Nabila ta tanadi qarfin hali da kyau kafin ta shiga gida, saboda haka babu wanda ya canki komai a fuskarta ko yanayinta.
Ta tarar Binta na wanka kuma shigarta ke nan, ga wankan Binta da dankaren dadewa kawai sai ta ware wadrob din kayanta ta ajiye mata saqon Mujahid.
gurguje ta fara shirin barin gidan kafin Binta ta fito ta mayar mata da hannun agogo baya.
Baqo zai yi halinsa Hajiya.
Da faraarta ta riski Hajiyan Binta a falonta tana rataye da jakar kayanta.
Hajiya da Karima suka yi saurin kallonta da ayar tambaya, Hajiya ta fara tankawa.
Za. . .