Skip to content
Part 22 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Alhaji Ibrahim dawowarsa  ke nan daga masallaci ya karbi Mujahid da murna da mamaki.

“Barista ai na zaci karbar adireshina da sunan wataran za a kawo min ziyara duk bogi ne.”

Bayan Mujahid ya sauke kofin ruwan da aka tare shi da shi  ya amsa cikin dariya.

“Kai haba surukina, ai girman nawa ba a suna da fatar jiki ba ne kadai, ko ta ina muna kamantawa.”

Duk suka kacame da dariya.

Cikin tsananin farin ciki Alhaji Ibrahim ya ce.

“Ina murna da samun suruki nagari irinka.”

Cikin jin dadin nasara Mujahid ya amsa masa,

“Na fi ka murnar samun suruki mai sauqin kai irinka, ka fi Binta kirki, shi ya sa na fi sonka da ita.”

Alhaji Ibrahim ya yi dariya ya ce.

“Ah haba zance ka ke, ina jimawa ban ga mai kirki irin Binta ba, ita sam qyallin duniya ba ya dada ta da qasa ba, sannan ga ta so silent, ka san an ce zance ado ne, kawaici kubuta ne, ni shegen surutu ne da ni kamar na ci bakin Aku.”

Cikin gyada kai Mujahid ya ce.

“Wani shirun ba, amma wani shirun ai gara surutun da shi.”

Kai tsaye Alhaji Ibrahim ya wanke Binta da cewa.

“To ban da na Binta dai”

Mujahid ya kanne, ya ce.

“Haka ne.”

Suka saki wannan hirar suka koma wata, Mujahid ya ce,

“Mamaki na ke so in ba wa mutuniyar taka”

Alhaji Ibrahim ya tattara masa dukkan hankalinsa saboda muhimmancin Binta a duniyarsa, ya ce.

“Mamakin me?”

Mujahid ya yi fuska, ya amsa.

“Dazun nan na ji tana kurin ganinka ta ke son yi, ko da gaske ta ke ko da wasa ne oho mata, sai na yi niyyar na zo na kai mata kai kyauta a matsayin goron juma’a”

Alhaji Ibrahim ya ji ‘yar banzar murna ta kashe shi, shi a dole ga wanda a ke so, bakinsa kamar ya yage ya ce.

“To me ya sa ka ke son sai ya zama wasa? Ai gaskiya ne kurum, kai dai ka yi ta zama a bar ka a baya, 

ka qi yarda ko dandane ka yi wa soyayya bare ka nemo gora ka kamfata.”

Kamar Mujahid zai share sai ya ga asarar hakan, ya yi magana tun daga qasan zuciyarsa,

“Na fi ka sanin dadin soyayya Alhaji, tawa wuya da runtsi ba ta girgiza…”

Alhaji Ibrahim ya tare shi da raha.

“Mu ma tamu haka surukina, sannan ba boyayya ba ce, bayyanawa muke duk duniya ta gani”

Dariya kawai Mujahid ya yi.

“Yanzu na sanya a kawo maka abinci mu jira sallar la’asar sannan mu tafi.”

Cike da karsashi Mujahid ya kada kai.

“Dadina da kai surukina ka cika ganin abin da ya dace.”

Duka yi dariya suka yi, sannan Alhaji Ibrahim ya fice nemo mai samo wa Mujahid abinci, ya bar shi da dagewa roqon Allah ya tabbatar da taurin ran Binta a yau ta kori masoyinta da kanta.

Sai biyar saura Mujahid ya tura hancin motarsa harabar gidan.

Alhaji Ibrahim na zaune a gefensa, kuma tuni soyayya ta cika shi, a dokance ya ke da dora ido akan masoyiyarsa don haka ya fara rarraba ido yana addu’ar ya ganta ba tare da ya yi jiran a kira masa ita ba.

Tun tuni Mujahid ya ke sakin murmushin nasara da farin ciki saboda hango Binta da Yaks a zaune rashe-rashe  suna hira da nishadi, babu wanda zai gansu bai yi tsammanin riqaqqun masoya ba ne.

Tuni Mujahid ya lura da qawa zucin Alhaji Ibrahim, don haka ya yafito shi yana nuno masa Binta wadda a daidai lokacin nan suka lura da cewa Mujahid ne ya shigo, kawai sai suka hau wasan shirme, doke-doke da watsa wa juna lemo.

Da sauri Alhaji Ibrahim ya yi saurin dauke kansa lokacin da ya ga Bintansa da kanta ta kai hannu ta shafi labban Yaks ta kai yatsunta baki ta sumbata.

Ya dubi Mujahid wanda ya yi fuska yana qoqarin tsayar da mota tamkar bai san komai ba.

Cikin shesshekar numfashi Alhaji Ibrahim ya ce.

“Subhanallahi, wa’iyazu billahi, wane ne wancan suke shashanci da Binta?”

Kamar gaske Mujahid ya juyo a razane ya dubi su Binta wadanda a yanzu suke riqe da wani farin qyalle suna gwajin qarfi cikin annashuwa.

