masa magana.

**** 

Zaune suke tana taya Sajda yin homework ɗinta Dawud ya shigo da sallamar shi. 

Littafin da ke hannun Ummi Sajda ta karɓe da gudu ta ƙarasa wajen Dawud ɗin tun kafin ya zauna. 

“Yaya zo ka koya min.”

“Iyyee! Lallai Sajda. Kafin ki ga yayan wa yake taya ki?”

Dariya ta yi tare da faɗin, 

“Dama fa shi nake jira.”

Karɓar littafin yayi daga hannunta suka ƙarasa inda Ummi ke zaune kan tabarma. Zama yayi. Sajda tana gefenshi. 

Gaba ɗaya hannuwanta kan cinyarshi suke. Ya kalleta tare da faɗin, 

“Sajda son jikinki yai yawa wallahi. Ɗaga ni.”

Turo baki ta yi tana shagwaɓe mishi fuska. Girgiza kai kawai yayi ya kalli Ummi da faɗin, 

“Sannu da zama Ummi. Na ji gidan shiru. Ina su Tayyab?”

Murmushi Ummi tayi. 

“Tayyab sun fita da abokanshi. Zulfa kuma Labeeb ne ya zo.”

Da fara’a Dawud ya ce, 

“Yaushe ya dawo?”

“Ya ce ɗazun da safe. Amma zai fita anjima ko da za ka je ku gaisa da dare zaka same shi.”

Jinjina kai Dawud yayi. Daga fara’ar dake fuskarshi zaka gane kusancin da ke tsakanin su da Labeeb ɗin. 

“Tare suka tafi da Zulfa?”

‘Yar dariya Ummi ta yi ta ce, 

“Abin da ka sani ne ai. In ba Labeeb ya tafi ba ba za ka ga ƙafarta a gidan nan ba.”

Dariya Dawud yayi bai ce komai ba ya mayar da hankalinshi kan Sajda yana tayata homework ɗin. A zuciyarshi yasan Labeeb ɗin ma saboda Zulfa ya zo. 

Yana fama da aiki da mutane ina ya ga lokacin ziyara. Kowa a zuri’ar su fata yake da jiran lokacin da Zulfa zata ƙara girma. 

Don babu wanda bai karanci ƙaunar da ke tsakanin su da Labeeb ba. 

****

Zaune take kan kujerar office ɗin kanta dafe cikin hannuwanta. Sati biyu kenan ko a hanya bata ƙara cin karo da Auwal ba. 

Ta yi mamaki da aka ce mata ya bar aiki bayan kwana biyu da ta zo office bata ganin shi. Ta ɗauka zuciyarta zata haƙura. 

Inma akwai abinda ya canza shi ne ƙara haukar son auwal da zuciyarta ke yi duk rana. Son ganin shi take kamar ta saka ihu. 

Ta rasa kowacce irin jaraba ce wannan. Mukullan motarta ta ɗauka ta fito daga office ɗin. Zuwa ta yi ta fada cewar bata da lafiya zata je asibiti.

Ba ƙarya ta yi ba. Sai dai rashin lafiyarta ba ta zuwa asibiti bace ba. Maganin ciwon da yake damunta na tattare da Auwal. 

Ko da ta fito mota ta shiga ta nufi gidan Huzai. Tana shiga ko sallama bata yi ba ta zauna kan kafet ɗin ɗakin tana ɗora kanta kan ɗaya daga cikin kujerun. 

Kuka ta saki marar sauti. Tana jin Huzai na tambayarta ko lafiya ta kasa magana. Sai kukan ta da ke ƙaruwa. Tasowa Huzai ta yi tana dafa kafaɗarta.

Ta ɗago fuskarta jiƙe da hawaye. 

“Wace irin lalata ce nake gani yau Beeba m? Kuka kike fa.”

Huzai ta faɗi tana kasa yarda da abinda take gani. Rabon da ta ga hawaye a idanuwan Beeba tun ƙuruciyarsu lokacin da tai ciki ta koma gida aka korota. 

