Skip to content
Part 36 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Jikin Mujahid a salube ya shiga dakin da Binta ke kwance. Bai tarar da Salima ba sai Binta kawai zaune kan gado ta kwanta jikin filon da ta jingina da bango.

Fuskarta nan nuna farfadowa daga cuta, idanunta sun yi zuru-zuru, sai dai fa ko kadan babu wani annuri a tare da ita wanda zai sa a zaci tana cikin tashin hankali ko kuma nadama, kallon iskar da ta saba wa Mujahid da shi ta karbe shi yau ma.

Shi yau tasa fuskar babu walwalar da ya saba tarenta da ita duk irin yadda ta kai ga bori, hasalima bata taba ganinshi cikin bacin rai irin na yau ba tun saninta da shi, amma a hakan ta debe shi ta watsar.

Ya ja kujerar gaban gadon ya zauna yana miqa mata takardun da likita ya watsa masa cikin kallon fuskarta kai tsaye.

A wulaqance ta karbi takardar ba tare da ta duba ba ta yasar gefe, kuma cikin shan qamshi ta dube shi da kyau ta ce,

“Ni ya fara kawo wa na gani kafin ya baka”

Sai ya sake dubanta cike da mamaki, ya ce,

“Kin kuma duba takardar kin ga rainin hankalin da take dauke da shi?”

Ta sake watsar da kai gefe tana cona baki,

“Na gani, ai ba rainin hankali ba ne, iyakar gaskiyar kenan”

Yanzu duban mahaukaciya yake mata.

Dan ta nuna masa da hankalinta ta juye ta dubi qwayar idonsa fes! Ta ce,

“To wai kai meye na tashin hankali don an ce ina dauke da cutar qanjamau? Ko ka manta tuni ka ci alwashin ko yaya zan kasance kana so? Ai baka zabi in na zo da qanjamau baka so ba, in kuma zaka zaba yanzu ma bata baci ba”

Mujahid ya jima da hankalinsa tsakanin qarya da gaskiya a tunani da hasashe, sai can ya miqe cikin nuna yaqini da qumaji ya ce,

“Na tuna an yi hakan, ban zabi qanjamau ba, amma yanzu na zaba… nan gaba ma in zaki zo da abinda yafi qanjamau ke da su duk ina so… kar ki damu, ki ji sauqi ki zo mu koma gida mu cigaba da jinya… in ma lahira kika tafi zan nade qafar wando na bi ki”

Bai jira cewarta ba ya sa kai ya bar dakinta cikin rakiyar qwayoyin idanuwanta, lokacin da take jin wasu tashin hankula na barazanar fasa mata qirji, wato wannan dan anacin komai ma sai yayi masa tawaye?

Kai tsaye gida ya je ya kulle kansa ya dinga bawa kwanyarsa wuta yana lissafin daga inda wannan qaddarar zata taso, in abu mai kama da hankali ne yakamata a zaci ko Binta ta sha giya bai kamata ta laqabawa kanta qaryar cutar Sida ba, sannan ya dami kansa da neman sanin wacce riba zata ci a abinda ta yi in qaryar ne?

Har dare bai sami wata mafita ba ban da qarin cushewar hanyoyin nazari, wuni daya kacal shi ma ya fada tamkar dai daga musun da suka yi shi ma ta lasa masa cutar.

Bai koma asibiti ba, bai kuma yi waya ba, don haka bai san cewa an sallami Binta har an tafi da ita gida ba, saboda sun yi ta kiran wayarsa bai daga ba.

Da dare sai ga Nabila ta kira shi cikin tarin damuwa, da alama kuka take ma.

Yayi shiru yana sauraronta, don bai san da irin nata bacin ran da zata zo da shi ba, ya sallama tun ma kafin ya ji, don yana ganin yakamata kawai ya zama wani kamfanin Inshoran bacin rai tunda ya riga ya aure shi.

“Yaya Mujahid me ya sami Anti Binta?”

Ya cije lebe, yanzu ne kuma ya yarda makirci aka kintsa masa, cikin alamar boye damuwa ya ce mata,

“Yaks din da ya zo sanar da ke bai qarasa miki labarin ba ne?”

A gigice ta ce,

‘Wallahi ni ba na gane hirarsa, Yaya Mujahid na tsane shi ne, komai zai fito daga gare shi sai in ji sam ban yarda da shi ba.”

Mujahid ya shaqi numfashi da qyar,

“To ai kuwa gara ki yarda da shi, da gaske ne sakamakon takarda ya nuna Binta na da cutar qanjamau…”

Nabila ta qara fashewa da kuka,

“Wallahi qaharu ne Yaya Mujahid, sam ban yarda ba, don Allah ka sake bincike, kar ka hukunta Anti Binta akan haka.”

