Skip to content
Part 11 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Nabila ta tanadi qarfin hali da kyau kafin ta shiga gida, saboda haka babu wanda ya canki komai a fuskarta ko yanayinta.

Ta tarar Binta na wanka kuma shigarta ke nan, ga wankan Binta da dankaren dadewa kawai sai ta ware wadrob din kayanta ta ajiye mata saqon Mujahid.

gurguje ta fara shirin barin gidan kafin Binta ta fito ta mayar mata da hannun agogo baya.

Baqo zai yi halinsa Hajiya.

Da faraarta ta riski Hajiyan Binta a falonta tana rataye da jakar kayanta.

Hajiya da Karima suka yi saurin kallonta  da ayar tambaya, Hajiya ta fara tankawa.

Za ki tafi gida, ina kwanan?

Yanzun nan Inna ta sanar da ni wani dan uwan Ummina ya zo ganina.

Yadda ta amsa cikin sakin jiki da faraa, babu yadda za a yi a zaci qarya ta shara, amma duk da haka sai da Hajiya ta dan nuna shakka.

Ke dai Nabila ki fada min gaskiya, ko Yakubu ne ya korar min ke?

Da sauri ta toshe baki da hannayenta biyu gami da zaro ido, sannan ta saki cikin dariya ta ce.

Yaks kuma Hajiya?

Suka yi dariya duka.

Cikin dariyar Nabila ta zarce da cewa.

Ai Yaks bai isa hana ni zaman gidanmu ba Hajiya.

Na yarda Nabila.

Hajiya ta fada cikin sakin jiki da aminci.

Karima ma ta magantu.

To sai yaushe za ki dawo? Kar dai ki qara dauke mana qafa irin kwanakin baya.

Nabila ta zarce da dariyar da ta ke tilasta wa kanta tana cewa.

Wacce ni? Ai jumaa na yi da yamma za ku gan ni.

Shi ke nan, ga shi babu direba na aike shi, amma bari na kira Mujahid ya kai ki.

Cewar Hajiyar.

Ba qaramin namijin qoqari Nabila ta yi ba wajen tsayawa qyam ba tare da yunqurin wani aiki ko furuci ba, ta san duk inda ta yi qoqarn yin daya cikin biyu sai an fahimci wani abu tsakaninta da Mujahid.

Can cikin gayyar rudewarta ta jiyo Hajiya na cewa.

Karima zubo mata snacks din nan ta tafi da shi, ki kuma kawo min wayata na kira Mujahid, tana nan kan gado.

Har Karima ta fice daga falon Nabila ba ta farko ta zabi abin yi ba, ba ta son Mujahid ya kai ta, ba ta son a gane haka, sannan ba ta son jinkirtawa har Binta ta fito daga wanka ta san shirinta.

Hajiya na ta faman yi mata hira fatar bakinta kawai ke amsawa ba tare da zuciyarta ba, zuciyarta na can saqa yadda za ta kubuta daga wannan daurin gwarman da ake shirin yi mata.

Karima ta dawo da snacks din sai dai babu wayar Hajiya.

Au ina wayar?

Hajiya ta tambaya.

Da sauri Karima ta juya.

Au na manta.

A wannan gabar Nabila ta sami hanyar kubuta.

Hajiya bari kawai na same shi mu wuce, ai yana haraba.

Zuciyar Hajiya daya ta gamsu, suka yi sallama ta dan yi wa Nabila hasafi ta tafi.

Cikin sanda da boye-boye ta samu ta bar gidan, Mujahid na hangenta lokacin da ta ke ficewa, kansa na qullewa da neman dalilai iri-iri, amma qarshen su shi ne yi mata irin adduar da ta yi wa kanta dazu,don ya yarda adduar za ta karbe ta, ba kamarshi da ya ke jin ya fara son Binta ba don ya daina ba, komai runtsi.

*****

Tsawon lokacin da Binta ta dauka bayan tura Nabila wajen Mujahid daga zaman zulumi har fadawarta wanka da fitowarta ta shirya, duk cikin fargaba da fatan haqanta ya cimma ruwa.

Lokacin da ta fara lura Nabila ta dade sai fargabarta ta gushe, hankalinta ya fara kwanciya sosai, ta tabbatar qiyayya ba za ta sa mujahid ya riqe Nabila ba sai dai akasinta.

Tana ta walwala da nishadinta har lokacin da aka qwala kiran sallar magriba ta ga mujahid ya shigo gida a gurguje cikin alamun shirin tafiya masallaci ya kawo fulas din da za a zuba masa ruwan zafi kasancewarsa maabocin shan tea dare da rana.

Tun daga nan Binta ta fada waswasin ina Nabila?

