Binta mace ce da ba ta iya sanya wa kanta damuwa ba, musamman idan ta nemi abokin tattauna matsalarta ta rasa, dalilin kiran Nabila kenan wadda ta fi amincewa sama da kowa duk da kuwa idanuwan Mujahid na ratsa kansu tare.
Ta yi tunanin idan Nabila ta zo za ta farke mata komai dangane da shirin da ta yi da Yaks, ba don komai ba, sai don ko bayan mutuwarta a samu mai yi mata shaidar ita fa ba mazinaciya ba ce.
Sannan in so samu ne, ta so idan Nabila ta zo ta wakiltata ta je ta wayar wa da Alhaji Ibrahim kai, ba don a yo bikonsa ya zo ya aure ta ba, sai don a fita haqqinsa, kuma ya wanke ta daga baqin zaton da zai aza mata.
To amma kwana uku da faruwar lamarin ba Nabila babu alamarta, kullum cikin ga ta nan ta ke, sannan daga baya ta gabatar da uzuri.
Damuwa ta ishe ta, babu wadataccen rarrashi sai daga ‘yan qannenta, musamman Ummi qanwar Mujahid wadda a cikin gidan sun fi shaquwa, kuma ita kadai ce ba ta wani dada kanta da qasa a soyayyar da yayanta ya ke mata ba.
Amma Hajiya ban da kyautar harara da qyara ba ta samun koma a tare da ita, tamkar ita ta yi yekuwa ta hana Alhaji Ibrahim aurenta.
Tana fama da wannan jinyar kwana da kwanaki, rannan sati guda Mujahid ya kintaci yamma ya quga mata daki ya same ta sanye da zabgegen hijabinta riqe da zabgegen carbi tana kishiingide tana ja, duk da dakin a hargitse ya ke da shirgi nan da can bai hana shi tashin qamshin airfreshner mai dadi ba.
Qamshin ya yi tasiri a zuciyar Mujahid sosai, har ya yi tasirin rage masa fushin bogin da ya shigo da shi.
Binta ta dago kai a fusace ta tsura masa ido da alamun tsana qarara.
Shi kuma ya yi fuska yana nuna mata yatsunsa biyu.
“Kin ga kar ki tare ni da hayagaga, abu biyu ya kawo ni”.
Ba umarninsa ta bi wajen yin shiru da kawar da kai, kawai tsabar takaici ne ya hana ta magana.
Ya fara magana cikin tattausar murya.
“Na farko na ga kwana biyu kin buya a cikin daki ne, shi ne na biyo sawu in ga ko lafiya? Sannan in taya jajen abin da ya faru”.
Ya yi shiru yana jiran sababinta ko abin da ya samu, amma ta share shi.
Ya tsura mata ido da kyau yana nazarinta, ta rame sosai, damuwarta na tasowa ne tun daga tsakiyar zuciyarta a lurar da ya yi mata ke nan.
Da ya ke ya jima bai yi mata irin wannan kallon qurillar ba, yanzu sai ya ji miliyoyin sonta sun taso masa, muryarta kawai ya ke son ji, ga shi kuma ta datse lebe.
Ya hanga ya hanga sannan ya tuno abin da zai zunguro ta da shi, sai wata dabara ta fado masa.
Ya sake karkacewa yana yi mata dariyar da biyu.
“Au na manta ban miki wani jajen ba, kwana biyu kin guje wa mai debe miki kewa, wanda kuma zai debe miki ta gasken kin gurgunta aurenku”.
Tun kafin ya rufe baki a qufule ta ce,
“Ina zargin da sa hannunka, saboda haka zaman nan da na ke Ubangiji na ke kai wa qararka, kuma ga shi tun a yanzu ya bayyana min kai a cikin lamarin”.
Ya zaro ido yana dariya da nuna mamaki.
“Amma dai ya kamata a ce cikin kunya ki ka yi maganar nan.”
