Skip to content
Part 2 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Mujahid da Binta ‘yan dangi daya ne, wadanda iyayensu suka sha gora guda, mahaifin Binta Alhaji Hassan da mahaifiyar Mujahid Gambo uwarsu daya ubansu daya. Haifaffun garin Bauchi ne daga qauyen ‘Voto’. Su biyar mahaifansu suka bari a duniya, Malam Adamu, Hassan da Usaina da Gambo, sai auta Mairo. Bayan rasuwar iyayensu Usaina ta bi baya, Mairo ma haka, sai kuma Malam Adamu aka bar Hassan da Gambo a doron duniya cikin maraici, suka hada iyalan ‘yan uwansu  da nasu suka riqe.

Voto qauye ne sosai, wanda za a kira ya amsa sunansa na gaskiya a sunan qauye. Babu wani ci gaban rayuwa gare shi da mutanen cikinsa, ban da noma da kiwo. In ka ga wayewa ta sosai a wajen dan garin, sai wanda ya samu ya rurruma ‘yar firamare da sakanadiren garin, gwamnati ko wani na Allah ya dauki nauyin ficewarsa daga garin don neman ilimi,  kasancewar mutan cikin qauyen ba su damu da neman ilimin boko ba, sun fi mayar da hankali ga abin da suka saba da shi, noma da kiwo da kuma gargajiyarsu tare da al’adu.

Hassan na daga cikin samarin da suka sami wannan gatan ta hanyar daukar nauyin wani attajiri mai kishin al’umma, a cikin garin Bauchi, wanda al’adarsa ce shiga qauyuka zabo matasa wadanda su ne manyan gobe ya dau nauyin iliminsu domin kyautata musu rayuwa ko sa sami damar kyautatawa jikoki a gaba.

Hassan ya taso a matashi mai kaifin basira, tun a qauyensu da quruciyarsa ya ke da fasahar gyare-gyaren radiyo ko fitilu, bai kammala sakandire ba sai da ya sha qirqirar qananan abubuwa da kansa, kama daga tocilan,motar wasan yara, da fitilar ruwa, kuma bisa wannan doron ma ya samu aka dauki nauyin karatun nasa zuwa Bauchi Collage of art & sceince (bacas) domin karantun da ya dace da shi, sai dai kash! Bai shekara biyu yana karatun ba tilas ya bari dalilin rasuwar mai daukar nauyinsa, kuma maqiya Allah wadanda ihisanin daukar nauyin ya biyo ta hannunsu suka danne da kalma daya kacal, “Ai ya mutu”. Alhalin rijiya ce ta bayar da ruwa guga ya hana.

Shi ke nan karatun Hassan ma ya mutu, sai dai bai mutu tare da zuciyarsa ba, kuma bai masa sanadin komawa  qauye ba, sai ya yi zamansa cikin gari yana buga-bugarsa. Yau shi ne dako, gobe yaron kanti, jibi dan aike, gata amintaccen da za a sakar wa ragama. Amanarsa da basirarsa ya sami nasibi a rayuwa ta hanyar ubangidansa na qarshe Alhaji Nura, wanda ya dora shi a kula da kamfaninsa na matsar mangyada, mai kula da ma’aikata kuma mai kula da injina, har tafi-tafi ya zama jakadansa na siyo injinan daga waje suna siyarwa, sai likkafa ta yi gaba suka zama komai da ruwanka a harkar injinan ba na matsar gyadar ba kadai har komai da idonsa ya fada kai.

Alhaji Nura da Hassan amana da haquri suka tarar da juna, ba su hada shekaru goma ba sai fa suka tashi daga yaro da ubangida suka koma aminai, da ma tuni sun zama surukai don ko shekara biyu ba su hada tare ba Hassan ya aure Kilima qanwar Alhaji Nura.

Mace mai kirki kamar Yayanta, wadda ta zama kyakkyawan jigo, kuma ginshiqi a rayuwar Hassan da danginsa wadanda gidansa ya zame musu maboyar asiri, kuma sabulun wanke qunci, talauci da na takaici, tun Kilima na amarya ta fara riqon ‘ya’yan dangin Hassan har kawo yau ba ta fasa ba.

Mace ce mara qyashi ko kadan, wadda ta laqanci iya tarbiyya tun kafin ta haifi tata ‘yar guda daya tilo, wadda bayanta ba ta sake haihuwa ba, wato Binta. Don sai da suka shekara biyar da aure ma suka same ta bayan yawon asibiti da kai wa Allah kuka.

