“Yaya injiniya Ka sani, duk dadin da nakeji a rayuwata, duk irin farin cikin da nake ciki idan har na tuno da wannan lokacin ina jin na tsani wadannan mutanen da rayuwata gaba daya.”
Na idasa maganar tare da share hawayen da suke kwararowa akan kumatuna tamkar sabon idon ruwan da aka samu a lokacin gina rijiya.
“Kiyi hakuri kanwata, kowanenmu yanada irin tashi kaddarar rayuwar wadda bata goguwa dole saita auku” Ya ce dani tare da tsareni da idanu.
“Hmmm Yayana kenan, ni kadai nasan irin tashin hankalin dana gani alokacin da kuma bayan faruwar abinda ya faru. . .