Binta mace ce da ba ta iya sanya wa kanta damuwa ba, musamman idan ta nemi abokin tattauna matsalarta ta rasa, dalilin kiran Nabila kenan wadda ta fi amincewa sama da kowa duk da kuwa idanuwan Mujahid na ratsa kansu tare.
Ta yi tunanin idan Nabila ta zo za ta farke mata komai dangane da shirin da ta yi da Yaks, ba don komai ba, sai don ko bayan mutuwarta a samu mai yi mata shaidar ita fa ba mazinaciya ba ce.
Sannan in so samu ne, ta so idan Nabila ta zo ta wakiltata ta je ta wayar wa. . .