Gambo kuwa da ma tun kafin barin Hassan qauye aka yi mata aure da quruciyarta a nan Voto. Quruciyar ce kuma ta taimaka mata diban shekaru hudu gidan miji kafin ta haifi danta na farko Mujahid wanda ya ba wa Binta tazarar shekaru biyar. Bayan Mujahid ta yi haihuwa ta kai goma uku suka rasu, bakwai suke raye, maza biyu mata biyar wadanda matan kaf dinsu babu wanda bai tattaro tsumman rayuwarsa ya kai ta gidan Hassan zaman dindin ko kuma na jeka-ka-dawo ba. Hassan ya aurar da Aisha da Zainab wadanda suka biyo Mujahid, Sa’adatu aka aurar da ita a gidansu, yanzu ga Ummi a gabansu, Sani ke yi a Kano, yayin da Mujahid ya zama cikakken lauya bayan faxi-tashin karatu duk a aljihun Hassan. Ba ‘ya’yan Gambo kadai ba, ‘ya’yan Malam Adamu da Mairo da sauran ‘yan uwa ma da ke qauyen Hassan na daukar nauyinsu, banda wadanda ya ke daukar nauyin cancakat  a gidansa.

Wannan dalilin ya sanya zamowar gidan tamkar wani gidan sarauta saboda yawan dangi, kuma wannan ya hana Binta tashi cikin kadaici a matsayinta na mara abokin burmi a haihuwa na sama da qasa. Ta taso kamar mahaifiyarta da mahaifinta, a son mutane da fara’a tare da rashin qyashi, in aka kawar da kai a matsalarta ta kafiya da nacewa duk abin da ta sanya a gaba. Tana da son karatu don haka ta juya wa soyayya baya har sai da ta karbi kwalin digiri dinta a fannin kasuwanci.

Mahaifinta ma mai son karatu ya qarfafa mata gwiwa har ta kai gaci, musamman da ya fahinci manufa ce burinta a karatu ba neman kudi ba, saboda yawan cin alwashin da ta ke na cewa ba ta da sha’awar aikin ofis ko wanne iri ne, duk neman kudinta a gida za ta yi abinta, wannan ya kwantar da hankalin iyayenta ainun har zuwa lokacin da ta kammala karatu kuma ta qi tsayar da mijin aure, har ya zamana sun fara nuna damuwa sannan ta fara canki-cankin kawo samari, yau ta kawo wannan ta ce ta fasa gobe ta kawo wannan shi ma ta fasa bayan ta gabatar da hujjar fasawar, sau biyu ana sa mata rana tana cinye kayan sa ranar tana fasawa Shukuranu ne na uku wanda shi har lefe an kawo. A halin yanzu idan iyayenta suna da matsala a rayuwa to bayan wannan zata bi.

Binta na da yawan tsara wa kanta rayuwa, amma a fannin aure ta gaza, ita kanta ba ta san irin mijin da ta ke so ba, duk da kuwa tuni zuciyarta ta wadata da kallon rashin adalcin da mata ke samu a wajen yawancin wasu mazajen. An gadar wa da mata matsaloli na fuska da kan fata kawai tun iyaye da kakanni ana ta wanke matsalar ana sake mata kwalliya, amma matsalolin uwar dakin zuciyarsu wadanda su ne tushen matsala ba kuma su suke yin kansu ba, yinsu ake babu wanda ya cika damuwa da su.

Binta ba ta zurfafawa da tunanuwa a kan hakan ta ke watsarwa tare da dogaro a kan hujjar bai kamata a dami zuciya ko rai da bata lokaci akan abin da bai zo ba, ko kuma ba za a iya magancewa ba, sai dai hakan ya tasirantar da watsar da sha’awar aure gare ta gabadaya. Ta ji ba wani abin damuwa ba ne idan ma mutum ya rayu shi kadai, tunda da ma auren ba farilla ba ne sunna ne, amma dai dole ta dinga qoqarin rakito shi ta yi bisa dole saboda damuwar da iyayenta ke nunawa kan hakan, sai dai a mazan duniya kaf, ta shafa ta rasa ko wanda za ta aura bisa maneji, duk wanda ta rarumo don ta aura a maneji sai ta tona cikinsa ta gane ashe shi kansa zaman muhimmmiyar matsala yake.

Tun kafin yanzu yadda Binta ke mu’amalantar kowa cikin fara’a da karramawa a danginsu, haka ta ke mu’amalartar Mujahid wanda kusan shi ne bai mayar da gidansu wani kayan gabas ba, ba yabo dai kuma babu fallasa sai da dalili ya ke zuwa gidan, ba don raini ko wata mummunar fuska ba, a fahimtar kowa yana da dabi’ar qin mayar da hankali a kan dukkan abin da bai sha gabansa sosai ba.