Duban rashin fahimta kawai ta yi masa,
“Duk rashin tsarkinki ba ki ji kunyar Allah ba ki gurfana gabansa kina kai masa qarar mutumin kirki irina? Ko ba kya tuna abin da ya kori wanda za ki aura ne?”
Ta kasa magana.
Shi ya ci gaba cikin qarfin gwiwa.
“Da kina da kirki ko hankali, ya kamata ki ba ni jinjina, ni na ganki ya kai sau dari a yanayin da bai dace ba tare da Yaks, amma ban fasa yunqurin lallai sai na auro ki ba, ke ban ma fasa sonki ba, kin ga Alhaji Ibrahim daga ganin wannan a sha ruwan tsuntsayen naku na jiya ya fitittike ya janye wa aurenki, to ki ce da shi ya ga Yaks sagale da qugunki yana kokawar zira miki harshe a baki hadiyar zuciya zai yi ya mutu…”
Tuni Binta ta miqe zaune ta nemi kujera cikin haki ta zauna tana waige-waige tamkar tana zargin wani zai iya jiyo su.
Kamar za ta rushe da kuka ta ce,
“Kai Mujahid ka ji tsoron Allah, yaaushe ka ga yaks sagale da quguna?”
Tana rufe baki ya amsa.
“Kina nufin sagalo qugu bai kai tsoma harshe cikin baki ba ne? To ai na taba ganin abin da ya fi shi tare da ku, kuma ko a gaban waye zan iya bayar da shaida”.
Ta nuna masa qofa cikin tsananin tunzura.
“Tafi bayan duniya ka bayar da shaida”.
Ya zauna bakin gado yana tutture kaya.
“Ai ba sai kin aike ni ba ko dauka na rakiya ki ke lokacin da ki ke asharki?”
Wannan karon ma ta kasa magana.
Ya miqe tsaye yana fadin.
“Zan fadi dalilin zuwana na biyu kafin na wuce”.
Kallonsa kawai ta ke.
“Na zo roqon alfarma ne, tunda Ibrahim ya tsere, ga shi kina cikin damuwa saboda an guji aurenki, don Allah don Annabi ki taimaka ki ba ni dama na maye gurbinsa, duk abin da ki ke zaton ya iya da wanda ki ke shaidar Yaks ya iya, babu wanda ban iya ba, har alakoro sai kin samu, kuma ni ma da gaggawa zan fito, ke ko a gobe ne zan iya turo waliyyaina…”
Binta ta fara hawaye tana nuna masa qofa.
“Mujahid ka fita ka ba ni guri, in ka gwada cewa kana sona a gaban iyayenmu Allah ya isa ban yafe ba, hakazalika in ka qara shigo min daki”.
Yana dariya ya amsa mata.
“Allah ya isar shigowa daki dai zan guda, amma maganar kai zancen so tawa Allah ya isar ta riga ta qi zuwa, don ina jin maganar ma tana hanyar Voto ko ma ta je”.
Yanzu ta fara shesshekar kuka.
“Na yi kaico! Kuma na yi ina ma din ban rayu a matsayin jininka ba, ban rayu a cikin danginka ba ballantana har igiyar zumunci ta aura min kai bisa dole”.
Ya zaro ido cikin mamaki da tura haushi.
“Ya ya ki ka yi saurin bayar da gari haka? Amma dai zan tuna miki cewa, sa’a ce kawai ba ki da ita a rayuwa, ko ina ki ka sami kanki sai kin rasa ta don ba ki da jininta, ni da na ke da ita a jinina ba ki lura duk abin da na ke so samu na ke ba?
Na tsiru a danginki don na ci amfanin hakan ni kadai ba don ko kala ki samu ba.
Zan ci wannan alfarmar in aure ki don ina sonki ba dan kina sona ba, zan rayu da ke don haka na so rayuwa ba haka ki ka so ba, za ki haifa min ‘ya’ya a kira su iyalina, na so hakan, amma ke kin guda… alfarmar da zan ci a ke fa da yawa Binta, ke ba za ki tsira da komai ba sai wahala da qiyayya, saboda ba ki da sa’a…”
Ya tsagaita yana mata kallon tura haushi, duk da ya lura kamar numfashinta zai dauke saboda quluwa, bai damu da yanayinta ba ya ci gaba da cewa.