Hannu Hajiya Beeba ta sa ta goge fuskarta tana gyara zama. Cikin ƙunar rai ta ce, 

“Huzai ba za ki gane me ke damuna ba.”

“Ganar da ni. Don abin ya soma bani tsoro.”

Kallonta ta yi sosai. 

“Auwal. Huzai. Son Auwal zai kashe ni da raina.”

Tafa hannaye Huzai take yi. 

“Na ɗauka an wuce wannan babin. Na ga baki dawo ba na ɗauka kin gama da shi.”

“Hmm. Ko shi ya gama da ni ba. Bai amince ba kuma daga ranar ya ajiye aiki. Har yau bai sake dawowa ba…”

Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata. 

“Wallahi ina son shi har raina. Ban taɓa son wani namiji ba a rayuwata sai Auwal gashi ban san yadda zan yi in same shi ba.”

Dafata Huzai ta yi tana faɗin, 

“Kwantar da hankalinki. Kina da ni a garin Kaduna akwai namijin da ya isa ya gagare ki?”

Zaninta Hajiya Beeba ta kamo tana goge fuskarta sosai tare da maida gaba ɗaya hankalinta kan Huzai. 

“Da gaske aminiya?”

“Da gaske nake. Tashi muje wajen Malam Ɗanlami. Ai bansan abin ya kai haka ba.”

Da sauri ta miƙe. Huzai ta shiga ciki ta ɗauko mayafinta. Su dujkansu kan kafaɗarsu suke ɗora mayafan dama. A haka suka fice.

**** 

Tsaf Huzai tai ma malam Ɗanlami bayanin halin da Hajiya Beeba take ciki. Ɗan falankin da yashin shi yake ciki ya janyo gabanshi.

Suna zaune suna kallo. Ya zana ya goge. Kafin ya kakkaɓe hannayenshi ya kalle su ya ce, 

“Yana da mata da yara huɗu ko?”

Rausayar da kai gefe Hajiya beeba ta yi. 

“Na san yana da mata. Amma bansan ko ‘ya’yan shi nawa ba. Shi dai sunan shi Auwal.”

Sake zane yayi akan yashin ya goge. Ya ɗago ya kalleta da murmushi. 

“Shi ɗin ne dai. Akwai ƙaddara mai girma da zata shiga tsakanin ku.”

Da sauri ta ce, 

“Malam bangane ba.”

Murmushi ya sake yi. 

“Yanzun dai me kike so ayi?”

Kallon Huzai ta yi. Ta ɗaga mata kai tana nuna mata alama da ido cewar ta faɗi kome take so. Ɗan gyaran murya ta yi. 

“Ni nama rasa me nake so ayi.”

Harararta Huzai ta yi ta karɓe zancen da faɗin, 

“Malam akama mata shi a hannu. Ya ji duk duniya in bai kasance kusa da ita ba baya jin daɗi. 

Ya zamana jin muryarta da ganin ta sune kwanciyar hankalin shi.”

Wata shu’umar dariya malam yayi. 

“Dubu hamsin zata fara bayarwa na turaruka. Zan yanke kuɗin aikina idan ya ci. 

Inkuma bai ci ba ta zo ta karɓi kuɗinta.”

Da hanzari ta buɗe jakarta da kuɗaɗe ciki har da na albashin ta da ta karɓa tun satin da ya fita amma saboda bata da wata nutsuwa ko taɓa su bata yi ba. 

Ƙirgawa ta yi ta miƙa mishi. Yadda take ji har gidanta zata iya bayarwa indai zata samu Auwal. Ya karɓa ya ajiye gefe sannan ya miƙe. 

Cikin ɗayan ɗakin shi ya shiga. Ya jima sosai kafin ya fito. Ya zauna. Abubuwan da ke hannunshi ya ajiye a ƙasa ya ɗauki wata kwalba. 

“Kin ga wannan ki tabbata ko tayaya ne ya shaƙi ƙamshin turaren. In ma da hali ya taɓa jikinshi.”

Karɓa ta yi tana jujjuya kwalbar turaren. Sannan ya sake miƙa mata wata. 