In ka ganshi a gidansu sabgar karatunsa ta kawo shi karbar kudi, ko kuma wani aike daga qauye, duk kuma inda ya gabatar da dalilin zuwansa ya sami sallama zai dauke qafarsa har sai wata ta taso.

Hakan ya sanya ba a cika sabo da shi ba, hakazalika ba za a iya dorar da halayensa duk ba.  

Bayan kammala karatun Mujahid ya fara aiki da federal high court ta nan Bauchi, dalili ke nan da zamansa ya dawo Fadaman Mada gidan su Binta, shi ma ya zama dan gida, kuma ya toshe kunnuwa daga surutan da ya ke sha na zaman tuzuru babu aure alhalin bai rasa komai na damar auren ba, babu wanda ya taba la’akari da qwayar idonsa wadda tun tashen balaga karon farko ta farka cikin matsanancin son Binta wadda sam nata tashen balagar bai hado mata da soyayya ba face qumajin karatu a samu madafa.

Shi kansa Mujahid ya jinjina wa zuciyarsa wadda ta iya so, ta kuma iya ririta shi ta hadiye kowa ya kasa canka ciki har da wadda ake son, har na tsawon lokacin da ya tabbatar yanzu idan ya farka bai yi garaje ba, kuma fatansa ba zai yi nisa ba, wato kammala karatun Binta wadda ya dade da sanin alwashinta na ba za ta yi saurayi ba sai ta gama makaranta.

Mujahid ya fara son Binta tun kafin ta isa abar sha’awa, ba kyanta ne ya rude shi ba, domin duk cikin yawancin ‘yammatan danginsu Binta ba ta kai su kyau ba ma, tunda su zallar fulani ne, ita kuwa ta sirko abubuwa da yawa na mahaifiyarta bahaushiya. Ba baqa ba ce can, amma dai dole a kira ta baqar tunda ba za a kira ta fara ba, siririya ce sosai don ba ta shigo layin matsakaita ba, haka zalika tsawo ma bai mata yawa ba, bai kuma mata qaranci ba, haka ma fuskarta ba ta cika kyau ba, duk da ba ta cika muni ba. Yawancin komai matsakaici ne na Binta, abu mafi ban sha’awa da qaye a jikinta shi ne, yalwar gashin kanta wanda ya tashi tun daga gaban goshi haka ma na girar idonta wadanda duk da yana da yawa har kamar za su hade da juna, suna da ban qayen da ba sa buqatar reza ko kuma wata gwanar gyaran gira, sannan abu na gaba shi ne, zara-zaran yatsun hannunta da na qafarta.

Duk Mujahid ya lura da wannan tun daga fara tasawar Binta, kuma tun shi ma kafin ya gama bude ido ajin ya isa son mace ko a so shi, Binta ta ci gaba da burge shi har kawo yau duk da kuwa tana cikin mata ma’abota qin kwalliya ko gwalli, shi sai ya rantse ya kuma bai taba ganin Binta cikin kwalliyar nuna wa Sarki ba, hoda da wetlips kawai ya ke gani a fuskarta, ba ta cokala daurin dankwali ko fita za ta yi, kodayake mawuyacin abu ne ma a ganta ta fita da gyale face hijabi.

Bai ce wannan dabi’ar tata ta rashin kwalliya tana burge shi ba, ko kuma haka da ma ya ke son matarsa ba, a’a zuciyarsa dai na jin ko ya ya Binta ta ke haka ya ke sonta.

To shi da ya ke dan gayu ma dan kwalliya, wanda kwalliyar ta ke wa kyau kasancewarsa da ma kyakkyawan nuna wa tsara? Fari tas mai dogon hanci, kuma mai qirar jikin Zaki, shi mai kyau ne qwarai wanda ya yarda ko kana da kyau sai ka qara da wanka, saboda haka shi dan gaye ne sosai irin na zamaninsa, sai dai ba mai rawar kai ba, bai kuma yarda kyan nasa ya dada shi da qasa ba tunda ya fahimci cewa ba komai ke burge Binta ba, kyansa da kwalliyarsa kamar ma wani abin zolaya ta mayar masa da shi.