A gurguje ta gabatar da sallar magriba ta bazama falon Hajiya don neman baasi.

Ba kowa a falon da alama ita kadai ta idar da sallar, dole cikin tashin hankali ta nemi guri ta zauna tana rarraba idanuwa.

Ta yi zaman mintina ashirin kafin Hajiya ta fito.

Ba ta lura da halin gumin da Binta ke ciki ba duk da fankar da ke juyawa, ta ce mata,

Yau gidan babu dadi da aka dade aka bar mu ko? Karima ce kawai, wai ita ma kanta ke ciwo.

Kirjin Binta na bugawa ta ce.

Allah ya sauwaqe, duk kina suka je ne? Fitowata wanka na ji gidan shiru, na zaci ma ko kallo suke

Hajiya ta katse ta da fadin.

Kin manta yau qawar Ummi ke aure? Duk sun dunguma zun bi ta, Sani ne ya kai su.

Ba maganar su Ummi Binta ke son ji ba, don haka ta tare Hajiya.

Ke nan Nabila su ta bi?

Hajiya ta yi mata duban rashin fahinta.

Au baki san Nabila ta tafi ba?

Cikin zaro ido Binta ta ce.

Ta tafi ina?

Sai fuskar Hajiya ta shiga damuwa cikin saurin baki ta ce.

Wai ba ta sanar da ke ba?

Binta ta yi saurin girgiza kai.

Hajiya ta sanar da ni ta tafi ina?

Cikin saduda Hajiya ta rausayar da kai, ta ce.

Ta tafi gida.

Binta ta qara bajewa a kan kujera cikin zuciyarta tana ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun, ta faru ta qare Mujahid ya yi wa Nabila rashin mutuncin da ya gada.

Anya lafiya ce kuwa ta mayar da Nabila gida?

Hajiya ta tambaye ta cikin fuskar jimami.

Da sauri Binta ta rage kasalar baqin ciki ta watsar ta dubi Hajiya.

Fuskarta ta nuna wani sauyi ne kafin tafiyarta?

Hajiya ta girgiza kai.

Ko daya, ta ce min dan uwan Innarta ne ya zo ganinta, amma yanzu ina shakkar in gaskiya ta fada min.

Kamar Binta za ta yi kuka ta ce.

Me ya sa Hajiya?

Yanzu Hajiya ta fara yi wa Binta kallon nazari.

Duk yadda Nabila ta ke da ke amma ta kasa nemanki ta sanar da ke tafiyarta?

Binta ta yi saurin kawar da kai saboda kallon qurullar da Hajiya ke mata ya fara hudata, tana jin yaqinin idan aka ci gaba a haka sai ya zama tamkar Hajiya ta ciro zuciyarta ta baje ne ta ga abin da ta ke boyewa.

Cikin qoqarin shanye rikitarta ta ce.

Ni ma abin da na gani ke nan Hajiya.

Hajiya ba ta tanka ba har tsawon wani lokaci, kallon Binta kawai ta ke sai can ta nisa ta kawar da kai ta yi fuska da fadin.

Alamunki sun gama nuna ko ma me ye kin sani.

Binta ta debo in-nar da ba ta amfane ta komai ba sai fallasa kai a qoqarinta na ta nuna babu komai din.

Wacce alama na nuna Hajiya me na yi?

Hajiya ta qara zuba mata ido cike da shakku, da qyar ta shawo kan tarin tuhume-tuhumenta ta bige a guda daya.

Ki dai je ki nutsu Fatima, sai ki dawo min da gaskiyar lamari

Binta ta so tafiyar qwarai, domin ita za ta ba ta damar nutsuwa da tunani mai kyau har ta zo wa da Hajiya qaryar da za ta iya gamsuwa, sai dai ta tabbatar a wannan gabar idan ta tafin za a qara habaka mata zargi ne, don haka dole ta tsaya , kuma ta gayyato guntuwar nutsuwa muryarta cike da alamun tsoro da son fashewa da kuka, ta ce.

Wai Hajiya me ki ka zargi zan yi wa Nabila? Hajiya, Nabila ce fa wadda ko a wasa sabani bai taba shiga tsakanina da ita ba, ita ki ke zargin zan cutar?

Hajiya ta katse ta ba tare da ta saki fuska ba.

Wacce irin cuta kuma? Kawai dai na yi zargin kun hada baki da dan uwanki kun shiga hakkinta.

Kayan cikin Binta suka sake juyawa saboda firgici, cikin zaro ido da dafe qirji ta ce,

Hajiya, wanne dan uwan nawa?