“Wannan kuma a fuskarki zaki shafa. Wannan ki ajiye shi sai kin same shi a hannu zaki dinga shafawa a jikinki. 

Wannan maganin a abu za ki zuba masa ya ci. Ki tabbata ya ci shi fiye da sau uku. Komai zai yi dai dai.”

Kwashewa tayi. Sukai masa godiya sannan suka miƙe suna ficewa. Suna shiga motar Hajiya Beeba suka zauna ta kalli Huzai ta ce, 

“Ba aikata abinda malam ya ce bane wahala. Inda zan ga Auwal. Bayan bansan inda yake ba.”

“Mtsww kina bani mamaki wallahi. Wai yaushe kikai sanyi haka ne? A office ɗinku babu inda ake ajiye record na komai kan mutum in an ɗauke shi aiki?”

Dariya Hajiya Beeba ta yi. 

“Wallahi wannan tunanin bai zo min ba. Liti zan ba kuɗi ya ɗauko mun file ɗinshi.”

Tafawa suka yi suna yin wata shewa. 

“Auwal ya zo hannunki ya gama Beeba.”

Kallonta Beeba ta yi tana faɗin, 

“Beeba ba komai bace a garin kaduna in babu ke Huzai. Kina da babbar kyauta in aikin nan ya ci.”

Ta ƙarasa maganar suna yin dariya gaba ɗaya. Kafin ta tayar da motar suka ci gaba da tattauna wa a hanyarsu ta komawa gidan Huzai. 

**** 

Cikin wani irin nauyin bacci ta ji kamar ana kuwanƙwasa ƙofa. Sake juya ta yi tana gyara abin rufar da ke jikinta. 

Ƙwanƙwasa ƙofar take ji yana ƙara ƙarfi. Kamar a mafarki ta ji ana kiran. 

“Ummi…….. Abbaaaa.”

Sake ƙwanƙwasa aka yi da ƙarfin gaske wannan karon tare da kiran sunan nasu. Da sauri ta miƙe daga kan gadon. Muryar Dawud ce. Ta sake ji yana ci gaba da ƙwanƙwasawa. Murza idanuwanta ta yi. Ɗakin da duhu har lokacin. 

Da ƙyar ta hango hijabinta ta saka saboda yanayin kayan da ke jikinta sannan ta taka zuwa wajen ƙofar ta buɗe.

Wata irin ajiyar zuciya Dawud ya sauke tare da faɗin, 

“Ummi kun bani tsoro sosai wallahi. Lafiyarku kuwa?”

Da mamaki ta ce, 

“Lafiya ƙalau Dawud me ka gani?”

“Banga Abba a masallaci ba. Sa’adda na tashi ana ta sallah. Na ɗauka ko ya makara ne bai tsaya tashin mu ba. Sai da na dawo na kula da takalmanshi. Na zo kuma ina ta ƙwanƙwasawa shiru. “

Salati Aisha ta fara. Sukam wanne irin bacci ne yau sukai. Tunda take a karo na farko da ko sallar dare bata tashi ba. Gashi kuma sun rasa Asuba. 

Jikinta babu ƙwari ta ce, 

“Lafiya ƙalau Dawud. Bara na tashi Abbanku mu yi sallah. Lokaci na tafiya. Ka tashi su Sajda ma.”

Kai ya ɗaga mata yana sake kallonta sosai don ya tabbatar da lafiyarta ƙalau kafin ya wuce. Da sanyin jiki ta koma ɗaki. 

Auwal ta tasa. Shi kanshi mamakin kalar baccin da suka yi yake. Alwala suka ɗaura sukai sallar tare. Sukai azkar ɗin safe sannan ta wuce ta shiga wanka don tana riga shi fita yanzun.

Tana fitowa ta shafa mai ta wuce kitchen. Dawud ta samu a kitchen har ya sauke tea yana soya wainar ƙwai. Murmushi ta yi. 

“Fito in ƙarasa to. Ka je ka shirya.”

Juyowa yai yana faɗin, 

“Ina kwana Ummi.”

“Lafiya ƙalau. Ya kuka tashi?”

