Skip to content
Part 3 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Ranar wata juma’a da dare ya kwana gaya wa Allah zai fasa son da ya ke wa Binta duniya ta ji ta sani. Ya roqi dacewar lamura tare da sauqinsu babban ciki shi ne Binta, Ubangiji ya toshe zuciyarta daga kawo masa naqasu.

 Ya wayi garin asabar cikin saqe-saqen dabarun ta inda zai billo wa lamarin. Binta dai ‘yar qarama ce a qirar jiki, amma nutsuwa da kamalarta na tula mata kwarjini ainun sannan tana qara girma da kwarjinin a duk lokacin da ya kwatanta kansa gabanta yana farke mata gaskiyar shi fa sonta yake.

Ya jima yana saqe-saqe kafin ya samo dabara saboda jiyo muryarta a jiya tana cewa.

“Wallahi marmarin Qauyenmu Voto na ke qwarai, da zan sami mai kai ni da na shi masa albarka”.

Da tuno wannan ya ji wani qarfin gwiwa ya ziyarce shi, kawai da sanyin safiya sai ya hau shiri ya shiga cikin gidan a kintse.

Kafin ya ga hajiya da Binta ya fara cin karo, ta fito daga kicin dauke da abincin karin kumallo, kuma ita ta fara tankawa cikin raha.

“A’a dan kwalliya sai ina?”

Ba ta sa rai zai tanka mata ba saboda qyaliyarsa, ta yi gaba abinta.

Sai da ya dan zaga murya sannan ya ba ta amsa.

“Voto zan je, in kina da sautu sai ki bayar”.

Ta ajiye abincin da ta kwaso kan tebur ta juyo cikin murna.

“Ba wani sautu, ni za ka dauka mu tafi kawai”.

Ya yi murmushin cin nasara, cikin basarwa ya wuce falon Alhaji  yana cewa.

“Sai ki yi sauri ki shirya, don in kin yi qailula zan arce na bar ki”.

“Kar ka damu, ni ba ‘yar kwalliya ce irinka ba, wankana ba jira”.

Yana sane ya qi tanka mata duk don kar ta ramfo shi tun daga nan.

Ya shiga falon Alhaji kai gaisuwa, a can ma ya karya kumallo, Alhaji ya cika shi da saqonni zuwa ga jama’ar Voto, muhimmi cikin saqonnin shi ne,

Ka qara bawa su Kawu haquri, kunyar idonsu ta sanya ban sake zuwa na ba su haquri ba, har yanzu fishi suke da ni akan maganar da Binta ke jawo min

Cikin Mujahid na qugi yana binne qararsa da cewa,

In sha Allah komai zai wuce Alhaji, in Binta ta kawo miji kowa sai ya ce gara da aka yi haka

Kai tafi can ka ba ni guri, duk inda dadi baki yake dayake masu laifi ne ku kun san inda zaku ku yafito shi

Yana dariya baro falon tare da qarfin gwiwar yau zai dauki Binta a motarsa a matsayin masoyiyarsa, kuma a yau zai fito mata da sirrin zuciyarsa, sirrin da a wajensa ya zarce gold qyalli.

Amma me? Abin haushi yana shiga falon Hajiya sai ya ji Binta na hada masa gangami.

“Hey ‘yammatan gidan nan duk mai son zuwa Voto ta zo mu je”.

Ya ji kamar ta doka masa guduma a qirji, amma sai ya yi kasaqe cikin bata fuska yana binsu da kallo.

Gizagonsa ya taimaka wajen kusan dukkansu suka ce ba za su je ba, illa Nabila da ta karbi tayin.

Nabila yar wani shaqiqin abokin Alhaji Hassan ce mai suna Alhaji Yau. ita ma ta bi sahun yammatan da gidansu Binta ke musu dadi, ta shaqu da Binta qwarai hakazalika Binta ma ta shaqu da ita, tana sonta fiye ma da yadda take son wasu da suka zama jininta. Nabila in dai ta sami hutu komai qanqantarsa to ta kan yi a gidansu Binta har da hutun qarshen mako, yanzu haka ta zo hutun zango karatu na biyu ne da shigarta aji shiddan sakandare.

Wannan ya janyo ta zama yar gida sosai har ma wanda bai sani ba zai yi tsammanin a gidan ita ma take.