“Amma babu komai, a haka za ki ci gaba da burge ni, in na wawuro tawa nasarar zan kawo mu ci tare tunda ke babu a jininki”.
Kuka ya sake cin qarfinta tana kukan tana ce masa.
“In ka yarda ka aure ni, wallahi ka shiga uku Mujahid ba zan taba sonka ba har abada.”
Ya ja jiki ya wuce yana cewa.
“Ahaf! Zancen ki ke so.”
Har ya kama qofa zai murda ya fita sai kuma ya yi fuska ya juyo ya dube ta.
“Yanzu na zo kin same ni a fayau haka za ki bar ni na fita a fayau, alhalin na san kina cikin kewa tunda kin hana Yaks rabarki? Ki ba ni wata dama ko kadan ce, Yaks ba zai nuna min tsotsar harshe ba.”
Binta ta gama kai wa qarshe, don haka tun qarfinta ta takure ta kurma ihu tare da kiran.
“Hajiya!”
Tun kafin ta gama sauke murya Mujahidd ya bace daga dakin cikin tsananin dariya.
Hajiyar da Ummi da Karima har ma da Sani suka bazamo dakin a gigice, sai suka sami Binta tsaye dore da hannu aka tana kuka shabe-shabe da hawaye.
Hajiya da Sani suka tsaya suna kallon-kallo, sai Ummi da Karima ne suka balle littafin kashe Binta da tambayar abin da ya same ta.
Binta ta kasa amsawa face bin Sani da Hajiya da kallo.
Hajiya ta riga Sani magana.
“Ka fada mata ne?”
Da sauri ya girgza kai.
“Ni da na shigo gidan yanzu Hajiya?”
Cikin bata gira Hajiya ta dubi Binta ta ce.
“Ke wai sokuwar ina ki ke son ki zama, me ya same ki?”
Binta ta sake faashewa da kuka ta ce.
“Don Allah Hajiya ki yi wa Yaya Mujahid tsakani da dakin nan, in ba haka ba wataran za ku shigo ku tsinci gawata ya kashe ni da baqar magana”.
“Ikon Allah”
Hajiya ta fada cikin mamaki, kuncinta dauke da matsananciyar fara’a.
Ummi da Karima ma yanzu kallon-kallo suke.
Abin da kuma ya sake daure wa Binta kai ke nan, ba ta wartsake wannan ba ta ga Hajiya ta dubi Sani ta sake tambayarsa.
“Shi Mujahid din ka sanar masa ne?”
Sani ya ci laya.
“Wallahi Hajiya ni dai ban sanar masa ba.”
Dakin ya dan yi shiru na wani lokaci, kowa zuciyarsa cike da dokin ganin yadda za ta kaya idan qwai ya fashe.
Can Hajiya ta dake fuskarta a daure ta ce.
“Ai maganar tsakani ma ta wuce, miji da matarsa babu mai yi musu tsakani”.
Binta ta zaro ido, zuciyarta kuma na qoqarin zaro kanta ta tarwatse, a gigice ta ce.
“Waye mijin wa?
Kamar da doki Sani zai ce, Mujahid mijin Binta, sai kuma ya dake ya bar Hajiya da ta isa ta qarasa.
A tausashe ba kamar dazu ba Hajiya ta yi magana.
“Kin san yau Alhaji ya je Voto ko?”
Ba cikin hayyaci ba Binta ta gyada kai.
Hajiya ta dora da cewa.
“Tun ranar da saurayinki ya wulaqanta miki iyaye suka tunzura, Yayan Babanki Malam Adamu ya yi rantsuwar ba za ki debi kwanakin da har wancan mayaudarin zai ganki babu aure ya yi zaton jiransa ki ke…”
Binta ta dauke wuta tuni, don haka zuciyarta ba ta wassafa komai ba face zurara wa Hajiya idanu.
