Skip to content
Part 14 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Duk yadda damuwa da shiga bala’i suke taruwa su yi kisa, sun kai wannan matsayin a duniyar Mujahid daga yammacin jiya zuwa na yau, amma abin mamaki shi sun kasa kashe shi.

Tun tsakar daren jiya da ya dawowarsa gida ba tare da ya san inda ya kai kansa ba, yayi kwance a falo yana jiran mutuwa ko kuma qaninta, wato ya farka ya ga barin jikinsa a shanye, amma har daren ya qare rana ta hudo ta fara shan sharafinta ko ciwon kai bai marabce shi ba bare ya fara zargin ko ciwon ajali na masa sallama.

Ya je aikinsa duk cikin rashin sukuni ya dawo gida da zummar cin abincin rana kamar yadda ya saba, amma gaskiyar maganar dawowa gida yayi don yayi nazari akan Binta, mutuwa ta qi daukarsa ya tabbatar in dai yana numfashi ba zai fasa son ba, don haka gara ya samo hanyar da zai tsira da son ba tare da yayi kantafi da rayuwarsa ba.

Kenan a mafitarsa ita ce yayi qoqari ya san abinda zai yi ya rayu da Binta a yadda ta zabi ta kasance.

A ransa ya sha cika bakin ya san halayyar Binta da dabiunta ciki da bai, amma daga jiya ya haqiqance lallai Binta Rigar Siliki ce, ana saba ta ne tana jirkicewa. Sai dai ko bindiga zaa dora masa a maqoshi, zai iya rantsewa abinda ya faru jiya Game ne kawai ba daga halayyar Binta ya fito ba. To amma! Wacce hanyar zai bi ya tabbatar? Ba zai cigaba da son Binta ko son aurenta ba sai ya sami wannan tabbacin gudun yin kitso da kwarkwata.

Zazzafan nazarin da ya fada kenan. Ya dinga tsinto mutane makusantan Binta wadanda yake jin zasu taimake shi yana tantance su, amma bai samo aminin Binta kuma wanda zai bashi sirri sama da Nabila ba. Qaqa-qara-qaqa!

 ******  

Har Nabila ta fito harabar gidansu cikin karkarwar qafa da ta zuciya bata fasa shakkun kunnuwanta da wayarta ne suka yi mata qarya ba.

Qaryarsu ce ba Mujahid ne yayi mata waya ya nemi izinin ziyarta ta ba, kuma ba shi ne yanzu yayi mata waya ya ce ta fito ga shi ya zo ba, wannan almara ce, zuciyarta da wayarta ke son haukata ta amma ga ta ta biye musu ta fito din dan ta tabbatar.

Kasancewar a rude take bata damu da canja sutura ba sai ta fito a yadda take, tana sanye ne da turaren shudin wandon roba da farar  riga mai adon shudayen duwatsu a qirji, Allah ya sa dai ta yi azancin janyo farin hijabi wanda ya zo mata qirji ta zira kanta babu kallabi ta fita.

Zuciyarta ta kusa fadowa ta tarwatse lokacin da idanuwanta da hankalinta suka tabbatar da farin gani wato Mujahid.

Yana tsaye jikin motarsa da mukulli yana cilla shi yana cafewa. Shi ma sanye da shiga shigen tata, amma maimakon yadin roba shi nasa suwaga ne daga dinkin har yadin, tare da ruwan kasar riga mai gajeren hannu, idonsa sanye da farin gilashi.

Ko haramun ne mutum ya kalli mijin Antinsa ita dai ta kalla ta more sai da neman gafara ta biyo baya, Mujahid bai taba yi mata kyau irin ranar yau ba, don haka sonsa bai taba motsa mata kamar yadda ya motsa mata a yau ba, maimakon zuciyar tata ta fado ta tarwatse wai a qirjinta take neman ta dare gida biyu.

Duk ta zama ta bi wata sokuwa a tsaye, jinta take so na neman narka ta a wajen ta zama ruwa.

Mujahid na ankara da ita da yanayinta sai ya basar ya yafito ta da matsananciyar faraa.

Sai ta sami kanta da cika umarninsa cikin jin qwacewar hawaye amma qarfi da yaji tana hana kanta.

Har qasa ta zube tana gaishe shi ba tare da ta shirya haka ba, abinda kuma ya qara fallasa asirin zuciyarta kenan, Mujahid ke qara gane kalar son da Nabila ke masa ba mai barin mutum da hayyaci ba ne, sai dai babu yadda ya iya, ya fara yi wa Binta irinsa kafin ita ta fara yi masa irinsa.

Ya sake basarwa ya amsa mata gaisuwarta da faraar da ta fi ta farko, sannan ya bi ta da kallon sama da qasa, da yanayin zolaya ya ce mata,

Kin san yadda kika fito kuwa? In irinsu Yaks na kusa zaki hana su sukuni Nabila.