“Alhamdulillah. Abba fa?”

“Yana shiryawa. Allah yai maka albarka. Sannu da aiki.”

Murmushi yai yana fitowa daga kitchen ɗin da faɗin, 

“Bari inje in shirya Ummi.”

Ta ɗaga mishi kai. Duk ma ya kusan gama aikin. Ƙarasawa kawai ta yi ta fito. 

****

Tare suka yi breakfast gaba ɗayasu . Sannan suka wuce makaranta su ukun. Tunda Zulfa bata nan. Ummi ma ta ƙarasa shiryawa ta kalli Abba ta ce, 

“Allah bana jin daɗin jikina.”

A kasalance ya ce mata, 

“Ni kaina na rasa me ke min daɗi.”

Sauke numfashi tayi. 

“Allah ya tabbatar mana da alkhairi to. Sai na dawo.”

Ya amsa da amin. Yana ɗorawa da, 

“A dawo lafiya. Allah ya bada sa’a.”

Ta amsa shi tana mishi addu’a shima kafin ta fice. Kwanciya yayi kan kujerar, bacci kuwa ya ɗauke shi. 

***** 

Wani irin mafarki yayi nai firgitarwa daya sa shi miƙewa yana salati babu shiri. Zufa sai ɗigar masa take. Tashi yayi yaje yai wanka. Ya duba agogo goma har ta gota. Ya ɗauki mukullan gida dana mashin. Sai da ya fita da mashin ɗinshi ya kafe sannan ya dawo ya kulle gidan. 

Yana hawa mashin ɗin ya tayar, zuciyarshi ta doka da ƙarfin gaske. Kafin ta ci gaba da bugawa da sauri sauri. 

Bai yi Addu’a ba sam. Abinda bai taɓa yi ba. Ko da ya manta Aisha zata tuna mishi. Kashe mashin ɗin yayi da niyyar komawa ciki yayi addu’a sannan ya fito. 

Yana saukowa kamar daga sama ya ji muryar matar da ya fi tsana fiye da komaina duniya. 

“Auwal manyan gari. Kana tunanin ka guje min ko?”

Duk da ya girgiza. Ya kuma yi mamakin yadda akai ta gano shi bai hana shi juyo wa ba. Ya sauke idanuwan shi kanta. 

Kwalliya ce sosai a fuskarta kamar ko da yaushe. Bai tsaya ƙare wa sauran jikinta kallo ba ya tsayar da fuskarshi kan tata. 

Ƙamshin ko wanne turare ne a jikinta ya cika mishi hanci. Yanajin yadda koma wane irin turare ne yake sa kanshi juyawa.

Yana masa wani iri a zuciya. Ya ɗauke mishi hankali yasa ya kasa samun nutsuwar da zai gane wace addu’a ya kamata yayi. 

Buɗe baki yayi da niyyar magana. Idanuwanshi ne suka soma ganin hannunta ya ɗago riƙe da wani abu. Kafin ƙwaƙwalwar shi ta gama gane me ke faruwa ta watsa mishi a fuska. 

Hannu yakai ya kare yana faɗin. 

“Hajiya Beeba. Ya Rabbi. Meye haka?”

Duka hannuwanshi biyu yasa yana goge fuskarshi. Ƙamshin da ya gauraye ko ina na jikinshi ne yasa shi gane turare ne. 

Sosai kanshi yake juyawa. Ya sake saka hannu ya goge fuskarshi. Kamar ma ya sake gauraye ko ina na jikinshi ne da turaren.

Bai ga tafiyar Hajiya Beeba ba. Ya dai ga bata wajen. Kuma bai damu ba saboda yadda yake jinshi kamar yana cikin wata irin ƙatuwar kwalba ne da ya rasa hanyar fita.

Da duk numfashin da zai shaƙa da ƙara zurfin shiga cikin ko ma menene yake faruwa da shi da yake yi. Kan mashin ɗinshi ya zauna yana riƙe kanshi. 

Har sai da ya ji ya daina juya mishi. Hankacin da ke aljihun shi ya zaro yana sake goge fuskarshi amma a banza. Kamar turaren ba a fuskarshi yake ba wannan karon. 