Hajiyar ba ta damu ba ta ci gaba.
“To da ma yayanki Mujahid ya bayar da cigiyar a samo masa mata, shi ne su kuma suka ga ke din me da ke ma ba za a samo miki miji ba? Suna wannan laluben ne kawai sai suka samo muku juna, kuma da ya ke abin na gida ne daga zuwa kai sadakin suka qudura aure suka huta, dazun nan Alhaji ya yi waya ya sanar da ni!”
Iyakar qarfin Binta ta dage ta sake kurma ihu, cikinsa ta ke ta faman maimaita.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”.
Kafin ta koma sambatu.
“Wannan qofar bala’in me na yi na bude ta? Allah ka yi min qatuwar jarrabawa, Allah Binta ce Ka aura wa abin da ba ta so Mujahid, Allah dauki raina na huta da wannan azabar da na ke dandana…”
A hankali sai ta sulale ta fadi wajen a sume.
Faduwarta ta yi daidai da shigowar Nabila dakin da gudu saboda hayaniyar kukan Binta da hirjinta.
Kafin kowa ya yunqura tuni Nabila ta isa ga Binta ta tattaro ta cikin kuka ta rungume tana fadin,
“Anti Binta me ya same ki, ki yafe min kar ki tafi ki bar ni, ba a son raina na qi amsa kiranki ba har zuwa yau…”
Ko ba’asi Nabila ba ta nema ba ta rungume sumammiyar Binta ana zubo mata ruwa tana shafa mata a fuska.
Kowa a firgice ya ke, sai dai firgitar Hajiya ba ta kai yawan da ko kusa da jin nadamar auren ba.
Da gudu Sani ya ba-zamo ya kira Mujahid, shi ma bai sanar da shi dalili ba kawai dai ya ce masa, ya zo Binta ta fadi ta suma.
Suka shigo dakin a hargitse, Mujahid bayan kaduwar suman Binta yana cike da fargabar ko abin da ya yi mata ne ta kasa jurewa har ta gayyato wa kanta suma, idan haka ne shi da kansa bai kamata ya yafe wa kansa ba.
Ya durqusa gabansu yana neman ba’asi, ita kuwa Hajiya ta nutsu ta karanto masa yadda aka yi.
A durqushe nan shi ya kusa suman farin ciki, amma Nabila da zuciyarta ta kufce sai da ita ma ta zube wanwar a wajen.
Masoyinta ya kubce mata ya auri Binta, wannan asarar ita da gangar jikinta ba za su iya dauka ba, dole su runtse ido su yi sallama da wannan duniya.
Dakin ya kaure da hirji da sallallami, ana ta tarairayo marasa lafiyan, amma Mujahid ya qi shiga cikin karakainar.
Ya miqe cikin rashin hayyaci yana tafiya da baya, tuni idanunsa sun cika da qwalla.
Yanzu Hajiya ta yi mugun rudewa, fadi ta ke.
“A je a fito da mota dukkansu a kai su asibiti”.
Kowa ya cika wa Mujahd kunne da zuciya, Hajiya na umartarsa fito da mota, Ummi na kiransa ya kama mata Binta Karima na kiransa ya kama mata Nabila.
Wasu zafafan hawaye suka fara ratso idonsa, qirjinsa ya yi nauyin da bai taba jin irinsa ba.
Wa zai je ya sanya hannu ya kama don nuna kulawa?
Wadda ya ke tsananin sonta amma qiyayyarsa ta sanya ta suma, ko wadda ta ke tsananin sonsa baqin cikin rasa shi ya sanya ta suma?
Binta zuciya ce kawai ke azabar sonta, amma Nabila ce ta cancanci kulawa don cancanta.
Yanzu so ya ke ya fara shesshekar kuka ba tare da ya iya zabar komai ba sai kukan.