Mujahid yayi murmushin qarfin hali, yana jin muhimmancin Nabila cikin ransa, ita ce kawai take fahimtar abubuwansa yadda yakamata, ita ce kawai take dacewa da komai da ya dangance shi, yayi fatan dama sonta aka jarrabe shi da shi ba na Binta ba,Ya san da sai ya shiga sahun farko na wadanda suka dace da iyali nagari.

Ya jiyo Nabila ta saki wani salati, daga can kuma sai ya ji rashin hayyacinta ya qaru lokacin da yake jiyo ta cikin alamun son shidewa tana ambaton

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”

Sai kuma ya ji kukanta tare da sakin wayar, lokaci daya kuma ta tsinke.

Kansa ya tulle tare da rashin shakkun lallai ba a kan labarin Binta na da Sida ta shiga wannan tashin hankalin ba, nan da nan sai ya ji wani tsoro da rashin nutsuwa ya shige shi, da sauri ya tashi zaune ya hau shirin fita.

Yana zama a motarsa da ya duba agogo sai ya tarar qarfe daya na dare, kai tsaye ya figi motar sai asibitin da su Nabila ke kwance.

Nan ya tarar da baqin labari, cewa Allah yayi wa Inna rasuwa. Tunda ya girma ba zai iya tuna lokacin da wata mutuwa ta bashi kuka ba, amma wannan in akwai mai son kukan alakoro ma  kamar in ya roqa a wajensa zai samu.

Shi ne me rarrashin Nabila don ba wanda ya kula da damuwar da take ciki, mahaifinta yana ta tasa uwar da ya rasa, matarsa kuwa ta kanta take, don haka shi ne a wajen don Nabila, amma ba don ya rarrashe ta ba sai don ya taya ta damuwa ko ya qara mata, tunda sa ta a gaba yayi tana kuka shi ma yana yi.

A daren aka gama komai suka dauko gawa zuwa gida, qarfe hudu Mujahid ya nemi gidansa, Allah ya sani sai lokacin ma ya tuna cewa matarsa Binta na asibiti, matar da take zage qarfi ta nuna masa qiyayya, take kuma zage qarfi ta nuna lallai sai ta raba musu rayuwar da Allah ya hada musu tare. Ita ce ya fara shafe lissafinta a muhimmiyar zuciyarsa da take ganin bai kamata ya damu da damuwar kowa ba in dai ita tana cikin damuwa, bai fasa sonta ba, amma bai san dalilin da ya sanya shi mantawa da ita tsawon ranar jiya da tsawon daren yau ba, alhalin ba shi da tabbacin halin da take ciki.

****

Duk da wannan ne tarkon Binta wato Mujahid ya nisance ta, ga mamakinta sai ta ji wani azababben maqaqi ya zagaye rayuwarta, tunda Mujahid ya bace a asibiti yana yi mata gadarar ta dawo su je gida su cigaba da rayuwa tare, sai gashi tun ba a je ko ina ba ya gaza cika gadarar tasa.

Wannan da janjanin maganar mutanen gidan wadanda ba su san haqiqanin cutarta ba bare bacewar Mujahid din, su dai an ba su gwaje-gwajen hawan jini da na zuciya, Ulcer da sauransu, ciwon Sidar Binta ya faku daga gare su, don haka suke ta faman tararradin ko lafiyar Mujahid qalau? Tsakar daren ranar Sani ya kasa daurewa sai da ya bishi gida ya tarar baya nan, don ya sha bugu, kuma da ya leqa ta wata kafa sai ya tarar ma babu motarsa. Saboda haka ya koma gida hankali a tashe, duk aka yi tsumu-tsumu ana jiran wayewar gari a shiga nemansa.

Da duku-duku kuma sai gashi a gidan, lafiya lumi sai idanuwansa da suka nuna lallai fa yana cikin damuwa.

“Da rana zazzabi ne ya kwantar da ni a gida na kashe waya, da dare kuma na taho zan koma asibiti na sami saqon rasuwar Innar Nabila, hankali a tashe na nufi asibitin, to ba a sallami gawar ba sai wajen qarfe uku na dare, ban koma hayyacina ba sai bayan sallar asuba”.

Bayanin da ya koro kenan, Hajiya da Alhaji da Sani na tsaye cirko-cirko a falo, yayin da Binta ke kwance cikin dakinta tana jiyo bayanin nasa da kuma Hirjin da ya kauraye na rasuwar Innar Nabila.

Tabbas ita ma ta ji rasuwar, amma abinda ya damu ranta shi ne, wanne muhimmanci Nabila take da shi a wajen Mujahid da har ya manta da ita da yake kirarin yana qauna ya bata wuni da rana a wajen hidimarta? Wannan ma ciwo ne daga ciwukan da ta ji a zuciyarta, amma ta rasa dalilin jin sa.