Nabila kyakkyawa ce jerin farko na kyawawan mata, komai nata mai kyau ne, tun daga matsakaicin dirin jiki, tsawo da qiba, mulmulalliyar farar fata tas tamkar ka taba jini ya fito, dogon hanci dara-daran idanu, baqin gashi mai santsi, da kyakkyawan matsakaicin baki. Kodayake Nabila ba ta dau kyau a qasa ba, mahaifiyarta balarabiyar Misra ce, wadda mahaifinta ya auro a yayin zaryar kasuwanci, cikin hukuncin Ubangiji kuma ta zo haihuwar Nabilan Allah ya karbi ranta, sai aiki aka yi mata tana mace aka ciro Nabilan.

Kamar ba marainiya ba haka ta taso cikin kyakkyawar kulawa a hannun kakarta, wadda ta haifi mahaifinta, wadda son da take wa mahaifin Nabilan a matsayinsa na da daya tilo a wajenta ya koma kan Nabila, musaman kasancewar mahaifin Nabila bai yi saar dacen matar da ta maye gurbin mahaifiyar Nabila ba, wata azzalumar mace ya hadu da ita mai suna Baraka, ba ta qi ta bude ido ta ga kowa a dangin mijinta ya mutu ba sai ita sai yayanta uku, don haka duk inda kyakkyawar rayuwa take Innar Nabila wato kakarta tana bin ta ta yafito mata.

Babu wata kyakkyawar alaqa tsakanin Nabila da Mujahid a zahiri wadda ta fice gaisuwa, gaisuwar ma irin ta rashin shaquwar nan ko mai alamar nuna ji da kai, amma gaskiyar maganar kawaicin Nabila ne kawai ya janyo haka, cikin birnin zuciyarta babu komai sai Mujahid kwance yana gasa wa zuciyar tata aya a hannu, ya fara da matuqar birge ta musamman saboda tsabar gayu da iya kwalliyarsa, da tafiya ta tafi sosai sai ta gane matsanancin sonsa ne ya kafa mata qusa a maqoshi, ta yi ta yi ta zare abu ya gagara sai ma kullum da take sabbaba mata mugun gyambo mai raunata zuciya, ya haukata ta ya kuma sanya ta maye, duk inda ta waiga hasashen mijin aurenta sai ta hango Mujahid, amma dai kawaicinta ya shanye komai, ba a ganin komai a fuskarta sai haquri da nutsuwa, ba a ganin komai tsakaninta da Mujahid sai girmamawa a matsayinsa na babban Yaya, shi kuma yana karba mata da Matsayinta na qanwa amma wadda ido bai cika kallo ba.

Yau kuma ko me ya cinye haqurinta? Sai ga shi ta zaga hannu ta ce.

“Anti za ni”.

Cikin kakabin murna Binta ta ce.

“Yauwa qanwa, taho mu je. Maza ki ciyo kwalliyar taki, da ma da dan uwa sarkin kwalliya za mu tafi”.

Ta qare da zolaya tana kallon Mujahid wanda ya yi saurin kawar da kai yana kokawar hadiye bacin ransa. Tabbas da wata ce cikin danginsa ta ce za ta bi su sai ya yi dabarar saba mata ta zauna a gida, to Nabila baquwa ce, kuma mai nutsuwa da hankali, ko ya ya ne ya kamata kar a nuna mata mugun hali.

Binta ta zaci dan kwalliyar da ta ke kiransa ne ya nata masa rai ya ke wannan ciccin maganin, cikin dariya ta ce.

“Sunanka na gaskiya na ke kiranka da shi fa Yallabai, mata aka sani da jarabar son kwalliya, dole in mun ga namiji ya ara mu yi ta masa gori, na ga sai wani bata rai ka ke…”

Dole ya murmusa ya ce.

“Ni bata lokaci ne ba na so, kwakwazon kwalliya ki yi ta yi, ba hoda da jambaki na ke sa wa ba bare ki ce na zo da bidi’a, wanka ne mai sheqi kawai, ke ma in kin yi zuciya mu ganki a fagen”.

Ta yi gaba tana dariya.

“Allah ya ba ka haquri, ni in ma za ka fanshe ni jambakin na yafe, kai dai ka yi wa qanwarka Nabila sarkin kwalliya uzuri ita ma ta shiga ta caso tata”.