Ya sha wuya da qoqarin ririta son nata da boye shi, ba shi da ko wanne irin makami sai addua da kuma jarumar zuciyarsa mai zuga shi da cewa duk abinda ya so zai samu, Binta ya so kamar rai don haka ita zai fi saurin samu tunda shi mai nasara ne, saboda haka a gabansa Binta ta dinga neman auren wadansunsa yana kwanciya a daki yana yi mata kallon mai bata lokacinta kawai, domin kuwa bata da wani miji bayan shi.

*****

Ba qaramin kaduwa mahaifan Binta suka yi ba da fasa aurenta da Shukuranu, dan ma Mujahid na tsakiya yana ta sassaita alamarin da siyasa da dadin bakinsa har sai da suka yi shiru da maganar ba cikin miqa wuya dari bisa dari ba.

Babanta cikin fishi ya ce,

Na rantse da Allah duk wanda ta sake kawowa ta ce zata aura bata isa ta dawo daga baya komai aibunsa ta ce min ta fasa ba, sai dai in idan shi da kansa ya ce ya fasa aurenta

Jin wannan ya firgita Mujahid kwarai don ya tabbatar mahaifin Binta mutum ne mai kawaici da haquri, amma zazzafa ne idan aka zo masa da rainin wayo, yana da tabbacin tabbas zai aikata abinda ya fada.

Ya shanye fargabarsa ya mayar da batun wasa kasancewar mahaifin Binta mutum ne mai sakin jiki da iyalinsa,

Ni ma matsalar nan ta Binta na damuna, in ta cigaba dole ma a dangana ga malaman Ruqiyya

Alhaji ya zabga masa harara sannan tsaki ya biyo baya,

Wai kura ce take shirin cewa kare maye? Ai da kyau kenan, idan an tashi danganawa ga malaman Ruqiyya babu shakka sai an hada da kai, in ba ku yi wasa ba ma zamu roqi walqiyya ta hasko mana ku

Mujahid ya dinga dariya tamkar rahar da suke da Alhaji ce ta sanya shi dariyar, nan kuwa tsabar farin cikin fata da kudurin Alhaji ke shero shi.

Hajiya ba ta kai Alhaji sassauci ba, macace mai tsayawa kan tarbiyyar duk wanda ke qarqashinta, sannan ga ta da sanya ido, wannan ne dalilin da ya sanya Binta ke shakkar hukunci ya fara biyowa ta kan Hajiya ya bar Alhaji, don in ta tashi hukunci danye take yankewa bata kuma damuwa da halin da mutum zai shiga.

Rabuwarta da Shukuranu da Hajiya ta sako ta gaba sai da ta yi gwammace ko zata koma ta auri shi haka? Mujahid ne yayi ta yi mata famfo yana qarfafa mata gwiwa da cewa,

Zamma akan wannan dan fishin nata in kika yarda kika shiga gidan wancan mutumin kin jefa kanki kurkukun mutuwa, wataran da kudinki ko hawayenki zaki so bude ido ki ga Hajiyar tana fada babu dama saboda ya sanya almakashin zalinci ya datse zumuntarku

Da yake dama janyewar ta Binta bata gama kai wa zuci ba, nan da nan sai ta karbi shawarar tasa, amma cikin yanayin jimami ta ce,

Duk da haka zan yi qoqarin daure raina na samo miji kwanan nan, ni kadai suka haifa bai kamata na zame musu kayan sanya baqin ciki ba

Mujahid ya dan ji sanyin jiki da qudurinta wanda bai shiryawa ba, amma dai ya hadiye abinsa a zuci, cikin dariyar zolaya ya ce mata,

Neman miji? To ko na taya ki lalube?

Zabga masa harara,

Ba don ba sai mu bawa juna kwantaragi, ka samo min in samo maka, to inda matsalar take shi ne ni ba kowa ke birge ni ba.

Kamar ni kenan, ni a duniya ke kadai kike birge ni.

Kai tsaye ya furta maganar da tun daga zuciyarsa ta taso, amma dai fuskarsa na nuna kamar wasa ne.

Ta ce,

An sami dan banzan akasi gaskiya, ni dai ga ka nan ne, ko kadan baka birge ni sai a fagen shawara, a matsayin Yaya dai kam masha Allah ka gama yi.Dariya take tana maganar, duk da haka Mujahid bai kasa fahimtar gaskiyarta take fada ba.

Wannan hirar tasu ce kuma ta bashi aikin tunanin hanyar da zai sanar da ita gaskiyar cewa shi fa da gaske yake, kuma bai fara sonta dan in bai birge ta ya daina ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 1Rigar Siliki 3 >>

1 thought on “Rigar Siliki 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×