Cikin tsokar fuskar yake. Wani waje ya shiga ya zauna inda babu ruwa ko sabulun da zai iya taddo shi balle har ya fitar da shi. 

Yana jin wani abu nashi da yake da muhimmanci yana barin jikinshi. Wani sabo na samun wajen zama. Amma ya rasa ko menene yake fita da kuma wanda yake shigowa ɗin. 

Cike da tunanin da baisan ko na menene ba ya gyara zamanshi kan mashin ɗinshi ya kunna ya wuce kasuwa.

**** 

Ta rasa abinda ya sa a kwana biyun nan sai gabanta yaita faɗuwa. Tana yin Inalillah wa inna ilaihir raji’un. Kamar yadda shine abinda ya kamata ta faɗi yayin rashin nutsuwa. Sai dai ta rasa kan Auwal kwana biyu. Baya dai magana. Abinci ma in yana ci da wani yanayi a fuskarshi da ta kasa fahimta yake ci. 

Ta yi tambayar duniya ya ce mata bakomai. Da ta sake tambayarshi ma yadda ya amsa ta zata rantse bata taɓa ganin yanayin a tare da shi ba. 

Ya kuma tsorata ta, don haka sai bata sake tambayarshi ba. Yanzun ma zaune suke cikin falon da dare bayan sallar Isha’i kamar yadda suka saba. 

Sajda ce ta tashi daga wajen Dawud ta zo wajen shi tana faɗin, 

“Abba ka ce za ka siya min sabon takalmi in na zo na ɗaya wannan karon ma ko?”

Ɗan yamutsa fuska yayi. Ya kama Sajda ya tureta gefe ɗaya tare da miƙewa ya bar falon. Abin ya taɓa zuciyar Aisha sosai. 

Haɗa idanuwa suka yi da Dawud. Tana ganin tambayar da ke fuskarshi. Tana kuma jin duka yaran suna kallonta. Ita suke jira tai musu bayanin wannan sabon abin da Abbansu yayi. 

Shekaranjiya da suna mishi hira baya amsa su yadda ya saba ya ce musu su barshi ya gaji. Jiya ma babu wani bayani. Yau kuma abinda yaima Sajda. Sun kasa ganewa. 

Abban su ba haka yake ba. ‘Yar fara’a ta ƙaƙaro ta dora saman fuskarta tare da faɗin, 

“Abban ku baya jin daɗi ne. Ku tashi ku je ku kwanta kuma.”

Miƙewa suka yi. Sajda duk surutunta bata ce komai ba tayi wani shiru da Dawud baya son gani. Kowa tafiya yayi banda shi. 

“Ummi me ke faruwa? Akwai wani abu da ya kamata in sani?”

Sauke numfashi ta yi. Ita kanta bata san me yake faruwa ba. Saboda haka ta ce mishi, 

“Ka ƙara addu’a kai dai. Koma menene Allah yasan dalilin faruwar shi. Komai zai yi dai dai in sha Allah.”

Murmushi ya ɗan mata ganin damuwar da ke fuskarta tare da faɗin, 

“Allah Ya sa. In dai da Ummi a kusa da mu, ai komai dai-dai yake.”

Dariya ta yi ba don ta kai zuciyarta ba sai don tasan abinda ɗan nata yake son gani kenan. Murmushin shi ya sake faɗaɗa ya miƙe da faɗin, 

“Allah ya tashe mu lafiya Ummi. Sai da safe.”

“Amin. Kar a manta da Addu’a”

Ya amsa da In sha Allah yana wucewa ɗakin shi. Sauke wata ajiyar zuciya ta yi. Jikinta babu ƙwari ta miƙe zuwa ɗakinsu. 

Sai da ta rage kayan jikinta sannan ta hau kan gadon ta kwanta. A hankali ta ke kallon Auwal daya juya mata baya.

Tun shigowarta ɗakin ta kasa gane baccin gaske yake ko kuma ya rufe idanuwanshi ne don baya son magana da ita. 