Yana murmushi har ta qule sannan ya yi fuska ya mayar da ganinsa ga Nabila, fuskarsa babu yabo babu fallasa ya dubi agogo, sannan ya dube ta.

“Ki yi sauri don Allah, ina da sabgogi a gabana”.

Nabila ta ji durum da yanayin umarnin nasa, sai ta ji kamar ita ma ya kamata ta burge shi kamar yadda a duniya ba ta da mai burge ta sama da shi. In haka ne kuwa wannan gizago da umarnin nasa da ba ta same shi ba, amma dai fuskarta da gangar jikinta ba su nuna ba, ta shanye ta zarce daki.

Yana zaune yana jiransu cikin shiru da tunanin ta inda zai billo wa Binta alhalin ga Nabila tare da su. Ba wai don idanuwan Nabila za su soke shi su hana shi furta manufarsa a kan Binta ba, sai don bai san takamaiman yadda Binta za ta karbi al’amarin ba, zai iya dacewa ta so shi, kuma yana sane ba za takasa marabtarsa a gaban Nabila ba, za a iya samun akasi ta qi karbar tayinsa, ya san tsarin ra’ayinta tsaf ba za ta kasa nuna masa gaban Nabila ba. Baya da wannan ma yana son sirri qwarai a cikin soyayyar tasu ko da kuwa ta amince, so samu sai ya gama yaqin yada manufa soyayyar za ta fasu, dangi su ji.

Hajiya ta fito daga cikin dakinta, dole ya ajiye damuwa ya ba ta hankali suka gaisa, sannan suka fara dan taba hira.

Can sai ga Nabila ta fito daga dakinsu riqe da soson hoda tana murzawa a fuska.

Haushi ya qara cika Mujahid, ya kasa hadiyewa sai da ya dube ta cikin bacin rai, ya ce,

“Au har yanzu a iyakar murza hoda ki ka tsaya? A gaskiya zan yi tafiyata…”

Ba ta barshi ya dire ba, cikin taushin murya ta ce.

“Lah! Hajiya zan fada wa ba ta san da ni za a ba”.

Ta mayar da ganinta ga Hajiyar tana fadin.

“Hajiya zan bi su”.

Hajiya ta ce,

“Kai haba? ke da Ummi fa na so ku raka ni gidan bikin nan yau…”

Ai Mujahid bai ma bari hajiya ta dire ba ya figi mukullin motarsa ya miqe.

“Shi ke nan ma bata lokaci ya rushe, Hajiya ta ‘yanto ni”.

Hajiya na dariya, amma Nabila ba da son ranta ta miqa wuya ba, sai don haqurinta bai bari fuskarta ta nuna ba, ta amsa wa Hajiya da,

“To na fasa binsu”.

Sannan ta juya daki tana ci gaba da murza hodarta.

*****

Daga Mujahid har Binta tafiyar  yau ta zame musu wata ta musamman, dukkansu zaqinta suke ji fiye da suga, Mujahid hau layin yada manufa shiyasa Binta ta ga ya canja mata sosai ya rage fada mata baqar magana cikin hira da zummar wasa, kazalika ya saki jiki sosai suna hira, duk raayin da ta zo da shi ba ya kufcewa, wannan ne yayi wa Binta dadi, don ita mutum ce mai son hira da nishadi tare da girmama raayinta, in ta shiga gurin da aka fiye shiru da daure gira ba qaramin takura take ba.

Daga cikin hirar da suka dinga yi, Mujahid ya yi amfani da  wannan damar ya dinga cusa mata abin da ya ke so a matarsa, shugabannin ciki su ne, tsafta da son kwalliya, tare da ba shi muhimmanci a dukkan lamuranta, kuma wadda za ta dinga zama tare da shi idan yana cikin gida ya zamana tana katararsa, ba ya son ma’aikaciya don ba ya qaunar gidansa ya zama kango, ko kuma rayuwar ‘ya’yansa a hannun ‘yan aiki.

