Skip to content
Part 4 of 4 in the Series Rayuwata by Tripleaaa

Karar harbin bindigar daya ratsa koina cikin dajin ne yasa naga matashiyar budurwar data tunkaro ni kai tsaye tana murmushi danafi misaltashi dana keta ko zalinta ta taja ta tsaya kamar wada aka takawa burki gaba daya, kafin ta sake yin wani yunkuri wani sautin harbin ya sake karade kunnuwan mu.

Mutumin da kusan kow yake kira da oga yayi jugum sannan ya sake nazartar karar harbin dake tashi.

“Akwai matsala”

 Ya ambata da alamun kaduwa hade da razana a tattare dashi.

“Kinga sakata cikin ki rufe mubar gurin nan.”

Dai-dai lokacin harbin yaketa kara yawa hakanan kuma karar harbin tana kara kusan to wajajen da muke.

Da gayya ta kama gashin kaina tajani hade da wullawa kamar wani kayan wanki.

Tim! na fada saman rairayi yashin da yake cikin yar bukkar, koda yake zafin kama gashin yafi zafin fadawar da nayi. Hakan yasa siraran hawaye gangarowa kan kumatuna, tausayin kaina ya kamani naji gaba daya na tsani rayuwar, na gwammace inama mutuwa zata daukeni na daina ganin jerin gwanon bakin cikin dayayi mani dabai bayi tako ina.

“Allah ka kubutar dani daga hannun azzaluman nan” na ambata a cikin raina.

Har yanzu harbe-harben sai karuwa sukeyi hakan yasa cikin gaggawa akaja marfin karan daya raba tsakanin tsakiyar daji da cikin bukkar da nake ciki aka rufe.

Ina kishingide a inda na fada ina maida munfashi bana iya wani kwakkwaran motsi sai kuma naji ana taba kofar.

Ahankali har ya shigo tare da maida kofar ya rufe.          

“Baiwar Allah! Baiwar Allah!”

Tabbas na gane mai wannan muryar shine sanadin keta mani haddi, cikin bacin rai da kunar zuci nace dashi,

“kaima kazo keta haddinawa ne?”.

“subhanallah, Don girman Allah ki daina hadani da wadanan mutanen.”

“Ai cikin su kake kuma duk halinku daya ne”

Nayi saurin tarar numfashin sa cikin bacin rai.

“Kiyi hakuri wallahi ban san za’ayi maki haka ba, na fada maki nima dolece tasa nake zaune a nan”

“oho maka dai, nidai Allah ya isa,

Kiyi hakuri ya fadi a marairaice kamar zaiyi kuka.

Zuwa nayi na fitar dake daga nan don akwai matsala abokan gaba ne suka kawo hari.

Shiru nayi kamar banjishi ba har saida ya sake mai-maita maganar da yayi,

“Suzo su kashe ni, ai bani da bambanci da gawa”

Na fadi ina kokarin gyara zama cikin turbayar dake tsakiyar dakin.

A daidai lokacin ne naji wata irin karar bindiga wadda ban taba jin irin mai karar ta ba.

Kara nayi hade da dafe kaina ina jiran naji fitar rai na. Shi kanshi saurayin saida ya duka kasa. Saboda tsananin razana da yayi.

“Wallahi da gaske nakeyi kuma ba cutar dake zanyi ba” yayi maganar cikin rawar murya alamun da suka nuna hankalinsa a tashe yake.

Kamar banji abinda ya fada ba haka nayi biris dashi kamar bansan abinda ke faruwa ba.

“kiyi hakuri da duk abinda ya faru a baya ki bani dama na goge laifina a gareki ta hanyar tseratar da rayuwar daga cikin dajin nan”

Saurayin ya sake magiyar rokona a karo na biyu.

Shiru na sake yi bance dashi komi ba yayin da tunane tunane barkatai suka fara ziyartar zuciyata hade da kawo mani labarai iri daban-daban.

“Kila so yakeyi ya cutar dake fiye da yanda akayi maki anan”

Wani sashe na zuciyata ya ambata mani yayinda a zahiri kuma na bawa kaina shawarar kin binsa.

To idan ya kasance na kirkine kuma da gaske yeki yanason taimakon kine fa?

Tambayar da wani sashe na zuciyata ya bijiro mani da ita kenan kuma a lokaci guda ta daure mani kain har na sauya tunani na fara yunkurun amsar saharar da sha mafi rinjaye na zuciyata ke bani na bin sa din koma ne zai faru ya dade bai faru ba.

Cikin azama nayin zumbur na mike tare da nufo inda yake a durkushe

A hankali ya rarrafa hade da bude marfin kofar sannan ya juyo ya kalleni.

“Rarrafawa zamuyi har mu kara shiga cikin duhuwa dan gudun kada a gammu”

Hakan kuwa akayi, sanda nan kutsacen rarrafa na a haka har muka fara yin nisa da inda ake harbe- harben. Daga nan kuma muka dosa na gudu, saurayin na gaba ina biye dashi.

A haka muka dunga keta daji da gudu wani lokacin na fadi sai ya tayar dani ya hada da bani hakuri da kwarin geuiwar juriya akan wahalar da nakesha.

Mun kwashe kusan muntuna talatin muna gudun da ko kusa ko alama bansan inda muka dosa ba.

Sannu a hankali har a zamto mun daina jin karar habe harbe saidai kukan tsirrai da kuma tsananin duhun dare.

A daidai wata yar farfajiya naga yaja ya tsaya yana maida numfashi hakan yasa nima na tsaya ina maida nawa numfashin,

“to baiwar Allah, inaganin  daga nan zan tsaya na koma ke kuma kinga wannan hanyar itace zata kaiki har kauyen ku”

“Kiyi iyakar yinki ki isa ki nemi mafaka a cikin daren nan dan akwai yiwuwar abiyo sawunki”

 Shiru nayi na kasa magana yayin da shi kuma yaci gaba da magana.

“nima kokari zanyi na koma dan kada a fahinci mine na kubutar dake karshe kasheni za’a”

Allah tsare sunana Bello idan Allah yasa kwai rabon haduwar mu gaba to.

Yana gama fadin haka ya juya da gudu

“Bello”

Na kwala mashi kira, ahankali yaja ya tsaya tare da juyo wa.

“Na gode Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi”

Na fadi hade da goge yan ziraran hawayen da suka gangaro mani akan kumatuna.

Duk da cikin duhun dare ne maga daga mani hannun da yayi sannan ya juya hade da rugawa da gudu ya koma ta hanyar da muka baro.

Jim na tsaya a wajen na rasa irin dadin da nakeji, take sai tunanin yayana da kakannina ya baibaye zuciyata hakanne yasa cikin azama na nausa da gudu hade da dokin zan saka su a idanuna.

Rashin sani yafi dare duhu dana san abinda zan tarar da kuma irin cin kashi dazan hadu dashi a rayuwa da ko kusa ban nemi hanyar garin mu ba.

<< Rayuwata 3

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×