Da sauri Mujahid ya kawar da kai zuciyarsa cike da farin ciki, amma fuskarsa ta tattaro alhinin duniyar nan ta dora wa kanta, muryarsa na rawa ya ce.

“Lah…kar ka damu, dan uwanta ne.”

A qufule Alhaji Ibrahim ya tare shi.

“Wancan mai ruwan ‘yan iskan?”

Cikin saurin murya ya katse yana girgiza kai, sannan ya sake duban Mujahid idanunsa har sun fara kadawa ya ce,

“Yi haquri na zagi dan uwanku, amma wallahi iyakar gaskiyata na fada, bai yi kama da kowa ba sai dan iska, ya sami ‘yar uwarsa Binta…”

Har yanzu alhini ne narke a fuskar Mujahd, ya dakatar da Alhaji Ibrahim da cewa,

“Na fada maka kar ka damu, wallahi gaskiyar ke nan, dan uwanta ne…”

A matuqar qufule Alhaji Ibrahim ya katse shi da fadin,

“Ka daina fadar haka don Allah Mujahid, dan uwanta kamar ya ya? Dan uwanta sai ka ce a cikin tasha… Gaskiya kun yaudare ni…”

Ya fara maganganu masu kaushi na nuna fita hayyaci.

Sai da Mujahid ya fahimci an kai gejin da ya ke so sannan ya juya da motar a guje ya fice daga gidan tamkar mai shirin tashi sama.

Binta da Yaks suka tuntsire da dariya, Yaks har da kwanciya a qasa, yayin da Binta ta kasa misalta farin cikin da ta yi, ita a fadin duniyarta yanzu babu abin da ke faranta mata sama da ta muzguna wa Mujahid.

Sai da Mujahid ya yi nisa da unguwarsu sannan ya sami gefen titi ya faka,kafin wannan lokacin tuni Alhaji Ibrahim ya gama sambatunsa, ya yi shiru yana ta faman hada gumi.

Duk son da ya ke wa Binta bai rabi juriyarsa da kuskuren aura wa ‘ya’yansa uwaa tagari ba, ‘yan iska ma da suke iskanci gidansu suke bari su tafi daji su yi, wasu har garin haihuwarsu suke bari, amma ita Binta wani loko ta ke lafewa a cikin gidansu ta yi sharholiyarta, babban abin qazantar ma wai da jininta, wannan lissafin ya fi qarfin kwanyarsa.

Mujahid ya kwaso ustazancin duniyar nan ya yayyaba a muryarsa da fuskarsa ya fara magana.

“Ban ji dadi ba idan ka bari wannan qaramin abun ya taba zuciyarka a kan Binta, ina qara rantse maka da Allah Binta mutumiyar kirki ce, iyakar sanina.”

Alhaji Ibrahim ya daga kai ya dube shi idanunsa jajir tamkar hadarin da ya yi fushi ya ke son zubda ruwa.

“Na ji dadi da ka ce iyakar saninka, ni kuma iyakar sanina shi ne abin da na gani yau…”

Mujahid ya tare shi a tausashe.

“Ka maida hankali surukina, wannan bai zama abin zafin da zai damu ranka ba, ba auren Binta za ka yi ba? Ai za ka iya mayar da ita duk yadda ka ke son ta zama”

Alhaji Ibrahim ya kashe Mujahid da wani mugun kallo mai kamar yana shirin tashi ya shaqe shi, ransa raya masa ya ke duk jirgi daya ya kwaso Mujahid da Binta, jininsu daya, komai ma babu laifi a wajensu, don haka ya ce masa ganin da ya yi wa Binta tana wasan banza ba wani abu ba ne, wataqila rashin samun tarbiyya managarciya ce ya sa suke kasa  bambance fari da baqi.

Idan dai duk tunaninsu ke nan, to tabbas bata wa kai lokaci zai qara idan ya ci gaba da qoqarin wayar wa da Mujahid kai game da irin radadin da zuciyarsa ke shaqa a halin yanzu.

Ya tattare dukkan qawa zucin saya hadiye, muryarsa a shaqe ya ce,

“Ka ga kai ni gida ko ka mayar da ni ofishina, ko ma ka bude min na sauka na nemi abin hawa.”

Cikin halin ko-in-kula Mujahid ya tashi motar yana cewa,

“Haba duk abin ai bai yi zafin haka ba, bari na mayar da kai ofis din… amman dai ba haka na so ba. Na yi niyyar na faranta muku ne ku duka.”

Alhaji Ibrahim dai bai tanka ba, illa ya bar Mujahid na ta yi masa batutuwan kwashe tabarmin kunya da hauka a ganinsa, har ya kai shi ya dire.

“Gobe qarfe nawa za ka turo ne? an fada min a gida amma na dan sha’afa ga shi ina son kai wata ziyara.”

Kamar Alhaji Ibrahim ba za yi magana ba sai kuma ya daure ya yi cikin yanayin boye fushi.

“Sai dai yadda ta yiwu qila, kana iya zuwa ziyararka ka dawo.”

“To babu laifi.”

Mujahid ya fada cikin shanye farin ciki, ya tashi motarsa ya bar gurin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 22Rigar Siliki 23 >>

1 thought on “Rigar Siliki 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×