Addu’a ta yi ta tofa musu su dukkansu. Sannan ta gyara mishi rufar da yayi. Itama ta gyara tata. Sai dai me. Sam bacci ya ƙi kawo mata ziyara saboda zuciyarta da bata da nutsuwa. 

Garin yayi shiru saboda yanayin dare. Bata jin ƙarar komai a ɗakin sai na agogon da ke bugawa tik tik. Bata san meke damun Auwal ba. Ta yi tunanin duniya ko ta mishi laifi ne amma ta kasa tuna ko me tayi. 

Ganin saƙe-saƙen sun mata yawa yasa ta miƙewa. Banɗaki ta shiga ta ɗauro alwala. Bata da wani makusanci da ya rage mata da zata kaima damuwarta don ya bata shawara. Auwal shi ne ya zame mata uwa da uba. Aboki da kuma ‘yan uwa tun bayan auren su. Tana fitowa ta sake kayan da suke jikinta ta shimfiɗa darduma. 

Tunani ba zai mata maganin komai ba. Allahn da ya ɗora mata Shi Yasan dalili. Wajen Shi zata kai kukanta. Ta jima sosai tana gabatar da sallolinta kafin ta duba agogo. 

Miƙewa tayi ta ƙarasa kan gadon ta gefen da yake kwance. Tasa hannu ta tashe shi. Buɗe idanuwan shi yayi ya sauke su a kanta. Kallonta yake kamar ba ita yake tsammanin gani ba. Kallonta yake kamar baisan me yasa take a gabanshi ba wanda yasa zuciyarta kai kawo a ƙirjinta. 

Yasa wani ɗaci ya taso daga ƙirjinta zuwa maƙoshinta yai tsaye cak. Da ƙyar ta haɗiye yawu ta ce, 

“Ka tashi kai sallah.”

Kallon nan dai ya sake mata sannan ya juya kwanciyarshi yana jan abun rufar har kai. Bata gaji ba ta kama bargon ta janye. 

Miƙewa yayi ya ce, 

“Don Allah Aisha ki ƙyaleni tunda ba farilla bace ba.”

Da mamaki ta ce,

“Abban Sajda….”

Sake komawa yayi ya kwanta. Bata san me zata ce mishi ba kome ya kamata tayi. Jiki a sanyaye ta miƙe. Wasu hawaye suka zubo mata. Wannan baƙon al’amari ne a wajenta. Da yake da ciwo yake kuma yi mata wani iri. Tasan ko ta koma ta kwanta ɓacin ran da take ji ne zai sake danne ta. 

Don haka ta koma kan dardumar ta ɗauki Qur’ani. Tun tana hawaye tana karantawa har ta fara samun sauƙi da nutsuwa a zuciyarta. Ta kai hannu tana goge hawayenta. 

**** 

Yana kallonta don ba bacci ya koma ba shima. Ya rasa meke damunshi a kwana biyun nan. Kanshi yake ji kamar zai tarwatse. 

Abu ne tsaye a zuciyarshi da ya rasa inda zai cire shi ya ajiye ya huta. Komai ƙunci yake masa. Indai yana zaune cikin gidan baya jin komai sai ƙunci. 

Ko wa ya buɗe bakinshi yai magana yanaji kamar ya rufe musu baki su bari saboda ba sautin da yake son ji bane ba. 

Ko ya su Dawud suka zo gabanshi haka yake ji kamar ya rufe idanuwanshi saboda ba su yake son gani ba. Can wani waje a zuciyarshi da ya rage mishi yana faɗa mishi baya kyautawa. 

Yana faɗa mishi abinda yake ma Aisha bai kamata ba. Amma baisan yadda zai yi ya daina ba saboda ba ita yake son ji da gani ba. 

Baya son faɗar ko wa yake son gani a fili saboda ɓangaren da ke gaya mishi baya kyautawa Aisha yana faɗa mishi bai kamata ba. 

Ji yake kamar ya kurma ihu. Jikinshi ya ɗauki ɗumi saboda abinda yake son yi yanajin in baiba kamar ana yanka mishi naman jiki.

