Skip to content
Part 30 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Tana jin motsin taba qofarsa ta shigowa cikin gidan ta yo fit ta fito daga daki ta yi tsaye a tsakar gidan ta yi fuska tana kallon qofar shigowa yadda yana shigowa zai yi arba da ita kuma zai fahimci cewa tsaiwarsa ta ke.

Haka kuwa aka yi, ya shigo da sallamarsa muryarsa sake kamar yadda ya saba duk da ya san ba ya samun amsawarta, yana sanye da farar shet mai dogon hannu da bakin wando, akwai alamar mai kwat ce ya cire ta ya huta, hannunsa daya rike da wasu litattafai, hannu dayan kuma riqe da ledar take away, sai a yau ta san cewa daga waje yake shigowa da abincinsa.

Karon farko ya hada ido da ita, zuciyarsa ta bijiro da mararin ganin idon abar so, amma kuma wata jarumar zuciyar nan da nan ta halarto da gizago, yayi saurin kawar da kai ya doshi hanyar benensa yana qara jin takaicin rashin amsa masa sallama da ba ta yi ba, duk da tsaiwarta na nuna lallai fa shi take jira, sai kuma yayi sauri ya kori jin haushin don wataqila ma jiran bai wuce na ta bude shafin nuna masa qiyayya ta karanta ba, in haka ne lallai ta yi daidai in ba ta amsa masa sallama ba, don masoyi ake nemarwa aminci, duk da ba haka qa’idar sallamar ta ke ba, amma ai ita Binta ba ta damu da karya ko wacce irin doka ba.

Yana sanya qafarsa a matakalar bene ta farko ta yakice tsoro da fargaba muryarta na rawa ta ce masa,

 “Ina magana.”

Yayi biris ya cigaba da da hawa matakalar cikin azama.

Ta sake daga murya ta ce,

“Na ce ina magana.”

Ya sake sharewa.

Cikin takaici ta biyo shi qafar benen a hasale ta ce,

“Wai Mujahid ba ka ji ina cewa ina magana ba ne?”

Ya dakata da hawan ya juyo ya dube ta fuskarsa a bace,

“Kike magana kike cewa me? To ba sai ki yi ta maganarki ba, ni na hana ki magana ne.”

Ta gwaro ido alamun razana da mamaki, bakinta na rawa ta ce,

“Sai na yi ta yi ka ce?”

Tana rufe baki ya amsa mata,

“Haka na ce, ko kina so na maimaita miki ne?”

Ta qara hasala,

“Eh maimaita in ba ka da aikin yi”

Ya juya ya cigaba da hawa Benensa yana cewa,

“Ke da kike da aikin yi ai sai ki ja tsumman maganarki da quncinki ki je ku ji da juna, ni babu mai sa ni haushi.”

Cikin fishi Binta ta daka tsalle ta bi saman har suka hau, kafin ya shiga daki ta sha gabansa,

“Ka san Allah, sai ka saurare ni.”

Yayi fuska ya nuna mata qasa,

“Kin ga qasan can? In ba ki yi wasa ba zan cilla ki, ba zan saurare ki ba yanzu wallahi, ke kullum ma ba zan saurare ki ba, in dai zan shigo gida in miki sallama wai sunan kina ‘yar musulmi kina kallon idona ina kallon naki ki qi amsawa, kuma don fitsara ki kwaso magana ki yi da ni, ko wacce ce ba ki isa ba na rantse miki… saboda haka ki matsa ko na wurga ki.”

Ba tsoron wurgin ya sa ta jan jiki ba, jin dalilin rashin sauraronta ne ya sa jikinta yayi sanyi don ta san dalilin ya isa dalili, kawai ba tare da ta tanka masa ba ta ja jiki ta sauka qasa, inda shi kuma yayi wucewarsa daki yana nuna ba komai, duk da zuciyarsa ta rune da qauna da kuma son jin maganar da ta zo da ita, amma tunda ita ‘yar qwaya ce, zai shekara yana nuna mata irin kanta me tururi.

Ya shiga falonsa wanda nan ne falon nan ne kuma dakin baccinsa, shimfide yake da darduma sai kuma qaramar katifa, akwai takardunsa da litattafai barbaje nan da can sai fulasan shayi biyu da kuma jakunkunan kayansa, rakin takalma da kuma rakin kaya, da sauran tarkace. Dakin dai a cunkushe yake, ga shi ba ya samun wani cikakken gyara, dama ko fenti ba shi da shi.

Cikin matsawa kai kwantar da hankali ya zauna ya ci abincinsa, ya dan huta sannan ya tashi ya koma sabgarsa. Binta ce dai ba wata ba, to tunda ya mallaka ba ya garajen ranar da zata zama tasa ciki da bai, zai sami hakan ta hanyar da ba zai taba sarayar da mutuncinsa kamar yadda take neman yayi ba.