Har ga Allah kasada ta yi ta tambaya, don ta qaddara idan Hajiya ta ambaci sunan Mujahid sai an kwashe ta a wajen cikin halin suma, amma sabanin haka sai cikin sakewa Hajiya ta amsa.

Yaks mana.

Binta ba ta gama sauke ajiyar zuciyar kubuta ba sai ga Mujahid ya shigo falon.

Sallamarsa kawai Hajiya ta amsa tun kafin ya zauna ta tare shi da cewa.

Yauwa Mujahid, ka kai ta ka dawo?

Yana zama a kujera yana jahiltarta da ido.

Hajiya wa na kai ina?

Ta dan tare gira nuna alamun alhini da fargaba, ta amsa masa.

Nabila mana.

Da sauri ya girgiza kai.

Ina zan kai ta Hajiya?

Nan da nan Hajiya ta daburce ta hau koro masa labari.

Binta na tsaye tana sauraronsu tamkar ta je ta shaqe Mujahid ta kashe, don tana da yaqinin akwai saka hannunsa cikin korar Nabila daga gidan.

Duk cin maganinta sai da Mujahid ya yi qoqarin sako ta cikin hirar.

To Binta ko Yaks ne ya fusata ta?

Binta ta yi qoqarin ta hadiye fushinta ta kasa, sai da ta yarfe hannu ta doshi qofa tana cewa.

Sai ka ce wata damisa za ka ce ya fusata ta, da ma ana so dole ne?

Da alama ba ta tambaaye shi don ya amsa ba, ta yi maganarta ne kawai mai sunan zagi a kasuwa, tana qoqarin ficewa.

Hajiya da ba ta san dawan garin ba ta zaga murya ta kira ta.

“Zo ki ba ni waya na kira ta na bi sawu.

Binta ba ta ko juyo ba ta qarasa ficewa tana ce mata.

Ni ma kiran ta zan yi yanzu Hajiya, yadda muka yi zan sanar da ke, kodayake ma tun yanzu na fara yi wa wanda duk ya kore ta Allah ya isa.

Wanda ta aika wa saqon ya karba, kuma bai iya komai ba bayan murmushin da ya ja hankalin Hajiya ta tanka.

Wai ma dariya ka ke tana wannan danyen kan, maimakon ka ci zarafinta? Me ya yi zafi da za ta dinga wannan zafin kan?

Mujahid ya zarce murmushinsa zuwa dariya yana cewa.

Ki barta kawai Hajiya, ita ta san abin da ta qulla

Hajiya ta tare shi.

Ni ma haka na ce mata wallahi, gari banza Nabila za ta tafi ba ta sani ba?

Mujahid bai tanka ba illa cigaba da dariyarsa.

Binta ba ta kira Nabila ba sai da ta qoqarta ta yi sallar ishai  don ta gama yanke qaunar duk labarin da za ta ji daga Nabila sai ya yi mata shegen bugun da za ta ji jiki kafin ta tashi.

Ta dinga ayyana cikin kuka za ta ji Nabila ta zaga wayarta ko ma ta qi zagawar, amma sabanin haka sau biyu ta kada, ta dauka kuma cikin walwala matuqa.

Anti yanzu na ke shirin kiranki na nemi afuwa.

Binta ta sauke wata gundumemiyar ajiyar zuciya ta ce.

Da ki ka yi min laifin me?

Nabila ta qara bangalewa da dariya.

Na taho bagatatan ba ki sani ba, wai ashe ban yi miki sallama ba, haba hankalina ne ya yi gaba.

Binta ta hau laluben qofar da za ta qalubalance ta ta rasa, sai da ta sha uban shawagi, sannan ta wasko ta.

Wane ne ma ya zo? Uncle masud?

Har Nabila za ta amsa da eh, sai ta tuna Binta ta san Uncle Masud har ma suna da lambobin wayar juna, don haka ta waske ta hau in-ina.

Aa. la ba shi ba ne wani ne.

Binta ta jima ba ta tanka ba, sannan ta tanka din.

Nabila ba na son qarya.

Anti

Nabila ta so yin gardama Binta ta sake tare ta.

Na dai fada miki ba na son qarya Nabila.

Sai kawai Nabbila ta ja baki ta yi shiru.

Dukkansu suka jima cikin shirun, sannan can Binta ta nisa a tausashe ta ce.

Ki sanar da ni gaskiya, me ya faru?

Da qyar Nabila ta daure ta kori raunin muryarta.

Me ya faru Anti?

Wasa za ki ci gaba da yi da hankalina Nabila?

Binta ta tambaye ta cikin taushin murya.

Dariya kawai Nabila ta yi.

Binta ta sake tausasa murya.

Ki sanar da ni me ya sanya ki tafiya gida a yau?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 10Rigar Siliki 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×