Daga ambatar Yaks dukkan annurin fuskarta ya dauke, shi kansa sai da yayi danasanin ambatar. Yayi ta jiran cewarta cikin nadama ta qi tanka shi. A sanyaye ya ce mata,

Ki yi haquri ba zan kuma ba.

Da qyar ta qwato wani murmushin yaqe, bata tanka ba.

Ya dinga wani kallonta a kaikaice tamkar yana nazarin ta kafar da zai saci imaninta ta yi marhabin da abinda ya zo mata da shi.

Bai san cewa wannan kallon kadai ya isa rufe mata idon ganin kowa bayan shi. Babu abinda kallon yayi sai tsuma mata sonsa tare da jaddada mata matsayinsa na wanda ya fi ko wanne irin Namiji a filin duniyarta.

Ta dai yi duf tayi kasa da kai sai kallon nasa ne kadai ke qara huda dukkan qofofin gashin jikinta yana isa zuciyarta da kwanyarta kai tsaye.

Na zo da qoqon barar neman wata alfarma.

Kamar daga can qololuwa ta ji maganarsa saboda kafar da zata ji maganar ta da inda zata kai duk sun toshe da sonsa, duk da dama cikin dasasshiyar murya yayi maganar.

Ta yi qarfin halin dagowa ta kalle shi, tana qoqarin idanuwanta su shanye son su bayyanar da rashin fahimta. Ta ci nasara hakan ta faru.

Bai yi qasa a gwiwa ba ya amsa mata,

So nake ki zame min aminiya kuma abokiyar shawara.

Har yanzu kallon rashin fahimta take masa, ta yi qoqarin ta yi magana amma harshenta da zuciyarta duk a daure suke.

Qila fahimtar hakan ne ta sanya ba ya jiran cewarta yake cigaba da maganarsa,

Duk duniya kin fi kowa cancantar na amincewa a lamarin Binta.

Nan ne kuma kanta ya kulle, da dalili ta cigaba da yi masa kallon neman baasi zuciyarta na bugawa. Mujahid ya ambato mata Binta, tamkar yana jaddada mata ne akwai fa wata mai riqe da takobi zata datse jijiyar wannan halittar son nawa da ke maqare a birnin zuciyarki.

Wannan karon bai bar ta da sukuni ba, dora mata idonsa yayi qir alamun yana jiran cewarta.

Wannan kallon da yake mata ne ya qarasa tankwabar da ragowar qarfin halinta har ta ji tana neman bayyana kai, dole ita ta dauke nata idon ta sunkuyar qasa tana jero ajiyar zuciya, har tsawon minti guda bata tanka ba shi kuma bai fasa jiran cewarta ba.

Can ta samu ta tanka duk jikinta a sanyaye,

To ka zo mu shiga daga ciki mana.

Ya daga mata hannu cikin walwala,

Nan ma ya isa wallahi.

Ta dan yi turus tana nazarin kanta da kanta. 

Ya fahimci shigarta ce ta dame ta, ba dan zata bata rai ba, in gaskiyar zuciyarsa zai fada mata zai sanar da ita cewa shi ba Yaks ba ne, babu macen da zata ja shaawarsa sai Binta. Amma tunda wata gaskiyar wahalar saiduwa gareta, sai yayi murmushi ya ce mata,

Kar ki damu Yaya Mujahid ne, qanwa kawai na ke kallonki.

Maganarsa ta cancanci sanya ta kuka, wanda ta ke so fiye da kowa a halin yanzu, yana neman jingina zumunta ya haramta mata wannan son. Amma tunda jaruma ce ta yi qarfin halin shanyewa, a nutse ta dube shi ta ce,

Ka zarce kai tsaye ka fadi buqatarka a gurina, na yi maka alqawarin zame maka amintacciya

Kamar yadda nayi ta cin laya a kanki kenan.

Ya fada cikin shauqi.

Kallonsa kawai ta yi ta kawar da kai.

Cike da qarfin gwiwa ya sanar mata,

 Ina da yaqinin kin sani ko kin san wani abu a dalilin da ya sa Binta ke gujewa aurena, na san ta da kyau, ba haka ta ke qin maza ba in bata yabawa soyayyarsu ba.

Nan da nan jikin Nabila ya mutu, jikinta sai rawa take ta tare shi,

Yaya Mujahid da na san wannan ce buqatar gaskiya da ban yi alqawari ba.

Ya girgiza mata kai a nutse,

Don Allah kar ki damu, ki fada min ko wacce irin magana akan Binta komai muninta ba zata zamar min abin tashin hankali ba, sai dai ta zamar min wani abin hobbasa, ina son Binta fiye da duk wani so da kika taba ganin wani yayi wa wani, babu abinda zai sanya ni in juya in fasa son, don haka bana neman komai sai na ture abinda zai hana ni kasancewa da ita.