A ranar ma bai  koma gida da wuri ba, don gidansu ya wuce ya sha hirarsa da mutan gidan, masu karamci da girmama mu’amala da mutane, ya sha rantsuwar da Binta ta biyo halin Hajiyarta dari bisa dari ko gaba da qiyayya ta ke masa ba ma wai qi ba, ba zata dinga karya doka tana cin mutuncinsa da qin ba ko kuma cin alwashin har abada ba zata daina ba, ko kuma shirin a kula ta ta ci fuskar mutum.

Bai waiwayi gida ba sai qarfe tara na dare, kamar dazu ya same ta tsaye, ya boye razana yayi fuska yayi sallamarsa cikin walwalar murya kamar yadda ya saba.

Ita kuma da alamun dolenci da rawar murya ta amsa sallamar, sannan ta qara daure gira ta ce,

“Sannu da zuwa.”

Ba tare da bata muhimmanci ba ya doshi bene yana amsa mata da,

”Yauwa.”

Ta qara bata murya ta ce,

“Yanzu zaka iya saurara ta.”

Ya dan dakata yana duba agogon hannunsa,

“Ina jin ki, ni yaqi ne bana so don ba ni da lokacinsa, ke kika zo da magana ba ni na zama kare na zo da maganar ba, amma sai wani cin magani kike kamar na zo ki yi min alfarma, ni wadannan tashe-tashen hankulan ne sam ba ni da lokacinsu.”

Hawaye ne ke son bullo mata a ido tana doje masa,

“Eh, ka fadi duk abinda kake son fada a kaina, lokacinka ne Mujahid, ni ce karya na balla gabarka na kula ka.”

Ko daya fuskarsa ba ta nuna sha’awa a abinda ta fada ba, sai ma sake bata rai da yayi ya dubi agogo ya sake kallonta, muryarsa ba yabo ba fallasa ya ce mata,

“Shikenan maganarki na tafi?”

Ta daure ta amsa,

“Dama inda na nemi aiki ne suka kira ni tantancewa gobe”

Har ya fara tafiya,

“To babu laifi Allah sanya alkhairi, sai ki kira Yaks din ya kai ki kenan ko?”

Ta yi saroro a wajen tana bin sa da kallo yana qulewa, sai yanzu ta fara tunani a kansa, wai ma me yake nufi da ita ne? da gaske ya kawo ta gidan nan ya garqame ne don kawai ya dinga gasa mata aya a hannu kamar yadda ya gada, in ba don haka ba na menene wannan zafin kan da qoqarin nuna mata ba ta isa ba? 

Ta juya daki cikin hawaye da radadin qirji, a ranar duk da tana murnar zata sami aikin da zata dinga baqanta masa rai amma ta fara shakkun in ma zata sami cikar burin, bisa la’akari da yadda babu wani dar ya shiga sanyawa aikin alkhairi, sannan don cin fuska da son ya cigaba da zarginta ya ce wai ta kira Yaks ya kai ta.

Ko ta qi Allah ta san yanzu ba fansa ba ce ta cigaba da hukunta Mujahid da batun Yaks, don zata iya dibar zunubi sannan zata iya daure kanta yadda babu mai kwance ta sai Allah, don haka ta ji wani tsinanne qunci ya ishi rayuwarta, da alama ba Mujahid ne kadai naqasu a rayuwarta ba, rayuwar tata ma gabadaya zata iya zama naqasu tunda an cakuda ta da Mujahid din.

Ranar dai bacci rabi da rabi ta yi gauraye da da tashin hankali da neman mafita, ita buqatarta yanzu ba ta wuce ta wuce wannan siradin na fara sa qafa ta fita ba, in ta wuce nan duk darun da Mujahid zai zo da shi dazun ne, don ba ta da wajen ajiyar baqin cikinsa.

Ta hana kanta baccin safe don kar ya fice ya bar ta, ta yi tsaye qofar daki tana, hangensa yana sakkowa daga bene, ya sha gayunsa, ya kuma sha kyansa, da ta qara lura sai ta ga shi sam ma ba ya tare da ko wacce irin damuwa, don har ya murje  ya ma yi qiba, kenan duk wata asara ita aka tarawa, ita aka aurawa abinda ba ta so kuma ita zata mutu cikin wannan damuwar.

Ta jajibi takaicinta suka fita suna jiran sakkowar Mujahid. Wannan karon ya dan dube ta da fuskar rahma, kamar zai yi magana kuma sai ya cinye abarsa, yayi fuska zai wuce,

Ta daure da rawar murya ta ce,

“An tashi lafiya.”

‘Lafiya qalau.”