Kamar ba zai sake samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba sai yayi abinda yake son yi ɗin. Rufe idanuwanshi yayi yana jan numfashi da sauri.

“Beeba….”

Furta sunanta kawai dayayi a zuciyarshi yana jin nutsuwa. Yana jin abinda ke masa nauyi cikin kai yana ragewa. Kallonta yake a zuciyarshi yana jin numfashin shi na kaiwa inda ya kamata yakai. 

Da tunaninta a zuciyarshi bacci ya ɗauke shi mai cike da mafarkanta masu firgicin gaske. 

**** 

Hannu take sakawa kan takardun gabanta ba tare da ta karanta ko na menene ba tana buga musu stamp. Ba aikin bane a gabanta. Rashin zuwan Auwal ne ya dameta. Ko jiya ta koma wajen malam ita kaɗai ya sake tabbatar mata da ta ƙara haƙuri zai zo. 

Sai dai haƙurinta ya kusan ƙarewa. Rashin ganin shi na azabtar da ita. Ta soma tantama ko aikin malam ya ci ko bai ci ba. 

Yau zata rubuta takardar ɗaukar hutunta na ƙarshen shekara dama. Amma so take tai amfani da lokacin tare da Auwal. 

Ji ta yi ana ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin. Ta ja ƙaramin tsaki.

“Ko waye kuma. Bana son takura wallahi.”

Ta faɗi ƙasa-ƙasa. Tana ɗorawa da,

“Come in.”

Turo ƙofar aka yi. Ganin ko waye yasa numfashinta barazanar ɗaukewa. Ta kasa ɓoye jin daɗinta. Ta kasa ɓoye yadda zuciyarta ke ihun murna. 

Miƙewa tsaye ta yi. Kallonta yake. Kallonta yake babu ƙyamata ko tsana a idanuwanshi. Duk da bata gane kalar kallon ba. 

Ya mata daɗi.

“Auwal!”

Ta furta kamar ta kasa yarda cewa shi ɗin ne a gabanta. Shi ma kallonta yake. Daga kasuwa ya hawo mashin ya taho. 

Jinshi yake kamar baya cikin hayyacin shi. Amma ya kasa farkawa daga ko menene. Abu ɗaya yake da tabbaci akai a yanzun. Ganin Beeba. Jin muryarta ya sama mishi nutsuwar da ya kasa samu a kwana biyu. Wata irin gajiya da baccin da ya rasa a kwana biyun nan ya saukar mishi. 

“Me nake yi a nan?”

Ya tambayeta kamar ƙaramin yaron da yake tunanin ya ɓace hanya ya tsinci kanshi wajen da yake son kasancewa amma bai kamace shi ba. 

Wani shu’umin murmushin nasara ta yi tare da faɗin, 

“Gaisawa ka zo mu yi. Taho mu je in sauke ka.”

Ɗan girgiza mata kai yayi tare da yin hamma. Matsawa take kusa da shi. 

“Bacci ma kake ji ko?”

“Na gaji ne wallahi. Bana jin daɗin jikina ne. “

Cike da wata azababbiyar ƙaunar shi ta ce, 

“Mu je ka huta mana.”

Ya rasa ko me yasa ya kasa yi mata musu. Hanya ya nufa ya fice daga office ɗin. Tai wani tsalle tana faɗin, 

“Yessss!!!”

Kafin ta bi bayanshi. Kan mashin ɗinshi ta same shi har ya kunna. Bata son ce mishi ya sauka su tafi da motarta ta rasa shi. 

Tunda ba gama maganin ta yi ba. Don haka ta hau bayan mashin ɗin tana nuna mishi hanya har suka kai gidanta.

**** 

Zaune yake a falonta. Ba don baya son ganinta ba. Ko jin muryarta. A yanzun su ya fi so fiye da komai saboda nutsuwar da suke samar masa. Amman wani ɓangare na zuciyar shi na faɗa mishi ba nan ya kamata ya zama ba. Kuma da alama ɓangaren ya soma kokawar gaske da wanda ke son zama tare da Beeba. 

Miƙewa yayi yana faɗin,

“Bari in tafi gida.”