Yakamata zuciyar Nabila ta tarwatse da jin wannan labarin son na Mujahid, amma zuciyarta maabociyar daa ga Allah ce, komai take tana gauraya shi da bin Allah don haka maimakon ta ji tausayin kanta mai son maso wani, sai ta ji tausayin masoyinta yana so ana gudunsa, ba ta da amfani idan bata taimake shi a abinda yake so ba.

Wannan ne dalilin farke masa layar Binta,

Ba na sonsa, ban taba mafarkin auren zumunci ba, kuma aqidata ba za ta bar ni auren mutumin da silarsa ba su san darajar mata ba don ina tsoron ya yo gado

Komai bai bashi mamaki ba, amma ya canja masa qudurori a zuci, ya kuma sanya shi jin tilashin ashe yanzu yakamata ya ci gaba da son Binta, tunda tana qin sa ne da dalili, dalilin da ya san zargi kawai take, kama da wane ba wane ba ce don haka ko wanne irin lokaci zata iya samun gamsasshiyar hujja ta janye qin, sai dai ba ya son a yanzu ta ga hujjar, ita wacece da ba zata yi so don Allah ba, Shi ne zata sanya kakkaifar wuqa ta datse masa maqogwaro da qiyayya? In haka ne zai bata mamaki.

Fuskarsa cike da walwala ya dinga shara wa Nabila godiya.

Faraarsa da godiyar suka dinga bawa Nabila mamaki don ta san labarin da ta bashi ai ba mai dadi ba ne.

Ba ta fita daga mamakin ba ya ce mata,

Wannan ya zama sirri a tsakaninmu sannnan ina cigaba da neman alfarma duk lokacin da buqatar taimako ta taso min zan rugo wajenki ki taimaka min

Ya katse maganarsa daidai lokacin da ya ji shi ma tasa zuciyar ta rakito zata fado, sakamakon ganin motar da ta shi go harabar gidan har ta kusa isowa garesu tayi fakin sannan Binta da Yaks suka bude suka fito a lokaci guda kuma suka yi arba da juna.

Mujahid jarumi ne na qin qarawa, cikin sakanni kadan ya girgije kaduwarsa zuciyarsa kuma ta shinshino nata makircin.

Nabila a birnin so take, in mujahid na kusa da ita komai nata rasa shi take, ba ta san mota ta shigo ba bare wadanda suka fito cikinta, sallama take wa Mujahid tana shirin tafiya har ta juya ta ji Mujahid ya danqo hannunta ya juyo da ita,

Zo Nabila, ga wata alfarmar zan nema.

Ta kadu kwarai da riqon hannun da yayi mata, sai dai ba can ba domin ta kalli qwayar idonsa ta hango aminci kwance, babu cin amana ko kadan, ko kuma so ne ya rufe mata ido? Ta kasa tantancewa.

Ya kashe ta da wani kallo mai shiga jiki musamman hudajjen jiki da so ya gama hudawa da kibiyoyi irin nata, ba tare da ya dauke ido daga kanta ba ya shiga ce mata,

Ga Binta da Yaks nan sun kawo miki ziyara duk a wani salonsu na ci min fuska, abinda nake buqata a wajenki shi ne, a idon Binta da Yaks duk runtsi ki nuna akwai alaqar soyayya a tsakaninmu.

A tsorace Nabila ta zare hannunta daga nasa cikin zaro ido, sannnan cikin dabara ta saci kallo su Binta da ke tsaye suna kallonsu cikin muzanta, ta mai da kallonta ga Mujahid muryarta da bakinta na rawa ta ce,

Ba zan iya wannan alfarmar ba Yaya Mujahid, don Allah ka janye ta.

Ya lumshe ido yana girgiza kai,

Ba zan janye ta ba Nabila, domin ta hanyarta ne gabadaya zamu samu cikar burinmu.

Kallonsa kawai take ta kasa magana.

Ki daure don Allah.

Ya fada mata cikin rarraunar murya.

Tuni qwalla sun cika mata ido har sun fara zama hawaye, ita ma cikin rarraunar murya ta ce,

Yaya Mujahid kana son amfani da ni domin cika burinka, wallahi da zaka iya ratsa zuciyata zaka san ban cancanci haka ba

Ta zarce da shassheqar kukan da take ta faman riqewa.

Jikin Mujahid yayi mugun sanyi wani matsanancin tausayinta ya kwarfe shi, shiyasa yayi qoqarin yayi magana amma ya kasa, da ido kawai ya dinga jifanta da alamun rarrashi, sai can ya daure ya ce,

Bai kamata ki min wannan mummunan zargin ba, domin kina da martabar da ko giya na sha ba zan cutar da ke ba.