Ba ta dawo hankalinta da sauraron halin da suke ciki a falo ba, sai shigowa Mujahid dakinta a nutse ta ji.

Sai da ta yi dabarar goge dukkan hawayenta da bargo sannan ta yi dabarar tashi zaune jiki a sanyaye, suka dubi juna ita da shi duba na nutsuwa, shi ba a gane abinda zuciyarsa ta boye, amma ita ana gane zuciyarta tuhumarsa take.

Ya fahimta amma ya nuna ko in kula, ya je ya sami kujeara ya zauna, a tausashe ya ce mata,

“Sannu da jiki”.

Ta motsa baki da qyar ta amsa,

“Yauwa”

Bai damu da shan qamshinta ba ya rage murya,

“Ina son sanin cewa, mutan gidan nan sun san ciwon da ke tare da ke? Na ga kamar ban ga haka a fuskokinsu ba, babu wanda ya tare ni da zancen…”

Ta tare shi a qufule,

“In ka na da muradi yanzu ai sai ka sanar da su.”

Da sauri ya ce,

“Yauwa dama ba na so su sani, wannan matsalar mu kadai ta shafa, bai kamata mu fitar da sirrinmu waje ba, duk da cewa ban san hikimar da kuka tanada ke da Yaks da har kuka zabi sanar da Nabila ba…”

Binta ta ji wani tashin hankali ya fado mata qirji, ashe sai da Yaks ya sanar da Nabila duk da hana shin da ta yi? Kodayake ya sanar mata hujjarsa ta cewa,

“Dole na ceci ranta na fada mata mana, na san za’a iya samun ko wanne sauyi, qila ki ga ta zabe shi ta ce shi zata aura… sai ta shigo gidanku kenan ku sa mata ciwo?”

Da sauri ta binne wannan tunanin sannan ta yi wani dan nishi, maimakon amsar da zata ba wa Mujahid bisa tsokacin da yayi kan sanar da Nabila da suka yi.

Ya gaji da bin ta da kallo ya sake tankawa,

‘Yau zaki koma gida, na sanar da Hajiya, don me za’a wani kawo ki nan…”.

A qufule ta sake tare shi,

“Don bai kamata na koma gidanka na cutar da kai ba, an taba zaman aure tsakanin mai irin cutata da wanda ba shi da ita…”

Cikin halin ko in kula ya amsa mata,

“Sai a fara yanzu”

Zata yi magana ya tare ta,

“Don Allah kar ki cigaba da daga mana hankula, dama muna cikin wani tashin hankalin, kin ji Innar Nabila ta rasu ko?”

Ta matso hawayen tausayin Nabila da sabo da Inna da kuma na jin haushinsa,

“A ina zan ji? Na dai jiyo dazu a bakinka, ai kai ne jelar Nabila, babu daga wanda yakamata a ji mutuwar sai kai.”

Mujahid ya ji wani dum! Farin ciki da murna na cika shi, yanzu yake son ya fahimci Binta, wato akwai kishi ma a matsalolinta, sai yayi murmushi ya ce mata,

“Kar ki damu, in ma akwai qudurin son Nabila a raina yanzu ai dole na janye, tunda kin qala wa kanki ciwo kuma takanas kika tura aka sanar wa budurwar tawa ai kin gama hana ni aure, na san kin sawa kanki ciwo ne don tsananin son da kike min, ba kya son in yi miki kishiya ko? To sha kuruminki ke kadai ce…”

Bakinta na rawa ta ce,

“Wai me yasa kake zargin qarya ake maka ne, kuma ni me zan so a kai? Wallahi ba na sonka, kuma zan yi komai don na rabu da kai”

Ya miqe yana dariya,

“Ba zargi ba ne gaske ne, saboda haka ki kwana da sanin yau muna komawa gida zaki ba ni nawa rabo, qi kuma ki yi ta qina har a tashi duniya”

Bai saurari hanzarinta ba ya fice daga dakin ya bar ta a razane.

Awa daya Binta ta yi a gidan rasuwar ta dawo gida, don ba zata iya ganin Nabila a halin da take ciki ba, sannan ba zata iya jure kallo da zunden mutane ba, bisa yadda duk bayan wasu ‘yan mintuna Mujahid yake shigowa cikin gida ya kira Nabila yayi ta cika ta da rarrashi ko ya taya ta kuka, har an fara gane cewa lallai duk wani da zai bi bayan taya Nabila damuwa to bayan Mujahid zai bi.

<< Rigar Siliki 35Rigar Siliki 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×