Ba ya son mai yawan qawaye kamar kasuwa, kamar yadda tun farko ma ba zai auri mai tara samari ba, duk yadda ya ke sonta. Ba ya son hayaniya, don haka zai tara kudi sosai ya mallaki gida a unguwanni masu shiru, duk da shi dan dangi ne amma bai yarda dangi maza su dinga yi masa zirga-zirga a gida ba…

Ba su ke nan sharuddan ba, Binta ce ta tare shi cikin tsananta dariya,

Kamar fa ka yi kama da Shukurunu Yaya Mujahid

Ya amsa mata cikin qarfin gwiwa yana dariya,

Ni ba mai yanke zumunta ba ne, ba na son yawan zirga-zirga bai yi kama da kar wanda ya zo min gida ba, kishi fa halak ne, na shukuranu tsanani ya cika ko ma kamar yana neman ya saba qaida

Ba ta bar dariyarta ba ta amsa masa,

“Malam wadannan sharuddan naka sun yi mugun yawa, da farko da ka fara maganar tsafta da kwalliya wallahi har na hango matar da ta dace da kai, amma da ka zarce da wadannan miliyoyin sharuddan naka sai na ji ai sun mata nauyi duk da ban gama sanin ra’ayinta a mijin aure ba…”

Ta qara fashewa da dariya, ta ce.

“Kai ko ma wace ce ta aure ka gaskiya ina tausayinta, in dai kafin auren nata ka rufe mata wadannan sharuddan”.

Cikin murmushi a tausashe ya ce mata.

“Ba fa sharudda ba ne”.

Ta tsagaita dariya tana goge hawaye.

“Me sunansa?”

Ya qara tausasa murya idonsa na duban titi ya ce.

“Yadda na so ta kasance na ce miki, in an sami akasin haka zan sadaukarwa da so”.

Cikin kada kai ta ce.

“Oho! Ashe sharuddan naka ba za su hana ka zama jarumi a soyayya ba…”

Kada kai kawai Mujahid ya yi, tare da murmushi.

Suka dauki tsawon lokaci sannan ya nisa ya tanka bayan ya dan kalle ta.

“Wace ce matar da ki ka hango min?”

Kai tsaye ta amsa masa.

“Wannan yarinyar Nabila”.

Nan da nan ya tara gira.

“Wace ce haka?”

Ta sake amsawa cikin karsashi.

“Kyakkyawar yarinyar nan da ta so rako mu, yarinyar ta yi kyau wallahi, har gaban Ubangiji na sha kai roqon wani cikin ahalina ya aura”.

Ba ta kula da yadda Mujahid ya yi mugun hada girar sama da ta qasa ba, ta ci gaba da maganarta cikin yanayin nuna ai abin kirki ta ke.

“Wallahi Yaya Mujahid ka sa kai za mu taya ka yaqin yada manufa, kuma tana da sanyin hali, za ta dace da tsarinka…”

Dole Mujahid ya tanka don ta san fa tuni ta gotar da shi daga saiti, muryarsa a raunane cikin kada kai, ya ce.

“Ba ki da wayo Binta, ba ki taba sanin so babu ruwansa da kyau ba, har kyan halin ma wasu lokuttan ba damuwa ya ke da dubawa ba”.

Ko a jikinta ta amsa masa.

“Haba Mujahid, Nabila fa ta hadu iyakar haduwa, mu ma mata yabawa mu ke bare ku maza, ina tsammanin ba ka taba dubanta da kyau ba ne…”

“Ya isa don Allah!”

Ya fada rai a bace cikin daga mata hannu, sai dai muryarsa a tausashe ta ke.

Binta ta juyo ta dube shi da kyau, sai mamaki ya cika ta, cikin yanayin mamakin ta ce.

“Ka kula da kyau Mujahid, ba fa tallan Nabila na ke maka ba, na fada maka dalilina har addu’a na ke wa dangina wani ya more aurenta, su haifo mana kyawawan ‘ya’ya masu kama da zinari…”

Tana rufe baki ya amsa.

“To don darajar manzon Allah ki zare ni daga addu’ar ba na ra’ayi”.

Sai ta qara yin sararo tana kallonsa cike da mamaki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 2Rigar Siliki 4 >>

2 thoughts on “Rigar Siliki 3”

  1. Rigar Siliki Shine Zababben Zababbu Acikin Littafanda Nake Matuqar So Bana Gajiya Dashi
    Tayaya Zansamu PDF Dinsa?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×