Tana qoqarin danne kukanta ta ce,

Bana zarge ka ba Yaya Mujahid, ba na so in ce ka cika son kai, amma ban ga ta inda wannan shirin naka ni zai amfane ni ba.

Ya jima cikin shiru sannan ya dago ya dube ta yana ta girgiza mata kai da sassaita hannu alamun rarrashi. Sai da yayi dabarar shigar da qwayar idonsa cikin nata ya sakar mata wani kallo mai sace qarfin halin masoyi sannan muryarsa a dashe ya ce mata,

Ki fahimce ni Nabila, ba nufina kenan ba, amma duk abinda kika zaba ki yi, wallahi ina da tabbacin ba zaki yi abinda zai cutar da ni ba, duk hukuncin da kika yanke min zan karba in gode.

Ya qare maganarsa da sakar mata wani qayataccen murmushi, sannan ya dinga tafiya da baya yana zaga mata hannu bai fasa murmushinsa ba.

Da kallon da yayi mata da murmushin da yayi mata da kuma yadda ya shige motarsa yana waiwayenta tamkar wata masoyiyarsa, wadda yake matuqar so har ba ya son rabu, duk wadannan abubuwan suka taru suka qarasa kwarkwarce dan karfin halin Nabila da son Mujahid da take dannewa, kawai ta ji ita da zuciyarta sun gama aminta da shi fiye da kowa a filin duniya, kuma babu abinda ba zaa iya yi domin shi ba. Haka ta saki baki tana hawaye cikin bin motarsa da kallo har ya qule.

Duk azancinta sai ta rasa ta bangaren da zata fara yafito wannan Game din, shin zuwa zata yi tayi fuska ta tari Antinta Binta ko kuma wata fuskar zata yi ta kada kai ta shige gidansu a zuwan ba ta san sun zo ba?

Hawayen fuskarta ne matsalarta, don haka ta zabi shawara ta biyu inda ta kada kai jiki a sanyaye ta tunkari qofar shiga cikin gida tana waiwayen inda motar Mujahid ta bace.

Tuni rudanin da Binta ta yi ya fara samar da kuka, ita da kanta ta fara neman manta Game din da ta zana wa Yaks. Hankali a tashe cikin mummunar fuskar da ta gaji da hada gumi ta dubi Yaks ta ce,

Yaks me ke faruwa ne? wancan gayen zai zo mana da halin karnuka.

Ya jahilce ta da idanuwansa wadanda suka kada suka yi jawur,

Wani abu ne ya faru bayan wanda kika sanar da ni?

Sai da ta sha kai komo da tunaninta sannan ta tuna cewa ta sanar da shi Mujahid ya hada ita da Nabila duk yana so, ko mummunan fata ne dai gashi nan ta yi ya tabbata.

Ta murje hawaye cikin muzanta ta hau karanto,

Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.

Ta zarce da sambatu,

Lamarin gaskiya ya zo min a bazata.

Da alama Yaks ba ya cikin nasa hayyacin, bai ma fahimci inda ta dosa ba.

Ita ma ta yi sagalo tana kallonsa a hankali tana bankwana da azancinta, shi da ya fi ta rashin hayyaci kawai sai gani ta yi da sauri ya shige motarsa cikin barin jiki, ta sunkuya jikin windo tana tambayarsa,

Ina zuwa?

Cikin fishi ya tabbatar mata,

Zan bi wancan dan iskan, wallahi sai na bi ta kansa da mota ko kuma mu yi mutuwar kasko.

Bai saurari cewarta ba ya figi motar har ta kusa faduwa, ta miqe da qyar cikin imanin babu abinda ya cancance ta yanzu face taqarqarewa ta rushe da kuka, amma a wannan kadaici menene amfanin ta rushe da kuka, wa zata nuna wa damuwar da take ciki ya tausaya mata har ya ji dalilin kukanta kuma in ta fadi dalilin wa zai fahimce ta?

Da ta rasa mafitar kawai sai ta tarkata kukanta da dukkan damuwoyinta suka runtuma cikin gidansu Nabila tana mai azama da qara daukar zafi, kaiconta daya duk abinda zata yi yanzu babu mai yi mata kallon sassaucin ba don kishin Mujahid ta ke ba, babu wanda zai fahimci ko daura mata Mujahid aka yi a qafa ba zata iya ja ba, amma qiyayyar da take masa ba zata bata damar zuba masa ido ya ci kashi a kanta da Nabila ba.   

*****

A nan zan dakata sai mun hadu a kashi na biyu.

<< Rigar Siliki 13Rigar Siliki 15 >>

1 thought on “Rigar Siliki 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.