Ranta ta ji ya ɓaci. Daga shigowarsu zai ce zai wani tafi gida. Murmushi tai saurin yi tare da faɗin, 

“Ka zo har gidana ba ka ci wani abu ba. Gaskiya ban yarda ba saika tsaya ka ci wani abu.”

Ɗan murmushi yai mata yana faɗin, 

“Bana jin yunwa sam.”

Shagwaɓe fuska ta yi cike da kissa ta ce, 

“Um um. Gaskiya ban yarda ba.”

Komawa yayi ya zauna yana faɗin, 

“Shikenan na ji. Kawo min ko ruwa in sha.”

Da sauri ta wuce ɗakinta ta ɗauko maganin wajen malam. Sannan ta nufi kitchen. Juice ta zuba a kofi ta barbaɗa maganin a ciki ta juya sosai tukunna ta fito. 

Gabanta ke faɗuwa sosai kar ya kula da ya’yan maganin dake yawo cikin juice ɗin. Ta miƙa mishi ta zauna ƙasa ta kafa mishi idanuwa kamar zata cinye shi da ranshi. 

Karɓa yayi shima da alama baya son idanuwanshi ya bar kanta. Kaiwa yazo yi bakinshi zai Bisimillah tai wani far da idanuwanta tare da yin ƙasa sosai da muryarta ta ce, 

“Ka ga yadda kai kyau kuwa?”

Jin yadda bakinshi ya bushe yasa shi manta Bisimillahr da zai yi ya kwankwaɗe juice ɗin gaba ɗaya ya ajiye kofin a ƙasa. 

Murmushin nasara ta yi. Aikam ko dubu nawa malam ya yanke mata ba zata ji komai ba zata biya shi. Irin wannan aiki haka. 

Kanshi ta ga ya dafe cikin hannuwanshi. Idanuwa kawai ta zuba tana kallon shi. Ji yake duniyar na wulwula mishi. 

Ga cikinshi da ke zafi kamar ba abin sanyi ya zuba mishi ba. Ƙafafuwanshi ya ja daga ƙasa ya ɗora su kan kujera ya zame yana kwanciya tare da rufe idanuwanshi. 

***** 

Bai sake sanin abinda ake ba. Wani irin bacci yayi daya kwana biyu baiba. Sa’adda ya tashi har yamma ta yi sosai. Agogon da ke hannunshi ya duba. Bai yi sallar Azahar ba balle ta La’asar. 

Gashi har biyar da rabi. Ko yunwa bayaji saboda tashin hankalin rasa sallah da yayi har guda biyu a jere. Yana mikewa hajiya Beeba na fitowa daga ɗakinta. 

Ta kalle shi. 

“Ya akai baki tasheni ba. Banyi sallah ba.”

‘Yar dariya ta yi. 

“Kanata bacci ne bana son damunka. Ka ci abinci sai ka yi sallar.”

Girgiza mata kai yayi. Ya ce mata

“Gida zan tafi.”

Duk da ta ji babu daɗi bata nuna mishi ba a fuska. Lokaci kaɗan ya rage ta gama kama shi a hannunta sosai.

“Sai yaushe kenan?”

Kallonta yayi sosai. Yana tunanin ya zai yi ya kwana bai ganta ba. Tashin hankalin hakan yasa cikin shi ƙullewa. Da kyar ya ce 

“Zan dawo gobe in Allah ya kai mu.”

“Allah ya kawo min kai lafiya. Muje in rakaka.”

Kai ya iya ɗaga mata kawai. Ta rakashi yahau mashin ɗinshi. Akwai wani abu sananne tattare da rakiyar da ta yi masa. 

Iri ɗaya ne da wani abu da ya kasa tunanowa. Son tuno ko da me rakiyarta tai mishi kama na neman saka shi ciwon kai don haka ya daina.  

Ya ja mashin ɗinshi ya fice yana nufar hanyar gida. Ƙuncin da yake ji kafin ya ga Hajiya Beeba na sake dawo mishi da ƙarfin da ya fi na farko.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 4Rayuwarmu 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.