Ya amsa mata a taqaice, kuma fuskarsa ba ta nuna farin ciki ko akasinsa.

Ta sake magana cikin rawar murya,

“Za ka sami sarari qarfe tara da rabi ka dawo ka kai ni? Qarfe goma ne lokacin da suka ba ni”

Ya dan jinkirta kafin yayi magana da yanayin lissafi, amma nan farin ciki ne yake ta qwallo da shi yana qwatar kansa da qyar, sai can a qasaice ya ce,

“Zan shiga kotu qarfe takwas, zan koma tara, me yiyuwa na samu kaina zuwa tara da rabi din, in hakan ta samu zaki gan ni, in ba ta samu ba kuma na dara minti goma kina iya tafiyarki.”

Ta shiga qunquni,

“Ni ba abinda ya shafe ni da shiga kotunka, ni maganar kai ni na yi…”

Ya sa ido qir yana kallonta don ba ya jin abinda ta ke cewa, har zai yi magana ya tambayeta sai kuma ya tuna tunda take boyewa ba abin kirki ba ne, jin ba zai amfanar da shi komai ba, don haka ya kama hanyar fita zai wuce abinsa.

Dole ta qara magana ba don ta so ba,

“Ni dai kawai ina jiranka.”

Ta juya ta shige daki.

Yayi dariya ya kada kai ya wuce abinsa, ka ji wauta, wai ita dai kawai tana jirasa kamar ita ta haife shi da dole ne yayi mata abinda take so. Ba don yana son ba ta dama ta yi duk iyakar abinda zata iya ko wanda ta tanada na jin da shi zata baqanta masa rai ko ta muzanta masa ba, da babu abinda zai sa shi dawowa ya kai ta, in yaso in tana da mataki sai ta dauka. To yanzu shi ne kan gaba wajen ganin ta fara aikin, ya ci wa kansa alwashin duk abinda ta rakito zata ba shi haushi da shi, ta sanadinsa zai mayar mata da abinta.

Ya kammala cikin lokaci, amma saboda tsabar ya guma mata haushi, ya kusa zuwa gidan yayi fakin a gefen hanya yana cinye lokaci a wofi, sai goma saura kwata ya isa qofar gidan, tamkar tana tsaye ne dama tana jiransa, yana kashe motar sai ga ta tafito, karo na farko kuma ya karbi saqon da ta ke da niyyar tura masa dalilin aikinta, wato ta fece ado tamkar mai zuwa gasar kwalliya, bai sha wahala ba wajen tunowar ya fada mata yana da kishi, don haka ba ya son mace mai kyau mai ado wadda za’a gani a yaba masa.

Ya ji mintsinin saqon nata amma dai ya murje abinsa a zuci, ya yi fuska ta shigo motar ya ja suka tafi ba tare da ko tari dayansu yayi ba, sai figar motar yake a guje don dai ya nuna mata yana sauri ya kaita wannan aikin jihadi da ta sa kanta.

Ita ma ta yi fuska sai taunar cingam take tana faman tabe-tabe a waya.

Cikin haka wayarsa ta yi qara ya daga, hantar Binta ta yi mugun kadawa da ta ji ya ce,

“Nabila barka da hantsi.”

Binta ta dauke numfashi saboda kar qararsa ta hana ta jiyo abinda Nabila take cewa a can bangaren kasancewar wayar tasa da ‘yar qara ana iya jiyowa.

A ladabce Nabila ta ce,

“Yaya Mujahid an tashi lafiya?”

Cikin kulawa ya amsa mata,

“Lafiya qalau wallahi, ya jikin Inna?”

“Inna ta ji sauqi, Yaya Mujahid na ga Missed Calls naka ne, ina fatan lafiya”

Yayi dariya,

“Ke kuwa sai babu lafiya zan kira ki? Ai na kira ki ne musamman don na gaishe ki kuma na ji lafiyarki.”

Ita ma tana dariya,

“Ina cikin qoshin lafiya Yaya Mujahid, na gode qwarai da gaske.”

Ya ce mata,

“Kar ki damu, haqqina ne, sannan kin cancanci fiye da haka.”

Cikin kunya ta ce,

“Ina qara godewa Yaya Mujahid, ka gaisar min da Anti Binta da kyau”

Sai da ya dan bata murya ya amsa, sai dai yadda Nabilan ba zata fahimci komai ba sai ita Bintan da aka yi don ta ji Haushi.

“Zata ji”

“To Yaya Mujahid sai mun sake waya”

“Babu laifi, cikin satin nan zan sake leqowa na gaishe da Inna”

Nabila ta amsa,

“Zata yi murna”

Suna dariya sannan suka yi sallama ya ajiye, kuma ya sake bata fuska tamkar bai taba dariya ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 29Rigar Siliki 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×