Tana jin motsin taba qofarsa ta shigowa cikin gidan ta yo fit ta fito daga daki ta yi tsaye a tsakar gidan ta yi fuska tana kallon qofar shigowa yadda yana shigowa zai yi arba da ita kuma zai fahimci cewa tsaiwarsa ta ke.
Haka kuwa aka yi, ya shigo da sallamarsa muryarsa sake kamar yadda ya saba duk da ya san ba ya samun amsawarta, yana sanye da farar shet mai dogon hannu da bakin wando, akwai alamar mai kwat ce ya cire ta ya huta, hannunsa daya rike da wasu litattafai, hannu dayan kuma riqe da ledar take. . .